Showing 54001 words to 57000 words out of 134888 words

Chapter 19 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

921

ba muje Oasis,yaje ya biya kudi suka kwashi kayan suka zuba a mota sannan suka wuce Oasis nan ma ta dauki bread manya biyu ta dauki wasu snacks din,ta dakko yogurt da lemuka da ruwan roba ta dakko Ice cream ya biya suka fito,tana shiga mota ta bude wani cake tana Sha da lemo ko kula Rafeeq bata yi ta cikinta take yi,kamar wani zai kwace haka take ci.

Joint na siyar da kaji gasassu ya tambaya ta nuna Masa Yahuza suya Suka je ya siyo musu har Leda uku,fura ya siyo suka wuce gida suka koma gida Inda yace driver ya jira shi, a Nan ya bashi motar yace ya tafi da ita gobe zai kira shi,Ledojin suka shigar ciki duk iya Wanda Ikhram tasan zata yi amfani da su a dakin Stella ta bar kayan sauran ta kaiwa su Asabe har da kajinsu na Yahuza suya,Uncle sai washe baki yake yace ko ke fa,ai Kinga yanda ake harka,da kin zauna shirme,ai haka nake kashewa mata kudi gashi ko yanzu kin rama min,ba karamin cin kudina Yan mata suke ba, Alhmdllh kina ta rama min Ikhram nima kina ciyo na wasu,Asabe ta kalle shi tace kayi asara kar dai ka kwaso mana kanjamau, Ikhram ficewa tayi ta koma wajen Rafeeq dinta.

Rafeeq ya zaro 2k ya Bata yace je ki siyo min doyar nan taku naci naji irinta,ai ta 2k tayi yawa yace kije dai ki siyo wacce ta dace ki rike canjin,Ikhram tace taso muje tare mana ai kaga gari,yace jeki dai ki dawo fitowa tayi itama ta aiki yaro ta dawo wajensa,tace me zan fada maka? yace karki damu a siyo doya da kwai,ga nama ga yogurt,lemo,snacks Ina zamu Kai abinci,tace to shike nan,yaron bai dade ba ya kawo doya da zafinta suka zauna tare da baje komai suna ci.

Rafeeq satar kallon Ikhram yayi tana ta cin abinta ba wasa ko kulashi bata yi" Sam bata magana,da alama a yunwace take,cikinta Yana fara cika tace Kai kazar ma wata dusa dusa ko? bayan duk ta cinye ta,Rafeeq yace lallai kin koshi da yawa,sai da kika cinye zaki ce kazar Dusa, yogurt ta bude tana korawa tace Kaza bata dame ni ba,nafi son tsire,dariya Rafeeq yayi yace a hakan? duk kin cinye ni ban ci ba,Ikhram ba kunya tace ka bari idan Allah yasa na aureka ka Sha a nono,Rafeeq zama ya gyara Jin anyi zancen da yafi so,yace Allah? tace da gaske tace ka bari ayi aure ka gani in saka a lungu,dariya ce ta kama shi wai shi bai ce zai sata a lungu ba sai ita.

Ta kora lemo ta sha ruwa sannan tace Alhmdllh Kai yunwa bala'i ce, yanzu sai ayi wacce duk za ayi,cinyar Rafeeq ta buga kadan tace to ya Abuja dan duniya? Rafeeq shuru yayi Yana kallonta tace mene ne tana dariya cike da nishadi,yace dazu naga ko magana bakya yi na zaci ma ko baki ji dadin zuwan nawa ba,Ikhram tace wlh babu Wanda naji dadin zuwansa irinka,kayi kyau sosai Friend,hannu ya mika mata itama ta mika Masa nata suka tafa,yace yau wai ya banji kalkala bane ba wa'azi bane? Ikhram tace wanne wa'azi hmm dama neman kudi ne kawai ni ba Malama bace, yace inane dakinki a gidan nan ki nuna min?

Tace ya kamata dai na baka tarihina,yace Ina jinki"
Sunana Ikhram Tahir, asalin Babana Yan Gombe ne,Mahaifiyata ma Hauwa'u yar Gombe ce,Babana Tahir su biyu Iyayensu suka Haifa Tahir da Rumanatu,Rumanatu ita tunda tayi aure ta haifi Danta Yahuza Wanda ake kira yanzu da Yahuza Donation, bata dade ba ta rasu,shi Kuma Tahir Abbana ya dauki Yahuza ya kaishi hannun matarsa ta farko wacce ita bata taba haihuwa ba, Allah ne ya azurta Tahir ya zama hamshakin me kudi ya koma Abuja da zama,suna rayuwa,sai da aka dauki lokaci sannan ya dawo Kano Yana Business,Yana da shaguna a Kasuwar Sabon gari.
Har Yahuza ya cika 25yrs sannan Babana ya auri matarsa ta biyu Hauwa'u itama Yar uwarsa ce suna da alaka,matarsa ta farko ganin bata haihu ba gashi an Kara mata kishiya sai ta fita ta auri wani,ita Kuma Hauwa bata Dade ba ta samu ciki,Tahir Yana da cuta ba a sani watarana sai kawai ya fara ciwon ciki,Hauwa tana kitchen Bata sani ba ma ashe ya mutu a daki ba Wanda ya sani.

Sai da ta shiga daki ta iske gawar sa ta fito tana kuka ta kira mutane, Yan uwansa suna zuwa suka ce itace ta kashe shi,suka kaita Kara kotu,lokacin sun dauki azzalumin lauya haka babu binciken kirki aka yanke mata hukuncin daurin rai da rai a matsayin ta kashe mijinta ta hanyar sa Masa guba,layin masu ciki aka kaita a gidan yari dake Kano,tun Yan uwa suna zuwa wajenta har suka daina sai dai a turo mata Dan abinda ya samu.

Kasan Mamata tana da Yaya kafin ma ayi mata aure to yayarta itace aka kaita Abuja aikatau me gidan yayi mata ciki,ta dawo dangi suka ki karbarta wani bawan Allah ance wai ya dauke ta ya riketa, ta haihu a wajensa ance dai wai namiji ta Haifa sunansa Haidar,Kuma wai a hannun me kudi yake wani Dan Fulani,wlh tana kasar waje bata San na fito ba,nayi nayi Uncle ya kirata ko ya bani number dinta yace baida ita babu Wanda yake da number dinta a gombe sabo da korar ta suka yi sanda tana da ciki,da itace nasan zata rike ni,Kai Ina so ma naga dan nata cousin dina Haidar,ance yanzu ya Kai 30yrs.

To Mamata Hauwa a can ta haifi yarta Mace taci suna Ikhram, haka muka taso da ita a gidan yari ban San kowa nawa ba har na Kai Shekara Sha biyar sannan ta kamu da lalurar ciwon sugar, lokaci daya ta rasu a cikin gidan yarin,aka barni ni kadai,lokacin ma'aikata sun Sha furta za a fitar dani a kaini wajen dangi itace ta hana tun tana da rai.
Sai da na cika shekaru 17 cif sannan Yahuza Donation yazo ganina duk wannan lokacin me tsawo,bayan Babana shine ya rike shi ya girma ya mutu, Kuma duk dukiyar Mahaifina ko Daya dangi basu raba gado ba, kwandala ba a bani ba,Yahuza ne ya cinye ya dinga neman mata da iskanci iri iri a haka ya lalata dukiyar,komai ya kare karshe ya dawo gidan haya da matan da ya aura.

Ko da yazo shi yayi komai aka fitar da ni ya kaini Gombe wajen dangin Ubana, tunda naje can suka kasa rikeni suna wulakantani,komai na samu su kwace basa so naci gaba ma,wannan yasa na dawo wajen Yahuza Donation,shi Kuma bazai Kore ni ba amma akwai wulakanci shi da matansa,sisinsa baza a ci ba amma Yana son a bashi na wani.

Yahuza Dan bariki ne Manemin mata Yana caca Yana Shan giya,har asibiti yake zuwa ya Bada jininsa a eba a biya shi kudi yazo ya nemi mata,sabo da haka aka sa Masa suna Yahuza Donation yanda yake donating Blood ana biyansa"

Yana da shagon siyar da lemuka amma duk ribar a wajen bariki take karewa da caca,baya iya ciyar da iyalansa bare sauran bukatun ganin na dawo hannunsa ya daina komai,yaransa ma duk makarantar gomnati suke zuwa,kullum idan kaga anci an koshi a gidan nan to nice na samo kudi ko iyayen yaran wato matansa,amma Yahuza ko Yana watsi da kudi sai yaga dama sabo da kawai Ina gidansa a zaune.

Dariya tayi tace Subhannallah ta riko hannun Rafeeq tana kallonsa tace duk Wanda ya aure ni zai ga yar duniya,Rafeeq yatsa ya daga yace gani, dariya ta sake saki tare da bude tafin hannunsa me Laushi ta hada da nata tafin hannun ta tafa fam,dariya suka yi a tare suna kallon juna"
Dake tana zaune a kasan carpet shi Kuma Yana Saman katifa suna facing juna"
Murmushi tayi hannunsu cikin na juna tace wa'iyazubillah
Rafeeq Allah ya yafe min na tsula iskanci a gidan yari,Ina da Ilimi amma ba a komai yake min amfani ba,duk da nasan Ina kamantawa amma magana ta gaskiya bani da kunyar yin Abu ta sake sakin dariya shi Kuma ita yake kallo sai murmushi yake faman saki idonsa a kirjinta,
Tace iskancin Uncle ne ya sha kan nawa kawai watarana dannewa nake yi kar sakin layin yayi yawa,dama can ni iskanci a Jinina yake Ina so inga Ina baje haja ta wajen namiji amma Allah ya kiyaye ban taba baje hajar ba har yau.

Kasan a gidan yari Ina iya zigidir nace kowa ya Kalli Haja, Rafeeq Ido ya zaro yace kice duk an Kalli Hajar tawa? Ikhram tace yo Kuma sai dai Alla??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????h ya yafe mana,ai baza kaga baje Haja ba sai munyi aski,ranar muna Shan iska subhannallahi,duk Ina daga cikin Wanda muke saka mace ko wace Dan Ubanta sai munga hajarta ko tana so ko bata so sai mun mata tsirara mun kalla,Chika da Beauty sabo da haka basa zuwa wajenmu,sabo da Chika da kake gani Yar duniya ce ta kirki.

Allah ya tsare ban fara feeling ba sosai sai da na nazo gidan Uncle idan naji ana ihun nan wayyoo,ai ranar da na dawo daga Abuja naji ihun Amaryar Uncle wash kamar nayi tsuntsu na dawo a Abuja na Maka fyade,Rafeeq ya dinga dariya tare da rike hannayenta biyu ya saka Masa cikin nata yace dama kin dawo.
Kafadarsa ta Dan buga tana turo baki tace labari fa nake baka bazan iya ba inshaallah sai nayi aure.
Rafeeq ya furta ya akayi ban sanki da wuri ba ne wai? ga kalata ban sani ba.
Dariya tayi ta sake rike hannunsa taci gaba da labarinta

Ta furta Rafeeq tace abinda yake damuna a gidan nan bai wuce matan ba, na farko kamata yayi ace tunda kowacce dakinta daya ne tal ita da yaranta Yahuza bin daki yake ai ya dace ace idan Yana dakin Asabe sai mu yaran mu koma dakin Amarya mu kwana dukkan mu,idan Yana dakin Amarya sai mu kwana a dakin Asabe.

Haka ya dace dama cewar Rafeeq,Ikhram tace to sun sa bakin kishi a ransu kowacce tare suke kwana da yaran su,shi Kuma,Uncle ya kasa cewa bai yarda ba,babu ruwansa sabo da Bariki tayi Masa yawa, wlh Rafeeq baya Jin kunyar kowa suma matan haka,wannan ai kunyata addinin musulunci ne da musulmai,talauci ai ba hauka bane, ace miji da mata suna Saman bed yara suna kasa Kuma fa ana jinsu suna sex, sometimes yara zasu iya farkawa ga yaran yanzu da wayo,kasan Allah nima da nake katuwa fa ko wacce sai tace bata yarda na kwana adakinta ba indai ba girkin ta bane,nima wai duk ranar girkin wata to fa can zan je, wacce ke da girki dakinta zanje na kwana,na fadawa Uncle gaskiya yaki karshe ma zagina yake,Ina so na rama zagin nan da kyar nake dannewa bai San halina ba,wlh ko waye zan iya zaginsa,Rafeeq yace har da ni? da wasa ta harare shi" taci gaba"

Haka na hakura na bar gidan kwanaki na koma makwafta suna taimaka min Ina Kwana a can,daga baya suka ce sai dai na biya kudi yanzu rayuwa tayi tsada kullum Naira Hamsim kudin kwana,watarana Naira biyar ma rasawa nake a haka ma Dan Ina sana'a amma a cikin mu kudin suke karewa,Ina kallon yara basu ci komai ba ai bazan hana su ba dole na bayar a ci.

Hakan yasa idan na samu kudi naje na biya kudin kwana na kwana idan bani da kudi haka nake kwana a gidan Uncle dakin wacce take da girki,wlh kusan kullum Ina jinsu suna sex,na zama budurwa bazan boye Maka ba dole naji Ina bukatar namiji,matarsa da shi suna ta ihu da Nishi,Kuma yaran watarana suna farkawa,wannan wanne irin jahilci ne,Kullum a cikin bukatar namiji nake kawai hakuri nake yi sabo da Ina da ilimin addini idan na lalata kaina yanzu nayi shirme ilimina ya tashi a banza.

Kudin da na samo a Abuja da naje wa'azi kayan abinci na siya da shi a gidan karshe,amma ya dauke su taliyar ya siyar, jarin nawa ma wlh ya karye sabo da nice karinsu na safe na rana da dare ta ya zan ajiye kudi,kayan matan ma da nake siyarwa watarana ni nake shanye abina sai a Dade ba a siya ba, a haka ma Dan Ina unguwar Yan bariki ne,wannan yasa na samu Maman Chinyere Ina tayata suya in na gama zata bani Dan kudin kashewa Dari uku dari hudu sannan zata bani doya da kosai na ci kaga ai na rage zafi,to bana samun kudin Kwanan gidan,sabo da wasu kudin kadan ne Ina zuwa gida zasu kare a cikin yaran Uncle.

Sai Abu na gaba Yahuza ya matsa min sai na dinga neman Maza wai Ina samo kudi,sabo da naki yarda babu irin zagin da baya min da wulakanci,shi yasa ya daina bada abinci ma a gidansa sai na samo na ciyar da su,in ba haka ba babu sauran mutunci,ko rance bazai iya bani sisinsa ba,komai kaga nayi da kudina nayi shi,duk ma ba wannan ba Rafeeq, ni kawai kwana daki daya dasu shi ya dameni tunda bana bacci da wuri,zan danyi chat da sauran su shi Kuma bazai fasa neman matansa ba,kullum ihu da Nishi kullum suna Sambatu wlh abin ba tsari,shi yasa da nazo gidanka naga normal yafi min safe,nafi Jin dadin zama na a gidan yari,da wannan rayuwar gwara gidan yari.

Rafeeq yace tab ni ban ma taba Jin wannan rayuwar ta dabbobi ba sai yau,Ikhram tace jiya Kuma rabona da abinci tun garin kwakwi dana Sha da dare sai yanzu da kazo,yace shi yasa kika kasa magana,ba dole ba ta furta,tace dan mugunta idan bana gari kayan abinci yake siya musu har da nama amma idan na dawo gidansa sai ya janye sai dai duk abinda na samo ya kare a gidan,Rafeeq yace zai barki mu tafi Abuja sai na kaiki gidanmu wajen Mama ki zauna a can,indai zata rike ni ai yafi na dinga Jin ihu da gurnanin sex kullum,wallahi Dake a cikin mata na girma gidan yari Sam Sam Rafeeq ban San wani ya ake sex ba sai da na fito yanzu,idan nace Masa zanje tayaka kwana Abuja da gudu zai yarda tunaninsa na zama Karuwa zai samu kudi,yace da kin fada min ma tun dazu ai da tuni mun tafi kawai.

Ikhram tace wlh yunwa ce ta hanani magana, Rafeeq yace yanzu dai babu bukatar namiji ko? Ikhram dariya tayi tace Ina yi mana aure nake so wlh nayi kawai na huta,yace sabo da sex din? yace gani indai zaki aureni,Baki ta bude tace idan baka so na fa? bana sonki zanzo har Kano na batawa kaina lokaci,kin San Rafeeq kuwa to mace ma in tace tana so na na tsaneta kenan,to ai bai dace na bika ba, na zauna a nan sai ka fadawa danginka su kawo kudin aure kawai,yace Inshaallah za a kawo to tunda haka kike so,tace amma ka bani kudin kwana naje na biya na wata daya kaga shike nan sai da safe Uncle zai ganni,Rafeeq yace sai kinyi breakfast ma zaki dinga zuwa da yawo kina tafiya,gobe Inshaallah zamu je a nemi gida a kama miki daki kema kiyi zamanki,Tace a nan gidan ma akwai daki wata ta tashi shekaran jiya,yace sai na kama miki kiyi zamanki a ciki har lokacin aure,amma kiyi hakuri sai na shirya kin san dan makaranta,Ikhram tace ba damuwa ko a ya kake Bai dameni ba.

Kwanciya yayi a katifar tace good night 11pm ta wuce ta mike ta fita ya rufe kofar kamar kar ta tafi haka yaji,Spark ya kira direct,dagawa yayi yace ya jikin Mummy? Yace da sauki Dan love,dariya Rafeeq yayi yace Yaya please kudi nake so dubu dari biyu wani taimako zan Maka da shi ka samu lada
Spark yace makaryaci ance kazo a baka babban aiki ka zauna da Shawarma Joint Dan Allah ka barwa wani wajen nan ka dawo na baka Office a company na,Rafeeq yace ai jira nake na gama school ga aurena Yana tahowa,Spark yace au aure zaka yi? Yace ae tun yaushe ma nima a dinga baje min Haja,bari dai na baka bashi,ranta Maka nayi,Rafeeq yace to na gode yasan kawai Spark fada yayi,haka yake cewa idan mutum yace ya bashi kudi sai yace rance ya bayar Kuma ko ka biya bazai karba ba.

Nan take ya tura Masa kudin,Rafeeq har da kiran Naila kamar abin arziki ta daga, yace Aunty Dan Allah ki bawa Spark bado sosai yau,ya kashe wayarsa ko amsar Naila bai jira ba,dariya tayi kawai ta ajiye wayar,tace hmm Dan kawai ka zama kanina ne da kaji iskanci na fiku iskanci.

Dakin Amarya Ikhram ta nufa itace da girki, sun kulle kofa tuni bugun duniya suka ki budewa,Yahuza da masifa yace ki koma wajensa ku kwana, ai na zaci kwana zaki tayashi ke wacce irin jaka ce ne Ikhram? Kije ki sa yaro nutsuwa ya sakar miki kudi,kije ki bashi fadama ya kwaso shoki a ciki, bazan bude ba,dole Ikhram ta juya ta dawo dakin Asabe bugawar duniya taki budewa, haka ta koma dakin da Rafeeq yake tayi knocking ya bude,shiga tayi tace sun kulle kofa sunce baza su bude min ba,Rafeeq farin ciki ya kamashi yace sun kyauta min wlh kwanta ni ai gwara ma ki kwana a nan wlh yafi miki Jin ihu cikin dare.

Da kayan jikinta ta shiga toilet din Stella, ita tata toilet a cikin dakinta take, tayi fitsari ta fito da kayan jikinta ta kwanta a karshen katifar Yana gabanta tana daga bayan lungu,Juyowa yayi suna facing juna tayi sauri ta juya Masa baya,murmushi yayi bai taba ko yatsanta ba,ita kuwa Ikhram wani feeling take ji.

Chika Kaduna ta koma gidansu da kudadenta tayi bajinta a gidan,ba abinda ya farantawa Ubanta mahaifi rai sai da tace ta samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login