Showing 42001 words to 45000 words out of 134888 words

Chapter 15 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

920

biyu kema na sa miki suna Karima,Bayan ta yayeki ta samu miji naga tana sonsa matashi ne me rufin asiri da na fahimci tafi sonsa sai na aurar da ita ga matashin Abubakar,yanzu yayi kudi sosai ya zama Alhaji Abubakar amma an mata kishiya sabo da itama daga kanki bata sake haihuwa ba.

Abba yace watakil kwanta daya ne a duniya Kuma tayi kuskure taje Arne ya mata ciki,Jauro yace su a tunanin Iyayen Saratu idan ta Haihu a bawa Dennis yarsa ko dansa,Kinga mu musulmai munyi asara bamu San ko zai amfani duniya ba wannan dalilin yasa nace cikina nane Kuma na hana Saratu kisan kai tunda zubarwa zata yi.
Na rufawa Dennis asiri yaci gaba da kasuwancinsa Wanda har ma yanzu yafi karfin shagon kauye ya koma cikin birnin kano sabon gari ya bude Mall katafare,a dalilin wannan taimakon da na Masa Shekara daya data wuce yace min ya musulunta sabo da abinda nayi Masa,shi baya kyamar Dan shege sabo da su sun Saba ba ruwansu kawai sabo da mutanen gari sunce sai sun kashe shi yasa bai karbi yarsa ba.

Karima idan zaki tuna akwai wani yare babban mutum da yake yawan zuwa gidana duk state din da na koma Yana zuwa da Sha Tara ta arziki,har dinkuna Yana miki,Yana daukanki ya fita Dake kina karama ya kaiki wuraren shakatawa lokacin Christmas da Sallah idan tazo,yawanci ma ke bana siya miki Abu shine yake miki,sannan tunda ya musulunta ya auri mace Musulma Zainab kin Santa yazo da ita wajenki,sannan Kinga ya haifi yara uku yanzu kannenki ne,Karima tana hawaye tace dama Uncle da nake cewa Mahaifina nane? Jauro yace tabbas.

Tace ai ko rannan Kawu yaje gidana ya kawo min Leshi da atamfa da shadda harda kayan yarana,Jauro yace mahaifinki ne to,sannan ya siya miki gida da fili takardun suna hannuna tunda ya musulunta yaji ance baza kici gadonsa ba tunda ba a same ku ta hanyar aure ba,Jarin da kike juyawa kina siyar da magungunan mata shine ya bani kudin yace na Baki ki duba sana'ar me kyau kiyi.

Abba yace wlh na Dade Ina mamaki gaba daya Karima kalar inyamurai ce da ita har hasken fatar irin nasu kana ganinta kaga Igbo,Jauro yace wlh da tuni an markade ki a Injin nasara nace a bani Ina so,Karima tace na gode Kawu,Abba yace sai wa Kuma?Jauro yace sai Haidar,Abba yace Dan ubanka marar ji bude kunnenka shike nan yaro sai dai a samo Maka mace a dangi,Jauro yace ai ni da nake so ka bashi Hidayan ka,Abba yayi dariyar yake ya share zancen yace ci gaba kaga.

Haidar watarana da dare na dawo daga Adamawa na biyo ta garin Gombe Jikin wata bishiya a bayan gari,lokacin duniya na kwance naga wata me tsohon ciki tana murkususun Nakuda tana kuka da alamar haihuwa zata yi,na tsaya na taimaka mata na kaita asibiti bamu Dade da zuwa ba ta haifo Danta namiji santalele,Ina waje Likita ta fito ta kirani tace wacce ta haihu tana son Ganinka,Na shiga tana kwance taji jiki gaskiya sosai,Jaririn ta Mika min na karba tace sunansa Aliyu Haidar, na baka shi ka rike shi da Amana,a Nan ta bani tarihinta tace ita marainiya ce,aka kaita aikatau gidan masu kudi a garin Abuja,me gidan da take aiki a gidansa matashi ne sabon aure ne shima,matarsa zasu yi shekaru daya da ita,shine watarana matar tasa tayi tafiya ya mata fyade ta samu ciki,da suka San tayi ciki suka mata duka suka korota,gata marainiya bata da wajen zuwa Yan uwa sun takura mata,haka ta dinga yawon aiki gidajen masu kudi kowa ya ganta da ciki baza ta Dade ba zasu Kore ta har cikinta ya tsufa haka take yawo gari gari tana Fadi tashi,Haidar yace Allah sarki Umma ta,Babana ka cuceni bazan yafe ba tunda ka wahalar da uwata, Jauro yaci gaba yace karshe da cikin ya isa haihuwa sai ta dawo gida tana zuwa Yan uwa suka koreta shine ta fito daga lokacin ta fara nakuda na dauketa na taimaka mata.

Naso na aureta Haidar amma Allah bai sa min sonta da aure ba,Kuma kyakyawa ce sosai wlh kamar Yar India,gaka Nan kamarta ka dakko sak Amma tace hancin ubanka kayi ita bata da hancinka,na dauketa ta zauna da mu ta yayeka,itama ta samu mijinta ana kiransa da Alhaji Tijjani Salo,me kudi ne a kasar waje suke rayuwa sai dai tazo da yawo Allah ya azurtata yanzu in ka ganta tab,amma itace da kanta tace baza ta dawo ta ganka ba idan ka girma sabo da ka karka kalleta a Yar iska ko wacce ta cuceka,Haidar yace wayyo ta fita sol ko ba soso a hadani da ita Dan Allah a fada mata Dan dakan kukan ta ya girma gani ma ni Ina Jin dadina,Kawu Ina da Kai wa zan zauna Ina damuwa da shi,Ni wlh har abada ma bana son ganin Ubana,Jauro yace yo me za ayi da shi tambadadde,amma dai Yana nan a Abuja lokacin mun kaika can ya mana korar kare yace sharri aka Masa matarsa ta Goya Masa baya Yana Nan ko sunansa Alhaji Kabeer ko wa na manta da matarsa da yaransa amma naji kamar ance matar ma basa tare ko an kamata oho dai nasan gidansa, Haidar yace kyale shi zan tayar da kura in na samu time inje dole ya bani kasona na kudinsa kafin ya mutu,Abba dolo yace a'a mahaifi ne kaji ,Abi a sannu,Haidar yace ni babata a sannu ya bita ya mata fyade gashi nan ya jawo min na fara tambadewa nima amma daga yau na tuba wlh na daina ko Dan Na farantawa Kawu rai,Kawu yace kowa ya tuba Dan wuya ba Lada da ai Ina fada muku gaskiya bakwa ji,dariya Haidar yayi Dan shi yafi kowa fara'a a gidan Jauro.

Abba ne yace Rahma,Jauro Yace Nabeela dai,Annoor yace na girmi fa su Rahma amma ake tsallake ni,Hashimu Dolo kawai ya karbe zancen yace naka labarin yayi Muni da yawa sai a karshe,gaban Annoor ya yanke ya Fadi,Iman tace nifa? Yace kece Auta fa 'Yar jakar Uba sarkin so??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n namiji Jauro ya furta.
Nabeela ta zuba tagumi Jauro yace Nabeela Babarki ai kin Santa sunanta Halima Yar Bauchi ce soyayya ce ta rufe mata Ido wani saurayinta Umar Kwalta ya dinga yaudararta ita Kuma tana sonsa sosai duk abinda yace sai tayi,shi Kuma baya sonta tsakani da Allah lokacin muna Niger Minna,na Sanshi ya sanni abokinane a garin,baya son Halima da aure da iskanci ya sota ya lallaba ya mata ciki a dakinsa,mata masu biyewa soyayya Dan mace na son namiji duk abinda yace tayi sai ta aikata sabo da kar ransa ya baci ko kar ya fasa aurenta,basu San sakin jikinki ga da namiji Yana rage soyayya ba ko da Yana sonki,har dama dama ma Dan romance akan ace kin bashi kanki daga lokacin ya gama sonki,Halima bata gane ba sai da ya mata ciki,Allah sarki Halima sabo da wannan bakin cikin Mahaifan Halima suka mutu,babanta ya fara mutuwa sai uwar sabo da Hawan jini ne ajalina uban Halima,ita Kuma Babar Halima ciwon zuciya.

Halima ta rasa gata gashi ciki Ya girma ta bani tausayi ita kadai a gidansu kamar mayya,dama basu da wani gata tausayi ta bani yasa naje na dawo da ita gidana itama ta haihu,ta tuba ga Allah sai kuka ko yaushe,Shima Umar Kwalta yayi nadama na hada su aure,bayan sunyi aure da Shekara daya ta samu ciki da cikin a jikinta Allah ya mata rasuwa,shima Umar shekarunki biyar a duniya Bai Kara auren wata ba mota ta Kade shi ya mutu,Nabeela lokacin kina wajena Shar da ke abinki.

Nabeela tace yanzu dai kenan iyayena sun mutu? Jauro yace ae sai yan uwanki na wajen Uba Dana uwa suna Nan sanda kina yarinya na Sha kaiki fa sabo da irin wannan ranar yasa na dinga wahala sai da na San asalinku da dangin ku ,suma suna zuwa ganinki kina karama sabo da Dan uwansu ya mutu kakarki ma ta wajen Uba tana yawan bugo waya taji kina lafiya.
Nabeela tace Allah yasa mu dace suka ce Ameen.

Rahma kuwa ke ki saurara kiji labarinki, Mamanki,Bushra wato a Yobe state take, kafin tayi aure tana da tarin samari Allah ya bata farin jini,ta yi yayin tara samari,taci kudin wannan ta yaudari wannan,taci kudin waccen,bata iskanci amma tana bari samari suna latseta kamar yanda kike yi yanzu Rahma,ni nasan gado kika yi,sai da ta gama yaudarar samarinta ko wanne tayi Masa alkawarin aure amma katsam sai akaji ta auri wani Attajiri Alhaji Yusuf, a cikin Samarinta akwai wani Aminu,talaka ne sosai ya sota tsakani da Allah,Yana make make da buga buga ya samo kudi duk ita yake bautawa da iyayenta,tun tana karama yake sonta,shine kudin makarantarta cinta da Shanta komai Aminu Yan gidansu,sun Maida shi bawa,amma bai sani ba ya tafi neman kudi Lagos,ya samo kudi yazo zaiyi gini ya aureta kawai ya samu labarin ai ranar ma za a kaita dakin miji an daura mata aure,Aminu ransa ya baci matuka ya gaza hakuri.

Ya samu Yan daba da makamai ana Kai Amarya daren farko Bushra Angonta ya shugo suna hirar soyayya kafin a fara sunna,Aminu da abokansa suka Fado dakin da makamai,suka yiwa mijin duka suka daure shi itama Kuma a wajen Aminu yayi mata fyade ya sadu da ita a gaban mijin suka gama suka fice abinsu,Rahma tace Aminu yayi daidai,ni kuwa banga laifinsa ba an cuce shi,Abba yace yi shuru Muji,Jauro yaci gaba,tunda Aminu suka tafi sai mijin Bushra ya tsaneta kamar ma da saninta aka mata haka,ya dinga gallaza mata Yana gana mata azaba,tayi kuka ta gode Allah tayi nadama,tasan ita ta jawa kanta,tunda ya aureta bai taba saduwa da ita ba,aure ma ya Kara ya rabu da ita ta zama Yar aikin gidansa,ciki Yana fitowa ya tabbatar cikin Aminu ne, bai sake ta ba yaci gaba da gallaza mata.

Ni business ne ya hadani da Mijinta har muka Saba yake bani labarin komai,nayi nayi ya hakura ba laifinta bane yace Sam shikam ya sake ta ma,ni kuwa Yana sakinta na dawo da ita gidana da sanin iyayenta,a garin da nake Kuma nace ai aurenta nayi alhalin ba aurenta nayi ba,har Allah ya sauketa lafiya ta haife ki na saka miki Rahma,lokacin haihuwarki Allah ya azurtani har sa na yanka,Ina fada miki a karshe dai Aminu da kansa hakki ya bisa ya dinga nemanta ruwa a jallo.

Ni na sasantasu da danginsa da na Bushra ya aureta suna zamansu yanzu yaransu Shida,sannan mijin Bushra da ya gallaza mata sai bayan tayi aure ya dawo nemanta lokaci ya kure Masa Kuma.
Rahma tace Kawu ai Nima watarana kace na rakaka unguwar ka kaini wani gida sau Daya yace sune iyayen naki,Rahma tace wlh muna kama da Bushra din Kuma haka kawai naji Ina ta kaunar Bushra,Abba Dolo yace uwaki Umma zaki ce,Rahma tace amma ba ace itace uwata ba sai aka ce ta mutu,Jauro yace ita tace kunyarki take kar a fada muku.

Bari muzo kan Iman,Iman Mahaifiyarki ke Mahaukaciya ce,sanda muna zaune a Jigawa,a titi take tsince tsince a bola,mahaukaciya ce ta gaske,duk mutane da dama sun Santa kyakyawar mace ce fara amma ciwon hauka yasa ta koma baka amma da yanayin gashinta ya nuna Buzuwa ce domin da buzaye tayi kama yanda kike me gashin Larabawa haka take,fara ce itama duk da ciwon haukar bai Hana a gane b,to a kwana a tashi ta koma wani kango da kwana,akwai wani Hamshakin Attajiri da yake zuwa daga Sudan,ance gidan da yake ginawa ma a lokacin kangon nasa ne,Yana zuwa ganin aikin ginin,daga baya sai aka ga yana daukan mahaukaciyar a mota,za a ga ya fito da ita a sume alamun ko wani magani yake shaka mata sai ya dakkota ya dinga fadawa mutane da larabci bata da lafiya asibiti zai kaita sai ya fita da ita,ana haka haka katsam sai ga mahaukaciya ta fara laulayi,ciki ya fito ya girma ana ta Jin tausayinta,sai da mutane suka fara zargin Dan Sudan din sai kawai aka ga ya siyar da gidan da yake ginawa ba a sake Jin labarinsa ba har gaba da yau Iman ban San waye ubanki ba,Mahaifiyarki Kuma haka cikinta ya tsufa ta haihu a Jikin gidana,muka fito da Habiba Jin hayaniya ana cewa mahaukaciya ta haihu,Habiba ta gyara mahaukaciyar tsaf tare da taimakon wasu mata Yan unguwar, ana tunanin ya za ayi da yaro Habiba tace tana so nace mu dauka muka dauki yaro sannan ita Kuma Mahaifiyarki na dauketa na kaita gidan mahaukata sabo da gudun kar a saceta ko a Kuma yi mata wani cikin yanzu mutane basu da Imani.
Kinji Iman yanda kika fito Mahaifiyarki tana Nan tana ciwon hauka,amma tabbas waccen Dan Sudan ana da tabbacin shi yayi mata ciki,Abba Dolo yace Allah ya bayyana gaskiya.

Annoor Kai Kuma kasan Mamanka ai kana yawan zuwa wajenta a Nan Kano,to bari kaji Kai Allah ya tsallakar dakai Kai Dan sunna ne Kai kadai ne,Mahaifiyarka Almajira ce da, sadaka yalla ce take bara, tace itama tashi tayi da iyayenta ta ganta a Nigeria amma ba Yan kasa bane suna da asali,talauci yasa take bara suna cin abinci da iyayenta har iyayenta suka rasu,a yawon bara ta samu wani Usman ana ce Masa Shegu,asalin Dan sokoto ne,Yana dan kasa yalo a titi,Abba yace ya Sunanta? Jauro yace Jumana,Jimina? Abba ya sake tambaya, Jumana nace cewar Jauro,Jumana ta aure shi bayan ta aure shi da Shekara ta samu ciki Ashe baya son haihuwa,sai daga baya taji labari Ashe auri saki yake duk Wacce ta samu ciki tana haihuwa zai karbe dansa ya saketa ya barwa uwar gidansa Dan,Jumana kuwa bai saketa da wuri ba amma ya gallaza mata,ita take ciyar da kanta da komai,da ta haifeka yace ba dansa bane,juyin duniya yace ba Dansa bane baya so,Mutane suka buga aka buga da danginsa da kowa yace Sam shi ba dansa bane.

Aka kaishi Kara kotu a kotu ya amsa dansa ne amma ana fitowa yace wlh ba dansa bane, ba ya so bazai karba ba sabo da ya ga Jumana bata da gata bata da kowa,sutura sai wani me sai da gwanjo ne ya bata sadaka ta saka maka,da kanta ta rada Maka suna Annoor ba hakika ba komai,a haka take goyaka Annoor ta tafi bara ko sati bakayi da haihuwa ba take bara da Kai a titi,aikin gidaje ma ta rasa sabo da kyawunta babu matar da take daukanta aiki kar ta aure mata miji,wani ne ma a haka ya bata gidansa da bai karasa ginawa ba iya rufawa kawai aka yi a ciki take kwana tare da kai.

Mace ce me hakuri da addini,ta tsare mutuncinta Maza suna yawan zuwa zasu lalata ta su bata kudi taki yarda,akwai masu kudin ma da suka ce zasu Gina mata gida ta amince da su amma taki yarda,tana Tara kudin barar ta sai ta koma saro masara danya tana gasawa a gefen titi a haka take ci take Sha,sabo da kyawunta ita duk Yan banza ke zuwa nemanta,da masu sonta don sha'awa,lokacin da me gidan yazo ci gaba da gininsa yace tayi hakuri ta bar Masa gidansa,ga lokacin da damuna ana ruwa da dare haka ya korota,ta goyaka ta lulluba Maka tabarma tana tafiya ruwa na dukanta tana rusa kuka,ta samu Jikin bishiya ta fake,ni Kuma na zo Kano wani Business nayi dare Ina sauri zan tafi Jigawa, ga lokacin Habiba ta Murda kambunta tana masifa na Dade ban dawo ba nayi sati biyu a Kano ta gaji da kewa ta ko ba haka aka yi ba?

Abba yace haka aka yi ci gaba muna ji,Jauro yace da Kai nake? ko kasan lokacin ne Kai,ni wallahi ka dameni wannan wacce irin hayyata ce,Habiba taji kunya tace lokacin ai da kuruciya,Jauro yace sarkin tsufa ke dai kawai kin girma kullum kin girma haba,Abba yace ke haka ake yi ai sai kice yanzu ma wlh in ta kama Murda kambun zanyi,amma sai ki wani ce ke kin girma shi yasa nake Sarawa Kubra,Yar Inna duniya Labari.
Jauro ci gaba yayi yace daga nan na hango mace ita daya kwal a gefen titi a Jikin bishiya,na zaci gamo nayi sabo da kyawunta ya tsoratani,Annoor kayi hakuri naso nayi wuff da Tsohuwar ka na Dade Ina sonta sorry Habiba ranar wanka ba a boyon cibi,itace tace baza ta iya kishi da Habiba ba tayi mata halacci baza ta auri mijinta ba,na buga na buga taki yarda,ai Habiba boye miki nayi amma sai da na dinga zuwa zance,Baki gani ba Ina yawan siyo mata ice cream,Habiba tace ai nasan kana sonta Malam tun yaushe ta fada min a boye tace kar na fada,Abba yace kinyi gulma Habiba kunyi munafunci ai sai ki fada Masa mijinki ne fa,wato ta zama kawa mace tafi miji ko? Habiba tace ni nace kar ya aureta? ni bazan ce ayi min kishiya ba amma in ya auro maraba bana ja da ikon Allah.

Hashimu yace karya kike Habiba da wata a kasa,Jauro ka kiyayi Habiba irin kishin karkashin kasa suke yi irinsu,Jauro yace duk ita ta korar min mata,Habiba tace ni a wa tab ka auri dubu ma wlh,Allah sarki Jauro ba a sonka ba a kishinka da ace Yar Inna ce ai yanzu ta fashe min da kuka daga nan Kuma fita ma baza a barni ba kullum sai lallashi,in mata danwake,in mata kunu,in soya mata kwai,Jauro yace kayi asara Hashimu,Habiba baza ta barni na shiga kitchen bama sabo da kauna,Abba yace baka San soyayya ba an barka a Tsohuwar kwalta kana garari,Yaran Jauro sai dariya suke babu shiri.

Jauro labari yaci gaba yace Dana kawota gidana,na yanka katon raguna biyu na hakika dama ta sa Sunan Danta,Jumana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login