Showing 39001 words to 42000 words out of 134888 words

Chapter 14 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

916

nake so yafi kowa haduwa,Idan ya Kalli mutum sai naga wani tauraro a idonsa,rannan da yayi dariya Allah sai da nayi hawayen farin ciki sabo da kyau,nidai na rantse da Allah idan ban same hi ba zan fada kwalabati tunda gidan Nan babu rijiya.




Kadan zan Baku tunda sharhi kadan ne suka yi jiya.

In Baku Sharhi na daina yi da yawa wlh.



AsmaBaffa
[1/15, 11:13 PM] +234 806 252 6950: A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

31-35

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


Page naki ne
Maryam T Baliya




Baseeru suna haka da Mero sai ga Spark yazo gidan a galleliyar motocinsa biyu tsala tsala bakake,yau harda escorts dinsa,motar aka bude masa ya fito sanye cikin kana nan kaya Yan ubansu kana gani kasan ba karya ne,zagawa yayi da kansa ya budewa Naila mota ta fito cikin Egyptian gown white me adon Maroon,ta Sha kyau matuka sai kamshi suke yi,hannunta daya ya rike dayan hannunsa Kuma rike da robar ruwan,suna tafiya a nutse,Naila tace sai na ganni na dawo Yar gajera a kan ka,yace ba dole ba Maza wasa ne,murmushi tayi,tace zan sha ruwan,Spark ya bude robar ya bata a baki ta Sha shima ya Sha suka yi gaba,Mero waya take amma tunda ta hango su ta kasa magana sai da Baseeru ya gaji ya kashe wayarsa.

Mero ta zubawa Spark Ido kamar mayya suka zo suka wuce Mero,har sun wuce Spark yace wait ya dawo baya Inda Mero take, yace ke cire min abinda kika gani a jikina,kina ta kallo na,Naila ta karaso wajen tace mene ne? Yace yarinya sai kallo na take kamar taga namiji da nono a kirjinsa,Naila tace Mero ki kiyayi halaliyata, Mero bani da mutunci in na tashi yanka Miki rashin mutunci baza ki gane garinku ba wlh,Mero kawai kallon Spark take ta saki baki da hanci ta sa yatsa a baki tace yau naji dadi kayi min magana da kanka,dariya ta ba Spark Dan shi bai taba ganin kidahuma irin Mero ba.

Naila wani haushi ya kamata sai Spark yayi murmushi ya juya zai tafi ,Hannun Naila ya jawo let's go,Naila ta dage ta tirje tace bazan tafi ba wlh sai ta fada min dalilin kallon mijina da take yi,ta Kama Mero da kokawa,Mero tafi Naila karfi sau dari,Mero zata tika Naila da kasa,Naila ta dinga kwalawa mijinta kira,Spark....Baby...kazo Spark dariya ta kamashi a duniya ya Dade bai ga marar karfi irin Naila ba,tana cewa zan fadi Spark...Mero tace ni banyi kokawa dake ba amma ai ya halatta mutum ya kare kansa, kare kaina nake yi,Mima ce tazo gidan itama driver ya kawota.

Mero ta gani tana kokawa da Naila, Spark Yana ta dariya Dan Naila itace ta Kai kanta dariya abin ya bashi wai a haka fada suke yi,gashi wani dadi yake ji Naila na fada a kansa,ya gyara tsaiwa yace duk a kaina ni kam,Mima tana zuwa ta dakawa Mero tsawa tace Dan uwarki da matar Dan masu gida kike kokawa,Mero tace ni kare kaina nake yasin alqur'an itace ta kamani da kokawa hine ni Kuma....Mima ta zubawa Mero Mari har biyu,tace baki da hankali Yar kauyen inace ke,Spark ne yayi magana yace a'a Mima please mu muka kulata fa wlh Dan Allah ki daina itama mutum ce kamar kowa Kuma tana da yanci, bai kamata ba ai ba baiwa bace,Naila ta kumbura ta cika fam wucewa tayi zata yi kuka ta shige ciki wajen Mummy ta zauna tana kuka,Mummy da fitowarta kenan daga bedroom tace ke lafiya sakinki yayi na fara tikar rawa ko kuwa? Naila tace yana waje shi da Mero tace tana sonsa shine yaji dadi dama ashe yana sonta har dukana tayi,.

Mummy tace Kai nidai Mero ta dameni haka Misam yazo ta dinga kallonsa tana cizon yatsa yar iskar yarinya me Spark zaici da ita wannan kazama,ko girki bana sata sabo da kazantar Mero,tab lallai Mero ta girma matar Spark din zata taba,Naila tace wlh har da dukana,su Mummy haka suke matukar ka shiga cikinsu ka hada alaka dasu ko basa sonka to wani bai Isa ya takaka ba indai ba a family yake ba,son kai ne da su sosai,Ina Mero tazo ta koma kauye gidan Ubanta na koreta Cewar mummy.

Mima dake tsaye tare da danta suna hira tace mene amfanin Mero a gidan nan gata kazama ga rashin kunya,Mero tazo wajen Mummy ta zube a kasa tana kuka ayi hakuri Mummy tace wlh sai kin tafi ai ba gidan ubanki bane ko kina da gado ne,ki Kalli yarinya kalar Madara kice zaki kokawa da ita,matar dana, baki da hankali Mero,Mero a kasa ta zube tana rokon Mummy tace wlh ban karawa dama son hi nake hine nake kallonsa Yana birgeni,Mummy ta taso da ihu kan Mero Spark ya shugo yace Dan Allah ku rabu da ita sai kace yara Kuna yin wani Abu,Mero na gode da Kauna kinji amma ni ki daina Sona baza ki samu ba,babu wani aure da zanyi kinji,Mero taji dadi tace na gode wallahi, yasin Allah ya baka abinda kake nema duniya da lahira kafi kowa hankali a danginku,Mima tace harda mu kenan ya fi mu wato so kike ki fada mana bamu da hankali? Mero tace a'a amma dai...Kuma...Kuma.....ai...dai....kai yafi kowa hankali na fada da gaske,Mummy tace ni na Raine shi fa wato banda hankali? Mero tace kina da daidai naki hankalin mana amma ai ana haifar yaro yafi uwa hankali,ko ni ai nafi babata tunda tana zagin Baffan mu taci kwalarsa ni nake mata fada,Spark yace Mero na baki Arham ganin Arham ya shugo gidan da kakin sojojinsa,Arham yace ban karba ba wlh, Allah ya kiyaye ai gwara a bani Wahida duk da ta girmeni,Mima tace Allah ya Maka albarka na baka ita,gwara fa nace ba cewa nayi a bani ba,Wahida kyakyawa ce amma farin jini shi daga Allah yake bashi a kyau,ni bana sonta yace,Mima tayi shuru kawai.

Mummy tace ke Mero tashi ki bar min gidana ayi kauye,Spark yace ba Inda zata je wai Yan aiki ba mutane bane, Dan kawai tace tana so na,duk uwa tana so ace ana son danta amma ku in mutum bashi da kudi Bai Isa ya motsa ba,yanzu wlh da wata Yar gidan me kudi ce tace tana so na da yanzu kuna murna Kuna cewa na Kara aure,amma sabo da tana karkashin ku tazo daga kauye,aiki fa taimakon juna ne mutum ya Maka aiki ka biya shi ai an taimaki juna,Dan Allah ki kyaleta ku Kun san ba sonta nake ba bazan Kuma Kara aure ba to mene laifi Dan tace tana so na? Mero na gode kinji Allah ya baki miji na gari,karki Kuma fadawa namiji kina sonsa,ki bari Allah zai kawo wani ya soki a yanda kike har kuka sai yayi a kanki.

Mero hawaye ya zubo mata tace ni waye zai so ni bare ma yayi kuka ma a kaina,bani da ilimi,Yar kauye Kuma mu talakawa ne ai mu Kam bautar masu kudi muka zo duniya,Spark yace Baki sani ba Mero ko ki auri Wanda ya fini ma,tace to Allah yasa tunda Allah kace,ai dai kace kar na sake fadawa wani Ina sonsa ko? Spark yace ae ki dinga Jan aji kina yanga,tace to na gode,Naila hawaye take tace wlh bazan koma gidan kaba mayaudari,dama Abba yace namiji ba Dan goyo bane,Mima ta harari Naila tace ke komawa zakiyi sanda kike makale Masa duk rashin kunyar da kika mana wai ke me miji,Mummy ta tuntsire da dariya tace muyi zaman mu karki koma kinjim

Spark ya zauna a gefen Naila ta matsa nesa tana fushi,Mummy da Mima farin ciki ya ishe su, Naila da Spark yau anyi fada,rada yayi wa Naila yace jibi zan kaiki gidanku Kano ki yini,Naila tace bana so itama cikin rada ta fada Masa tana goge hawaye,tashi tayi ta shige kitchen,abinci ta Gani Mummy ta shirya Naman ne ya birgeta ta dauki daya ta fito ta manta da muguntar Mummy ta fara cin Naman tuni,Mero ta kwala ihu tayi tsalle ta fisge Naman hannun Naila ta jefar.

Tace kar kuci wallahi Mummy ta barbadawa Baseeru mijinta magani ko na mene ne oho,Spark zumbur ya mike yace wlh idan matata ta mutu sai kowa ya mutu,Naila ciki ta rike tace kwadayi na ya ja min shike nan Kuma ni a kaini asibiti wayyo Abba,Baseeru ne ya shugo ya samu abinda akeyi yace yawwa ke Mero kunna video a kwashe abinci a Kai su wajen gwaji idan ta tabbata gubar mutuwa ce to na shigar da Kara kotu.

Mero ta kunna video ta nunawa Mima,ta nunawa Spark,Mummy hankalinta ya tashi sai gumi take,ta mike da gudu zata je ta kwashe abincin ta zubar Baseeru ya tare kofar kitchen ya jawo ya kulle ya sa key ya zare key din ya jefa a aljihu,Mima ce ta sake karbar video din ta gani tace Alhmdllh ko ma mene ba a Naman ta zuba ba a cikin Fried rice ta zuba gashi,Spark ya karba ya kalla yace duk da haka ban yarda ba ya dauki Naila suka tafi asibiti,aka auna komai na Naila,yace ayi mata medical checkup,komai a duba, a garin yin medical check up Likita yace Yana son ganinsu sabo da ko wanne test asibitin sunsyi indai kace medical check up to fa ba ruwansu matukar da kudi na komai ma sai sunyi Maka.

Naila Likita suka samu a Office suka zauna gabanta na dukan tara tara ko wata masifar aka gano mata,Likita yace Spark matar nan taka a Ina ta girma ne? Spark yace a rigar Fulani,Likita yayi murmushi yace ai naji ma maganarta nayi zargin haka sannan mun mata test har na koyayen haihuwa,Spark yace na saku kuyi mata wannan,ni nace ayi mata har da shi? Likita yace Kai fa kace min duk wani text na tabbatar da lafiyar Dan Adam matarka kalau take ba wani Abu bane shawara zan baku.

Spark yace Ina jinka idan ma ta hana sex ne bazan ji ba bazan hanu ba gwara ma karka fada,Likitan yayi murmushi yace ba shi bane,yace Mrs Spark kina Shan madarar shanu sosai wacce ba a dafa ba fresh? Naila tace sosai lokacin ma Baki muke sawa a Jikin nonon saniya idan mun raka Shanu kiwo,yace to a cikin nonon saniya madarar ba kindirmo ba,akwai wani sinadari a cikin nonon saniya wanda Yake kashe kwawayen haihuwar dan Adam, Ina so in tambayeki kin taba ganin wani cikakken dan Fulani na riga ya tara yara da mugun yawa? Naila tace a'a ai sunyi yawan gaske ka gansu da biyar wlh Mafi yawa cikakken dan Fulani na riga baya haihuwa da yawa duk da ana samun masu Haifar yara da yawa amma sai an tona,Likita yace to Alhmdllh cikin nonon saniya akwai wani sinadari Wanda ke kashewa mutum kwayayen haihuwa,idan an barshi an dafa ya zama kindirmo to sinadarin Yana mutuwa ko ya ragu yanda bazai cutar da mutum ba.

Naila tace to yanzu Likita kwayayen nawa sun mutu na zama juya ko kuwa? Likita dariya yayi yace basu mutu ba amma duk kusan sun kare saura kadan,shawara zan baku a tattala kwayayen Nan indai kin samu ciki a kula da cikin sannan kar kiyi family planning Dan kwan ki basu da yawa kinyi sa'a ki haifi yara uku ko hudu,Spark yace to ni ai Alhmdllh wannan ai murna ya kamata kace zaka tayani,dama burina yara uku ko hudu,Likita yace Allah Yana da Iko akan komai zata iya ta Haifa su wuce Hakan ma, Spark yace wlh ni bazan bari matata tayi min kwanika ba planning zata yi,Likita yace kar ka bari tayi planning Yana kashe kwayayen mace,zai iya karasa mata su,Naila tace bazan yarda ba ma doctor wlh in kaga nayi planning sai dai idan na haifi hudu,Spark yace ai shike nan 'ya'ya sun fini ko?Idan ban haihu ba ai kishiya zaka min wlh bazan yarda ba babu wani soyayya da zaka rudeni da ita akan Jin dadinka,da Kaine kake so ban isa ba ai,Spark yace Likita ka hadamu fada ka kyauta ka barmu bamu San ikon Allah ba kaje Na'ura ta nuna Maka karya.

Koda suka fito Naila tace ni dai mu dage da sex ko na samu da wuri kar Kwan su karasa,Spark ya kalleta yace Wanda ya yarda da Allah ya huta da baki sani ba fa? Duk wannan abin da nake ke bai Kai ki samu ciki ba? Naila tace a kara sauri gudu sau biyar tunda sau biyu sau uku muke yi,yace to bazan yi ba,yawan sex Yana taba kwakwalwar mutum sannan Yana sawa mutum ya rasa Ido da wuri,Naila tace karfin Gani yake karawa ai Halak dinka kake kallo,dariya ta bashi shi farin ciki yake zai more yace a wata majiyar haka naji ance Ido Yana Kara karfin gani Ina kallon Badon matarka,Naila tace ae mana Kai baka yarda ba? Allah sarki ai sai yau na tabbatar a bakinki,Naila tace af a fada mana ai mu mune muka san kan tsiyar,yace naga alama yanzu muje gida direct? tace Mummy fa ai gwara mu koma Muji wanne magani aka zubawa Baseeru,Spark yace ba zai wuce na mallaka ba, ni muje gida Dan Allah ki mallakeni a Bado,Naila tace to muje Allah yasa dai a samu ciki,Spark yace ke wannan ciki ya dame ki,to ta ya bazan samu Yar Minal dita ba na dinga mata kitso da kwalliya,Spark yayi murmushi Yana driving yace Allah yasa,Naila tace Ameen ko dan Mohsin dina in dinga Masa wankan swagg,Spark yace Ashe sunan Mohsin za a fara mayarwa? tace Inshaallah indai namiji ne Rabin raina zan saka Mohsin.

Spark yace to yanzu Mohsin ya zama Rabin ranki ni Kuma a Ina nake? Naila tace Kai ai zuciyar ce gaba daya,hannunsa daya ya sa cikin na Naila tare da Maida hannun nata Saman Hallarensa,Naila ta Harare shi tana murmushi tace so kake muyi hatsari ta kwace hannunta.

Abba ya baza kunne Yana Jiran Jauro yace baron mata Kai muke jira Karima yarrrrrrrrrr....ci gaba,Jauro ya bude baki ya Kalli Hashimu yace wlh sai na Sha ruwa,Abba yace Habiba hanzarta ki kawo a hado min da Jus wai Juice,Habiba ta kawo,Abba yace Jauro ka tuna yanda muke Shan ruwa a kauye mu kafa baki a Saman Moda kwat kwat kwat mun shanye Maza kayi irinsa bama son yanga tunda har ka koma ga Allah baza ka zama Dan birni ba,Jauro yace inji uban wa? to tsufa yazo Maka baka dawo birni da wuri ba kafin kayi Shekara arba'in ai ka tafi Ingila me tukane Kuma,Jauro yace na daina biye Maka Hashimu naga alama ka kama hayar gida a Zaria,sai da su Annoor suka yi dariya sabo da wai Abba ya fara zarewa shine ya kama hayar gida a Zaria,Abba yace a'a ka manta gida na siya a zaria,shi Kuma Abba yace Jauro kafin ya zama cikakken Dan birni ya mutu Yana kabari shine Ingila me tukane,Haidar yace sabo da ana binne mutum da tukunyar kasa shine wai Ingila me tukwane,Nabeel yace ku Kuna da bakin magana ma yanzu,Haidar yace kashe kanmu zamu yi tunda iyayenmu sun biyewa Dan dadi na mintuna an haifo mu ya zamu yi.

Jauro yace Karima....Abba yace ae Karima muna ji,Jauro yace Karima a wani kauye tudun wada Dake Kano state, Allah ya kaini wajen wani abokina Inda a asibitin Tudun wada yake aiki,Likitan amma yayi kaurin suna wajen zubar da cikin shege,a asibitin sa private sana'arsa kenan zubar da ciki,muna zaune muna Hira sai ga wani Arne Igbo me suna Dennis,ya kawo wata mace bahaushiya Yar Fulani me suna Saratu,ya kawo yarinya karama ce lokacin sai kayan nonuwa kamar tulu haka take randamdam randa guda,Dana kalleta sai da na sake kallonta sabo da nonuwanta sai an hada kaina dana Hashimu,suna zuwa Dennis yace shi Dan Enugu ne shago yazo ya bude a garin Tudun wada Yana siyar da kayan masarufi.

To Saratu Kuma kawarsa ce suna mutunci shagonsa a Jikin gidan su Saratu yake,Saratu in taje shagon sai Dennis ya dinga bata biscuits da alawa,idan yaga ba kowa sai ya dinga tattaba mata kirji,a hankali Saratu ta saba sai ya fara kashe mata kudi Yana siya mata har kayan Sallah,su Kuma wasu iyayen babu bincike idan suka ga namiji Yana bawa yarsu Abu basu bincika akan wanne dalili wasu ma karba suke suna Murna,Dennis ya lallaba Saratu ya dinga kulle shagon da ita a ciki idan ya faki idon mutane har ya samu ya dirka mata ciki.

Dake yare ne Yana da wayewa har kwayoyin Hana daukan ciki yake bawa Saratu tana Sha,sun dade suna tafka masha'a ba a sani ba sai da Saratu ta daina Shan magani bai sani ba tayi ciki,har ta samu mijin auren za a mata aure kawai sai ciki ya bayyana,da iyayenta suka fara dukanta sai tace Dennis ne,Mutanen kauyen suka ce sai Dennis ya bar musu gari,shine Dennis ya dauki Saratu a boye ya taho da ita wajen Likita ya biya kudi za a cire cikin ba tare da sanin kowa ba,can Kuma a gari ana ta cewa Saratu ta gudu ta bar gida.

Ina Zaune tare da Likita suka zo za a zubar da cikin nace kar a zubar ni Ina so kawai Dennis yace nawa ne,Likita ba yanda baiyi dani ba akan na fita safgar naki ji muka tafi da Dennis da Saratu gidansu nayi ruwa nayi tsaki nace nawa ne cikin ba ruwan Dennis,Iyayen Saratu sunji dadi sun ganni Musulmi suka ce da Zina da Arne ai gwara Musulmi,sannan gasu da son kudi,lokacin naso idan Saratu ta haihu na aureta kiyi hakuri Karima sabo da nonuwan Saratu naso na aureta sabo da na samu natural Pillow Allah yasa Kuma Saratu da na tafi da ita gidana bayan ta haife ki na Yanka Miki raguna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login