Showing 99001 words to 102000 words out of 134888 words

Chapter 34 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

934

Arham yace hmm ni ba macen da ta isa ta sani ko ta hanani,Rafeeq yace tab ni kuwa gani,girki Dan ubanka a jera min hadaddun flask ana ci mana,Ina sani nace na koshi,a dinga lallabani Kaci pls My Heart,ba sai naji Kuma na koma shagwababbe ba ahh sai shagwaba ana Lilita ni,Arham Yana ta dariya yace yanzu duk a 2days aka yi haka? Ana amarci da wasa ne Malam babu lokacin banza a amarci every single minute,second a ciki Jin dadi ake tunda mun gaisa tashi kafin Dan Allah,Ikhram ce ta fito dauke da abinci tace Ango na biyu....mene ne haka? Waye Ango na biyu nine na farko nine na biyu kar na sake ji Bada ni ba wasan kanin miji a gidana Ina wlh ban so,tsakani da Allah ya fada,tace to kayi hakuri bazan a sake ba,farin ciki ya kama Rafeeq yace Kai Malama ce wannan ta gasken ni gani har tsoron fushina akeyi yi.
Arham bai dade ba ya tafi gida yace gobe Kuma sai naje gidan Misam na Gani.

Washe gari Spark Kano ya wuce Gidan yari akan maganar fidda Mero,Ma'aikan ya samu har Office din Ogan suka Masa Iso,bayan ya shiga ya zauna suka gaisa Sosai,ya Masa magana akan Mero da duk abinda Mummy tayi mata,yace me sauki ne wannan amma baza mu fitar da ita ba yanzu dole sai an Kai kotu idan kotu ta saurari komai za mu shigo da ita Mummy dinka sannan a fitar da Mero,yace ni yanzu bazan iya Kai uwata Kara kotu ba gaskiya,yace ai dama ba Kai zaka yi ba,Inda Mummy ta Bada cin hanci suka kawo Mero nan su zasu dawo su tura su kotu dama abinda ya kamata sunyi kenan suka karbi kudi,sai kayi hakuri dole haka zaka jajirce amma wani taimako da zanyi ni zan kaiwa kotu case din ya koma can sai su kaiwa Mummy takadar sammaci shike nan,Spark yace na gode ya bashi kudi ya fito.

Yana fitowa ya tambayi na bangaren ziyara ya kwatanta musu Mero suka ce gaskiya su basu San wata Mero ba sai dai Khadija wacce yake tambaya,Spark bai San ta da Khadija ba yace a kira min ita na ganta ko itace,ba ranar ziyara bace amma sabo da kudi da gudu suka Nemo Khadija,tana ciki Allah sarki Mero duk tayi duhu ta lalace sabo da Bata da gata,Fitowa tayi Taga Spark Mero ta washe Dan karamin bakinta tace Ina Kwana,Kallonta Spark yayi ta bashi tausayi shi da ya San Mero Yar dumimi da ita me haske, da sakin fuska ya amsa yace ya ciki din? Mero ta fara dariya tace da dadi,yace da dadi naga kin rame,Mero tace abinda yasa tunani nake da dare ban San matsayi na ba a gidan nan ba,ba fa a yanke min hukunci ba, duk zaman da nake a banza nake yinsa,shine ya dameni,amma komai Ina ci ni,ga Ummata son kudi ya mata yawa sau Daya fa suka zo min wai kudin mota tsada Kuma fa a Kano ne Dan kawai suna kauye,Baffa na Kuma Umma ta mallake shi sai abinda taga dama tsoronta yake ji,Spark yace Allah ya kyauta,tace Ameen Ina matarka? Spark an tambayi Naila harda sosa Kai yace tana Nan lafiya,yanzu me kike bukata? Mero tace a yanke min hukunci kawai shi ya dameni,ni wahalar rayuwa bata dameni ba ko wacce iri ce na Saba da ita zan jure,yace to ki daina tunani za'a fitar Dake kwana nan Inshaallah,Mero tace a jinkirta Dan Allah ba yanzu ba,yace sabo da me uban me kike yi a ciki? Mero tace wani ne nake ganinsa a TikTok sanda Ina gida,kawai sai na ganshi a nan,dariya ta ba Spark yace idan ba shine ba fa? Mero tace shine ma,to ta ya zaki hadu da shi Yana bangaren maza ke kina bangaren mata? Mero tace tab baka san tsiyar da nake hadawa bane a gidan nan,amma bari saura kadan,Spark yace to yanzu sai yaushe zaki gama? Mero tace wata Daya,kyale Mummy Kaci gaba da ganin abarka ni na gano arzikina a nan,Spark Yana jinjina shiriritar Mero yace to kudi zan baki ko me kike so a kawo miki? Mero tace bani kudin kayi tafiyarka zan ji da kaina,Spark ya bude mata asusu a cikin ya sa mata 50k yace gashi nan ki dinga karba,idan baki fito ba sun kare zan tura wasu ga number dina na bawa ma'aikata in kina bukatar wani abu ki kira,Mero tace na gode Allah ya Kara budi,suka rabu ta koma ciki ya sallami ma'aikatan da kyautar kudi ya wuce abinsa.

Hanan gajiya tayi da zaman gidan miji take nema Ido rufe wai so take yi tayi auren kisan wuta ta fito ta koma gidan Mohsin,wani Dan babban mutum kawarta ta fada mata tace wani Dolo Dolo ne ta aure shi kawai tana tarewa sati daya ta Masa tijara dole ya saketa,aurensa uku duk baya dace fita suke yi kuma ko wacce tace tana sonsa sai ya gode miki Kuma ya aureki,in kika ce sakeni sai ya dankara miki saki yace ai itace tace na sake ta,idan kika je kika ce Hamza aureni sai yace to, Kuma wlh sai ya aure ki,Yana samun kudi Kuma a kasuwa yake shagon wani,Allah ya Masa baiwa duk abinda ya taba sai an samu kudi,Hanan tace kice Lubna wannan ai yayi wlh,tace Kuma zai Kai 40yrs Kuma gashi da tsabta da gayu ke baza kice Dolo bane,Ki samu kiyi gyaran jiki,Hanan tace ai na siyo supplements dina gasu Nan dana kiba da na haske ai fasowa zanyi gari kwana nan,yawwa idan kika yi kyau sosai dama ke ba mummuna ba har gidansu zan Kaiki,bashi da iyaye sai kakarsa kawai a gidan itama Kuma bangarenta daban,tafawa suka yi tace to sai na kiraki a waya,kina zuwa kice Hamza dama sonka nake aure ni,zai aureki.

Kakan Naila ne yazo Kano gidan yarsa Yar Inna,Abba suruki yazo sai zumudi akeyi,har kasa ya durkusa ya gaida shi,yace Affa an zo lafiya yace lafiya Alhmdllh,Abba yace lallai kamatuddini tudan haka Nima surukaina suke durkusa min su gaishe ni,sai yanzu na tabbatar da bin na gaba bin Allah da bana yi Maka waye zai min nima,Affa ya Kalli Hashimu kawai yace Hashimu ya yaran? Suna Nan lafiya kalau,ya wajen su Naila? Sumul suke dazu ma ta kirani,itama Hidaya tayi miji Inshaallah saura kwana hudu za a daura auren kaninsa zance kawai a hada a daura da Ita Hidayan daga baya sai ta tare mene amfanin jiran,Affa yace Mashaallah dama naga ta wani girma,Abba yace yaran ne ba irin na da ba,Yar Inna a gida ta fara Al'ada amma su Hidaya tuni muke ta asarar kudin auduga,Zarah ma tunda naga nono ya fito mata nace shike nan Kuma yanzu zata fara daukan Albashi duk wata sai an Bada na pad,Kaka yace Allah ya kyauta ai ni Hidaya ma na kawowa magani ta Sha Yana sawa a danyi Kumari ayi bulbul,Abba yace Yar jakar Uba ni ta gado,Affa yace a'a ba Kai bane wlh zata cika Dan Bata girma ba,to tunda kasan zata cika me yasa ka kawo magani,kaka yasan halin Hashimu sai ya bar zancen,yace Nidai kira min Hidaya.

Bayan an kira Hidaya ya bata magunguna yace gasu Nan yanda nace ki Sha haka zaki yi na Sanyi ne,Hidaya ta karba tace na gode,Abba yace a fada Mata gaskiya ke Hidaya ranar asabar zan daura miki aure Inshaallah,Hidaya tace Abba aure Kuma da wa? Abba yace da Wanda yake sonki tunda kina karbar kayansa kina cinyewa ai shike nan kina sonsa,Hidaya tace Abba Bai taba cewa fa Yana so na ba,yace to ya fada miki I love you din a gidanki,kunyi candy me zakiyi in Yana ra'ayin karatu ya saki da kansa,Hidaya ta fara kuka tace Dan wlh ba Naila bace da Naila ce baza a mata haka ba,an fi son Naila dani,ita kudin samari nawa ta ci,Abba yace kafin bikin dai ki shirya gobe ki tafi gidan Naila Dan wlh kika sake aka daura ba Inda zai barki kije kiyi kwanaki,ko sati kiyi acan idan an daura ma kina can tunda ba yanzu za a kaiki ba,ni na yaba da hankalinsa na bashi.

Kaka yace kayi daidai Hashimu bai dace a dinga barin Yan mata haka ba a gidan iyaye,Hidaya juyawa tayi wajen Umman su,Abba yace ko kin fada Mata a banza bakin mu daya,idan nayi magana da yawun Kubra nayi idan Kubra tayi magana da yawuna tayi,Kaka ya washe baki yaji ana son yarsa Kubra,Kubra yarsa tayi dace bata da wata matsala,Abba ya Kalli Kaka yace Affa yaji ana son yarsa to ai tarbiyyarka ce Kaine ka fiye yiwa Kubra tarbiyya har tayi yawa,yanzu gashi ta hana nayi aure,Affa yace Allah ya Kara bada zaman lafiya,Baki Abba ya bude yace a'a mu lafiya muke zaune,Affa yace ai ya karo nace Abba yace wannan ma ya isa ni na gode Allah in ba so kake Kuma na hadiye ta ba wanne zaman lafiya kake nema.
Kaka yace to shike nan Hashimu.

Yanzu ai sai na zauna ayi daurin auren Hidaya da ni,Abba yace ba damuwa,zan kira su Naja'e su tattaro suzo sabo da a sheda,in za a kaita Kuma Tani da Goggo sai suzo idan an tsaida rana,Kaka yace Ina tsoron auren Nan na Hidaya karfa Kato ne ya balla mata Kwankwaso,Abba yace a'a irin yaran nan sunfi manya ba abinda zai faru Dan matashi ne fa son kowa da shi,Kaka yace shike nan to.
Hidaya kuwa tana zuwa wajen Umma ta fashe da kuka tace Umma kinji Abba wai auren dole zai min mutum bai ce Yana so na ba,Kubra tace Bai ce Yana sonki ba amma yake ta zuwa kullum Kuma kike fita kina karbo abin hannunsa,kullum raba dare kike waya da shi ko baki San mun sani bane,duk iyayen da basa saka Ido akan yaransu ai sun shiga uku,muna jinki to,har tambayar Aslam kike ko yaushe zaizo,ki sa Aslam a gaba kina Masa hirar Nabeel Ina jinku fa.

Yanzu baki da aboki sai Aslam sabo da Nabeel Yana Aiko shi wajenki,shi yasa muka ce a daura kawai Kinga kin huta,Hidaya tayi mukus tana Jin kunyar kanta tace Amma Umma ai abokina nane,Aboki da namiji bada 'ya'yana ba wlh bari a daura in kinje sai kuci gaba da abotarku,ai Aboki bazai guji abokinsa ba,Hidaya tace gwara ma na tafiyata gidan Aunty Naila tunda ba a so na,Umma tace kamar wani shiri kike da Naila,kina shiga lamarinta ne? Wlh Hidaya ki canja hali hassada ba Inda zata kaiki,ki rasa wacce zaki wa hassada sai Yar uwarki,tunda kika yiwa Yar uwarki uban waye baza ki Masa ba,Hidaya tace ai na daina ni wlh na Dade bana ma Jin Haushinta kawai Nailan ce sai ta dinga nunawa ita ta girmi uban kowa tana wani iskanci,dariya Umma tayi tace Naila ce take iskanci? Bata girmeki ba?

Ai da kadan ta girmeni ni bana so a dinga rainani,Umma tace sannu sarkin girma,in kin San gidanta zaki je ki mata rashin kunya karki je,shi Mohsin ai zuwa kike ki ta yiwa matarsa Aiki,ni kwana biyu ma Banga Beauty tazo gidan Nan ba ko lafiya take oho,bari na tura Aslam da Zarah su gano min lafiyarta,Hidaya tace zance,a'a ba Inda zaki ba gobe zaki tafi Abuja din ba,dama Ku tafi tare da Zarah da Aslam gaba daya,Hidaya tace ni kar a hadani da yara,ke wai a duniya sai son girma wlh tare zaku tafi.

Washe gari Hidaya suka shirya da sassafe Mohsin ya kaisu tasha ya sasu a mota ya biya kudin motar gaba daya sannan ya basu kudin dawowa Dana kashewa,Zarah tace Yaya kaga nama a siya mana muna hanya muna cin abinmu,yaje ya siya musu a can ciki ya kawo musu da yogurt da ruwa yace karfa ku Sha ruwa a hanya da yawa ku fara Jin fitsari suka ce to,Yace ke Hidaya ki kula da su Kuna zuwa tashar ki kira Naila kafin ku karasa zata je can,tace to,mota dama ta cika wata Sharon ta tashi suka tafi.
3hrs Kafin su karasa Hidaya ta kira Naila tace sun kusa,ai kuwa Naila ta fito ta samu Spark Yana aiki a Palo da takardu tace Baby su Hidaya sun kusa karasowa,yace zuwa zasu yi baki fada min ba?Naila tace nima da safe Mohsin ya kira ya fada min ban sani ba,yara Kuma su taho a mota ai sai ki fada min a siya musu ticket,Naila tace hidimar tayi yawa shi yasa ma ban fada Maka ba,kudinki ne ko nawa? Naila tace naka ne,ya mike tsaye yace Ina za a dauke su to? ta fada Masa ya karbi number Hidaya yace a sa driver ya dakko su ko kece zaki je? tace ni zanje tana murna yace nasan dama haka zaki ce Yana murmushi,Allah ya yiki da son tuka mota,Naila tace dadi nake ji idan Ina driving in ta yanga ni ga me kudi.
Dariya yayi tace bari na zaba a ciki,sanye take cikin doguwar riga Abaya mayafin ta yafa ta fito da key din mota tace na tafi to,Spark yace a dawo lfy ta fita,har can taje ta riga su zuwa ma tana jiran su karaso.

Sai da ta kusa 1hr a mota tana jiransu sannan suka kira suka ce gasu a tashar sun fito a mota da kayansu,ta bude mota ta fito ta hango su,Zarah tace ga Auntyn ma suka taho wajenta,a mota suka saka jakankunan su sannan Hidaya ta shiga gaba Aslam da Zarah a baya,Naila Mohsin ta kira tace sun sauka gasu suna tare,yace to Alhmdllh,ta kira Umma da Abba duk ta fada musu sun sauka lfy sannan taka mota suka nufi gidanta,su Hidaya sai baza Ido ake,tace Aunty kin more,Naila tace ba yanzu zaki San na more ba sai kinje gidana,suna karasawa gidan suka dinga kallo suna yabawa,Hidaya tace kin caba gaskiya,Naila ta kalleta tace kyaji da shi Hidaya ke baza ki canja hali ba,me nayi Kuma Naila? Wlh ni ba hassada nake miki ba tsakani da Allah na yaba,na gane baida amfani abinda nake yi anyi mana wa'azi naji illar hassada ni wlh na daina Kuma inshaallah Ina neman tsari da ita ma,ki daina ganin ko Ina miki hassada ne,Naila tace Masha Allah anyi hankali.

Jakansu suka dauka suka shiga ciki Naila tace kuyi sallama fa me gidan Yana nan,Hidaya tace to ai ko baki fada ba,sallama suka yi suka shiga,Spark ya amsa da fara'a yace yara sun girma sun zo Abuja da kansu,Aslam yace ko ni sai na kawo kaina,Zara tace Kai Aunty kina Jin dadinki sai na Dade ban koma gida ba,Spark yace da Abba zai bar mana ma Kinga kin huta,tace bazai barni ba Abba Yana so na aure zai min,Dariya suka yi,Hidaya tace Ina Kwana Yaya Spark,yace Ina yini dai ko yunwa kike ji ne,dariya tayi shi bai taba ganin Hidaya tana dariya ba sai yau,sai yaga suna yanayi da Naila,Zara da Aslam Kuma sunfi kama da Naila sosai,bari muyi Sallah mudai cewar Zara,Naila tace to ku kwaso kayan naku,Hidaya tace wai mutum yazo gidanki babu taimako jakar ma baza ki daukar mana ba,Naila tace kawo na daukar miki ta dauki jakar suka haura sama dakin Naila,tace Aslam zo na nuna Maka dakinka,ta kaishi wani dakin daban Hidaya da Zarah dakinsu daban,tace to kuyi wanka kuyi sallah sai kuzo kuci abinci,suka ce to,wurin Spark ta koma.

Mika yayi yace na gaji wlh,ya jawota jikinsa yace Baby na manta ban fada miki ba naje prison wajen Mero Allah sarki ta bani tausayi,Nan take sai Naila ta bata fuska,fushi da kishi ya taso mata,ta daure tace fito da ita zaka yi?

Yace ae ya Bata labarin komai yace wlh Baki gani ba Mero da take Yar bulbul da ita da haskenta duk ta rame tayi duhu ai an dauki alhakinta,Naila tace kace dama kallon Mero kake yi shi yasa ka gane Yar bulbul ce me haske,ba so me ya kawo tausayi,Baki Spark ya bude yace nifa labari na baki ba son Mero nake yi,Dan Allah ka Adana kalamanka wato shine baza ka fada min zaka je ba sai ka tafi ban ma sani ba sabo da son Mero yana ranka,kin San fa komai akan maganar me yasa kike haka? in banje na fitar da ita ba sai yaushe,an zalunceta Kuma uwata fa za a kulle a madadinta,Naila tace a kyale Mummy din mana in yaso ka biya kudi a saki Mero na mene zaka je,farko sanda nice acan ai Rafeeq ka tura da Islam yanzu Mero ka kyasa tana birgeka shine ka tafi can kanwarka ce ko muharramarka,Spark yayi dariya yace wai ke kishi kike da Mero? Allah ya kiyaye nayi kishi kayi ta zuwa idan kullum zaka je kaje,ta mike ta shige kitchen,Spark shi dadi ma yake ji ana kishinsa ko a jikinsa wani ma nishadi yake yi,Naila ta wuce dining tana fushi,yace tace ma a gaishe ki na manta,ke ta fara tambaya,Ashe ma sunanta Khadija,Naila ranta ya Kara baci ko magana bata iya yi ba.

Su Hidaya ne suka fito sunyi wanka tare da canja kaya tace har kunyi sallar? Suka ce ae suka wuce Dining,Zarah harda radawa Naila yau zamu ci abinci a dining,Naila tayi dariya kawai,Hidaya tace an dai dage an koyi abin kirki,Naila tace ya na iya,suna cin abincin Hidaya tace tunda kika iya girki ai kowa ma ya iya, yayi dadi sosai,Naila tace ai nasan dole yayi dadi yarinya.

Spark tashi yayi yace yau ni Amarena sun zo Kuma bana yayin Naila ga Zarah itace Babyna,Zarah ta fara dariya tace mu za a siyawa abin dadi,Spark yace ashe kin gane,Hidaya tace mudai a kaimu yawo Yaya,to ai Kya bari ku huta dai zuwa kwana biyu,wayar Spark ce tayi ringing ya daga Yana bin Steps yace Papa sun bani tausayi a Kai musu shinkafa da wasu abubuwan,Papa yace karka Kai musu komai gwara su dinga zuwa gidajen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login