Showing 81001 words to 84000 words out of 134888 words

Chapter 28 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

938

take tace wannan wacce irin rayuwa ce wacce irin masifa ce wannan,Arham ya Bada amsa yace rayuwa irin ta Mummy ce,masifa Kuma ta danginku ce,yanzu wa gari ya waya,dadin abin duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka,yanzu waye a cikin wani hali? Itace,za ace Mima ta kashe mijinta ne? Za ace Arham yayi kisa ne? Yusra za ace ta gidan su Mima,ko ace Maman Spark abin kunya ya ganka Spark babarka tayi kisa.

Spark Yana hawaye yace shike nan na daina yawo a gari,Ina zan fita a dinga nuna ni uwata tayi kisa,Mummy ce ta kalle su da kyar, Spark yace Wanda kike fada Jamilu gashi a gabanki ba namiji bane mace ce itace Naila gata Nan Kuma itace matata ita nake aure,a shigar maza kika Santa shi yasa kika kasa gane ta sannan Baku dade ba daga zuwanta kika mata sharri,yanzu gata nan ko zata iya yafe miki oho,kin Sa an bata mata suna,kin Rabata da iyayenta kin kaita gidan yari taci wahala cikin kartan Maza,badan Allah ya kaini ciki ba da shike nan,Mima ce tace haba shi yasa wlh nake ta mata kallon sani,Dan Allah ki yafewa Yar uwata,Naila a ranta tace wlh bazan yafe da wuri ba sai kowa ya roke ni cikinku Allah yasa ta sheka lahira yanda zaku zo neman Alfarma wajena,baya ta juya ta koma tayi zamanta tana kuka.

Arham lallabawa yayi Naila ta tura Masa recording din Mummy duk ya turawa dangi kaf ta Whatsapp,kowa yaji sai ya zaro ido,sai kiran Mima da Spark suke a waya,Misam ya kira Mima yace Mima ashe Kuma haka wani sabon abinunyar ta danno Allah ya tsare gaba Kune da kuka gaskiya,dole kuyi kuka wlh ni dai ta taimaka min karta sheka yanzu Dan aurena ya matso kar ace an daga bikin,Rafeeq Yana gefe Yana cewa Allah ya tashe ta mu dai a samu ayi bikinmu tukun koma me za ayi sai ayi daga baya.

Sai da Mummy ta Fadi gaskiya Kuma sannan kwanaki kadan ta fara Jin sauki sosai kullum sauki samuwa yake,yanzu har abinci take ci,Spark ya daina walwala Sam yasan ko Mummy ta warke karshenta gidan yari amma indai zai dinga Ganinta da sauki,ta samu chance na nemiyar yafiyar ubangiji idan ta shiryu.
Naila kuwa bata nuna ta damu ba sai ma kwantarwa da Spark hankali da take yi.

Suna masaukinsu a kwance,tana jikinsa suna Hira kasa kasa yace Dan Allah Baby zaki iya yafe mata? Naila ta Harare shi tana dariya tace ni din banza ai ko sabo da Kai na yafe mata wlh da zuciya daya amma sabo da Kai,Ina sonka fa ta rainar min Kai na aureka kaddara ta kaini gidan yari badan haka ba baza ta iya kaini can ba,yanzu Baseeru shi dake bai da rabon wahala Kuma da tsawon ransa gashi ya Sha ras da shi,Kuma ni gashi Sila ta sa mun hadu na aure ka,badan haka ba Ina zanga me kudi irinka, ai ni Alkhairi ya zame min amma idan mun koma dole mu koma gaban hukuma a wanke ni fess sannan naje naga su Dan Indo da Goje su tabbatar,yace Inshaallah indai kin yafe ai shike nan,tace na yafe mata har abada sabo da Kai amma karka fadawa dangi har su Mima na yafe so nake suyi darasi pls,yace Inshaallah Yana murna ya rungumeta kamar zai cinyeta Yana sa mata albarka.

A hankali tace Bado Yana bukatar Hallare,Ido ya zaro yace wannan son Hallaren naki kuwa na lafiya ne? Yau how many times muka yi karfa na koma Baseeru da Mummy,Naila tace Kuma wlh ba ciki bane ko ni Ina mamaki naje a asibitin sun min test sunce ba shi bane,naso ace shine na Maka surprise,yace Allah ya baki tace Ameen inyi nakuda ta in haihu,Spark yayi dariya yace ke Nakudar ma birge ki take yi? Naila tace sosai na dinga wash...ahhh Spark....bayana...kuguna...harda yin goho a Saman bed tace sai Da ya fado aji Inya Inya,ace Namiji ta haifa ko mace,Spark ya kama dariya yace haka fa kika yi a first night sai gashi kinfi kowa raki,Naila tace banda haihuwa,Kai yaro guda wasa ne Allah ya bani mace,yace masu Albarka dai,tace ko namiji ne ma Allah ya amfana Ina laifi,Allah yasa ya gado hallarenka matarsa ta kwashi dadi,Naila harda rawa da Kai ana Jin dadi sai Shoky ahhh....Spark dai Yana ta dariya Yana latsa waya,kwanciya tayi a jikinsa tana mika,wayarsa ya ajiye yace idan na kamaki Allah sai kin gudu yau,Naila harda adungure a Saman bed ai haka nake so yeee ai ni sai yanzu na balaga ashe,da ban balaga ba,sai dariya take ba Spark da gaske kullum Naila Kara fetsarewa take a bed,wani abin da take har mamaki yake.

Nabeel ne ya tsiri zuwa gaida Abba duk bayan kwana biyu sai yaje,Abba ya gaji ganin yau ma ance yazo inji Nabeel,Abba fitowa yayi yace Kai idan kana da manufa ka fito ka fada sai kace Kaine Jauro sai sintiri kake,nema kake lallai sai kayi Aboki dani Kuma bazan zama abokinka,yau naji yaro Dan Albarka kullum sai kazo wajena na gaji,bana sonka da aboki ni karka ganni wani saurayi saurayi da shekaru na,Nabeel dariya yayi kyakyawa ne sosai,Abba yace yau dinma gaisuwar ce? Nabeel yace ae Kuma yarinya zaka turo min ta karbi sako,Abba yace ai Ina da yaro Aslam me yasa baza kace yaro ba sai kace yarinya,Nabeel yace to a turo Aslam din duk Daya ne,Abba ya shiga ya turo Aslam,Aslam Yana fitowa ya gaida Nabeel Wanda kofar motarsa a bude take ya fito da manyan Ledoji shake da kayan ciye ciye yace Auntynka zaka bawa, yace wacce a ciki? Nabeel yace Yar Kwaila dai gata nan wata kamar tana na manta sunanta,Aslam yace Zarah kenan yace ba ita ba ai na San Zarah yarinya ce sosai,yace Aunty Hidaya? yace yawwa ae ita,Aslam yace Kai kace mata Kwaila sai na fada mata,Nabeel yayi dariya a ransa yace yaro yayi gadon Ubansa,a fili yace to fada mata mana tsoronta nake yi,kace ta cinye idan ba haka ba Ina dawowa naji ance bata ci ba sai na balla ta,Aslam yace a nawa? Yaro da wayon tsiya,yace sa kudi yace dubu daya sai na Maka CID,yace yawwa yaro ya bashi 2k yace idan bata ci ba ka fada min,yace bani number waya zan saci wayar Abba na kiraka,Nabeel ya rubuta number dinsa ya bashi sannan ya tafi.

Annoor kuwa tunda akace an tsaida ranar aure duk ya rude da shirye shirye wata Daya aka sa tal,Habiba ta fara gyara Amarya sosai tana zuwa wajen gyara,sosai suke shiri,yayin da Maryam tana ji tace wlh baza ta sabu ba,Kauyen Maman su ta shirya ta tafi,tana zuwa ta samu Yan uwanta na wajen uwa tace Dan Allah wajen gagararren malamai zaku raka ni,miji na samu zan aura naga yanzu Yana min Wala Wala zai gudu,mutanen kauye da masifar son ayi aure ko za a mutu,wata Dausiyya matar aure ta raka tace akwai Malam Musa aikinsa kamar Yankan wuka wlh,idan zai yuwu zai fada miki daret (direct).
Suna zuwa suka same shi a zaure ya dawo kenan daga Kasuwar kauye ya siyo kayan taushe,Yace a'a Dausiyya kece tafe? tace Malam Yar uwata na kawo maka,yace mashaallah to ta shugo,Maryam anci wanka ita ga Yar birni ta shiga cikin zauren ta zauna,Dausiyya ta tsaya a waje sabo da sirri.

Maryam bayan sun gaisa tace Malam wani nake so kamar na mutu Malam amma yaki so na wata yake so gashi har an sa bikinsa an kusa ma,Malam gashi da kudi ga kyau Inda kasan shi yayi kansa wlh,Malam komai da ake so a wajen namiji ya hada,amma yaki so na,Malam yace Kash me yasa baki zo da wuri ba ai da tuni ma kina gidansa idan da rabo ma an samu.
Yanzu bari a fara dubawa aga ta yanda za a bullowa aikin,Kasarsa ya jawo a faranti ya fara Zane Zane,sai da ya dauki lokaci sannan yace babu alheri a auren ku,kece kike sonsa amma shi baya sonki ko kadan, dai dai da digo baya sonki,gashi Nan zuciyarsa babu hasken sonki a ciki duhu dundum,Maryam tace to ya za ayi a kulla kaunar ya dawo Yana so na? Malam Musa yace aurensa fa babu fashi sai anyi shi ko me zaki Masa,Maryam tace to a haukatar da Iman din mana,Malam yace babu Hali babu hauka a kaddararta,duk Kuma Wanda zaki je sai dai ya miki karya yaci kudinki sannan ni bana haukatar da mutum bana kisa Kuma,Abu daya zan iya miki idan anyi auren kar ya kusance ta,Maryam tace yawwa tace Hakan ma yayi,Malam yace indai ya sake ta kwance Mazagi ma'ana tazuge to shike nan sai ya kawo,Maryam harda dariya tace haka yayi ni Kuma zan San yanda nayi ya Soni,Malam yace idan ta tabashi sai ya kawo kawai,Maryam tace wlh yayi min,nawa zan bayar yace wannan karamin aiki ne ki Bada sadaka kawai,ta bashi dubu goma,Malam ya haukace yace zaki ga aiki,ya Saba da mutanen kauye Dari biyar dubu daya akan wannan wani sai yayi kisan Kai.

Maryam tana fitowa tace an gama Dausiyya gaskiya ya hadu Malamin Nan,suka tafa tace ai zaki ga aiki wlh,a ranar Maryam ta koma gida birni,Malam yace sati biyu yayi yawa Amarya tana tarewa bazai iya komai ba.


Masu Sharhi Ina godiya,Baby Ak Ina godiya sosai.



Arewa book
AsmaBaffa1

TikTok
AsmaBaffa




AsmaBaffa
[1/22, 9:25 PM] +234 806 252 6950: A GIDAN YARI

BOOK 2

61-65

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKI NE
Amina Maman Ibrahim





Rafeeq ranar da aka Kai kudin aurensa aka tsaida da rana sai murna gashi sun kusa karasa final Exam dinsu,har an canjawa Ikhram suna ta koma Wifey, gidan su Ikhram kuwa uncle ya samu kudin aure ya hau kansu ya danne,Asabe da Amarya baki suka hada akan dan me Ikhram zata bari Uncle ya karbi kudi gashi ya cinye kudi ba kayan abinci,sai suka Hana yaransu zuwa dakin Ikhram su kwanta, Ikhram fitowa tayi tace yaran baza su bane? Zan rufe kofa,da gadara Asabe baza su ba,Ikhram tace ni da na taimaka muku na huta, kayan shayina sun huta Kuma wlh baza su dawo min daki ba ko Kun huce,ni da aka cuce ni aka danne min kudin aure, tunda ku a duniya baku da tunani,na ma kusa aure na huta da jaraba,Asabe tace dama mu mun gaji Dake me kike tsinana mana.

Dakinta ta kulle ta kwanta a Saman katifarta taga wayarta na ringing dama tasan shine,dagawa tayi yace Amaryata,na'am Angona barka da dare Ina yini,ya school zance ko? yace ai an gama yau baki min murna ba,wow congrats na manta wlh sorry,yace ba komai,me kike yi yanzu? A kwance nake ni kadai a dakin,sun sake kwashe yaransu sun Maida su dakinsu wai fushi suke dani,Rafeeq yace gaba ta kaimu dama ni takura min akeyi Ina so inyi maganganu na ba dama yara suna nan suje suci gaba da Jin ihun Sex din Iyayensu.

Ikhram dariya ta saki tace Kai wanne iri zaka yi ihun? yace ni ai haukacewa zanyi na sani kawai,a karbo min magani a dawanau idan na haukace a bani na Sha,dariya Ikhram tayi tace kasan wlh ba Inda yaci sunansa da Hausa irin dawanau Kai da kaji ance Dawanau kasan ba hankali a cikinsa,yace haka naji mutane suna fada cewar Rafeeq, Ikhram ta furta Ina cewa wash Rafeeq zaka kashe ni,yace ai abin Kuma sai kisa nayi wanka da ruwan da ruwan kankara to nasha duminki ya ratsani,Ikhram tace ranar ana kawoni zaka yi baza ka bari a huce gajiya ba ko kwana daya ne? Yace wa? Ni na hakura ai sai in suma nake.

Yanzu dai ai babu suyar kosai ko? tace ae yace to idan zaki fita hijab da Nikaf,Malama tayi murmushi tace ya zama dole,Lefen fa me dame kike so? tace duk abinda Allah ya hore Maka ka saka,akwati Daya zanyi ya furta da wasa tace idan ma baza kayi ba duk daya haka za a kawoni kasan dai bani da gata ni,kina da gata mana ai babu Wanda bai da gata a duniya tunda kina da Allah,tace hakane kuma,kudin me da me zan baki yanzu? tace kudin gyaran jiki bari dai anyi lissafi na tura Maka,yace to Ina jira,jibi zanzo inshaallah amma ba kwana zanyi ba fa Ina zuwa zan wuce,tace Allah ya kaimu,suna ta hira abinsu har dare can sannan suka hakura da juna.

Yana kashewa ya kira Spark suna asibiti wajen Mummy lokacin,yace ya me Jikin? Spark yace da sauki da sosai gashi tana cin komai har toilet tana Kai kanta ma, sai dai bata amfani da hannayenta tukun, yace mashaallah Allah ya taimake mu dai ta tashi,dama kudi zaka turo na gyaran Jikin Amarya,Spark yayi dariya yace sabo da ga famfon kudi ka samu ko,auren ni zan Kara ne wai? ka kira Khalid Yana can,Rafeeq yace in zaka bani ka bani ai nasan da Khalid din na tambayeka bana karbar abinsu ace za a min gori ko a juyani a sani nayi abinda banyi niyya ba,to ni na haifeka ka fadawa iyayenka mana,ai ni na gama Maka komai tunda nayi Maka gida, furniture uban waye zai saka Maka nifa zanyi,na siya maka mota,duk Inda zaka je zance wajena zaka zo kawo kudi za a bawa Ikhram,Ikhram this Ikhram that,Rafeeq yace to ba yayana bane Kai ko me ka min ai baka Fadi ba Allah zai baka Lada,Kuma ma ni nace wani ya bani ne in ba Kai ba wlh da Naila ce da tuni ka bata,dariya Spark yayi yace kana da Bado ne?,in zaka bani ka bani kudi wlh sai ka min auren nan komai,da Misam ba aure zaiyi ba bazan ma saurare ka ba.
Ka turo min Ina jiranka ya kashe wayarsa,murmushi Spark yayi yace lallai ma yaro,Mima tace waye wai Rafeeq ne? Yace ae shine,tace auren ne wai ni Dan Allah wa zai aura ne nifa ana wulakantani na haifi yaro amma ace auren ma ban San matar ba,Spark yace wata fa Yar gidan Baba Nadabo ce wani Ambassador a kasar China,Mima tace da gaske ko karya? Spark yace Ina muku karya ne ni,sunanta Ikhram,Mima tace mashaallah yanzu suna China? Spark yace a can ma suka girma amma suna Nan Kano sai biki ya rage 1week zasu dawo shi yasa ai Baku ga tazo gaida surukanta ba Kuma zance a bata number dinki ta dinga gaida ke.

Mima ta washe baki tace Masha Allah Rafeeq duk ya fiku hankali da sanin ya kamata,Kai kayo mana kwashe kwashe Misam ma ba a San tasa ba,tunda ya kasa nuna ta a dangi babu arziki a cikin lamarin yasan ma baza muyi na'am ba,ai daga Jin Sunan ta Rafeeq kasan Yar manya ce,amma wata Naila ba a San ma ma'anar suna ba hmm ta tabe baki,Naila tana Jin Mima tana aibata ta ko ta kanta Bata bi ba,Arham yace ai sunan Naila yafi Ikhram dadi,Kai rufe min baki tace,Arham yasa hannu ya rufe bakinsa yace Kalli Mima ya rufu kuwa dai dai? dukansa tayi a baya tace ka Mai dani kakarka ko.

Spark yace Naila haka nake son abata bani da kamarta ni,Mummy duk kunya take ji ta tonawa kanta asiri bata iya magana,Mima tace ka turawa Rafeeq kudi yaran manya sai an kashe kudi ni nasan bazai karbi nawa ba amma ka bashi mana Kai, Spark yace sai Naila ta yarda idan Baby ta yarda na bashi ya juya Yana kallon Naila,tace karka hadani da mutane ni ba ruwana kunfi kusa,Spark yace bazan bashi ba sai kin yarda,Naila tace bacci nake ji ni zan tafi ka sameni a can,ta gaji da maganar da Mima ke yaba mata tana so ta rama tana ganin idon Spark.
Spark yace tsaya mu tafi tare,Mima tana sani tace yau bazan kwana a nan ba ka zauna kayi jinyar uwarka,Arham yace ni kuje zan zauna Kuma wlh ba ruwana ko fitsari zatayi kaita zanyi nayi mata tsarki har Kashi wanke mata duwawunta zanyi tunda kina mace baza ki zauna ba,bayan kin san tsarki sai an mata hannayenta basa aiki kice baza ki zauna ba sabo da ki takurawa Naila,ku tafi din ni kuwa na ga kanwarki tsirara in Sha kallo,to marar mutunci fitsararre Mummy ta furta,Mima ta zauna badan ranta ya so ba tace kuje.

Tafiya suka yi Naila tace zan fa daina zuwa asibitin nan Kaine kake cewa na shirya muje,zanyi zamana a gida kullum sai an fada min magana wlh bazan sake zuwa ba,ya kike so nayi to yanzu kina gani Ina kokari amma kin damu kanki,ni Banga abin damuwa ba a nan tunda ba yau kika fara ji ba,Naila tace ae ai dole kace ba abin damuwa bane tunda ni ake wa ba Kai ba,kullum sai an fada min magana ba dama nayi motsi wlh ni na gaji kawai ni ka sani a jirgi na tafi gida,wani takaici da ya kama Spark da kyar ya danne ya share ta,ta sake cewa ni gida kawai nake so a Maida ni gida, Bai kulata ba,Arham Yana jinsu bai shiga maganar su na har suka Isa masauki ya wuce room dinsa.

Sparka ma wanka ya wuce yayi abinsa bai kulata ba itama haka tana fushi,Yana fitowa ta Harare shi ta wuce abinta tayi wanka da brush ta fito ta samu Yana fesa turare,yau jikinta zata boye harda daukan man shafawarta ta shige toilet kar ya kallar mata jiki,dariya ta kama Spark yanzu Kuma ake boye jiki,tana gama shafa mai ta fito ta kwashi kayanta na bacci ta zabo riga da wando dogaye har kasa ta saka abinta tazo ta kashe light ta haura gefen bed karshe tayi addua ta kwanta tare da juya baya.

Har yayi niyyar ya shareta sai yaga zata Raina shi ma,hannu yasa tare da juyo da ita ta karfi tana daddagewa ka sake ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login