Showing 51001 words to 54000 words out of 134888 words

Chapter 18 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

917

nayi wanka , wlh yau sai na wanke Hallare ta da kaina,yace kina taba ta kin sani kema,Naila dama so take ya daina bacin rai akan wata uwar tuggu Mummy,Ai kuwa tana taba ta mike shike nan suka romancing juna sai da su jiyar da kansu dadi ta hanyar Romance.

Shirin bacci suka yi suka kwanta bacci amma Spark baccin Yana yi Yana farkawa Yana kiran Mima Yana tambaya ya jikin Mummy a haka ya kwana,Yana yin Sallar Asuba bai dawo gida ba ya wuce gidan Mummy, Itama Naila sai 11am bayan ta gama komai nata na gida Sannan tayi wanka ta shirya cikin Dubai Abaya hadaddiya pink,ta yafa mayafin rigar Dan karami tasan sai sunyi fada da Spark,amma ganin mota zata shiga shi yasa ma ta yafa guntun na rigar duk wata Abaya da ya saka a lefe mayafi biyu gareta da dan babba da guntun,wannan bata ga babban nata ba Kuma ta mata kyau,takalmi tasa me tudu silver da jaka silver ta kulle ko Ina na part dinsu dama Yan aikin ma matan ba Kwana suke ba suna gamawa ta sallame su,fita tayi ta shiga motarsa tayi driving kanta zuwa gidan Mummy.
Tana zuwa tayi parking a cikin gidan,duk Yan uwane dankam a gidan Maza da mata na nesa Dana kusa Maza da mata,har Wanda suka dakko ta lokacin bikinta da za a kawota gidanta duk gasu nan a compound sunyi group group suna hira,Wahida ta hango a cikin wasu Yan uwan,su Anam,Shahid,Arham,duk gasu nan tsabar sa Ido tun kafin ta fito suke kallon motar jira suke suga wace zata fito a motar Spark.

Motar ta bude ta zuro kafa daya sannan ta dakko hand bag dinta ta fito ta kulle motar sannan ta nufi ciki ,sai kallonta suke kamar mayu,Anam tace da Wahida ta samu kudin banza har tayi kiba ta wani Kara haske da kyau,Wahida sai da ta bari Naila tazo saitinsu tace babu a gidan Uba ana fama da tuwon Dawa da miyar kuka yanzu anzo Abuja an auri Spark ai dole a dinga kiba kamar Yar jaka.

Naila tsayawa tayi tace ba dole ba tunda kullum Yana Yana bani Sperm ai abin ba a abinci bane Yan mata Sperm ne a bani ta baki da gaba ta ko Ina karba nake,Wanda yafi karfinki ya miki Nisa har abada baza ki samu nasa ba,ko da muna cin tuwon dawar a haka ya Gani yace Yana so ya kashe kudade ya auro ni,wata kuwa kyauta sadaka ake rokonsa yace Yana so amma yace sai dai a Kai kasuwa,to anyi kwantai ba farin jini,kaninsa ma an bashi yace Ina da wata bana so,na ukun ma anje shi yaji ma yayi ya daina kula kowa sabo da bakin jini,ni yanzu ba sa'arki bace na wuce layin Yan mata ki bari a fara mika miki Hallare kina karba sai kizo muyi magana,duk Yan wajen suna ji suna gani sabo da Naila bata kunyar fadar magana ko wacce irin ce ko a gaban waye Kuma,dalilinta duk sun San mece Hallare wasu sunji sun bada labari,su Misam ma fada suke suce Hallare sun ji a wajen su Chika.

Tsaki Naila ta ja tace banzaye mahaukata ta wuce abinta ba Wanda ta kula,da Spark suka hadu a hanya Misam ya fada Masa ga matarka tazo su Anam sun tare ta suna zaginta,shi kanshi ta window ya gani bai San me suke cewa ba amma yace je Kaci Uban su shine ya fito
Naila tana ganin Spark yace mene naga kina fushi kuka ta saki ta nuna su Anam da yatsa tace iyayena suke zagi wai Yar matsiyata nazo Ina cin kudinka.
Spark ko gama ji baiyi ba ya nufi wajen Anam,tunda ta ganshi a fusace tace Yaya ka tsaya Kaji yanda aka yi,fisgo ta yayi tana da aure amma Spark ya zuba Mari har uku ya rike Kuma ya hanata guduwa,yace da ke za a dinga zagin matata ko Dan ubanki sa'anki ne ni,ke kika auro min ita,Misam ne ya fito ya mika Masa wata wayar Charger,da kyar su Arham suka kwaci Anam tana ta kuka ta tafi wajen Mima,Wahida kuwa tana tsaye Kam wai ita tsagera baza ta tafi ba tunaninta Spark bazai iya dukanta ba,yana Juyowa ya kwada mata Mari ta kwala ihu tare da dafe kumatu,kafa yasa ya kwashe mata kafafu ta Fadi rim a kasa bakinta ya fashe,Misam Yana daga nesa yana zuga yace use your charger,tana yashe a kasa yace ke naki San ko a titi ma naga mutum zaiyi hauka ba gyara shi nake yi wlh,ko ban sanki ba Ina iya tsayawa in chasa ki,ya dinga tsula mata wire,sai da Mima ta fito tana masifa wai haukacewa kayi ne na shiga uku ni dai Ina zan sa kaina? Arham yace Saman pillow mana,Mima ta bi shi da duka ya gudu,Spark yace wlh daga yau duk Wacce ta Kuma zagin matata sai taga abinda zan mata.

Mima ta fashe da kuka tace wlh asiri suka yiwa Dana sun bashi manta uwa baya ganin kowa a gabansa sai matarsa akan Naila ka zauna ka daki kanwarka uwa daya uba daya Kuma tana da aure ni dai Ina ganin jarabawa,ya zanyi da rayuwata duk cikinku ba na dauka, to wa kuke so na kama? Arham Yana daga nesa yace Allah,indai Mima zata yi magana ya dinga bata amsa kenan.
Spark yace ni fa idan zaki musu fada ki musu wlh duk Wacce ta sake zagin matata ko gobe ne sai na zaneta,me tayi musu a kyale min mata ta wala idan Kuma ba haka ba wlh zan hanata zuwa wajen kowa muyi rayuwarmu daga ni sai ita,nine dolenku ni sai nazo,ta ya za ayi yara suna ba daidai ba baza a fada musu gaskiya ba,Mima tace Kai din dai dai kake yi? ni dai na fada muku ku fada musu gaskiya kar nazo Ina balla yarinya ace nayi laifi,baza su Kara zuwa gidanka ba inshaallah cewar Mima, Spark yace da na huta wlh dama ni takura min suke mutum Yana soyayya ana ta sallama kar su zo ni na zo mu gaisa,abinda take bani duk duniya babu me bani sabo da haka a kyale min abata,Misam yace wlh kuwa kana haka Kai haka sai dadi,suka kama dariya yaran Maza sabo da yanda Misam ya gwada da hannu yanda ake lagude mace, Mima ta juya tace Allah ya shirye ku ni ba fitsararriya ce ba.

A cikin bedroom Inda Mummy take kwance a Saman bed bata motsi malamai sun zagaye ta sai sheka mata karatun Qur'ani ake yi,Mima ce a gefenta tana amsawa Ameen Allah ya tashe ki Yar uwata,Mero tana zaune a Palo a cikin yan uwan Mummy,ganin Spark ya zane su Anam shine suka kira Anam da Wahida suna lallashinsu,Wahida tana kuka tana goge lebenta da ya dan fashe tace kawai dan anga babu uwata tana gidan yari shine ake min wulakanci gani ake kamar bani da mijin aure, kamar kowa baya Sona Ina da samarina kawai na aure ne Allah bai kawo ba,Mero kamar an saka da ita tana cikin manyan iyaye duk wulakancin da ake mata da kallon banza amma sai zaraf tayi ta karbe zancen tace ai kuwa mazajen aure basa wahalar samu ki nuna bakya son kudi ki Gani in baki samu miji ba,ko dan talaka ai zai fito,wata ce a cikin kannen Mima ta gasawa Mero Harara tace dalla tashi yar kauye gayyar neman talauci,Mero tace Kuma ai ba daga birni kuka tsiro ba asalin tsoho da tsohuwa daga kauye ne,Maman Rafeeq ce ta fisgo Mero Allah yasa ta kwace ta gudu.

Naila ce ta kara so ciki tayi Sallama da kyar suka amsa mata,suna mata kallon banza ta durkusa ta gaida su lokacin Spark ya shugo palon,tana gaishe su yace taso Baby ya rike mata hannu ta mike ya zaunar da ita a kujera daban yace yi zamanki a nan ba ruwanki da kowa,tace to, rada ya mata a kunne yace kinyi kyau amma an yafo guntun mayafi ga Maza ko Ina,Naila tace Banga babban bane,dole sai ita ba sai a canja wata ba,ai ni ita nake so,shike nan to ya zanyi da ke Allah ya yafe miki,murmushi tayi.

Rafeeq baya gari yau shi tun safe ya dira a Kano ya kama hotel zai je gidan su Ikhram ya kasa hakuri da rashinta,tunda suka yi waya ya lallaba ta har ta bashi address dinta wani abokin Spark ya kira a Kano ya bashi mota da driver dan bai San ko Ina ba in banda gidan yari,Driver ne yazo da hadaddiyar mota bai fadawa Ikhram zai je ba sai yamma 5pm ya nufi unguwar su dake Sabon gari Kano,Ikhram a unguwar arna suke Bariki ce dandalin iskanci,duk wasu club da wani wajen karuwanci da iskanci a nan suke,Address din da ya rubuta driver ya dinga bi,suna zuwa layin kadan suka tsaya suna tambayar gidan Yahuza donation.

Wata Rafeeq ya hango kamar Ikhram a wata Yar rumfa cikin dandazon mutane tare da wata dattijuwa da alama matar yare ce tana tsaye tana zubawa mutane doya da kwai sai Egg in to Egg wata budurwa tana soyawa,daya kaskon Kuma Ikhram ce a zaune tana ta soya kosai tana zubawa a kwandon tsane Mai tana mikawa matar tana zubawa mutane,hayaki ya tirnike,Kuma abinda ya gani shine Ikhram sanye take cikin doguwar rigar material boubou ta yafa dan siririn mayafi,Rafeeq yace da driver daina tambaya ma gata can wajen wacce nazo wajen masu doya da kwan can,driver motar ya ja suka karasa wajen a hankali,yace jira ni,ya bude motar a hankali ya fito cikin shadda Sky,Rafeeq Dan gayu ne na gaske shima ya Sha kyau kamshi kawai yake,Ikhram bata taba zato ba ko motar bata kalla ba tayi zaton ma masu siyan kayan su ne,ta dukufa tana suya,kamshi taji a kusa da ita ance a bani kosai,dagowa tayi da sauri taga Rafeeq.

Dariya tayi tace wow shine ko waya? Dattijuwar ta kira da Maman chinyere nayi Bako zo ki karbeni,Maman Chinyere da bala'i tace to a kudinki na yau sisi bazan baki ba karki ce ban fada miki ba woooo, Kuma karki rasa abinci kizo gidana roko,Ikhram tace na yafe kije da kudinki Madam,kin San halina duk girmanki zan iya chasa ki Maman Chinyere karki Raina min hankali ga mata nan da yawa zan iya komawa wajensu su bani aiki ta ja tsaki.

Rafeeq let's go ta rike hannunsa,shi mamaki yake wai ita ya rayuwarta take ne ya kasa ganewa,yace har an nuna mana gidan Yahuza Donation sai na ganki,tace ae ba nisa ai,Rafeeq yana ta kallon Yan bariki ana ta harka da giya musamman da yamma ce kida ko Ina tashi yake,sannan musulman basu da yawa duk yare ne a unguwar.

Wani gida suka je Wanda ba nisa da Inda suke soye soye,gidan haya ne da alama irin katon nan ne daki daki ,duk daki uku da toilet dinsu haka gidan yake,duk gidan ya kwararrabe sannan musulman ciki kawai su Ikhram ne da bangarensu me gidan daki biyu ya kama,daki daya na Yahuza Donation ne da matarsa uwar gida Asabe ga Asabe da yaranta har shida duk,daki daya na Amaryarsa da yaranta uku, sabo da kishin da suke ko wacce yaranta a dakinta suke kwana ana musu shimfida a kasa ita Kuma matar da shi suna Saman gado kamar rayuwar arna.

Ikhram babu dakin da zata Kai Rafeeq ko daya sai kujeru farare ta aro musu guda biyu,suka zauna a Jikin katanga,Donation ne ya shugo cikin kana nan kayansa yaci zanzaro gashi Dattijo kana ganinsa kaga dan duniya,murna yayi ganin Ikhram da me kudi yaga katuwar mota a waje dama Mayen kudi ne Kuma ya matsu shi dai Ikhram ta bar Masa gidansa tunda baza tayi abinda yake so ba.

Uncle sannu da zuwa nayi bako,Yahuza yace madalla,Rafeeq ya durkusa ya gaida shi ya amsa Yana washe baki,ba ruwansa yace Ina Stella.... where are you come,Stella ta fito wata matashiyar arniyar ce Karuwa ce Yar gayu da ita,yace ki bawa kanwata dakinki zata yi zance tayi bako, Stella tace dama fita zanyi zanje na'ibawa a can zan kwana ko kwana zasu iya yi,Rafeeq Yana Jin haka yace ai kwana zanyi dama,Ikhram ta Harare shi,Uncle harda Jin dadi yace ba damuwa daga nesa kake ko? yace tun daga Abuja Uncle,Yahuza yace ahh dole ka kwana ai dole a baka masauki,Stella jaka ta dakko ta fice bayan ta mikawa Ikhram key, Rafeeq yace na gaji dama Yana dariya a boye,Ikhram tace shiga, suka shiga dakin Stella ya Sha uban gyara sai kamshi ko Ina Kal Kal komai na ciki me tsada ne.

Ikhram tayi bako bata da ko sisi,Rafeeq driver ya sallama yace yaje gobe zai neme shi,su kansu yaran Yahuza da matan haka suka yini da yunwa ba ayi girki ba,bare Ikhram rabonta da abinci tun jiya da dare,fitowa tayi taje wajen uncle tace Uncle Dan Allah ko rancen kudi ka bani na samu na sallami bako,Dan ubanki me yasa bakya wayewa Baki ga yanda ake karbar kudin samari ba ai su suke nada kudi ana musu girki Muma idan ya bayar a dafa damu muci arziki,Ikhram tace sai kace Karuwa,yace to ki barshi haka dan tani,komawa tayi wajen Rafeeq kamar tayi kuka tace Masa Ina zuwa again ta fice duk Wanda ta sani suna mutunci taje neman bashi bata samu ba dake Bariki ce ba mutunci,sake dawowa tayi ta kasa shiga dakin da Rafeeq yake ta fara hawaye sai data yi kuka sosai marar sauti sannan ta goge hawayenta ta koma ciki,kallonta yayi yaga alamar kuka tayi,yace Ikhram mene ne? tace ba komai,Driver din yayiwa waya yace ya kawo Masa motar,driver yace gashi Nan,yace je ki shirya mu fita,tace daga zuwa Kuma ban kawo Maka ko ruwa ba fa, yace ba komai je ki shirya dai,Ikhram fita tayi ta karbo Masa bashin ruwan roba kato Eva da lemo a wajen me kanti ta kawo Masa,yace wa ya saki,tace ka Sha bari na shirya ta fice.


Masu Sharhi Ina godiya


Dan Allah kuyi following dina

Arewabooks AsmaBaffa1

TIKTOK
AsmaBaffs



AsmaBaffa
[1/17, 9:55 AM] +234 806 252 6950: Paid group 300

ACCNT NO
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

YAN NIGER
+22790795939

A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

41-45

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAFE NAKI NE
MAMAN SAMHA



Yaran Yahuza Donation duk kana ganinsu abin tausayi sai iyayen ne mata suke samu suka Dan siya musu wani abin suka sa a bakin salati, shi Yahuza ya riga da yaci me kyau a waje ba abinda ya dame shi"
Yayi mutuncin gaske ya bayar ayi girki sau Daya a rana, yawanci matan ke ci da kansu suna yan sana'o'i, ko shugowa mutum yayi suna bin hannunsa da kallo ko zasu samu na ci,
Ikhram itace ma idan ta samo kudinta a gidan suke karewa kawai taimaka musu take yi badan halin Iyayensu ba sai dan Allah da tausayin yaran.

Wanka tayi ta fito,Uncle Yana zaune Yana danna waya a dakin Asabe,yace wanka aka yi? yawwa ko kefa Maza ki shirya,idan aka yi kwalliya ai anfi cin kudin mu,mu Maza ai sai da gayu,wacce bata gayu zata hadu da wulakancin samari kuwa ,Dan Allah ki bashi hadin Kai ko me yake so ki samu ki yago mana rabon mu,ki rama min yanda mata suke cinye min kudi nima ki ciyo kudin wasu Kinga kin rama min.

Ikhram tace ba Dan iska bane fa shi,,yace wato nine dan iska? haba Ikhram karki raina min hankali budurwa dake haka kyakyawa me farin jini kice ba a yin komai da ke ai bazan yarda ba,yanzu yan mata duk haka suke,Asabe tace mu take rainawa hankali wai ita ta gari ta gama raba shi ga Maza ta dawo tace daga wa'azi take,Ikhram tana jinsu kayanta ta eba Wanda zata saka ta bar dakin Asabe ta koma na Amarya Rakiya,a can ta Shafa manta da turarukanta sabo da tana siyar da su,wani Leshi ta dakko me tsada ne dark blue and Golden,sai mayafi, jaka da takalmi golden ne, ita dama Ikhram idan ta samu kudi Bata dinka kaya me araha,sai ta dan dade bata yi dinki ba amma in ta samu zata yi sai me tsada,shi yasa zaka dinga ganinta kamar Yar wani duk ranar da bata sa Hijab ba,riga da skirt ne, Yar kwalliyarta tayi sama sama tayi kyau sosai ta fito da kyar take tafiya sabo da yunwa ta gama da ita sai ruwa take sha kawai.

Dakin Stella ta shiga Inda Rafeeq yake,Yana kwance a gefen katifar Stella Yana latsa waya Ikhram ta shigo bai taba ganinta a haka ba daga hijab sai kananan kaya,kinyi kyau ya furta Yana kare mata kallo kamar maye,tace na gode, gashi bata cikin nutsuwa sabo da yunwa, tashi yayi yace muje Yana jiranmu kin San gari zaki iya nuna min hanya na karbi motar? tace ae na sani kace ya tafi sai ya bar motar kayi driving,suna fita ya sallami driver ya karbi key,gaba ta shiga ya ja mota suka tafi,yace shopping mall,sai ta nuna Masa Sahad store,a Nan yayi parking ya fito suka shiga.

Yace to Malama zabi abinda kike bukata,Ikhram a ranta tace gwara a bani dafaffen abinci naci akan komai ko na samu sauki" ko magana ta kasa sosai sabo da yunwa,yace wai ya na ganki shuru shuru ne? tace ba komai wlh tana murmushin dole,ta fara zabar abinda zata iya saukar bakonta da shi,ta dauki Indomie Eggs,su Lipton,Madara Milo sugar,duk wani Abu na dafawa, na ci shi ta dauka bata dauki komai ba sai iya su,ta dauki wata Rice ta Yar Leda guda uku,ta gama yace Banga bread ba?,maganarta a sanyaye sabo da yunwa tace ba a nan zamu siya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login