Showing 21001 words to 24000 words out of 134888 words

Chapter 8 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

906

innailayhirrajun wannan waye kuwa? wanne marar Imanin ne jahili,Iman Allah yasa da gaske ne fyade aka yi Ina tantama ace fyade aka miki yanda aka ruruce miki kirji da murji ya wuce ace fyade ne,ki fada min gaskiya Iman Dan Allah,Iman tace nifa na hakura Yaya wlh na barshi da Allah,mijina aka cutar shima mijin na sani ko Yana can Yana tattabe yaran mutane ai gashi Nan an taba tasa shima Kuma haka zai aureni ya zaiyi tunda ya yiwa na wasu,tunda kaga haka maybe Wanda zan aura shima ya yiwa na wasu shi yasa matar da zai aura aka mata itama,tsaki Annoor yaja yace nifa bana son zancen auren nan,nawa kike? shekarunki nawa gaba daya baki isa aure ba,tace to Yaya a sani a makaranta tunda takarduna sun fito yace waye zai kaiki makaranta Iman?

Ai yanzu barinki kina cudanya da Maza masifa ne ai sai a Kara lalataki ai Kuma ke da karatu sai watarana maybe in kinyi aure watakil amma yanzu Kam ai Kuma ke da karatu sai dai Kiga ana yi kiyi hakuri,kuka ta saki tace dan Allah Yaya yace wallahi baza kiyi ba kinji na rantse gwara ma ki hakura,Iman tace na fadawa Kawu,yace ai mun gama magana da Kawu Iman bake ba school yanzu,unguwa ma in kika ga kinje to sai in nine zan kaiki ko da wani Dan gida amma ke kadai ma baza ki fita ba,shuru ta Masa kawai har suka koma gida.

Washe gari kawu yace Yana son ganin kowa ya Tara duka yaran gidan da matansa gaba daya,suna Palo ana jiran Kawu,Kawu a ransa yace yau zai fadawa kowa asalinsa a huta,ya fito daga dakinsa kenan ya hango yaran kaf a zaune suna jiransa tausayinsu ne ya kama Kawu yace yanzu idan na fada musu zasu shiga damuwa gaskiya na fasa fada yau sai watan jibi idan Allah ya kaimu na fasa,Yana fitowa yace dama taraku nayi muyi addua Allah ya rabamu da masifun duniya,Su Haidar suka fara dariya akace to Bismillah suka yi addoui sosai sannan ya sallami kowa har su Karima su Sajid sunzo amma yace addua dama za ayi.

Da dare Annoor Yana Palo Yana dannan waya,Rahma da su Haidar suna ta tv game,Iman daga kitchen ta fito dauke da ruwan roba ta saka kayan baccinta pink dogon wando da riga karama,har ta wuce Annoor ya sa mata kafa ta fadi,kamar ba shi yayi ba, bai kalleta ba ta mike zata wuce wayarsa ya mika mata tare da furta read,Karantawa tayi taga ya rubuta bance ki daina fitowa da kayan bacci ba? Goge rubutun tayi ta rubuta okay ta bashi ta juya zata wuce ya sake sa mata kafa saura kadan ta Fadi Allah yasa Bata Fadi ba,wayar ya sake mika mata,kin karba tayi ya zaro mata kyakyawan idanuwansa ba tare da yayi magana ba,karba tayi ta karanta ya rubuta kije ki saka Hijab ki dawo Palo kiyi kallon film.
Ta goge ta sake rubuta bana son kallo yau,Yana karba ya rubuta mata dole sai kinyi kallon film je ki fito bana son musu,haka taje ta sako Hijab ta dawo ta zauna a 2seater din da yake zaune gefe daya ta zurawa tv Ido.

Ina gaisuwa
MRS CHIEF


Ana sharhi pls






AsmaBaffa
[1/10, 9:12 AM] +234 806 252 6950: Arewabooks AsmaBaffa1
https://www.arewabooks.com/locked?id=65759f207c65b397e88b84b3

A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

16-20


Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

Page naki ne
MRS CHIEF




Beauty kwance suke suna hira da Angonta Mohsin" wayarta ya dauka zai kunna tayi sauri ta rike sabo da gudun Daddy take kar ya kira ta,Wayancewa tayi tace bari yau na baka tarihina My man,ta karbe wayar tare da ajiye ta gefe,ya sake dauka yace me yasa kika rufe wayar? Beauty tace kawai na gaji da wayar ne,idan aka kiraki important fa ki kunna wayar ki,Beauty ta kwanta a jikinsa sosai sannan tazuge zip din rigarta, Mohsin yayi dariya yace Kuna Raina min hankali da nono,wai ko wacce ta tashi zata rufe min baki sai ta bani nono ko Dan gidan saniya ne ni ai sai haka,bakya so ki kunna waya akwai wata a kasa koma mene zanji later bani na shanun Ina so kar nayi asara biyu ba a bani labari ba sannan na rasa na saniya.

Beauty tayi dariya tace to ai Kai ni wlh ko a labari ban taba ganin me son Boobs irinka ba,Mohsin yace ai abin so ne ni Ina so haka Allah ya yini a kyale ni inyi abinda nake so,yanzu bani labarin Kinga Ina ji ga na Shanu Kuma Ina Kwalbewa inji Naila,labarin ta fara bashi a nutse.

Tace sunana Bilkisu Kabir,asalinmu Yan Bauchi ne amma gaskiya duk Yan uwa da kowa namu suna Kano kamar yanda ka sani,Mahaifina Kabir duk Yan uwansa suna yara suka mutu shi kadai Allah ya raya sannan Kuma ya azurta shi,matarsa ta farko da ya aura bayan sunyi shekaru ta samu ciki amma da cikin Allah ya mata rasuwa,sai ya auri Aisha wacce itace Mamana bayan ta haifeni da Shekara biyu Allah ya mata rasuwa itama.

A hannun Daddy na taso na girma duk da ya Kara auren mata har uku bai taba yarda matarsa ta rike ni ba shike min komai,na taso cikin gata da tabara,sai abinda nake so wannan yasa na sangarce har na girma na taso a sangarce,nasa duniya a gaba daga yawon gidan kawaye sai tafiya party gidan biki,ganin zan lalace shine Daddy ya zabo min mijin aure wani abokinsa Alhaji Wada,bana sonsa ko kadan amma yace lallai sai na aure shi tunda bana Jin magana,haka nace to na amince amma a zuciyata na kudurce sai na Masa rashin mutuncin da zai janye da kansa.

watarana yazo zance wajena na fito Ina taku dai dai Ina yanga da gadara dake bani da kunya lokacin,Ina zuwa gabansa na fara zaginsa nace bana sonka aure dole ne wlh ko ka aureni nice ajalinka gwara ma ka janye,zafin irin zagin da na Masa yasa ya mareni shima,shine ni Kuma na bawa Yan daba kudi suka je har gidansa suka Masa dukan tsiya.

Yana da manyan yara to suka ce baza su yarda ba wlh sai sun daukarwa ubansu fansa,akwai wata marar kunyar Halima tazo har gida Inda nake lokacin Daddy baya nan mun gama zage zage da ita sai nabi steps ta biyo ni ta shako min wuya muka fara kokawa da ita sosai,da kyar na kwaci kaina na tafi zan gudu daki itama ta biyo ni da gudu sai ta goce, gocewa tayi tayi ta fado daga steps,Dake ajali ne steps da biyu kacal ta gangaro a kai,tana fadowa Allah ya dauki ranta nan take.

Yan uwanta dai dai lokacin suka karaso suka dinga kuka da ihu suka ce ni na kashe musu Yar uwa,daga nan suka kira hukuma tayi gaba dani,sanda Daddy yaji har kuka yayi,Yana ji Yana gani kotu ta yanke min daurin rai da rai, ni gaskiya a shiga ta gidan yari gyaruwa nayi,kuma ni hankali nayi ba lalacewa ba,domin a waje abinda nake yi ya zarya tunani bani da kunya ko kadan hasali ma ni da riga da wando nake yawo ko yaushe,amma da naje gidan yari na Sha wahala sosai naga rayuwa daban daban sai Allah ya shiryani,na koyo wani halin na watsar da nawa halin na baya,Mohsin yace masha'allah Allah ya kiyaye mu ya kiyaye gaba Kun Sha gwagwarmaya gaskiya,Beauty tace Chika ai tafi abin tausayi wlh,Mohsin yace kyale Chika zo ki bani sweet ya dauketa kenan suka ji bugun kofa.

Hanan ce ta banko kofar rike da hannun yarta Amal,tace ga Yarka Nan ai baka isa na ciyar Maka da ita ba,Kuma wlh Ina binka bashi nayi rancen kudi na siya mata Madara,nayi rance na siya mata abubuwa daban daban,jiya ma da zazzabi ta kwana sai da na kaita Chemist kudin Allura da magunguna dubu biyar,Miko min kudina na tafi,Mohsin ya kalleta duk ta rame tayi Baki,yace kice dai kawai kina neman na Koko,Allah ya kiyaye wlh nafi karfin arzikinka hakkin yarka ne dole ka sauke,Beauty tace wa yace ki dauke ta daga gidan Ubanta? sisi baza a baki ba,ki bamu 'Yar mu ehe,wlh ficika bazai baki ba gwara ya siya min tsire da kudin,makaryaciya kawai,ki bamu Amal Yar mu ai ba muce ki rike mana ita ba,tana da uwa ai,mamaki ya kama Hanan za ayi mata fashin yarinya ita da ta haifi abarta.

Uban waye ya Haifa min yarinyar? Uban Amal mijina Kuma Ex husband dinki a da,yarinya Kuma wlh sai kin bamu abar mu,dariyar takaici Hanan tayi tace ba wata Yar iskar matar Uba da zan bawa yata a kashe min ita,Karuwar banza matsafiya me bin boka,dama idan mutum Yana Abu ai gani yake kowa ma yi yake shi yasa kike zargin na San gidan Malam cewar Beauty,ta ci gaba da cewa bani da uwar da zata kaini wajen Malam,asha rubutu a daura laya ai sai ke,badan Amal ba da na nuna miki cikakkiyar Karuwa ce a nan,to kinci darajar Amal wlh, Hanan ta Kalli Mohsin dalla malambka bani kudina da nake binka bashi,Ina binka bashi ka biya ka huta ka biyewa karuwarka Yar burar.... wlh Kara zan kaika sai ka bani kudin da na kashewa Yarka sai na kaika wajen hukuma, kin dade baki Kai Kara ba cewar Mohsin yace Ina jira hukuma tazo ta kwatar miki.

Abba ne yayi Sallama a gidan yazo duba lafiyar matar dansa watarana Yana Dan zuwa har lokacin ma da Hanan tana nan,Abba Yana Jin Muryar Hanan yasan masifa ta kawota,yace yarinya an sakeki ba a huta ba,Ciki ya karasa yayi Sallama,Beauty tace sannu da zuwa Abba shugo ta rasa Inda zata saka Abba sabo da tarairaya da girmamawa,Abba ya samu kujera ya zauna,Beauty ta durkusa ta gaida shi ya amsa Yana murmushi yace Mohsin yanzu nasan kana hutawa,yanzu nasan kana Jin dadi,ai yanzu Kuma nasan Dana na cikina yayi dace,Ubangiji Allah ya kade fitina,Allah ya rabaku da Sharrin makiya,duk sharrin wata Tsohuwar mata da aka Bata Jan kati da dadewa Allah ya rabaku da shi,Beauty tana Ameen Ameen,yace wata masifaffiyar Tsohuwar mata da aka Dade da sallamarta Allah yayi maganinta,Ameen cewar Mohsin,Abba yace Allah ya tsare min ku,Beauty taje ta kawowa Abba abinci da kayan sha iri iri,ya kalli Mohsin yace shi yasa naga kana kiba,dole kayi kiba ga kwanciyar hankali ba hayagaga ba Kai Kara ga girki me kyau,Mohsin Yace Abba bana cin tazarce,yace da kyau yanzu ba gaba bare fada Alhmdllh,Hanan duk taji habaicin da Abba ke mata wani tsaki ta ja tace duk Wanda ya zageni bazan yafe ba,Abba yace kinji nayi magana dake ni? Kinji na ambaci Sunan ki,ai ni yanzu bani da hadi dake da surukata nake da Kuma Dana dana Haifa,Hanan zata yi magana Beauty tace wlh kina zagin surukina zanyi kasa kasa dake a gidan Nan,Abba ya ja abincinsa Yana ci ya kira Amal yace zo jikalle Amarya ta, ta tafi wajensa da gudu tana dariya tana kallon Mohsin tace Daddy,yace Amal ba gaisuwa ko?

Amal tace Daddy a can kullum Koko muke Sha watarana ma bama cin girkin rana,Abba yace to zauna kici Kinga harda nama a nan iyayenki ke Allah ya hore musu ubanki baya harkar kayan koli,ke iyayenki Allah ya hore musu,kakanki ma yanzu girmamashi ake yi a gari,sai nayi sati ban saro kayan miya ba",dan tani uban kowa ya daina Shan miyar dage dage ko wata jar Miya,Dan uban kowa miyar taushe ta gagare shi,Beauty tana ta dariyar Abba,Hanan cin mutuncin Abba ya mata yawa ta juya ta bar Amal tayi tafiyarta gida tana kunci.
Abba harda kawowa Beauty Omo da sabulu ta karba tayi godiya,Abba da zai tafi tare da Amal ya tafi gida da ita yace muje Amal Abbanki Ango ne yanzu baya son takura.

Mummy kuwa kwana tayi tana bakin ciki,tace amma Baseeru Allah ya kwashe Maka albarka,kwana tayi tana tunanin me zata yiwa Baseeru ta huce takaici kawai,murmushi tayi a nutse tace zaka ci ubanka Dan Basi kake ko me baka San wa ka tabo ba wlh,a daren ta Nemo number Baseeru a wayarta ta sa Masa My Alhaji a haka tayi saving ai da sauri ta goge ta canja DAN WATA SHEGIYA tayi saving sannan ta kira shi a waya,Baseeru Yana ganin kiranta yayi mamaki sosai amma sai ya daga,Yana jira yaji ruwan zagi sai yaji tace ya aiki? Ido Baseeru ya zaro yace Alhmdllh,dama hakuri zan baka lokacin dazu Raina ya baci ne abinda ka aikata min,idan ka fada min gaskiya ma mene ne ai zan iya aurenka,shi so fa daban yake ba ruwansa da talaka ko me kudi,tunda Allah ya tsaga sai ka zama mijina ai ba yanda zanyi,Kuma dole a haka zan so ka komai talaucinka,Baseeru a ransa yace wlh ban yarda Dake ba karya ne da wata a kasa,a fili Kuma sai ya fara sheshekar kuka yace ki yafe min nasan na yaudareki na miki karya ya zanyi sonki ya kamani idan na fada miki gaskiya baza ki yarda ba.

Mummy tace duk ka kyale wata Kwangila ka dawo gidana muyi zaman mu tare muci gaba da aurenmu Ina sonka a haka, Baseeru yace a ransa mahaukaci ne ni,a fili yace zan dai dinga zuwa Ina yini watarana amma Ina wajen aikina a nan zan dinga kwana zan dinga zuwa miki da rana shima ba kullum ba sabo da aiki,Mummy bata so Hakan ba amma tace ranar ma tayi ba damuwa kayi hakuri ka yafe min,yace ba komai ai ni indai zaki daga min buje yo ko mene na yafe,tace buje sai kace tsohuwa ko wata yar kauye,Baseeru a ransa yace da mece idan ba Tsohuwar ba a fili yace sai nazo tace na gode da ka yafe min.

Spark kwana daya anyi hakuri Naila tana period sai romance aka Sha,ai kuwa tayi aiki wajen tsayawa ta sa ya samu nutsuwa,kwana biyu har ya gaji,Naila ce ta shugo Masa da kunun gyada yaji hadi sosai da chips tayi da dare,Yana kwance a Saman bed ya Kifa cikinsa kansa Yana gefen bed,Naila tana kasan carpet din Jikin gadon a zaune ta juya Masa baya ta jingina bayanta da Jikin gadon,Spark hannayensa yasa tare da sarkafo wuyanta Yana shafa wuyanta,jikinta sanye da vest da dan wando,guntu tana zuba Masa kunun a cup,Boobs dinta ya taba da hannu biyu yace Allah Yana son mu harda abin wasa aka yi mana,Naila tace uhm ka taba kaji dadi nima naji dadi,gashinta ya koma shafawa yace ya kamata ayi min Daadaa,dariya suka yi yace ai gwara na tuna da Jamilu na,Naila tace ayi Maka kitso dai,yace twisting nake so a min,idan kika yi sai next ayi calaba,next ayi kitso daban daban,Naila tace to Ina missing Hallare wlh,Spark yace uhmmm daina tuna min zan shiga jimami na kasa cin abincina, Naila tace tashi to muci Kai fa kace a yi Maka, Spark yace sai naji awara nake so Kuma yanzu ,ko ciki ne da ni,kin min ciki,dariya suka yi a tare Naila tace yanzu dai ni bani da ciki duk wannan madarar Nido din da kake bani ashe ban samu ciki ba.

Haka nake so ba yanzu ba sai na Sha amarci da yawa ya furta Yana cizon kafadarta,nokewa tayi tace ashsh da zafi fa,Naila cup ta mika masa ya karba sannan ta mike ta zuba nata tare da daukan plate din chips din ta Koma Saman bed din tare da zama a jikinsa suna ci suna hira,Yace maza ki gama Baby kizo Muji dadi, sai da suka cika cikinsu yace dakko min Juice,tace yanzu fa Kaci abinci,yace gumina zan ci,shike nan sai a hanani morewa,murmushi tayi ta dakko Masa na kwali,yace sorry miko min wayata,Naila ta mika Masa,yace sorry jeki Palo ki dakko min remote na manta shi a can,Naila tace wlh in banda aure babu Wanda ya isa ya dinga sani wannan aikin ta fada tana tafiya tana doka kafafu da sangarta,dariya yayi, tace kawai dan ana baka ci da Sha shike nan sai ayi ta aiken mutum tun safe ban huta ba a gida ko tsinke bana dauka,Spark yace anan baki isa ba kuwa yanzu ma kayana zaki gyara gasu nan an kawo wanki Kuma a haka ma muyi masifa idan baiyi ba,yau Tantiranci ya motsa kenan? Naila tayi Masa shuru taje ta fara shirya Masa kayansa,kin kula shi tayi tana ta faman aikinta,tashi yayi yace kyale kayan sanda kika ga dama sai ki shirya,taki kulashi taci gaba da aikinta,tace tun safe kake aikena ko zama bana yi kana bakin ciki kaga na zauna Ina hutawa sai ka aike ni,yace yanzu tsakani da Allah aike nawa na miki,wlh ka aikeni da yawa da kafin na aureka wa kake aika kawai Dan ka girmeni sai kayi ta cutata,Spark baki ya bude yana kallon ikon Allah,to nace ki kyale min kayana idan ma baza ki gyara ba ni zan gyara,Naila tace wato in ki yi a rubuta min zunubi ai ka San da haka shi yasa kace na bari sabo da a rubuta min Alhaki,yace to ga Juice din mayar indai a kansa kike Jin haushi na aike ki gashi mayar,Naila ta karba tace dama nasan sai ka Kuma aikena ga gyaran kaya gashi kace sai na Kuma mauar da juice ta fice taje ta mayar ta dawo,Spark yace a'a ikon Allah wani abin sai mata.

Naila tace mace ta Maka komai wlh ta Maka riga da wando harda singleti,kullum kana kwana a Saman gajimare ka raina mu,yau dai fada kike ji baza kiyi da ni ba, Spark ya kyaleta ya jawo wayarsa ya fara latsawa,Naila tace nifa bana so ana tare dani ana chating,bai kulata ba har ta gama aikinta ta hauro Saman bed din ta kwanta ta dauki wayarta ta kira Mohsin,dagawa yayi tace my love wai Dan Spark yaji haushi,sai da suka gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login