Showing 75001 words to 78000 words out of 134888 words

Chapter 26 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

1207

turbine ba mutunci ya shiga,ana idar da Sallah ya fice yana fushi.

Naila tashi tayi sai bayan tayi sallarta itace ta musu abin Kari a gidan,tazo sabo da haushi taga kiran Spark amma taki bi tayi fushi,yau Kuma harda yiwa Umma kwalimar gida aka gyara ko Ina irin babba tazo gidansu,zuwa yamma ta shirya tare da kanwarsu ta rakata Makwafta daga Nan ta wuce ganin Hanan ya ta koma taci gaba ko kuwa,Naila tana zuwa gidan tayi Sallama

Baban su hanan ya tarbeta Yana murna yace Naila kece ko ba ita bace ne? Naila tace nice ta gaida shi a mutunce ta Sha kaya masu tsada tana baza kamshi,ta shiga ciki ta samu Hanan duk ta rame tayi baki,Hanan fuska ta bata ta Kalli Naila tare suke da yarta Amal da Zarah,Itama Maman Hanan ko wajen zama Bata bawa Naila ba tace idan Amal kuka kawo bama so kuje da yarku ku rike.

Amal tace ni wlh bazan zauna ba Nan gidan koko ake Sha da garin kwakwi sai dai mama ki biyo mu,Naila ta Kalli Hanan tana murmushi tace Hanan ba magana to Ina Kwana ya aka ji da rashin Hallare Kuma ga Sanyi yazo,Hanan ta kalleta tace Yayanki ne Mayen nono a haka zai kare Shegu Yan iska,Mayen nono Inshaallah Nono ne ajalinsa, inshaallah sai yayi bara a titi,Naila tace uban yarki ne ai kuma da yarki za a ci wahalar,na gaba yayi gaba na baya sai labari wlh ai tuni mu mun cuci Talauci dama zuwa nayi na gani kinci gaba da kika ce a sakeki,ai kamata yayi naga kinyi kinyi fresh,Ashe yayana ya iya kiwo yanzu ga halin da kika fada,to Yaya ma ki sani jirginsu yau zai daga sai Dubai zasu tafi Honey moon.

Hanan tace idan ban miki dukan tsiya ba Allah ya tsine min Shegu Yan iska masu bin malamai ko me aka muku baya cinku,dariya ta kama Naila tace ai Wanda baya nufin kowa da sharri asiri Bai tasiri a kansa madam ki sani yanzu ma Amarya ciki gareta, jiya ma wlh ni na dafa mata taliya da yaji,kinwa kanki Hanan kiyi karatun ta nutsu ki daina batawa kanki lokaci kina kashe kudinki wajen malamai makaryata,Hanan ranta ya baci matuka Jin Beauty tana da ciki gashi wai zasu tafi kasar waje ita ko tashar kwanar dawaki bata taba zuwa ba.

Babar Hanan tace fita ki bar mana gida,Naila ta Bada amsa nan har gida ne? Ke wlh kamata yayi yaranki su tsine miki ma,Baki cacanci uwa ba,Dake ubanki ne ya Haifa min yaran?,ke uwarki ta garin ce? Mene Bata yiwa Hashimu Dolo ba muna da tarihi ai cewar Maman Hanan,Naila tace to ta tuba yanzu ta gane gaskiya yanzu love suke zubawa,ke kuwa fa kin tuba ne?ku baku San mutum in ya tuba a kyale shi ba har mutuwa ana Masa gori haka hausawa muke.

Naila kudi ta zaro ya Kai 20k ta mikawa Baban Hanan tace gashi Baba ka ci tsire karka basu ko sisi ciki,ya washe baki yace dama Likita yace jini na yayi kasa na gode miki, Amal tace Mama zamu tafi baki ga yajin bane har yau? Dan Allah Mama mu tafi tare gida wajen Daddy Aunty ta daka mana wani yajin da yawa zata naki,Umma Kubra ma ta hada wani jiya akwai yajin da yawa harda tafarnuwa a ciki ma,Hanan ta daka mata tsawa dalla rufe min baki shashasha ubanki ma yaci ubansa,Naila tace Uwarki ma taci uwarta,Hanan ta taso zata daki Naila ai Naila da gudu tayi waje da su Zarah,Baban Hanan kuwa sai murna yake Yana yiwa su Hanan fadan rayuwa.

Naila Spark Yana ta kiranta sai yanzu ta daga tana hanya ta gaza share shi,yaji karar motoci da machines,da fada yace Ina kika tafi haka? Gaida dangi na kiraka kaki dagawa sai yanzu Kuma ka fara min fada,to ya kike ya su Umma da Abba? Kowa lfy suke,yace ke fa? tace Alhmdllh Ina ta Jin dadina,ni gaskiya na fasa barinki Kwanan ki dawo yau,Naila tace tab ai wlh bazan dawo ba sai nayi kwanaki na Umma tace ma sai naje Kauye na kwana biyu wajen Kaka kaga 5days kenan,Spark yace azo a dauki gawata kawai,ni gaskiya ban yarda Malama gida ba kowa,kaje gidan Mummy mana,ya buga ya buga Naila tace wlh baza ta dawo ba, fushi yayi ya kashe wayarsa ya mike a Office ya fito a fusace ba mutunci kadan yake jira ya ci mutuncin mutum.

Papa ne ya kirashi a waya yace yazo Yana son ganinsa,ya fito ya nufi gidansu, Yana fitowa a mota Haly kanwarsa haushinsa take ji sunci duka ta bata rai ta taho zata wuce ta gefen Spark Baki ta turo ta Harare shi harda zuwa kamar zata bangaje shi,dama Spark a wuya yake hannunta ya ruko tare da dawo da ita gabansa ya fesa mata Mari har uku,ya rike hannunta ya Murda shi ta bayanta,sai ihu take da kuka yace da wani Soja kawo bulala,ihu ta fara iya karfinta sai da su Mima suka fito,Spark ya sa balulala ya fara tsula mata yaga ma lokaci take bata masa takalminsa me tsada ya cire da shi ya dinga dukanta kamar Allah ya aiko shi gashi ya riketa ram,Su Anam ganin haka sun zaci duka na biyu yake musu duk suka gudu suka buya.

Mima kuka ta saki tana janye Spark tace kashe ta Zaka yi marar Imani, ka musu wacceen dukan ashe be isheka ba,Sam yaki sakinHaly yace ki tambayeta me ta min wannan yarinyar kanwar kanwata ni zata bangaje ta harare ni ya sake zuba mata Mari tana ihu wayyo na shiga uku zai kashe ni Papa Mima....wlh bazan yafe ba,tana fadar haka kafa yasa tana fadar haka yayi ball da ita,sai da kowa ya tausaya mata yanda yayi ball da ita sai da bakinta ya fashe sosai,amma kamar ana Masa Allura ya bita jikinsa har rawa yake ya damko ta tana jin wuya ta fara bada hakuri wlh na tuba ka yi hakuri bazan Kuma ba,wata farar kujera ya jawo zai buga mata Mima ta fashe da kuka ta rungume shi ta rirrike shi Dan Allah karka kashe min Yata,Spark yana huci yace ki fada musu kar su sake kulani daga yau bani ba su dukkan matan gidan nan idan ba haka ba wlh ko a hanya wata ta kira sunana sai na nakasa ta,akan wannan tsinanniyar matar taka zaka rabu da Yan uwanka wayyo ni ku kashe ni ku huta,Spark yace ai ba sai mun kashe ki ba idan kwananki ya kare tafiya zaki yi,sabo da na dawo Ina mutunci a gidan Nan shine za a rainani dama ni ba wajen ku nazo ba me zai kawoni Inda ba a kaunata,Papa ne ya kirani badan haka ba ma bazan zo ba,part din Papa ya wuce abinsa,Papa duk abinda suke Yana kallon su,yace dama indai ka sake ka kasa bawa yaranka tarbiyya karshe abin a kan iyaye zai kare,kafin Uba yayi kuka uwar tayi kuka sau dubu,Kun zubar da mutuncinku Kun takurawa yara bayan Baku musu tarbiyyar da zasu biku da abinda kuke so ba,gashi dan cikinki Yana fada miki magana me ciwo,ku baza ku tsawatar ba Kuma ku takurawa yara, Kuna so suyi muku biyayya ta ya hakan zata faru,ku godewa Allah ma da suka kare a haka da yaran, amma abinda kuka shuka shi zaku girba,sanda suna yara Ina fada muku gaskiya Maida ni banza kuka yi ga irinta nan.

Mima tace ai har da Kai bani Allah ya dorawa nauyi ni kadai ba,Spark Yana shiga Abba ya rufe shi da fada,Dan me zaka fadawa uwar da ta haife ka haka,Ina ganinka me hankali,Spark yace kayi hakuri Papa wlh Allah sun takura min,idan na bar gidan suce nayi laifi,naki aure sun uzura min naki aure,nayi aure sun hanani sukuni da matata,Mima tana gani yara Suna min rashin kunya amma sai ta goya musu baya,kowa yasan wlh Ina kokarin binsu basa gani,ni ban San me na musu ba,kamar Haly ta zageni ai wlh ba a haifi Ubanta ba, Papa yace gani kuwa an haifeni dan ubanka gani tunda baka ji wlh zan sa a saka min Kai a guard room, ka tabbatar ka bata hakuri,ka kiyaye fushin iyaye musamman uwa karka bari ta zubar da hawaye a kanka Spark,Spark yace shagwaba ce kawai badan haka ba me nayi mata na kuka,Abba yace shagwaba ko uwar taka? Yace ai dama in mata suka ga suna da yara manya sai shagwaba,Kai ya cancanta tayiwa,sabo da Allah ga shagwabar matata gata uwata da me zanji,a bari na dauki daya, Kai ka dauki taka baza a dora min nauyi ba,Papa dariya yayi sosai yace wai Spark a Ina kake koyar magana ne? Duk abinda aka fada sai ka bada amsa Allah ya shiryeka kaje dai ka bata hakuri,yace wata shagwabar zata yi fa,yace kaje dai ka dawo.

Tashi yayi yaje ya iske Mima a bedroom,tana zaune tana lallashin Haly yace kiyi hakuri Dan Allah ki yafe min,na Fadi magana ban tauna ba rashin bado ne ya kawo kin shi rashinsa fada yake sawa da ciwon hauka,matata tayi tafiya ni kadai na kwana shi yasa abin ya motsa,babu nishadi amma dan Allah Mima ki daina biyewa yaran suna raina babba, I can kill fa, Ina fada miki ki tsawatar musu bana daukan raini ni a rainani a raina matata bazai yuwu ba,mata ne gidan wani zasu je,akwai mutuwa idan basu ganin girman mu ta ya zamu rike so, sannan bana so ace akan mace nayi fushi da iyayena,matsayinku daban nata daban har abada bazan yi fushi da ku ba sannan bazan Raina ku ba,kece kike jawowa duk yaron dake gabanki kinfi fifita su kina sangarta su bata tarbiyya ne,Dan Allah ki dinga kamantawa abin da ake a family din Nan yayi yawa dan Allah ku gyara.

Kuma ki yafe min kinji ya dagawa Mima gira,tana so tayi dariya ta hade rai,kumatunta ya taba yace haba Yar Mima kyakyawa ta General Ahmad,bake ba kishiya kin tare gaba kin tare baya,kumatunta ya ja kadan tayi dariya tare da bige hannunsa tace na hakura ai na yafe Maka Allah ya muku Albarka,matarka dai ni bana sonta,yace Ina son abata ni kuwa ya fice abinsa ya koma wajen Papa.

Mima ta dauki yarta da kyar suka shiga toilet baza ta iya tafiya ba sai dai a dauke ta,Mima tace na fada muku ku daina shiga safgar Spark wlh in ta motsa Masa sai ya muku illa, Kun manta irin dukan da ya taba muku ko? ku fita harkarsa wlh.

Spark wurin Papa yaje,Papa yace Spark sai ya fara dariya yace Sunan naka dariya yake bani Kai Kuma har wani amsawa kake yi,Spark yace ae mana sai ma matata ta fada yake dadi,Papa yace uhm wannan mata dai ana sonta kaga kuwa Yar Albarka sau uku tana zuwa tana gaida ni, Spark yace ban ma sani ba tace dai zata zo gidanmu,ai kuwa tazo har da turaruka ta kawo min masu kamshi,Tafiya zanyi zan bar kasar dama wani sirri zamu yi da Kai na kira Khalid ma munyi magana,kar ku fadawa kowa Please,Yaji zanyi na bar gidan nan ko zasu gane gaskiya,zan Dade ban dawo ba sai sunyi kuka da idon su,duk kudina na janye na sallami masu aiki da kowa, komai na bar muku a hannunku wannan tafiyar da zanyi ku kula da yaran da uwarku karku basu dadi suji sosai komai a janye musu zanga gadarar kudin nasu.

Spark yace ba damuwa yanzu nima Kano zan tafi na dakko matata,kwananta Daya fa ka barta tayi kwanakinta Dan Allah ba kace 3days ba,Spark yace 5days fa tace,to ai kamar yau ne kayi hakuri ka barta Dan Allah, Spark yace ni dai gaskiya ba a so na,Dariya Papa yayi yace to jeka ka dakko ta Kaine zata gaji da Kai, ka barta ta ga danginta in ta dawo tafi yin missing naka.

Spark yace uhm ya zanyi na hakura suka gama hirarsu ya tashi ya bar gidan ya wuce wajen Kamal Yana Jin haushi gida ba dadi ba kowa a ciki,yace ni na shiga uku,Kamal Yana ta dariya.
Naila ta cika kwana uku sai gyaran Jikin take yi,tare da Umma suka je riga wajen Affa,kwana biyu suka yi,Goggo tana ta tsuma Naila,suna dawowa Kano Naila taje Saloon da lalle kamar wata Amarya ta Sha gyaran gashi da lalle.

Beauty sun riga sun wuce da Chika Dubai har Mohsin,Naila ita ta dauki motar Mohsin suka je gidan Jauro da Abba,anci sa'a kowa yana gida,suna Palo suka shiga,Jauro yace me kazo yi Kuma nace kazo mu tafi can gidan baka zo ba,Abba yace shadda ta na bayar dinki sabuwa,aje zance ba sabuwar shadda,Jauro yace ai Nima tawa na karbo ta an goge ta ma,Ina Habiba? Jauro yace tana wanka,yaran duk suka gaida Abba,Naila ta gaida su suka amsa,Haidar sai kallon Naila yake tunaninsa budurwa ce yace yayi kamu.

Abba yace wannan itace ta biyu a yarana itace take aure a Abuja me kudi take aure yara,Annoor Yana dariya yace ai munga Alama Abba gaskiya mijin yayi dace Nima nayi dace,yasan halin Iman sai taji kishi shi yasa yace shima yayi dace amma duk da haka baki ta turo ta hade rai,Abba yace to ke Kuma budurwa budurwa haka haka dai ba budurwa ba Kuma mene a ciki me gaki Buzuwa shi sadaka yalla mene na Jin haushi da kishi to,Naila ba bakunta sunyi hira har Habiba tazo suka gaisa tana ta kallon Haidar tace wlh kana min kama da wata Ikhram,kamar ku ta baci sai Kuma naga kamar wani shima da na sani a Abuja irinku Daya,Haidar yace ni? Naila tace ae,yace Babana nane Maybe a Abuja yake,tace amma baka zuwa zumunci ka dinga zuwa kana da kanne fa sosai,Haidar yace zanje ne Inshaallah,Abba yace ke tashi mu tafi kar mijinki yazo,me kudi ba a Masa wasa,dariya suka dinga yi,Jauro yace kiyi ki haihu Yar nan ki tara iyali Allah ya rabaki da zama juya Irina,suka yi dariya suka tafi.

Jauro har da yiwa Naila kyautar kudi,Rahma tace kin zama kawata bani number ki suka yi musayar Number banda Iman kishi take ita Annoor yace wani yayi dace ai yaga kyan wata mace ba ita ba,suna tafiya tace na fasa aurenka bazan aureka ba,Kawu bazan aure shi ni na fasa,Kawu yace ai gwara ya karasa wajen da ya lalata miki Iman,ya dauki saurarsa,Kawu nice saura ma? Yace to so kike na boye gaskiya? Nima hashimu ya koya min duk Inda gaskiya take a fadeta,Annoor yace to babu me Kwasa dai sai ni din ayi hakuri haka dani Yana wa Iman Gwalo.

Mummy da Baseeru tun sanda ta farfado Kusan sun sake shiryawa ta lallaba shi zuwan biyu suna Shan love,yau kwana na uku ya dawo da yamma sai ya iske Mummy bata nan ta fita sai Mero,yace Mero ba wani abinci ne a gidan? Mero tace an dafa mana ta shiga kitchen ta ebo Masa ta kawo ya karba Yana ci Yana ci yace fatan ke kika dafa? tace ae nice nan kaci kanka tsaye wlh,sai da ya Sha ruwa ya tashi ya shiga toilet ya dinga sheka amai ba tsayawa ya dinga kwara amai kamar an balle famfo tun Baseeru Yana yi da karfinsa har ya Fadi a toilet din kawai amai na bulbulowa ta bakinsa Mero ta fita ba Wanda ya sani sai da Mummy ta dawo ta ganshi a toilet ya sume,dariya tayi ta fito tana ihu Mero ta sawa mijinta guba ta fita waje tana jama'a a taimakeni,Yar aikina ta sawa mijina guba,mutane suka fito aka cika gida ga Mero an taru a kanta,Police Mummy ta kira aka dauki Baseeru ranga ranga sai asibiti,Mummy ta nace sai wani asibiti za a Kai Baseeru tana cewa yafi kyau muje can,bayan an kaishi dama ta hada baki da Likita ta biya kudi Yana fitowa yace ai guba aka sa masa ta mutuwa amma Allah ya rufa asiri Bata Masa illa ba zai tashi,Mummy Kuma kwaya ta zuba a girki wacce in mutum bai Saba Sha ba Yana Sha sai amai sai ya kusa zubar da kayan cikinsa indai ya Sha Kuma ya hada da ruwa,a ka'idar garin kwayar sheka akeyi ba a Sha,amma ta zuba yasha tasan Kuma abinda zai faru kenan.

Mero bata San hawa ba bata San sauka ba Mummy ta bawa Yan sanda cin hanci suka kama Mero aka tafi da ita,Spark yayi yaji ba zuwa yake ba,su Misam duk ba a San ya Mummy take ciki ba,ana Kai Mero police station ta samu Alkali marar Imani ta bashi kudi akan a kulle Mero a gidan yari,bata fadawa dangi ba dan kar ma ayi wani tunani daban.

Mero tana kulle a police station ko kuka bata yi ba tace bani nayi ba ace ni nayi kisa,ni wannan ai tarihi na kafa dama ban taba shiga police station ba Dpo ku sake kulle ni sabo da in kafa tarihi Yan iska azzalumai, mace suka sa tayiwa Mero duka Wanda yasa Mero tayi shuru,ko kotu ba a Kai Mero ba suka mikawa State CID aka Kai Mero gidan yari Inda ake tsare masu laifi Wanda ita ba ma San a wanne mataki take ba Kuma ba a yanke mata hukunci ba,Case din ma ba a Kai kotu ba kawai gidan yari aka kaita bangaren Wanda suke a tsare ba tare ma da an Kalli case dinsu ba bare a yanke hukunci,Sabo da zaluncin Mummy tana ta Bada kudi,Ashe muguntar data hadawa Mero kenan,ga Baseeru Yana asibiti tasa ana ta danna Masa allurar bacci.

Mummy sawa tayi aka Maida Mero gidan kaso na Kano Iyayen Mero basu sani ba ma tunda ba kotu aka Kai bama tukun sai an shigar da Kara an fara sauraro tukun sannan ma a yanke Maka hukunci,idan kotu bata yanke kuhunci ba to zamanka na gidan yari duk a banza kake yinsa daga sanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login