Showing 30001 words to 33000 words out of 199108 words

Chapter 11 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

792

yi ta shigowa yi wa mama jajen abun da ya faru, na kama Aliyu, sai dai a wannan karon mama a tsorace take da mutanen, dan kar su je su yi musu wani sharrin.

Rumaisa ta saba sa ta dawo, mama za ta ce mata, ga ruwan wanka ta wanke wannan gumin da ƙarin ranar, idan an gama abinci ta ci ta yi salla ta tafi islamiyya, amma yau ta dawo ba ruwan wanka, ga mama ba ta kulata ba, haka ta yi abun da zata yi ta tafi islamiyya.

A ƙa'ida, ta kan ci abinci sau huɗu zuwa sama a rana, ba wai abincin take tsayar da hankalinta ta ci ba, zaɓe-zaɓe ne da ita, ga irin cin abincin yara take yi, tana ci tana wasa, ko da ta fara ta ce ta ƙoshi. Kullum ta dawo daga islamiyya sai ta ci abincin yamma, sai dai a yau ɗin ma mama ba ta ajiye mata abincin ba, gashi bata mayar da hankali ta ci na rana sosai ba, bugu da ƙari ta ga mama ta ɗora tuwo a matsayin abincin dare.

Ba ta kula kowa ba, sai kukanta suka jiyo a ɗaki, Usman ya leƙa, ya tarar ta kwaso kayanta, tana ta ninkewa tana zubawa a bagco tana kuka, kamar mai shirin yin yaji.

Cikin mamaki ya ce "Ke! Meye haka?"

"Haɗa kayana nake yi, cikin dare idan kowa yayi bacci in bar gidan nan, tun da dai ba a ƙaunata" maimakon ya ji haushinta, wata uwar dariya ce ma ta kama shi.

"Waye ba ya ƙaunar ta ki?".

"Ba mama ce ba, ta daina kulani, wallahi duk faɗan da aka yi da ni nice mai gaskiya, ya za ayi ace in sayo sigari? Kuma dan meyasa wannan shamsiyyar zasu din ga ce mini ƴar iska, sai ayi ta yi mini abu ba zan rama ba"

Usman cikin salon tsokana ya ce "Gaskiya babu daɗi kam, yanzu to ina zaki tafi?"

"Tun da ba a sona a gidan nan, katsina zan koma wurin ƴan bindigar, wurin su barde, au ashe an kashe barde to dai daji zan koma na yi bukka na zauna a ciki" ta yi maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.

Usman kamar ya shiɗe dan dariya, Aliyu da su Huzaifa kansu dariya suke yi mata.

Aliyu ya ce "Mama ki yi biko, saboda ke za ayi yaji"

Mama ta ce "Idan ta tafi nima na huta, Allah ya raka taki gona, ku ƙara mata kuɗin mota".

Jin furucin mama ya sanya ta sake tunzura tana kuka ta ce "Shikenan, bakomai"

Ta ɗauko bagconta tana kuka, Huzaifa ya ce "Allah sarki rumaisa, zamu yi kewarki sai a darul salam" ta sake fashewa da kuka.

Yasir ya ce "Rumaisa a yafi juna, Duk in da ki ka je ki zauna lafiya da mutane, koda yake ai kin ce a bukka zaki zauna ke kaɗai, Allah ya kiyaye hanya ga wannan" ya baya naira ɗari. Ta saka hannu ta karɓa, suka cigaba da tuntsra mata dariya, ita kuma bil haƙƙi da gaske barin gidan za ta yi.

Ta waiwaya tana kallon mama, ta ga mama ko a jikinta, jajjagenta ma take yi, ta nufi hanyar soro.

Abdallah ya ce "Yarinyar nan fa ba hankali ne ya game jikinta ba, bari na bi bayanta.

Ta dafe kayanta ta fita waje, ta tsaya tana tunanin wace hanya za ta bi, kamar sama sai ga mai sunan baba.

Ya kalleta ya ce "Meye haka? Ina zaki? Kukan me ki ke yi?" Ya jejjero mata tambayoyin.

"Tafiya zan yi" ta faɗa tana share hawaye.

A kausashe ya ce "Zuwa ina?"

"Mama ba ta so na, kowa ya tsaneni shi ne na ce barin gidan zan yi, an bani kuɗin mota ma" tayi maganar tana nuna masa kuɗin hannunta.

Takaici ne ya ƙule mai sunan baba, gaba ɗaya rumaisa ba ta da wayo wasu lokutan cikin takaici ya ce "Dalla wuce ko na mareki"
Za ta yi Magana, ya daka mata tsawa zai kai mata duka, ta taka da gudu ta koma cikin gida.

Abdallah da ya biyo bayanta kuwa, dariya kamar zai shiɗe.

Mai sunan baba ya biyo bayanta zuwa gidan, su Usman ya saka a gaba ya din ga yi musu masifa, saboda sun bar rumaisa ta fita, ba sa tsoron ta yi wani wurin.

Mama ta ce "Ka daina yi musu faɗa, ita ta haɗo kayanta ta ce barin gidan za ta yi"

Mai sunan baba ya yi wa rumaisa wani mugun kallo ya ce "Zaki wuce ki ajiye kayan nan, ko sai na zaneki, idan ki ka bar gidan, wurin uban wa zaki je, mara wayo" sumi-sumi ta shiga ta ajiye kayan a falon mama.

Har dare suna yi mata dariyar abun sa ta yi, wanda hakan ya sake tunzarata.

Mama tana kallon rumaisa ta tada kai da kayanta, ta ƙi yin shimfiɗa ta kwanta, kuma ba ta ci Abincin dare ba.

Mama ta girgiza kai ta ce "Ubangiji Allah ya shiryeki, ya rabaki da wannan rashin ji haka rumaisa, idan auren nan alkhairi ne Allah ya tabattar da shi, ya san silar shiriyarki ne".
Ta gyara mata kwanciyar, ta lulluɓeta.

***
Takawa ya ji zafin maganganun Mahmud sosai da sosai, abun yayi masa ciwo, sai dai ya bar abun a ransa, wani irin takaici ya cigaba da ci masa zuciya, a rayuwarsa ya tsani raini da wulaƙanci, amma Mahmud ya ci masa mutunci haka.

Aliyu ne ya faɗo masa, dan haka ya kira shi, domin jin idan babu wata matsala.

Aliyu sai da ya ɗan ji kunya, ya ce "Tuba nake babban yaya, ni yakamata na kiraka, ya ka je gida?"

Adam ya ce "Lafiya ƙalau, ya mama?"

"Tana lafiya, ta ce za ta yi maka godiya, amma muka tarar ka tafi"

"Ahh haba, ba wannan tsakaninmu, ina fatan babu wata matsala, dan irin yaran nan, ka san suna da nasu yaran, duk da an kama su, kar su cutar da ku, ko kai ko ita da yayi iƙirarin zai kashe".

"Aliyu ya ce babu wani abu, duk muna Lafiya, mutuniyar ce dai ta tatara kayanta wai barin gidan za ta yi, ba a ƙaunarta".

Adam ya ce "What? Ku saka ido a kan ta sosai fa, na fuskanci za ta iya aikata duk abun da ta ce, kar ku je ta yi wani wurin"

Aliyu ya yi murmushi ya ce "Babu in da zata je, mai sunan baba ya tsawatar mata".

Adam ya ce "To Allah ya tsare, ka gaida mutanen gidan"

"Za su ji in sha Allah, a gaishe mana da mai sunan babanmu"

"Zai ji in sha Allah".

Ganin yadda rumaisa ta addabi kanta, ya sanya mama sakkowa daga fushin da take yi da ita, ta yi ta mata nasiha, duk da ta san nasihar tata ba ratsa rumaisa take yi ba, dan za ta iya gama nasihar tana fita tsakar gida, ta ɗora daga in da ta tsaya.
Bayan ta gama yi mata nasihar, ta dubeta ta ce "Ni kuwa rumaisa, ya batun al'ada ne? Tun da ki ka dawo baki yi ba fa, ko kin yi a can hannun ƴan bindigar?"

Rumaisa ta ce "Wace al'adar?"

"Jinin haila mana"

Rumaisa ta ce "Taɓ, ni fa tun da na yi sau ɗaya, na fitsarin jinin nan, ban kuma yi ba, Allah ya yaye mini, shi ma dan wannan mugun mutumin ya watsa mini ruwan kwata ne na yi" mama ta ɗan yi jimm tana kallonta, dama hakan ta kan faru ga macen da ba ta saba yin al'ada ba, amma ta ƙudirce a ranta za ta kai rumaisa asibiti.

Adam yana office ɗin sa, yana tsaye a jikin window yana kallon titi, hannunsa riƙe da kofin shayi, yana ta tunani daban-daban, ƙarar buɗe ƙofar office ɗin ce ta dawo da shi hayyacinsa, ya waiwaya.

Jamil ya gani kamar an koro shi, Adam ya ce "Ya dai? Ya na ganka a haka kamar ba lafiya?"

"Adam da gaske aure zaka yi?"

Adam ya ajiye kofin hannunsa ya ce "In ji wa?"

"Mai girma turaki ne ya sanar da ni"

"Ba yana umara ba?"

"Magana mu ka yi da shi ta video call"

Ya juyo ya fuskanci jamil sosai ya ce "Haka ne, Turaki ba zai yi maka ƙarya ba"

"Amma Adam idan ka yi wa Samha haka ka yi mata adalci kuwa? Meyasa zaka auri wata ba samha ba, ko dan ba ƙanwarka ba ce ba ka san zafin so ba?"

Adam ya shafi sumar kansa ya ce "Ba soyayya nake dubawa ba, makomar ɗana nake dubawa, samar masa da jajirtacciyar uwar da za ta kula mini da shi"

"Kana tunanin akwai wanda zai so ɗanka, ya nuna masa kulawa sama da ita da suke uba ɗaya da Aisha"

"Ba za a rasa ba" ya bashi amsa cikin ko in kula.

Cikin fushi Jamil ya ce "Anya kuwa kana da imani Adam, duk wahala da son da yarinyar nan take yi maka, ba zaka duba ba".

"Jamil, maganar ammi zan ajiye na bi son zuciyata ne?"

"Kana nufin ammi ce ta zaɓi wadda za ka aura?" Abun da Jamil ya faɗa, ya sanya Adam sanin cewa turaki bakomai ya gaya masa ba dan haka ya ce "Ina nufin ammi ma ta yi amanna da Yarinyar"

"Kenan menene makomar Samha?"

Adam ya numfasa ya ce "Da zan iya, da na haɗa su su biyu, sai dai ba zan so gidana ya zama irin gidanmu ba, bana son damuwa, kuma na san dole zan cutar da ɗaya a cikinsu, Samha ƙanwata ce, muna da alaƙa ta jini da ita, zan iya karkata gareta, saboda kusancin alaƙarmu, ita kuma waccan ta yi mini abun da ko duniya zan ba ta ba zan biyata ba, zan iya karkata gareta dan girman halaccin abun da ta yi mini. Sai dai a duk su biyun babu wadda zan gazgata cewar ita zuciya ta ke so, abu ɗaya na sani" ya taka gaban Jamil yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Bana son ɗana ya yi rayuwa irin wadda mahaifiyarsa ta yi, so nake ya rayu a matsayin sa na cikakken ɗa a gidan mahaifinsa, ka san abun da nake nufi".

Ayshercool.
08081012143
PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143.



Cikin tsananin mamaki, Jamil ya kalli Adam ya ce "Me ka ke nufi?"

Adam ya dafa kafaɗar Jamil ya ce "Ba sai mun zurfafa ba, ka san abun da nake nufi, kai ɗan uwana ne Jamil, Samha ma ƙanwata ce, ba na son zumuncin mu ya samu matsala saboda wani dalili, a madadina dan Allah ka bawa Samha haƙuri, ina fatan Allah ya zaɓa mana abun da ya fi alkhairi daga ni har ita"

Daga haka Adam ya fice ya bar Jamil a tsaye da buɗaɗɗen baki.

Ammi kuwa waya suke yi da rumaisa, rumaisa tana ba ta labarin yadda takawa ya fito da Aliyu bayan rigimar da suka yi aka rufe shi, wanda shi Adam ɗin sam bai gaya mata ba.
Ammi ta jinjina al'amarin, tare da yi mata Allah ya kyauta.
Gaba ɗaya rumaisa ba ta san wani abu wai kunyar suruka ba, mama na ta ƙifta mata ido, amma sosai take ta yi wa ammi surutu.

Ammi ta numfasa ta ce "Rumaisa na bayar da saƙo a kawo miki ki ka ƙi karɓa ko?"

Rumaisa ta ce "Laa ashe da gaske yake, na zata shi ya bani, na ce ba zan karɓa ba, bana son wataran yayi mini gori"

"Ahh haba dai, ba zai taɓa yi miki gori ba, duk abun da ya baki ki karɓa ba zai cutar da ke ba, sannan ki din ga yi muku Addu'a a kan lamarin auren nan na ku, turaki na daf da dawowa".

Ita gaba ɗaya ma ta manta da maganar auren, sai yanzu da ammin ta tuna mata.

"To, ammi kin san wani abu?"

Ammi ta ce "Sai kin faɗa"

"Kewar sabir nake yi sosai, daurewa nake yi dan kar na din ga takura muku"

Ammi ta ce "Subhanallah, rumaisa zan ci gidanku fa, ni akwai wani abu mai kama da takura tsakanina da ke, ba ni na ce duk lokacin da ki ke so ki gaya mini a kawo shi ba? Za'a kawo miki shi ranar da babu makaranta, na san shi ma yana kewarki".

Rumaisa ta yi murmushi ta ce "To ammi, na gode sosai ki gaida kowa da kowa"

"Yauwwa ko ke fa, za su ji in sha Allah" Ammi ta katse wayar tana murmushi.

A can falo kuwa, Iman ce take bawa sabir abinci, an fara gwada masa abu mai ruwa-ruwa.

Baba uwani na ta tsokanar iman "Ohh tsakanin uwa da ɗa sai Allah, tsakanin Sabir da iman sai Allah"

Iman ta yi murmushi ta ce "Tsakanin kaka da jikarta ma sai Allah ba"

Baba uwani ta ce "Uhumm kakar da yake yi wa ƙyuya, daga ke sai ammi sai babansa, sai kuma Nusaiba idan ya ga dama, yaro ba ya yadda da kowa"

"Kar ki damu baba uwani, zai yadda da ke ne"

"Mhmm, ni kuwa Iman, ina yarinyar da aka ce ta tsinci yaron nan, Haryanzu tana nan kuwa?"

"Laa tana nan baba uwani, baki taɓa ganinta ba?"

"Oho, yo ni a ina zan ganta ma"

Iman ta ce "Kai haba, ta zazzo gidan nan fa sosai da sosai, ai duk ƙyuyar nan da yake yi, ba ya yi mata, dariya sosai ke ba kya ce shine ba".

Baba uwani cikin son bugun ciki da gulma, ta sake ƙasa da murya ta ce "Ni kuwa wai babba ce ko yarinya?"

"Gaskiya Yarinya ce sosai, dan duk mun girmeta"

"Ikon Allah, ƴar nan unguwar ce kuma? Na ji kin ce tana zuwa gidan nan, ai ni fa ban zaci ma ƴar nan garin ce ba".

"A'a ba unguwar nan take ba, zuwa take yi, amma kwana biyu ma ba ta zo ba".

"Ikon Allah, ni kuwa dan Allah duk ranar da Allah ya kawota ki nuna mini ita"

Iman ta yi murmushi ta ce "Maman sabir, to shikenan in sha Allah" Baba uwani ta yi gaba tana jin alamun nasara.

Tafiyar baba uwani babu jimawa, sai ga Jabir yayi sallama, cikin sauri Iman ta rufe kanta da hula, ta gyara zamanta, tare da mayar da hankalinta sosai a kan Sabir.

Murmushi Jabir yayi, ya ƙarasa kusa da ita ya zauna ya ce "Gashin ake yi mini rowar gani kuma?" Ta yi masa shiru ba ta ce komai ba.

"Talk mana iman, ko miskilanci ne?"

Ta yi masa shiru, ta cigaba da bawa Sabir abinci, Jabir ya miƙe hannu ya ɗauki Sabir, yana ƙure Iman da wani irin kallo, wani irin abu yana fuzgar zuciyarsa game da ita.
Wuyanta yake bi da kallo, ya haɗiye wani irin yawu, ya zaunar da sabir a jikinsa, amma Sabir ya ce bai san zance ba ya sanya kuka.

"Ka bani shi abinci nake ba shi".

"Ba zan baki ba, sai kin kalleni kin amsa mini"

Ammi ce ta fito falon, cikin fara'a ta ce "Jabir, kwana biyu ina ka ɓuya ne?"

Yayi murmushi ya ce "Tuba nake ammi, ayyuka ne suka yi mini yawa sosai"

Ammi ta kalli Sabir ta ce "Rigimamme, kai ba ka gane iyayenka ne, kowa ma ba zai ɗauke ka ba?"

Iman ta tashi daga kan kujerar, ta karɓi Sabir ta bar falon, yadda ya ɗan shagala yana kallon iman ne ya sanya ammi jinjina kai a ranta ta ce "Yaushe wannan lamarin kuma ya kunno kai? Akwai ƙura idan Hajiya Lubabatu ta sani, amma da zan so faruwar hakan jabir ba shi da matsala'

"To ya gidan ya hajiyar taka?"

"Tana nan ƙalau Ammi, na je na duba Mahmud ne, na ji abun da ya faru sam bai yi mini daɗi ba ammi"

Ammi ta nemi wuri ta zauna ta ce "Kai dai bari jabir, lamarin ɗan uwan nan na ku sai addu'a kawai, dan ku din ga yi masa faɗa, yanzu a garin wannan zafin zuciyar ta sa da ya yi masa illla ko ha salwantar masa da rayuwa fa?"

"Kai, ai takawa sai haƙuri, iya masa sai Allan da ya yi shi, amma iya ƙoƙari muna gaya masa gaskiya, sai dai ayi ta yi masa addu'a, Allah ya yaye masa wannan azababbiyar zuciyar"

"To Amin, Allah ya iya mana"

Nan suka cigaba da hira da shi da ammi, sai dai hankalinsa ya fi karkata ga yadda yake jin iman a ransa.

***
Cike da zullumi Samha ke cin abincin da yake gabanta, ba dan yana yi mata daɗi ba, sai domin zullumin abun da Jamil zai zo ya gaya mata, tun da ya gaya mata sun yi magana da turaki adam zai yi aure ta rasa nutsuwarta, so take ya zo ya gaya mata idan har hakan da gaske ne.

"Wai Samha ba zaki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki ci abincin nan ba, sai jagwalgwala shi ki ke yi?"

Samha ta ce "Mama yaya jamil nake jira, hankalina ba zai kwanta ba sai na ji abun da nake son ji".

Ƙanwar Samha, wadda daga ita sai ita mai suna Zainab ta ce "Ni wallahi Samha mamaki ki ke bani, wallahi babu yadda za a yi namiji yayi mini abun da Adam yayi mini na sake kallonsa, ke kam kamar mara zuciya, shiyasa na koma zaman hostel ma na bar miki gidan, yadda ki ke zubar da classic ɗin ki a kan gayen nan yana bani haushi, kamar wani ɗan gold"

"Enough zainab, kar ki sake saka mini baki a maganata, idan ba so ki ke na yi miki rashin mutunci ba".

Mama ta ce "Ya isa haka, ni bana son faɗa, daga dawowarki".

"Mama kin san dai babu yadda za a yi ina ganin gaskiya in ƙi faɗa, Allah ya taimaki soyayyar wahala" ta ƙarasa maganar tana tashi ta bar dining ɗin.

Samha gaba ɗaya ba ta yanayi na yin faɗa, dan haka ba ta tankawa zainba ba ta shareta.

Jamil ne yayi sallama, mama ta amsa masa, Samha kuwa kasa amsa masan ta yi sai bin sa da ido da ta yi.

Ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin jerin kujerun falon.

Samha ta taso cikin sauri, ta ce "Yaya Jamil ya ake ciki ne? Tun ɗazu nake jiranka"

Yayi shiru bai ce mata komai ba, "Yaya magana nake fa"

Ba tare da ya kalleta ba, ya ce "Samha ki na ji na?"

"Eh ina jin ka"

Ya taso ya zauna sosai ya ce "Samha, ina son ki saurareni da kyau, ki yi haƙuri ki cire Adam a ranki, a wannan karon ma ba zai aureki ba, domin kuwa ya tabattar mini da cewa mahaifiyarsa ta zaɓa masa wata matar, kuma turaki na dawowa za a kai masa kuɗin aure"

Ras! Gaban Samha ya faɗi, ta dafe ƙirjinta ta ce "What, again ta sama mata? Iman ko? Iman ce na sani, wai dan Allah me na yi wa matar nan ta tsaneni haka? A wancan karon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login