Showing 132001 words to 135000 words out of 199108 words

Chapter 45 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

836

mini flashing?"

"A'a ba su ƙare ba, bana son ka ɗaga su ƙare ne, kuma ka sake saka wasu, shiyasa na yi maka flashing"

Yayi murmushi ya ce "An taso daga tahfiz ɗin ne?".

"Eh, yanzu na shigo gida ma"

"To shikenan, in ajima zan zo in sake jin haddar. Bari yanzu abinci zan ci"

"To my haidar, ka gaida mama, ka ci ka ƙoshi da yawa".

Rumaisa ta ce "A gaban maman ka ke waya da ƴan mata?"

Daƙuwa ya yi wa rumaisa, ta hau tafa hannaye.

"Yaya Aliyu, habiba ce ta koma sweet hibba?".

"Uban wa ye ya ce miki ita ce"

Rumaisa ta ce "Na rantse da Allah muryar habiba ce, munafuka, habiba take soyayya da yayana, ba tare da tana biyan subcidy ba, dole na je gidansu habiba, mama a gabanki ake soyayya?".

Mama ta ce "Ya ce zuwa za ayi ma ayi masa tambaya, nan da shekara biyu"

Ruma ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Su mai sunan baba ba su yi aure ba sai kai"

"Uban wa ye zai bari kansa ya kulle kamar su? Yaya Abubakar ma kuɗin aure za a kai masa, yana gama service. "

"Innalillahi, yaya Aliyu habiban da ka ke zanewa saboda ni"

Aliyu ya doke mata ƙeya ya ce "Ƴar rainin hankali ba, duk ke ki ka ja, na daki mata ta".

Mama ta ce "Too har an yi auren kenan" da sauri Aliyu ya ɗau plate ya fice daga ɗakin yana dariya.

Wani irin zullumi mai sunan baba ya shiga, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa gane tausayin iman yake ji, ko tashin hankali ya shiga jin wani na neman aurenta, wani irin kishi ne ya taso masa, tabbas ya fi jabir komai, sai dai jabir ya fishi kuɗi, sannan kuma wa iman take so

Yaya usy ne yayi sallama, rumaisa ta tashi da gudu ta tare shi, ta ce "Mussaman saboda kai na zo gidan nan yaya usy".

Ya ce "Ƙarya ki ke yi".

"Wallahi da gaske, zo mu zauna daga nan"

Ba tara da ta bari ya shiga ko wurin mama ba, ta ja shi kitchen ta rufe ƙofa, sannan ta ce "Yaya usy wani abu ne yake damuna, na ga kaine abokin shawarata, na ce bari na gaya maka".

Ya ce "To ina jin ki"

"Yaya usy, dama...dam..mm"

"Wai meye haka ne?"

"Kunya nake ji ne, amma shawara nake nema. Ka ga dama takawa ne kan ya tafi, yake yi mini abun da bai dace ba, kuma"

"Kuma me? Wane irin abu ne da bai dace ba".

"Yaya usy kiss yayi mini kuma, ba zan iya faɗar sauran ba dai, kuma kaga bai dace ba, bana son mama ta gane, ya ce mini wai ai ba komai, in tambaya in ji, wai tun da ihu nake idan ya taɓa ni, zai ƙara aure, kuma ni bana son ya yi mini kishiya. Dan Allah yaya usy ya zan yi, bana son ɓata tarbiyya ta, idan mama ta sani za ta yi fushi da ni, kuma bana son yayi mini kishiya"

Ayshercool.

08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels


Usman ya yi ƙuri da ido yana kallonta.

"Yaya usy ba ka ce komai ba?"

"Ji nake kamar in kama ki in maƙure mini wuya ne".

Cikin damuwa ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri"

"Ke dalla ware malama, ke yanzu duk zaman da ki ke yi, yake baki ci da sha, ya ɗauki nauyin karatunki, shirme kawai ki ke tafaka masa, zuwa ki ke kiyi masa ƙiri-ƙiri da ido, kamar gardi a cikin gida, ke kanki ba zaki taɓa waye ba, abun da aka koya miki baki san idan kin yi aure ki waye ba, sai kayan hauka da rashin hankali"

"Ni fa yaya usy ban gane me ka ke nufi ba"

Usman ya ce "Idan bai yi miki kiss ba, wata zai je ya yi wa a waje?"

"Yaya usy, ku fa ku ka ce mini haramun ne, Allah zai ƙona ni idan na yi"

"Kuma sai aka ce miki har da mijinki? Ai gara ya ƙara auren, kuma ba abun da zai hanamu raƙashewa da bikin, ki je ki yi ta shirmenki" Usman ya tashi ya bar kitchen ɗin.

Ta yi shiru tana tunani, ta yaya haka zai yiwu? Sun ce mata abu babu kyau, yanzu kuma an dawo an ce mata ya halatta ba tare da wani cikakken bayani ba. Ta basar da zancen ta cigaba da harkokinta.

Mai sunan baba kuwa rumaisa ta haɗa shi da assignment mai wahalar gaske, domin kuwa kasa sukuni yayi, maganar ta din ga damun zuciyar sa, ya din ga jin tamkar yayi tsuntuswa ya je ya ga Iman.

Da wayar mama, rumaisa ta kira Mahmud a waya, ta ce ya zo ya ɗauke ta, ta bashi adress ɗin gidan.

Yayyen ruma sun sha mamakin ganin Mahmud, basu san shi, ba sai dai wasu lokutan ta kan yi maganar sa.

Ya fi takawa sakewa da mutane wasu lokutan, dan haka nan da nan ya shiga cikin su Aliyu kamar sun saba.

Rumaisa ta ce "Daddy, ga Yasir, shi ne hacker shi ne ku ka yi waya da shi"

"Ki ka kuma ce mini hacker, ba zan sake yi miki wani abu ba"

Mahmud ya ce 'Rabu da ita, ai ni da kai muke aikinmu" ta nuna masa Abdallah ta ce "Ga masterna a wurin zane-zane, da shi nake koyi, duk da idan na taɓa masa kayan zane, wataran ranƙwashina yake, amma a hakan Alhamdilillah na koya, dan haka shi zai yi mana zane, sonake kan papa ya dawo, mun gama komai"

Ya ce "Lallai team ɗin nan an haɗa manyan ƙwari a cikin sa, Allah ya dafa mana". Mama sam ba ta san a kan me suke magana ba, bayan la'asar sosai, sannan ya ɗau ruma suka tafi gida.

Aikuwa ta sha faɗa a wurin laila, wai ta tafi gida, ba a kira takawa an tambayi izninsa ba, ruma tayi mata banza, irin kan ki ake ji ɗin nan.

Kusan sati guda, laila ta saka ruma a gaba, ta hanata sukuni, gashi ta yi ta mata magana da turanci, komai ruma ta yi sai ta ci gyaranta.
Ta hanata kwana tare da iman, tare suke kwana a ɗaki tare da ita, gashi ta kasa ta tsare ta hanata video call da takawa.
Abu ɗaya ne yake yi mata daɗi, kunun maman Khadija na sabaya da take sha safe da yamma, wannan kam tun da batu ake na ci, ruma tana jin daɗin haka.
Ban da wannan, duk wani wanke-wanke da gyaran fata rumaisa ba so take yi ba.

Rumaisa na zaune tana shan kununta, ita da sabir, dan idan suna sha, kamar ya shiga cikin kofin, ko zama ba ya yi, yana tsaye ayi ta bashi yana lashe baki.

Laila sai video call take da mijinta, ga mijin ya fara manyanta, amma ta shagwaggwaɓe, sai taɓara take, tana ce masa baby, suna wani abu mai kama da iskanci a wurin rumaisa.

Rumaisa har leƙawa take, ta sake kallon fuskar mijin, wai wannan gundumemen mutumin ne baby, 'Taɓ sukumbiya, wai baby taɓ' laila tana jin ta, taƙi kulata, su suke wayar amma ita take jin kunya.

Babu babban abun da yake bata mamaki, kullum da daddare sai sun yi video call, laila ta ɗau kwalliya kamar zata biki, ta sha ƙanan kaya, ta zauna a gaban waya ko system.

Yau kam da abun ya ishi kunnuwan rumaisa, ta saka hannu ta toshe kunnenta. Sai da laila ta gama wayar, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ba zaki iya ba ko, ni ƴar iska ce ni da mijina, shi ne ki ka toshe kunne?"

Ruma ta yi shiru. "Ban ce dole sai kin yi irin nawa ba, ni na yi shekaru a gidan aure, na saba da mijina sosai da sosai, ke nake fatan ki daina wannan shirmen, ki san me ki ke yi" ruma ba ta ji za ta iya abun da laila ke yi ba, a ganinta fitsara ce muraran, ga takura mata da take yi.

Da safe kan ta tafi makaranta, ta karɓi wayar iman, ta kira Adam voice call.

"Budurwata"

"Papa" ta kira sunansa a shagwaɓe.

"Ya aka yi?"

"Ni gaskiya wannan anty lailan ta takura mini, ta yi ta mini masifa, da na motsa ta yi mini faɗa, duk ta bi ta saka mini ido".

Adam ya ce "Haba mimi, baki kira ni kin ji lafiayata ba, sai kawo mini ƙara, ke ma ta ce mini ba kya ji, taurin kai ki ke yi mata".

"Yi haƙuri ya kake?".

"Ban sani ba, tun da baki damu da ni ba"

"In ji wa? To yau saura kwana ɗari da saba'in da biyu ka dawo, calendar ce da ni, kullim sai na yi marking kwanakin da suka rage ka dawo"

Adam ya ce "Wow, lallai kin damu da ni sosai, take care, kar ki makara"

"Ni kar ka kashe"

"So ki ke ki makara a school ko?"

"Hmm ka san me?" "A'a sai kin faɗa"

Ji tayi kamar ta gaya masa zancen kunun da take sha sai kuma ta fasa.

Jin tayi shiru ya sanya ya ce "Akwai matsala ne?".

"A'a"

"To ki shirya a kai ki school kin ji budurwata, sai mu yi waya anjima"

Ruma ta ce "Video call nake so mu yi in ganka, amma wannan anty lailan ta hana, duk abun da zai sani farinciki ba ta so".

Ya ce "nima dokar nan ta isheni gaskiya, mutum da budurwasa a hanasu sakewa"

Ruma ta yi dariya ta ce "To saurayina, sai na dawo, kun gama taron yaushe zaka wuce karatun"

Ya bata amsa da "sai Allah ya kaimu jibi".

Da ƙyar suka yi sallama, ta ajiye wayar ta tashi.

Wata irin kewar adam ce ke sake bijirowa rumaisa, ji take kamar sun shekara ba sa tare, tayi shiru tana tuna abubuwan da suka faru a tsakanin su, daga aurensu zuwa yanzu, a hankali ta yi ajiyar zuciya, ta tashi tana shirin makaranta.

Mai sunan baba kuwa tsayin lokacin nan, kullum sai ya ɗau wayarsa ya ji kamar ya turawa iman message, amma sai ya kasa, ya duba chats ɗin su, ko zai ganta online, amma ya ga sam ba ta fiye hawa online ɗin ba ma, gashi sai yana tsaka da jimami, da tunanin ya zai yi, Aliyu ya zo yana kashe murya yana waya da habiba, wanda ba ƙaramin ƙular da shi yake yi ba.

Mummy ba ta sake nunawa Mahmud fushi ko damuwa a kan abun da yayi ba, hasali ma taƙi yarda su sake ɗaukko zacen, kamar babu abun da ya faru, ta ƙarƙashin ƙasa kuwa, tana cigaba da shirin, sake rusa giwa, saboda ta yi alwashin sai baƙin ciki ya kashe giwa, in dai da ranta babu wani abun alkhairi da zai sameta, babban birinta yanzu bai wuce kassara rayuwar rumaisa ba, kasancewar ita ce babbar barazanar ta.

Ɓangaren Jamil ma, yana ta neman hanyar da zai yi magana da rumaisa, dan ya sha zuwa makarantar su, ya tarar da sidi yana tsaye yana jira, kuma alamu sun nuna babu wanda ya san adam yana zarginsa, dan haka so yake ya tutsiye rumaisa, ya ji me da me ta sani.

Baba uwani ma kullum zaman ɗar-ɗar take yi, a kan kar rumaisa ta tona mata asiri, dan tuni mummy tayi mata fata-fata ta sallameta.

Ammi na ta yi wa iman bayanin cewa Jabir ya ce mata, yana jira mai girma turaki ya dawo, wambai ne zai nema masa auren iman, kuma ya bata tabbacin cewa ya shawo kan hajiya Lubabatu ta amince masa ya nemi aure iman, kuma yayi mata zancen haɗa lefe ta ce masa wannan maganar su ce, su yakamata su tattauna.

Iman da ke shan kunun sabayar maman Khadija, dan ba a bar ta a baya ba, har ita ake sha, dan kuwa kogi bai ƙi daɗi ba, ta sunkuyar da kai tana sauraren ammi, ruma kuwa tana ta game a wayar ammi, kamar ba ta san me ake faɗa ba.

Ammi sai ta yi zaton kunya ce kawai irin ta iman, ya sanya taƙi magana, Nusaiba kuwa sai zaƙalƙalewa take yi, tana tsara yadda biki zai kasance.

Sallamar hajiya Lubabatu ce, ta katse musu hirar, Ammi ta amsa su kuma duk suka bita da kallo.

Ammi ta faɗaɗa murmushin ta, ta saka duk abubuwan da suka faru a baya, mussaman da Jabir ya ce mata ai ta amince da aurensa da iman, dan haka cikin murna ammi ta karɓeta.

Sai dai ta turɓune fuska ta ce "Giwa ba zama na zo yi ba, magana zamu yi dan Allah"

Ammi ta ce "To shikenan, ko zamu shiga daga ciki ne?"

"A'a ba wani daga ciki, magana zamu yi a buɗe a fai-fai. Wallahi giwa ki ji tsoron Allah, idan har kina son gamawa da duniya lafiya, mace sai tsabar son kanki a zuciyarki. Kawai kin juya mini tunanin ɗa, ki rasa da wanda zaki haɗa shi, sai auren ƴar tsintuwar ki, yarinyar da ki ka ce kin san iyayenta, ki ka gaza nuna su har rana mai kamar irin ta yau, kawai dan ki cuceni, wato sarauta ta bar gidanku, idan Allah ya yi jabir ya samu sarautar galadima, kin dai aura masa ita, dan ku mallake shi sai yadda ki ka yi da shi, wato kowa ya rasa, wanccan ba lafiya ce da shi ba, kin san ba sarautar zai yi ba, Mahmud kuma tun da Jamila ce ta riƙe shi, ba zaki bari abun arziki ya same shi ba, tun da ba ke yake yi wa kallon uwa ba, sai ki ka lallaɓa zaki aura mata ɗa na, to ba zai yiwu ba wallahi"

Ammi ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri Lubabatu, ki fuskance ni, Jabir fa shi ya kawo kansa, ya ce yana son iman, ba ni na takura masa sai ya auri iman ba, kuma shi ne ya bani tabbacin lallai kin amince wa auren nan"

"Ni ina na san ana yi, ana ƙulla mini kitimurmura, ina ɗan sarauta ina auren shegiya da aka tsinto, wallahi ƴar tsintuwa ba zata samar mini da zuriya ba, idan ba haka ba a nemo iyayenta a nuna mini"

Tuni jikin iman ya fara rawa tana kuka, rumaisa kuwa ji tayi kamar ta mari iman, ba ta da kataɓus, da an yi mata abu sai kuka saboda tsabar shagwaɓa.

"Lubabatu shi ɗa na kowa ne, iman kuma ƴar ku ce, meyasa lallai sun kun nuna mini, iyakata ne?".

"Ba wani ɗa na kowa ne, idan na kowa ne ki aurawa adam mana, ko dai sarautar ki ka ƙallafawa rai, sai kin mamaye komai, wallahi ɗa na yafi ƙarfin auren ƴar tsintuwa, baƙin halinki ne yake bibiyar ki da yaranki".

Tuni rumaisa ta hasala ta ce "Wai jabir ɗin banza Jabir ɗin wofi, me aka yi aka yi wani Jabir munafiki da shi, ban da ƙaddara ta Allah, ki kalli iman ki kalli jabir ɗin mana, wani sololo kamar an mari ɗan akuya. Wai ku baku da wani buri sai ku zo kuna zagin ammi, me tayi muku?".

"Ke rufe mini baki, ko na zo na talitseki, ƴar matsiyata ban saka da ke ba, sa'arki ce ni?"

Ruma ta ce "Wallahi talitseni, dai-dai yake da taka kan ɗan maciji, baku da magana sai ta sarauta, fir'auna ma ya mutu ya bar mulki, dan abun kunya, mijinki na can na jinya, ke da ɗan ki kuna nan kuna fafutuka a kan wata sarauta, wannan ne abun alfahari dan za a aure shi? Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, wallahi jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ai ni idan mutum babban banza ne, bana ganin girmansa, tun ranar da muka je gidanki, ki ka ci mini mutunci nake ƙullace da ke"

Ammi jikinta har rawa yake, ta ce "Rumaisa ya isa haka, ku tashi ku shiga ciki" dan ammi ba ta taɓa ganin ruma tana asalin tijara ba sai yau.

Laila ta ƙaraso falo ta ce "Ammi su shiga ciki su je ina? Rumaisa kin yi mini dai-dai, ai asara na ga matar da ta wofantar da mijin da ya gatantata lokacin yana da lafiya, yana ƙasar waje yana jinya, tana nan tana shirme a gari, ita da ɗan ta mara tarbiyya.
Ƴar wahala, tun da na sanki Lubabatu baki da alƙibla daga ke har Mummy, shiyasa rayuwa ta ƙi yi muku yadda ku ke so, kuma albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da alƙur'ani, cigaba yanzu muka fara"

Ruma ta ce "Kuma in sha Allah, sai na dawowa da ammi Mahmud"

Laila ta ce "Dan Allah malama kwashi banzayen ƙafafuwan ki, da aka saba bin bokaye, a bar mana part, kar a zuba mana masifa".

Hajiya Lubabatu ta nuna kanta ta ce "Laila har da su kaza a cin danƙo, ni ƴar riƙo za ta gayawa magana haka".

"Ƙwarai ƴar riƙo ba, ko nima zaki ce mini shegiyar ne? Ke sa'a fa ki ka ci, Jabir yana girmamani, da wallahi ashar zan ɗuɗɗura miki, zaki iya fita"

Su biyun duk suka ƙureta da ido, ba wanda ya fi ɓata mata rai, irin cin mutuncin da rumaisa ta yi mata.

"Giwa a gabanki sirikarki suka ci mini tuwo ko, duk saboda wannan yarinyar, na faɗa ba zan bari ɗa na ya auri wannan yarinyar ba, da ban san asalinta ba, wanda ba na raba ɗaya biyu, ƴar gaba da fatiha ce, kuma zaku ga abun da zai biyo baya" ta fice tana huci.

Bayan fitarta, Ammi ta kalli laila ta ce "Laila mey....."

"A'a Ammi, daga ni har rumaisa ba wanda yayi laifi, nima fa ba son aurenta da jabir ɗin nan nake yi ba, saboda duk wani abu da ya shafi mummy, bana ƙaunarsa na tsani matar nan kamar yadda na tsani mutuwata, ke kuma iman, idan aka kuma zuwa ana gaya miki magana, ki ka ɓare baki kina kuka, ubanki zan ci, sokuwa kawai komai kuka, bayan kin san larurar da ki ke ɗauke da ita".

Jikin Nusaiba duk yayi sanyi, ita dai tana yi wa iman sha'awar auren jabir, amma halin mahaifiyarsa ne sai a hankali, kuma wani point da ruma ta kawo abun dubawa ne, mutumin da mahaifinsa yake ƙasar waje yana jinya, an bar shi shikaɗai sai mai kula da shi, tilon ɗan sa namiji kuma yana nan yana gararambarsa.

Sai dai ba a fi mintuna arba'in, da tafiyarta ba, wambai ya kira ammi a waya.

Suka gaisa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login