Showing 6001 words to 9000 words out of 199108 words
babu walwala, ruma sai da ta ɗan tsorata ta yi zaton ko ƙarar ta ta maman su habiba ta kawo, amma bayan tafiyarta ta ji shiru mama ba ta yi mata faɗa ba.
Amma gaba ɗaya maman ta sauya, damuwa sosai ta bayyana a kan fuskarta.
Rumaisa ta ce "Mama ƙarata a ka kawo miki ne? Wallahi ban yi wa kowa komai ba"
Mama ta ce "A'a ba ƙararki aka kawo ba"
"To menene, na ga ba kya son yin magana"
"Bakomai".
Gaba ɗaya suka lura da yadda mama ba ta walwala, duk wanda ya tambayeta menene sai ta ce bakomai, mai sunan baba kawai ta iya gayawa abun da yake damunta.
Washegari da safe, bayan tafiyar rumaisa makaranta, jikin mama ya tashi, sai da aka kai ta asibiti likita ya dubata, sannan suka dawo gida.
Kusan kwanaki biyu kenan mama babu lafiya, babu walwala har rumaisa ta fara koke-koke.
Cikin ƙarfin hali mama ta ce "Ba zaki yi mini Addu'a ba sai ki sakani a gaba kina kuka?"
"To ba kin ƙi gaya mini abun da ya same ki ba?"
Mama ta ce "Ai na ce miki bakomai, amma shikenan tun da ba zaki yi mini Addu'a ba".
Rumaisa ta cigaba da kukanta, yayin da mama ta samu bacci. Wayar mama ce ta fara ringing rumaisa ta ɗaga sai ta ji muryar ammi.
Suka gaisa ammi ta ce "Rumaisa ina maman taki?"
"Bacci take ba ta da lafiya"
"Subhanallah, meya sameta?"
"Taƙi gaya mini" Rumaisa ta yi maganar tana fashewa da kuka.
"Ya salam, yi haƙuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta ji sauƙi, ki daina kuka kin ji ko?"
Rumaisa ta amsa da "To".
Lokacin islamiyya ya yi aka gama girki, rumaisa ta ga abincin ba nama ba kifi, ba salak, ta ƙi ci, ta je ta shanye youghurt ɗin da aka sai wa mama ta kasa sha. Ta saka uniform ta tafi islamiyya.
Da yamma ta yi suka dawo daga islamiyya, mai wanke-wanke ya kama, mai ɗora girki ya ɗora.
Rumaisa na yin sallama ta tsaya a tsakar gida ta ce "Me nake ji haka kamar warin daddawa?"
Huzaifa ya ce "Mama ce ta ce tuwo take sha'awa, shi za ayi yau".
"Taɓ mama ba ta da lafiya amma ta rasa mai za ta ci sai tuwo?"
Abdallah ya fito daga kitchen ya ce "Uban me ya hana ki cin abincin rana?"
"Abinci ba kifi ba nama, ba salak kawai tsuransa ni ba na ci"
"Iyeee ashe da gaske Huzaifa yake, ɗazu mai sunan baba ya tambayi abincin waye Huzaifa ya ce naki ne kin ce ba zaki ci ba ba kifi ba nama, ya ce zai gamu da ke idan ya dawo"
"Ku dai kullum burinku ku ga mai sunan baba yana tagayyara ni, ai shikenan"
Ta shiga ɗakin mama da sallama, "Mama ya jikin?"
"Da sauƙi, shi ne ki ka ƙi cin abinci ko ruma, ke idan baki samu abun da ki ke so ba ba zaki ci ba ko?"
Rumaisa ta girgiza kai ta fara cire kayanta.
Sallama aka yi mama ta amsa, rumaisa ta shiga uwar ɗakin mama da gudu, dan ta tuɓe daga ita sai phant za ta canza kaya.
Ammi ce ita da iman da Nusaiba, iman na rungume da Sabir.
A gurguje rumaisa ta canza kayan ta fito tana tsalle.
"Oyoyo yau ammi ta zo gidanmu"
Murmushi ammi ta yi tana faɗin "Ƴar gidan ammi, maman sabir"
Ta durƙusa ta gaida ammi, ta amsa mata cikin sakin fuska.
Mama ta ce "Bisimillah ku zauna"
Suka zauna su Nusaiba suka gaida mama, mama ta amsa musu cikin sakin fuska.
Ruma ta ce "Ammi ya aka yi ki ka san gidan nan?"
"Baban sabir ne ya saka yaronsa ya kawo mu, na ce bari mu zo duba mara lafiya"
Ruma ta fita da sauri, ta samu plate ta zubo musu ruwa, ta kawo musu tana ta murna.
Mama ta bi ta da kallo, ta tuna iskancin da ta yi da adam ya zo gidan.
Ammi ta ce "Ke maman sabir ya ki ka bar ƴan maza da aikin gida?"
Ruma ta ce "Idan na yi gwaleni za su yi su ce bai fita ba, shiyasa nake bar musu aikin su. Ammi wannan wacece?" Ta yi maganar tana nuna iman.
"Ƙanwar takawa ce, ita ce ƴar autana"
"Tubarkallah mai kyau da ita" iman ta yi murmushi ta ce wa ruma "Ina wuni?"
Ruma ta zaro ido ta ce "Kai ki ka gaishe ni, ni fa yarinya ce, kin ma fini tsawo". Dariya suka yi mata ammi ta ce "Ki daina gaya musu kar su raina ki, ai kin girma tun da ke maman sabir ce" ruma ta yi dariya ta ce "Eh kuma haka ne, ai kunya na ji da ta gaishe ni".
Ammi ta ce "Yau ba zaki ɗau sabir ɗin ba?"
"Hmm, ai da ni na yi zuciya na ce ba zan sake ɗaukar sabir ba, baki san me babansa ya yi mini ba ne"
Ammi ta ce "Subhanallah, me ya yi miki?"
"Ƙyaleshi kawai ammi, ai ba zan iya zuciya da sabir ba, a bani masoyina na ganshi" ta ɗauke shi a hannun iman, ya cika hannu, suma baƙa ƙirin ta cika masa kai. Suna cikin magana mai sunan baba ya yi sallama.
Wata irin razana iman ta yi da ya shigo ɗakin, wanda ita kanta ba ta san dalilin razanar ba.
Ya risuna ya gaida ammi, sannan ya tunkari rumaisa, ya durƙusa ya riƙe mata kunne ya ce "Abinci ba kifi ba nama ba zaki ci ba ko?" Ya ajiye mata leda a gabanta ya ce "Ki kai musu su dafa miki wani abun, dan yanzu ma sai ki ce yayi sanyi ba zaki ci ba, tuwo ma ki ce ba zaki ci ba, ki yi ta wahalar da mutane babu dalili". Ta sunkuyar da kai ta ƙi magana. Ya dungurar mata da ledar ya sanya hannu ya ɗau sabir a kan cinyarta ya yi waje.
Ammi ta din ga murmushi, gaba ɗaya rayuwar rumaisa burge ammi take yi.
Kifi ne manya ya kai na dubu, mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, ta tashi cikin murna ta tafi kai wa su yasir su yi mata wani girkin bisa umarnin mai sunan baba.
Ammi ta dubi mama ta ce "Amma dai kamar akwai wani abu da yake damunki, bayan rashin lafiya ma"
Mama ta ce "A'a, jinina ne ya hau"
"A tunanina zuwa yanzu mun zama ɗaya, dukkanninmu iyayene, masu fuskantar matsalar iyali kala-kala, dan Allah idan wani abu ne ke faruwa kar ki ɓoye mini ko ba zan yi wani abu a kai na yi addu'a"
Mama ta nisa ta ce "Babar ƙawar rumaisa ce ta zo, take gaya mini maƙwabtana na ta yaɗa jita-jita, wai rumaisa ciki ta yi, na kaita garinmu ta haihu, muka ce wai saceta aka yi, wai Allah ne kaɗai ya san yadda muka yi da ɗan"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maƙwabta kuma?"
"Wallahi kuwa shi ne abun ya dameni, wai abun ya cika unguwa, sun ɓata mini sunan ƴa, na san rumaisa ba ta ji, amma ko kusa komai zaki yi wa rumaisa ba ta san hanyar lalacewa ba, balle ta yi ciki".
Ammi ta ce "Wallahi ba sai kin faɗa ba, duk wanda ya ji maganar nan ya san son rai ce, ki yi haƙuri basu isa su ɓata mata suna ba, duk wanda yake son ta da gaske jita-jita ba zata hana shi aurenta ba, ki kwantar da hankalinki kuma kar ki bari ta sani, tun da da bakinta ta ce mini duk wanda yayi mata abu sai ta rama" shigowar rumaisa ɗakin ce ya sanya ammi sauya maganar.
Suka miƙe zasu tafi, rumaisa ta ce "Ammi, an ɗora mana abinci fa, ku tsaya a gama"
Ammi ta ce "Tuba muke, muna sauri ne, ayi haƙuri" rumaisa dai ba haka ta so ba.
Suka fito zasu tafi, mama ta ce ina ga mai sunan baba yana waje da sabir.
Suka fito aikuwa yana wajen, ammi ta ce "Iman karɓo sabir"
Jikinta har rawa yake yi, saboda gaba ɗaya mai sunan baba tsoro yake bata.
Kamar munafuka sai sunkuyar da kai take, ta miƙa hannu za ta karɓe shi, amma shiru bai bata shi ba.
Sai da ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, gabanta ya sake faɗuwa, har numfashinta ya tsaya na wucin gadi.
Ganin yadda ta tsorata ta rikice, sai da ya bawa mai sunan baba haushi, shi ba dodo ba meye na wani tsorata.
Ammi ta saka sidi ya buɗe booth, ya ɗebo cartons na lemo da kayan marmari, na dubiyar mama.
Ammi ba ta tsaya ba, dan ta san mama cewa za ta yi yayi yawa, suka shiga mota suna ɗaga musu hannu.
Tun da suka tafi ammi take saƙawa da warwarewa a zuciyarta, dole mama ta shiga damuwa, babu uwar da za ta ji daɗin a ɓata sunan ƴa a cikin unguwa dan wannan kawai sai ya hanata auruwa.
Suna tafe Nusaiba da iman na ta yi wa rumaisa dariya, yadda take gudanar da al'amuranta da yadda yayyenta ke kula da ita.
Tun a hanya ammi ta kira adam a waya, ta ce idan an yi sallar magariba tana son ganinsa.
Kamar yadda ta buƙata ya je ya sameta, ta idar da salla tana lazumi, bayan ta kammala ta dube shi ta ce "Mai ka yi wa rumaisa ne? Take cewa da tana da zuciya ba zata sake ɗaukar sabir ba?"
Ya kalli ammi ya ce "Wani abun ta ce na yi mata ne?"
"Ba ta ce ba, amma abun da ta faɗa ya tabattar mini da wani abun ka yi mata"
"Ba wani abu bane ammi, na mata gargaɗi a kan zuwa gidan nan ne? Idan aka fuskanci wacece, za'a iya ƙoƙarin citar da ita ko cutar da sabir ta hanyar ta".
"Na ji, yanzu ba wannan ba ma, wata shawara na yanke a matsayina na uwa na kira ka na sanar da kai, ba dan kana da hakki a kan abun ba ma sai dai ka ji na zartar".
"Wane hukunci kenan?"
"Ina son ka auri rumaisa!!!"
Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
*Littafin kuɗi ne, ₦500 ne via 0009450228 sai shaidar biya ta 08081012143, aisha adam jaiz bank, masu buƙatar vip kuma, zasu iya zuwa arewabooks su yi searching sunan littafin*
Waro ido adam yayi yana kallon ammi, yana tunanin ko haluccinations ɗin da ya saba ne ba gaskiya bane, ya tsatstsare ammi da ido.
"Ba ka ji me nace bane kake kallona?"
"Amm..mmm wai wace rumaisa?"
"Rumaisa dai ta zo da sabir, ita nake nufi"
"Amma ammi nan da shekara nawa?"
Ammi ta ce "Nan da abun da bai fi watanni uku ba in Allah ya kaimu"
Adam ya ma rasa me zai ce, "Amma ammi yarinya ce ƙarama, me ta sani a kan rayuwar aure? Ta yaya zan yi rayuwar aure da ita"
"Saboda kai abu ɗaya ka saka a gaba a zamantakewar aure ko?"
Da sauri cike da jin kunya ya ce "No, ammi ba abun da nake nufi ba kenan, amma meye manufar yin hakan?"
Ammi ta numfasa ta ce "Ɗazu muka je gidan su, mahaifiyarta babu lafiya a dalilin jita-jitar da ake yaɗawa, wai ciki ta yi aka kaita ta haihu, ni uwa ce na san raɗaɗin irin wannan abun. Abu na biyu kuma a duniya na san babu wata mace da zaka aura ta riƙe sabir da imani da amana kamar rumaisa, ba zan so sabir ya yi rayuwa irin wadda mahaifiyarsa ta yi"
"Amma, Ammi yarinyar nan ta daɗe a hannun ƴan bindiga, Allah ne kaɗai ya san abun da suka yi mata tsawon wannan lokaci"
"Ko sun yi mata wani abu, kai yakamata ka yi shahadar aurenta, ko dan albarkacin abun da ta yi maka. Sannan ka san dole za a saka mana ido, a fara zancen ka yi aure, ko ma ace gashi an baka mata, wanda idan aka baka bamu isa mu ce a'a ba. Dan haka kafin su motsa mu zamu motsa, idan ya so ko wani auren ne ka yi daga baya, amma ina son ka auri rumaisa ka inganta rayuwarta, ta yi karatu mai kyau mai zurfi, ka ciyar da ita abinci mai kyau, ta kwana a muhalli mai kyau, ba zamu biyata abun da ta yi mana ba, amma zamu iya kyautata mata".
Adam ya ja wani irin gwauron numfashi, dan ya san akwai ƙura, ita kanta rumaisan ba lallai ta amince dan ta ce a duniya ba wanda ta tsana kamarsa.
"Ka yi shiru ba ka ce komai ba"
"Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi".
"Amin ya Allah, Ubangiji Allah ya yi maka albarka, Allah ya sanya ta zame maka alkhairi a cikin rayuwarku" jinjina kai kawai ya yi, bai iya amsawa ba ya tashi tafi.
Tun da ya fita kansa har wani zafi yake yi masa, saboda tsabar caji da zafi, kamar shi ya auri wannan fitsararriyar yarinyar da take iƙirarin ta tsane shi. Lokaci ɗaya ya tuna yadda ƴan bindiga ke cin zarafin mata a hannunsu, Allah ne kaɗai ya san meyafaru da ita, duk da likita bai faɗi wani abu da ya shafi hakan a kanta ba lokacin tana asibiti, amma duk da haka ba shi da tabbas.
Har lokacin kwanciya baccinsa yayi, ya nemi wuri ya kwanta, bacci ya gagare shi, tunani kawai yake yi, tayaya zai zauna zaman aure da wannan fitsararriyar yarinyar mara kunya, wadda ko magana ba ta iya ba, shi ga saurin fushi da zuciya tsaf zai ɓallata wataran. Baya son bijirewa ammi, sai dai har ga Allah amsa matan da ya yi ba har zuciyarsa bane ba, dan shi auren rumaisa a wurinsa zai ƙwaru da yawa.
Shi a rayuwarsa ba shi da sha'awar zama da mace sama da ɗaya, sakamakon irin zaman da ya tashi ya ga yana yi a gidansu, ba ya son ɗan sa ɗaya ya tashi a irin yanayin da suka tashi na makircin matar uba. Hakazalika ba zai so ya zauna da mata biyu ya ƙwari ɗaya ba, ga uwa uba kishi da tashin hankalin mata shi ba zai iya ba, abubuwan kansa sun isheshi.
Auren rumaisa kuma a yanzu gara zamansa a haka ba mace, ina amfanin yayi aure da matar da babu duk ɗaya, sai ma da yayi raino, dan wannan raino ammi za ta ɗauko masa, tun da ta ce ya kula da cin ta shan ta da makarantar ta, ban da haka shi bai ga mai rumaisa za ta tsinana a gidan aure ba.
A hankali ya lumshe idanunsa ya na son bacci ya ɗauke shi, saboda tarin matsalolin da suke kansa, sun sanya har wani zafi cikin kansa yake yi masa.
Yayi ta karanto adduoi, a hankali bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukarsa, cikin barcin ya ji muryar rumaisa da kan yi masa gizo tana faɗin "Sarki mai koriyar alkyabba ka ɗanani a kan doki" da ire-iren maganganun ta, suka dinga kai komo a kunnensa.
A hankali ya buɗe ido, haryanzu ya kasa daina mamakin yadda rumaisa take yawan yi masa gizo. Ya canza bugiren da yake kwance yana karanto adduoi, a take wani baccin yayi awon gaba da shi, sai dai a wannan karon aisha ya din ga mafarki, mafarkin ƙarshe da yayi da ita ya ɗan razana shi, aisha ya gani tana ce masa.
"Takawa, dan Allah ka bawa rumaisa ɗan ta, kar ka ɗau hakkinta, bana son wata damuwa ta sameta, ita