Showing 105001 words to 108000 words out of 199108 words
neman abun da zai riƙe ya samu sassauci, makaranta wasu lokutan sai dai a jingine ta.
Sashin Ammi ya zama wurin faɗi tashin yara, wannan ya shiga wannan ya fita, ta koya musu karatu, ta yi musu girki, mai assignment ta yi assisting ɗin sa. Mummy ta yi ta jawa iyayen yaran kunne, a kan su yi hankali da yaransu, kar mahaukacin ɗan ta ya kashe musu ƴa ƴa, amma yaran sun riga sun shaƙu da ita.
Idan har Mahmoud yana hutu, Mummy ta din ga kitsa masa abun da zai je ya gaya wa galadima takawa ya yi masa, idan ya gaya masa, ba bincike haka zai hau Adam da faɗa, har ta kai ammi ta ce masa, kar ya sake hantarar mata ɗa, da wanne za su ji? Rashin lafiyarsa ko faɗan da yake yi masa.
Dan haka a duk lokacin da Adam ya san Mahmud yana nan, ba shi da sukuni, saboda faragabar abun da zai je ya ce ya yi masa, kuma hakan ya sanya Adam ya tsani Mahmud sosai da sosai.
Adam ba ya jin daɗin hantarar da ake yi masa, mussaman idan aka shiga da shi taro.
Kasancewar da shi da Aisha, da Iman, ƙaddarasu na kamanceceniya, ya sanya ba shi da wanda yake ƙauna sama da su.
Ya dai girmesu sosai, amma ya na jin daɗin rayuwa da su, a haka ɗan wani attajiri ya ce yana son laila, ba yadda Mummy ba ta yi ba, a kan kar abun ya yiwu, amma hakan ya ci tura, laila ta yi aure ta bar ƙasar.
Daga baya Mahmud ya samu labarin, Ammi ce ta haife shi, amma bai taɓa jin hakan a zuciyarsa ba, a ganinsa da ita ta haife shi, Meyasa ba ta son sa sai wannan Adam ɗin.
Idan ciwon Adam ya tashi, daga Ammi sai Aisha ko Iman, suke iya zuwa wurinsa, duk da ya taɓa ɗaga Iman ya yi cilli da ita, sai da ta suma, amma tana farfaɗowa ta fara kiran kakawa, lokacin ba ta gama iya faɗan sunan sa ba.
A lokacin iman ta yi ta rashin lafiya, aka kasa gane me yake damunta, sai da ƙyae, wai zuciyar ta ce take kumbura, Ammi ta tashi hankalinta, tana tunanin ko tsangwama ce ta sanya ta haɗu da ciwon zuciya da ƙuruciyarta.
Kwatsam rannan galadima ya yanke jiki ya faɗi, ya fara rashin lafiya, nan ma Mummy ta ce Ammi ce, ƙarshe dai Ammi ce ta yi jinyarsa, sai da ya kusa rasuwa, ya din ga neman yafiyarta, da ta takawa, dan bai san yadda aka yi, ya din ga wasu abubuwan ba.
Ɗa da uba sai Allah, bayan rasuwar galadima, Adam ya yi kuka, ko ba komai mahaifinsa ya nuna masa ƙauna, a baya, Mahmud ma ya ɗimauta da wannan babban rashi da aka tafka a gidan sarautar.
Mummy ta din ga dariya, dan ta san dai ba za a bawa takawa sarauta ba, na farko yaro ne, kuma ga larura. Dan haka ɗaga likkafar mahaifin jabir ya zama galadima.
Tana ta murnar tun da Adam ba shi da lafiya, nan gaba ko za a bayar da sarauta, ɗan ta za a bawa Mahmud, amma aka tunatar da ita, yanzu babu Galadima, giwa za ta iya duk mai yiwuwa ta karɓe ɗan ta, dan haka ta ce dole ayi biyu babu, ya din ga kwaɗaitawa ƙawarta Lubabatu, ɗan ta jabir yayi mulki, nan gefe tana kuma turawa Mahmud ƙiyayyar Adam tare da tura masa son mulki, amma sai dai sam, shi kamar mahaifinsu ne, bai damu da sarautar ba, duk da Adam ya fi gado kamanni da murɗaɗɗen hali na mahaifin su.
Adam yana girma ciwo yana ɗan raguwa, dan a haka yayi karatu, abu ne mawuyacin ciwon ya tayar masa a waje, Sai a gida.
Ya shaƙu da Nusaiba da Iman sosai, musamman iman da yake ganinta kamar wata ƴar ƙaramar mage mai kyau, ya cafata nan ya cafata can, sai dai duk da hakan suna girmama shi sosai dan akwai tsare gida.
Gefe guda, Samha ta ƙallafa rai, tana ta nuna masa so, amma mahaifiyarta ta dankwafeta, saboda rashin lafiyar Adam.
Yayin da shi kuma ya fi karkata, ga Aisha, duk a lokacin bai san son ta yake yi ba, muraran Samha da mahaifiyarta, da kuma ƴan uwanta ke nunawa aisha ƙiyayya, ganinta suke kamar ba ƴar uwasuu ba, mussaman yadda turaki yake tausayinta, komai sai ya ce 'yar marainiya. Sanin sassauci ta sai idan Adam ya je gidan ya ɗaukkota, ko Ammi ta aika a ɗauko mata ita.
Abubuwan da suke yi wa Aisha, ya sanya Adam ya fara tsanar mahaifiyar su Samha, Saboda ganinta yake muguwa kamar Mummy, saboda waɗan nan dalilan Adam yake jin ba zai iya auren mace sama da ɗaya ba, idan uwar ɗa ta mutu kuwa, ya ce majaifiyarsa zai bawa riƙon ɗan sa, babu wanda zai bawa riƙon ɗan sa.
Tun Samha tana ɓoye son da take yi wa Adam, har ta fito muraran, shi kuma sam ba ta ita yake yi ba.
Maman Samha ta shiga ta fita, ta na son a aurawa wani ƙaninta Aisha, Turaki ya ce ba zai bayar ba. Abun ya ƙular da ita sosai da sosai.
Babu tsammani, Ammi ta je ta samu wambai, yayan Sharif ta roƙe shi ya nemawa Adam auren Aisha.
Aka yi ta surutu, wai za ta aura wa mahaukacin ɗan ta marainiya, dan zalinci, Aisha ta ce ta ji ta gani.
Ammi ta yi haka ne, dan Aisha ta samu sassauci, saboda azabtarwa da ake yi mata, kuma turaki ya ƙi ya mata ita gaba ɗaya.
Samha tamkar za ta yi hauka, ta tsinewa Ammi da Aisha ba ta san iyaka ba, ta kuma lashi takobin ganin bayan Aisha, ta ƙuduri aniyar ko da bala'i sai ta auri Adam.
Mummy ta ja ta a jiki, ta din ga rarrashin ta, tare da zigata da bata goyon baya ɗari bisa ɗari.
Ayshercool.
08081012143
What's app only please
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Da fari saboda dagewa da neman magani, Adam ya ɗan samu sauƙi, dan ya kammala karatu ma, ya samu aiki a hukumar DSS, kuma ya shiga aiki da ƙafar dama.
Yanayin larurar Adam, da abubuwan da suka faffaru da shi, ya sanya mai martaba yake matuƙar jan sa a jiki, da kwantar masa da hankali, haka zalika turaki da galadima, iyayen nan maza duk suna ƙaunarsa, kusan halinsa ɗaya da mahaifinsa, amma har ya fi babansa taurin kai wasu lokutan, amma akwai ɗa'a da ladabi.
Hakan bai ishi Mummy ba, ta din ga bi wurin matayensu, tana ɓata Ammi da ƴaƴanta, da har sai da wasu suka fara jin haushin Adam a cikinsu.
Bayan auren sa da Aisha, ciwo ya cigaba da tashi lokaci zuwa lokaci, sannan kamar yadda ammi ta din ga yi, haka Aisha ta din ga ɓari, ciki ba ya zama a jikinta, ga ƙannensa suka sakata a gaba, su je har gida su yi mata rashin hankali, su ci zarafinta ga Samha ma a gefe ta sakata a gaba, da makirci da sharri kala. Sannan still daga can gida mahaifiyar su samha ma, ba ta ƙyaleta ba da sharri, da haɗata da Turaki, wai ba ta ɗauke ta uwa ba, komai sai dai ta yi ita da giwar galadima.
Idan Aisha ta samu ciki, da zarar zai zube, sai ta yi magafrki da adam, yazo mata da dogayen haƙora, da kuma farata ya kafa kai a mararta, sai dai da safe ya tashi da zubar da jini.
Adam bayan shigarsa Dss akwai cakwakiya daban-daban, sai dai ya tsaya kai da fata a kan gaskiya, ba ruwansa da cin hanci, da shi da Jamil suka shiga aikin, amma ya fi Jamil karatu, dan haka rank ɗin sa ya fi na Jamil.
Akwai aiki da ƙoƙari, hakan ya sanya shi zama sannane, mussaman da yake kama da mahaifinsa sosai.
Bashi da aiki bankaɗa, da tonawa mugwayen ƙasa asiri. A tone-tonensa, ya tono Usman wakili, da irin yadda yake yi wa ƙasa ɓarna, ya sako shi a gaba, a hukumar wasu suka goya masa baya wasu kuma suka ƙi.
Ba ƙaramin ragewa wakili mutuncin yayi a idon mutane ba, ya cigaba da fafatawa, amma aka ƙi bashi goyon baya, a hukunta wakili. Shi kuma yaƙi sakin aikin, ya cigaba da bin diddigin sa, babu irin jan kunnen da ba a yi wa Adam ya ƙi ji.
Ya koma ya bankaɗo wata tawaga, da suke yi wa kansu laƙabi da SMOKE, sai dai an kasa gano suwaye a ƙungiyar smoke, sai dai ana ganin miyagun ayyukansu, duk wani shige da fice na miyagun kwayoyi, da makamai ta hanyar da ba ta dace ba, suna da hannu a ciki, za kuma kaga tambarinsu na hayaƙi, an rubuta THE SMOKE.
Bincike a kan Smoke, ya sanya ya sararawa wakili, bai kuma waiwayar wakili ba, sai da ya ji ƙishin walili zai tsayar da ɗan sa takarar senator, shi kuma za a ɗauke shi vice president, su yi takara, da ɗan takarar da zai tsaya shugabanci ƙasa.
Wannan dalilin ya sanya, Adam sake saka wakili a gaba a karo na biyu.
Nan da nan sunan Adam ya shahara, shi ma ya haɗa tasa tawagar, da lauyoyi, da ma'aikatan Efcc, da ƴan jarida da suke da burin yi wa ƙasa aiki saboda Allah.
Iman kuwa tun kan ta kai shekaru goma, take samun masu cewa suna riƙo.
Iman tana girma samari kamar me, nan ma Mummy ta ƙwafe a ranta, ya sake mayar da jita-jita a kan Iman sabuwa dal. Na cewa shegiya ce ba wanda ya san iyayenta.
Saurayin babbar ƴar Mummy, Surayya, Wambai ya haɗata da wani babban mutum, amma yana ganin Iman ya ce shi nan duniya wannan jar yarinya yake so.
Ƙarshe dai aka yi biyu babu, Surayyan ta yi aure, amma Mummy ta kai sunan Iman wurin bokansu.
Manyan mutane duk wanda ya ce ya na so, sai ace masa shegiya ce, sai zance ya lalace, a ƴaƴan mai martaba, ɗaya shi ma ya liƙe Iman yake so, Mummy sai da ta yi dalilin da ya sanya, babar yaron ta hana zuwa da iman gidan. Yawan gorin da ake yi mata, ta daina shiga cikin mutane.
Ammi tana tausayin Iman, ga larura ga tsangwama.
Iman ba ta da wata ƙawa, kullum tana manne da Ammi, ko Nusaiba, sai kuma uwar ɗakinta Aisha matar takawa.
Duk wannan abubuwan, Ammi ba ta taɓa nunawa Mummy wani abu ba, kuma ba ta saka wa zuciyarta wai wani ne yake yi mata wani abu, kawai ta saka wa ranta jarabta ce daga Allah.
Sai dai har a lokacin Ammi ba ta daina son ɗan ta ya dawo gareta ba, ta kasa jurewa ta je ta sanar da wambai, dan Allah ya shiga lamarin gidansu, ya sasanta mata yaranta, ko Mahmud ba zai dawo hannunta ba, ya din ga zuwa in da take.
Wambai ya yi ta faɗa ya ce laifin Mummy ne, da ta raine shi a haka, amma ta nuna ita ba laifinta bane, yayi musu sulhu, amma suna zuwa gida, ta sake hure masa kunne.
Cikin ikon Allah, Iman kan ta yi candy, wani ƙanin abokin Adam ya fito zai auri iman, ɗan babban gida ne sosai da sosai, aka saka rana tana kammala sakandare ayi biki, ta cigaba da karatu a gidansa, dan Ammi ta fara tsorata da mazan da suke bin Iman.
Adam kuma shekara huɗu da aure, ciki ya gagara zama a jikin Aisha, ciki na ƙarshe da ta samu, Ammi suka yi shawara a kan Aisha ya je ta yi rainon cikin a saudiyya, wurin wani wan Ammi da yaki zaune a can shi da matarsa.
Ya ce karatu za ta tafi ƙarowa ƙasar waje, aka din ga surutu a kai, ya ce babu mai tsara masa rayuwarsa, tun da matarsa ce.
Iman kuma watan da za a yi biki, wanda zai aureta ya aiko a karɓar masa kayan aurensa wai ya fasa.
Hankalin ammi ya tashi, ta aika a tambaye shi dalili, iyayensa suka ce su manyan mutane ne a ƙasa, ba za su karɓi sirika da ba ta da asali ba.
Ammi ta sha kuka, laila da ba ta ƙasar ma, abun ya baƙanta mata rai, ta cewa Ammi visa za ta yi wa Iman, a tura mata ita can, Ammi ta ce ba mai rabata da ƴar ta sai mutuwa ko aure.
Ammi ta yi shawara da baba uwani, a kan ta bata shawara ko ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, dan ta lura wannan mugun tabon da Mummy ya yi mata, ba zai bari ta auru ba, baba Uwani ta ce ai ita babarsa ce, dan haka bakomai.
Daga nan ta kwashe ta je ta gaya wa Mummy.
Ammi ta keta billenta, ta je ta samu Mummy, ta ce mata dan Allah ta na son yin magana da Mahmoud, ta ce mata za ta turo shi.
Sai dai kan ya je, Mummy ta zauna ta kitsa masa, tare da sauya masa tunani.
Ammi ba zata iya tuna rabonsa da sashinta ba.
Ta roƙe shi Allah ma'aiki, ya auri Iman, ko ita kaɗai ce alfarmar da zai iya yi mata a rayuwa a matsayin ta na mahaifiyarsa.
A take ya ƙeƙashe ƙasa, ya cewa Ammi shi ma ba zai auri ƴar da ba ta da asali ba. Baƙin cikin abun da Mahmud ya yi mata, ya sanya ta kamu da hawan jini, saboda ta yi kuka ba kaɗan ba, ta shiga damuwa.
A lokacin Adam ya je umara, ya ga Aisha, cikinta ya girma sosai, ana ta addu'ar Allah ya sa ta haife shi lafiya, bayan ya dawo ya samu labarin, abun da ya faru tsakanin Mahmud da Ammi, ya din ga yi wa ammi mitar meyasa za ta roƙi Mahmoud ya auri Iman, ita kuma gani take ba ta da wata mafita sai wannan.
Ammi sai da suka kwanta da Iman a asibiti, dan ta so Al'amin saurayin da ya fasa aurenta, haka zalika ta so ta samu Mahmoud, duk da yana cikin waɗanda take bala'in jin tsoro, saboda dukan da yake yi mata da hantara idan sun haɗu.
Kuma zance ya fita a dangi, Giwa ta na neman kai da shegiyar ƴar ta, taƙi auruwa, kuma ta karya billenta ta nemi alfarmar ɗan ta, yaƙi yi mata.
A zahiri za ka ga ammi kullum cikin fara'a take, amma ƙasan zuciyarta, tana cikin damuwa da tashin hankali a kan iyalanta.
***
Gaba ɗaya jikin rumaisa ya yi sanyi, ta rungume Iman da take ta sharɓar hawaye, ta rungumeta ita ma ta fara kukan, ta kasa rarrashinta.
Sai da suka yi mai isarsu, danna rumaisa ta din ga share mata hawaye ta ce "Ki yi haƙuri Anty iman, tun da dai ammi ta san iyayenki, meyasa za ki damu dan an ce miki baki da iyaye? Ki fuskanci rayuwarki kawai, kuma in Allah ya yarda zaki auri miji na gari, wanda zai kula da ke, ki daina kuka"
Ta yi maganar tana sharewa iman hawaye, Nusaiba ta yi sallama a ɗakin, suka amsa, ta ɗan yi turus tana kallonsu, yanayinsu ya nuna mata akwai wani abu, amma ta share, ta ƙarasa ta ɗau Sabir da ya yi barci, ta fice daga ɗakin".
Jabir kuwa rai a ɓace ya koma ɗakin Ammi, ya dubi ammi ya ce "Ammi, dan Allah idan ban takura miki ba, ina son mu yi magana ne".
Ammi ta ce "To" ta tashi ta bar ɗakin, Adam ya bi su da kallo.
Falonta suka koma, Ammi ta ce "Ya aka yi ne?"
Ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, sannan ya numfasa ya ce "Ammi wani abu ne ma daɗe ina son in gaya miki, amma na kasa ban sani ba ko zaki bani dama".
"To ni ɗin baƙuwar ka ce? Faɗi ina jin ka".
"Dama..dama game da Iman ne Ammi, dan Allah idan babu wani a ƙasa yanzu, ni a bani mana, ina son ta".
Ammi ta ce "To fa! Babbar magana, ya aka yi ba ka gaya mini tun da wuri ba?".
"Ina jin nauyi ne Ammi".
"To meye na jin nauyin ban da abunka, ka san yanayin da take ciki, ta daina saurarar kowa ta daina bawa kowa dama tunda abubuwan nan suka faru, amma na yi mamakin da baka taɓa faɗa ba".
"Ammi Iman ai ƙanwata ce, na daɗe ina ɓoyewa ne, yanzu kuma na ga yakamata na faɗa, wataƙila dama rabona ce".
"Haka ne, amma ka san dai case ɗin da yake kanta, kuma babu lallai hajiyarka ta yarda, na san ba za ta amince ba".
Jabir ya ce "Ammi zan shawo kan ta, in dai kin amince shikenan, idan har ba a cikinmu ba, haka zamu zauna mu cigaba da zuba ido, kowa ya zo ya fasa, Saboda wani dalili mara tushe, ina ga ni ɗin na fi dacewa, na san abun da yake faruwa da ita".
Ammi ta ce "Na yi farin ciki sosai Jabir, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ai kai ɗana ne, na gode da ƙoƙarin share mini hawaye ni da marainiyar Allah, Allah ya biya ka".
"Amin Ammi, na gode sosai, ina ga zan yi wa mai girma wambai Magana, a nema mini aurenta, zan yi ƙoƙari ya shawo kan Hajiyata ma".
"To, Allah ya ji she mu alkhairi, ya sanya albarka na gode sosai" Ammi ta ji tamkar ya yaye mata kaso mafi rinjaye na damuwarta.
Da ta koma wurin takawa, ya kalleta ya ce "Ya dai na ga kina fara'a?"
"Ina ruwanka?"
Yayi murmushi ya ce "Tuba nake".
Ta zauna ta ce "Kai ban gaya maka ba"
Ya tattara mata hankalinsa.
"Laila za ta shigo cikin sati Mai zuwa"
Ya waro ido ya ce "Yanzu muka gama magana a waya, amma ba ta gaya mini ba".
"Oho muku dai".
"To ta koma ba ma so, ba ta zo lokacin rasuwar aisha ba, ba ta zo ta ga ɗan ta ba, na yi aure ba ta zo ba sai yanzu?"
Ammi ta ce "Ai ka san yanayin aikinta a can, amma ta ce za ta daɗe sosai idan ta zo, yaran ne za su koma da wuri, tare da babansu idan ya zo, shi sai next month in Allah ya kaimu zai zo".
"To Allah ya kawota lafiya, gashi ni zan yi tafiya. yauwwa Ammi, mai girma turaki ya kirani,