Showing 114001 words to 117000 words out of 199108 words
lashe hannu. Ya ɗaukko tissue, ya goge mata hannun.
Sannan ya dubeta ya ce "Cikin satin nan zan yi tafiya in sha Allah, zan yi sati biyu, idan na dawo kuma, zan je ƙaro karatu, na tsawon watanni shida. Wannan asabar ɗin in sha Allah, za a saka ki a Makarantar islamiyya ta matan aure".
"Islamiyyar matan aure, salon su rainani, ba manya ne matan auren ba? Kuma wai ka tafi ka barni nikaɗai?"
Takawa ya ce "Eh, sidi zai din ga kai ki yana dawo da ke makaranta"
"To sai in daina ganinka?".
"Kina son ki dinga gani na ne?"
Ta ce "Eh mana, nafi son ka dinga kaini makaranta da kanka"
Yayi murmushi ya ce "Abokin gabar naki? Da ki ke yi wa rashin kunya?"
Tayi dariya ta ce "Ai amanarka aka bani, sai na gama sauke amanar, sannan zan rama abun da ka yi mini, dan ban manta ba, kuma kai ne ka ke sawa na yi maka rashin kunya ai wataran, amma dai ka yi haƙuri.
Wani irin murmushi yayi, yana jin daɗin jirar ta su.
Ya ɗora hannunsa a kafaɗarta, kamar ƙawarsa ya ce "Ban haƙura ba, fitsararki ta yi yawa, haƙurina ya kusa ƙarewa"
Ita ma ta ɗora hannu a kafaɗarsa ta ce "Allah ya sa kar haƙurinka ya ƙare, ai da ban taɓa sanin kana da haƙuri ba ma sai yau. Allah ya sa in yi tsawo in kamo ka a tsayi"
"Ba wannan nake so ba, ki yi girma ki biyani bashina nake so"
Ba tare da ta gane me yake nufi ba ta ce "Ai da na gama makaranta, na fara aiki, dubu goma ma zan baka".
"Zaki ga idan kin gama makaranta, na gaji, baby nake so, ayi wa sabir ƙani ko ƙanwa"
Ta ce "Eh wallahi, nima ina so"
Yayi dariya ya ce "Are you sure?"
Ta ce "Yes" cikin murna.
Yayi dariya ya ce "zamu gani ai".
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Duk da na yi maganar a baya, amma yanzu zan sake jaddadawa, ki din ga iya bakinki, a al'amuran da suka shafi masarautar nan. Abu na gaba a duk lokacin da abu ya faru, idan nayi magana ko kina da laifi ko baki da laifi, bana son musu, idan baki da laifi, da kaina zan yi bincike in gane"
"Idan bani da laifin sai ka bani haƙuri?"
Ya ce "Ya danganta, ba sai lallai na fito kai tsaye na ce kiyi haƙuri ba, sannan a duk lokacin da wani daga familynmu, ya sake zuwa, idan har suka yi miki magana ta rashin kyautawa, kar ki kula su, idan na zo ni ki gaya mini. Sai kuma alaƙarki da wancan yaron Mahmud, ina sake maimaita miki bana so, ki kiyaye abun da ba na so mu zauna lafiya".
Rumaisa ta ce "Gaskiya papa, ni ba kullum nake ƙarya ba, maganar gaskiya ba za aci mini mutunci nayi haƙuri ba, tun da dama can Allah bai yi ni a cikin masu haƙuri ba. Sai kuma maganar daddyna, dan Allah meyasa ba ka son alaƙarmu?" .
"Ban ji na yadda da alaƙar bane, zai iya yin komai dan ya cutar da ni, dan haka ba zan so yayi involving ɗinki da Sabir ba. Mussaman da ki ka kasance abokiyar gabata"
Ruma ta yi murmushi ta ce "Amma ka yadda ka yi mu'amala da su Jamil ko? Kai baka san farincikin ammi ne papa? Ba zai cutar da kai ba, idan kuma kana son mu rabu, to ka rabu da su Jamil kai ma".
"Alaƙata da su daban...."
"Amma duk wata alaƙa barin jini ce da ciki ɗaya, wai ba Jamil ɗin ba ne yake yekuwar sai ya bincike ka ba a kan Anty Aisha, haka son da yake makan yake? Maiyasa da tana raye basu damu da ita ba, sai bayan ranta har da barazanar zai yi bincike a kanka, wataƙila ma da saka hannunsa, shiyasa yake son ya ji ta ina kake binciken naka, ya ji ko asirinsa zai tonu, ka din ga wayo kamar ni mana"
Gaban Adam ya yanke ya faɗi, kar maganar rumaisa ta zama gaske fa, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, take ya ƙaryata maganar rumaisa a zuciyarsa, ya san abun da ba zai taɓa faruwa ba kenan. Ruma ta tashi ta ce "Papa sai da safe" ta kwashi kwanukanta, ta bar shi da tunani.
Haka ya kwana wa wayi gari, maganganun rumaisa na kai komo a kansa, idan ya ƙaryata sai yaji abun bai kama zuciyarsa ba, kamar da wayo clue ta bashi, a kan binciken, idan ba rami meya kawo rami?
Washegari a wurin aiki, takawa da kansa ya je office ɗin Jamil, Jamil ya wani tsuke fuska.
Adam ya ce "Jamil lafiya kuwa? Tun da ka kaini gida, na ce ka ɗaukko rumaisa, ban sake ganinka ba"
"Me zan zo na yi maka? Dama kana sane ka tura ni ɗaukko fitsararriyar matarka, ta yi mini rashin kunya, tun da ka gama zubar mana da mutunci a idonta, ni zata kalla ta ce wai ba ƙaunar aisha muke ba, ka je ka gama zazzage mata sirrinmu, meye amfanin dawo da abun da ya wuce? Adam turaki yaƙi gaya mini komai a kan abun da ta gaya masa, dole na cigaba da bibiyarka da tuhumar ka akan dalilin ɓatan aisha bamu sani ba".
"Kuma ni ta ce maka na gaya mata?"
"Idan ba kai ba waye ya gaya mata? A ina zata sani ko ta ji? Kuma dole ka gaya mini abun da kake ɓoyewa, dan na fika kusanci da Aisha, ai jini ya fi ruwa kauri. Kuma zan cigaba da bibiyar yarinyar nan, sai na san gaskiyar abun da yake faruwa.
Adam ya haɗiyi yawu ya ce "To shikenan, ai matata ce, na gaya mata ɗin, kuma Jamil kar ka fasa tuhumata da bibiyata, ka yi duk abun da zaka yi"
Ya daki tebur da ƙarfin gaske ya ce "Kuma ina yi maka rantsuwa da Allah, idan wani abu ya samu matata, sai dai ayi mutuwar kasko da ni da kai, ka je ka cigaba da bincike a kaina, amma idan har zaka bibiyi matata ita za ta gaya maka abun da ya faru, ka shirya cewa watan faɗuwarka ya tsaya, dan tana da ƙwaƙwalwa fiye da lissafinka, kuma gaskiya ta faɗa, a da baku damu da ita ba, kun cutar da ita meye na tayar da jijiyoyin wuya a yanzu? Idan ka matsa za ta saka ka a sarƙa, kuma muddin ka faɗo cikin suspect ɗina, aikina zai bi ta kan ka"
Ayshercool
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
A rikice Jamil ya kalli takawa ya ce "Kana nufin ni ne ke da alhakin yin garkuwa da aisha, kai ba a zargeka ba sai ni?"
Adam ya ce "Ni dama a can a cikin zargi nake, ban ce kai kayi garkuwa da aisha ba, amma abun da ka yi ya jefa ka cikin zargi, madalla da yarinya mai kaifin tunani kamar rumaisa" yana gama maganar ya fice daga office ɗin.
Wani irin gumi Jamil ya yakice, yana wani irin huci.
"Da ni ka ke zancen Adam, zaka gane ba ka da wayo, daga kai har wannan shegiyar yarinyar mai ƙulla mini jakar tsaba, saboda kaji su bini".
A daren jiya kuwa, Mahmud yawonsa ya din ga yi da Sabir, har da zuwa yawon ciye-ciye, ya sayawa Sabir kaya ba kaɗan ba, soyayyar da yakamata ya ji game da ɗan uwansa Adam, shi yake ji a Sabir, koma ya ce fiye .
Ammi tana nan tana dakon dawowarsu, Nusaiba da Iman ma, duk suna tare da ammi, suna jiran dawowar Mahmud.
Wajen ƙarfe tara da rabi, sai ga Mahmud, sidi ya biyo shi, da uban faggon kaya niƙi-niƙi, zuwa shashin Ammi, da da yake ji kamar wata baƙuwar duniya, amma yanzu the more yake shiga, the more yake zama familiar da wurin.
Mahmud ya nuna masa wuri ya ajiye kayan, ba tare da ya kula kowa ba, ya ƙarasa kan kujera, ya kwantar da Sabir da yake bacci, ya durƙusa a gabansa yana ta shafa gashinsa, kamar ya tafi da shi, ya kwana a wurinsa.
Ya miƙe a hankali ya juya zai fita, Ammi ta ce "Wannan kayan fa?".
"Nasa ne" ya faɗa a taƙaice ya fice.
A sashin Mummy ya tarar da Mummy ta rako Samha, tana ta rarrashinta, idonta yayi jawur, alamar ta sha kuka, ya san ba zai wuce ta gaya mata saƙon Adam ne ba, shiyasa take wannan kukan.
Sai da Mummy ta rakata har mota, sannan ta koma sashinta.
"Ina ka je ne? Tun sallar magariba baka dawo ba, baka kirani ba kuma, na san baka yawo da daddare".
"Na fita da Sabir ne"
A ɗan razane ta ce "Waye Sabir?"
"Ɗan mu da Adam ya haifa"
"Au yanzu dan rashin zuciya, har ɗan sa ka je ka ɗauka kana yawo da shi? Wurin giwar ka je kenan?".
"Sirikarta na saka ta ɗaukko mini shi, ina ƙaunar yaron nan sosai da sosai"
Mummy a ranta ta ce "Lallai tsuguno ba ta ƙare mini ba, akwai sauran rina a kaba, aikin malam na kan dutse ya fara sanyi"
Ya ce "Mummy, ya dai na ganki wani iri, akwai damuwa ne?".
"Damuwa akwaita Mahmud, ban gane maka bane kwana biyun nan, ka san dai a duniya bamu da maƙiya sama da giwa da Adam, yanzu kuma naga kamar alaƙa ce tsakanin ka da matarsa, ko ka san yarinyar nan cewa ta yi wai ina yi wa Adam asiri?"
A ransa ya ce "Tom, hasashena ya tabbata, matar nan ta faɗa tarkonmu"
"Na gaji da wannan rashin albarkar, nan ya zo ya gama yi mini rashin mutunci, a gabana ya ci mutuncin ƴaƴana, saboda wannan hatsabibibiyar yarinyar, kuma ta ce wai ina yi masa asiri, a gidan ubanta ta ga asirin, zai maimaita a gaban mai girma wambai, dole ayi mini iyaka da ita".
Cikin ko in kula Mahmud ya ce "Amma dai idan ki ka kai ƙarar wannan Yarinyar, za ace girma ya faɗi, raƙumi da shanye ruwan ƴan tsaki".
"Ba ita zan kai ƙara ba, shi Adam ɗin ita a wa, ina ruwana da ita, amma dole ayi mini iyaka da su".
***
Daf da la'asar, rumaisa ta shiga ɗakin takawa, tana dudduba abun da za ta gyara.
Daga toilet ta ji ya ce "Waye a nan?"
Ta amsa masa da "Ni ce nan"
"Rumaisa duba drowern mirror, ki bani shaver".
Ta yamutsa fuska ta ce "Rumaisa kuma?"
Ya ce "Eh"
"Ba cewa ka yi mimi zaka din ga ce mini ba?"
"Anƙi ace mimin, miƙo mini da sauri"
Ta ɗaukko shaver ɗaya, ta tsaya a ƙofar banɗakin ta ce "To shigowa zan yi?".
Ya ce "Eh miƙo mini"
"Au kai ba ka jin kunya, to ni ba zan shigo ba, zuro hannu ka karɓa".
Ya ce "To ai ba tsirara nake ba, miƙo mini abu nake yi"
Ta tura ƙofar a hankali, ta ɗan leƙa, yana tsaye a gaban mudubin toilet ɗin, ya shafa wani cream a fuskarsa, da wata shaver a gabansa, ga wani towel ɗin a wuyansa.
Duk da haka sai ta ji wani iri, ta ƙarasa a hankali, ta tsaya tana kallonsa.
Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ya dai?"
"Bakomai, so nake naga me ake yi da shaver"
Ya ɗan waro ido ya ce "Baki san me ake yi da ita ba?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Ba kya aski kenan?"
Rumaisa ta ce "Ni namiji ce da zan yi aske kaina"
Ya girgiza kai ya kerɓi shavern ya ce "To tsaya ki ga me ake askewa da ita".
Aikuwa ta tsaya, ta zuba masa ido.
Ya kammala gyaran fuskarsa da ita, sannan ya ɗebo cream a wata container, ya shafa a hammatarsa da ta fara fitar da gashi, ba sosai ba.
A hankali ya sanya shaver yana cire gashin. Ta ce "Innalillahi, dama abun da ake yi kenan, to ni ya aka yi bani da shi, sai yaushe zai fito mini?"
Ya ce "Da gaske baki da shi?"
Rumaisa ta ce "Bai fito mini ba, kuma ina so, in ga ya fito mini da yawa, idan na ɗaga hannuna a din ga gano shi".
Adam ya ce "Saboda ƙazama ce ke? Waye yake ado da gashin hammata, ƙazanta ne to"
"Eh, amma dai ina son ya fito mini"
"Duk ranar da ya fito, ki ka bar shi, ni da ke ne, idan kin ga ya fara fitowa ya taru, ki yi mini magana in sake koya miki yadda zaki aske shi. Amma gashin hannta ba abun so bane, ba abun ado bane. I even wonder kin fara period but still a child"
Rumaisa ta ce "To ni dai Allah ya sa ya fito da wuri, sai ka sai mini shavern nima ko?".
Ya ce "To, jeki zan aske ɗayan"
"Me?".
"Gashin" ya bata amsa kai tsaye.
"A ina yake shi kuma, ko na ƙafarka, ga hannunka ma"
"A'a towel ɗin ƙuguna zan kwance, nan ma akwai wani, shima ba a barinsa cirewa ake yi, idan ba haka ba mutum ya din ga wari, idan ya fito shima ki gaya mini a sayo shavern, sai in koya miki"
Yatsunta ta saka, ta toshe kunnunwata ta bar toilet ɗin, saboda ta daina jin abun da yake faɗa, a tunaninta ai wannan abun kunya ne.
Ta fice daga ɗakin sa, ta sauka ƙasan bene.
Asiya da barira, suna ta yi mata sannu da gida, ta amsa musu tana gaishe su, sai dai ta lura da yadda baba Uwani ke ta wani kumbura fuska.
Ruma ta ce "Baba uwani, me nayi miki ne?"
Ta kalleta ta ce "Hmm tambayata ma ki ke yi?"
"Papa yayi mini faɗa, ya ce kar na sake ai, ranar ma dan raina a ɓace yake ne".
Asiya ta ce "Ranki ya daɗe, wata jita-jita na jiyo, da na je karɓo miki saƙo a wurin Ammi".
Ruma ta ce "Wace jita-jitar kuma?".
"Wai saƙo ya iske cewa, kin ce hajiya jamila, babar Yallaɓai Mahmud, wai tana yi wa maigida takawa asiri"
Rumaisa na jin haka, ta san mahmud ne ya bayar da wannan saƙon, yana nufin baba uwani ta kai tsegumin, kuma shi ya saka ta faɗa a gaban baba uwani.
Rumaisa ta waro ido ta ce "Ni ɗin, waye ya faɗa? Ni harkar wa ma na shiga balle na faɗi wannan maganar?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Anya babu munafuki a sashin ammi? Idan ma na faɗa, ai ba a gaban wasu bare na faɗa ba, balle ma ban faɗa ba. Amma ai ba ƙarya nayi ba, idan ma na faɗa, idan ta san ba ta yi, ai ba zata tsargu ba, idan kuma yin take, A'uzu bi kalaimatillahi tammat.
Tsuru-tsuru baba uwani tayi, tana ta yaƙe baki ta ce "Ai uwar ɗakina, asirin ma ba za a rasa yi ba, saboda abu ne na gidan sarauta, kowa kansa kawai ya sani, galibi ba Allah a ransu"
Ruma ta ce "Yauwwa, Aisya kin ji ko, barira ma kin ji, ga baba uwani ma ta faɗa, mummy na yi wa takawa asiri, ashe bani kaɗai na fuskanci hakan ba".
A rikice baba uwani ta ce "Ba haka nake nufi ba, ki yi wa Allah da ma'aiki kar ki ƙulla mini sharri".
"Ba sharri bane, ai ke ki ka faɗa"
Rumaisa ta nufi hanyar satairs, cikin tashin hankali, da mamakin yadda jikar cikinta, take yi mata wayo, ta bi bayan rumaisa. Ruma ta tsaya ta waiwayo ta ce "Idan ki ka biyoni sai na gaya masa" ta juya ta cigaba da hawa.
Ta koma a sukwane kitchen, ta ce "Aisya, da ku za a haɗu a ƙulla mini sharri ko?"
Barira ta ce "Ba wani sharri baba uwani, mu ba butulu ne irinki ba, idan baki yi wasa ba, an ƙulla miki kyakykyawan tarko kema, kamar yadda ake haɗa baki da ke, ake cin dudduniyar giwa".
"In ji uban wa? Waye ya haɗa bakin da ni?".
Asiya ta ce "Oho, a juri zuwa rafi da tulu...".
Barira ta ce "Wataran zai fashe".
Ruma kuwa daɗi take ji, ta san tana daf da tonawa baba Uwani asiri. Ta shiga kitchen ta duba fridge, taga takawa ya kawo kaji, amma bai gaya mata ba. Ga kayan miya duk ya ajiye bai gaya mata ba, balle ta yi aikin su.
Tana aikin tana mita, ya zo ya tarar da ita a kitchen.
"To uwar ƙorafi, menene kuma?".
"To ba kaine ka kawo aiki ba, kuma ba ka gaya mini ba".
Ya ce "No, su Aisya na ce idan sun gama aiki, su zo su gyara miki, sai ki ɗibi naki, ki basu na gida".
Rumaisa ta ce "Saboda ni ban iya aiki ba ko? To Wallahi ina ƴar ƙaramata, na iya gyara nama, ko kaza ko kofi, ni fa tun ina shekara uku mama ta ce nake kuka, a bani ɓare maggi, da daka, na iya aiki sosai da kake ganina".
"To Allah ya baki haƙuri, idan kin gama, ki dafawa mama wani abun, ko mu saya a waje, mu je ki gaishe ta, dan ni ina zuwa mu gaisa".
Tsalle tayi a kitchen ɗin "Yeeee, zan ga mama, amma shine ka yi mini wayo, ka ke zauwa kai kaɗai?".
"Eh, ai da yake maman tawa ce, ba taki ba, kuma a kyauta zan kai ki ba, da sharaɗi".
Cikin mamaki ta ce "Sharaɗi kuma?"
"Eh sharaɗi mana.
Ta ce "Na me?"
"Kiss zamu yi"
Ta kwaɓe fuska ta ce "Kiss, iskanci fa kenan".
Ko a jikinsa ya ce "Eh, shi zamu yi".
"Taɓ wallahi a'a, ƙazantar?"
Matsawa ya yi kusa da ita, ya sunkuyar da fuskarsa dai-dai tata, ta rintse ido ta kame jikinta.
Ya ce "Wai ke haryanzu kamar robot ki ke, ba kya jin komai ne?"
Ta sake kawar da kanta gefe, tana rintse ido.
Ya rungumota a jikinsa, ya kai fuskarsa tata.
"Wallahi idan ka yi mini zan yi ihu, kuma ma ba kullum nake yin brush ba, bakina wari yake" ba ƙaramar dariya ta bashi ba, gaba ɗaya ta tsorata sosai.
Ya girgiza kai ya ce "Ki yi girki mu tafi da shi, idan an yi sallar magariba zamu tafi" yana fita, tayi ajiyar zuciya, tana ta sauke numfashi.
***
Iman ce zaune a gaban Ammi, ta tattara mata hankalinta, jin ta ce mata, akwai maganar da take son su yi mai muhimmancin.
Ammi ta ce "Iman, Jabir ne yazo mini da wata magana, wai yana sonki, kuma nan kusa yake son ayi komai a gama, baki ji daɗin da na ji ba, kin ga shi na gida ne, kuma ya