Showing 60001 words to 63000 words out of 199108 words
wai dama da gaske ne, ta tabatta aure zaka yi?" Ya ɗaga kai ya kalli Samha da tsoro da kishi ya bayyana a fuskarta, ya jinjina mata kai a hankali cikin tausayawa.
"Shikenan, bakomai na gode " ta tashi ta bar falon. Jikin Adam ya yi sanyi, mama kawa jan tsaki ta yi ita ma, Zainab kuwa cewa ta yi Allah ya sanya alkhairi.
Ɓangaren ammi ma, da ta bawa mummy katin gayyata, masifa mummyn ta din ga yi, wai har ace adam zai yi aure, amma a kasa sakata a cikin lamarin bikin, sai dai ta zo a ƴan gayya, saboda ba a mayar da ita a bakin komai ba.
A gidansu rumaisa ma, shirye shirye sun yi nisa. Mai sunan baba ya buga wani invitation ɗin na ɗaurin aure, aka rubuta sunan Adam sharif, ba tare da sanya cikakken sunan Adam ba. Ba ƙaramin mamaki ƴan unguwar su rumaisa suka yi ba, jin za ayi mata aure, wasu suka din ga surutu suna cewa sai ka ce a ƙauye, wasu kuma suka ce ta tabbata rumaisa ta yi cikin shege ne, ake son a liƙawa wani, kuma aka kasa gane wanene mijin, sai dai hatta wurin da aka rubuta za ayi bukukuwan a wurin ba ƙananan wuri ba ne, nan ma aka yi ta surutun ina suka samu kuɗin kama wannan wurare.
Zaman Gwaggo a gidan, ta din ga yi wa rumaisa faɗa, tare da nasiha a kan aure, da yadda za ta kula da miji, sai dai sam rumaisan ba ganewa take yi ba, yadda aka sakata a gaba ana sake koya mata girki ya fi komai ci mata rai, a ganinta ana hanata hutawa, girkin nan da karambani ta iya shi, dan tun shekara tara take gwadawa, tun mama tana hanata har ta haƙura ta rabu da ita.
Samha ta yi kuka kamar zata yi hauka, gaba ɗaya ji take komai ya fita daga ranta, ko abincin kirki ba ta iya ci, sabuwar soyayyar adam ta dawo mata sabuwa fil, sai dai ta yi alwashin yadda ta zubar da hawayenta a kan sa karo na biyu, daga shi har matar ta sa sai sun ɗanɗana kuɗarsu.
Fauziyya ta din ga zigata a kan ta san duk yadda za ta yi, ta cuzgunawa matar da adam zai aura, har da ba ta tabbacin cewa, ta ji an ce auren haɗi ne ba son ta yake yi ba.
Ana gobe za a yi wa rumaisa jeren kaya, Adam ya ɗauki Aliyu da Abdallah, zuwa gidan rumaisa, dan su gani daga nan ya basu mukulli.
Sai dai da suka je, Aliyu ya raina kayan da suka saya, da suna ta murna sun yi wa rumaisa kaya masu kyau da yawa, sai dai gidan babba ne sosai.
Sama da ƙasa ne, ƙasan akwai babban falo, da ɗakuna biyu, da kitchen da store, saman bene kuma falo biyu, bedroom uku, da kitchen da dining, kowane ɗaki da toilet.
Gidan ya tsaru yayi kyau, dan an kashe kuɗi wurin yin sa sosai.
Aliyu suka yi ta santin gida, suna yi wa Adam godiya. Sai dai tun da suka koma gida suka sanar da mama, gidan yafi ƙarfin abun da za a kai, jikinta yayi sanyi, dan ba dan kar ta nuna halin ƙaranta ba, cewa za ta yi idan da ƙarami a saka rumaisa a ciki.
Kaf ƴan unguwa ba wanda mama ta ce su je yi wa rumaisa jere, ƴan uwanta da ƴan uwan mahaifinsu rumaisa, sai yayyenta ne suke je suka jera mata abun da ya samu a saman benen.
Gado biyu aka yi mata, dangin babansa suka yi mata ƴan waje guda ɗaya, yayyenta suka yi mata ƴan gida, masu matuƙar kyau.
Kitchen ɗin ta ma babu laifi, a dai ƴar talaka, iyayen rumaisa sun taka rawar gani sosai da sosai, ga kujerunta da labulaye, ga dininga komai dai-dai gwargwado.
Ƴan uwa suka dawo, suka din ga santin gida, suna yi wa mama barka da arziki, rumaisa ta je gidan hutu.
Da daddare Adam ya je gida da shi da su ammi, suka ga jeren da aka yi, ammi ta jinjinawa ƙoƙarin iyayen rumaisa, ba ita ba shi kansa adam, abun ya bashi mamaki, aka jere mata akwatunanta goma sha biyar a bedroom.
Washegari Adam ya saka aka kawo abubuwan da babu, wanda basu ƙarasa ba.
Rumaisa ba ta yadda aurenta za ayi ba sai da satin biki ya kama, dama Aliyu sun shirya football match, a nan cikin unguwa.
Tun da rumaisa ta tabattar da idan aka yi auren barin gidan za ta yi, ta fara koke-koke tana fasa.
Ranar da za ayi bridal shower, daga gidan su adam, aka aiko da mota, aka ɗauki rumaisa zuwa gidan kwalliya, ita da ƙawayenta, babu ko sisinsu, aka yi musu kwalliya aka wuce da ita wurin biki.
Su Iman tuni suna can, sun sha kwalliya iman kamar balarabiya, da ita da wasu daga cikin famylinsu, da su ƙawayenta.
Rumaisa gaba ɗaya ta kasa sakin jikinta, mussaman yadda ake kallonta, wasu suna jinjina wannan ƴar yarinyar takawa zai aura?.
Su hauwwaliya kuwa, sai iyayi ake da rawar kai, su gasu ƙawayen amarya.
Babu zato babu tsammani, sai ga ƴan mazan mama sun dira a wurin, da shigar ƙananan kaya, rigunansu mai kalar kayan da rumaisa ta saka maroon.
Washe baki ta yi, ta nufesu da gudu tana dariya, suka rungumeta suna juyata.
Yasir ya ce "Taɓ, kin ga fuskarki kamar sarauniyar aljanu?"
Ta ɗan kwaɓe fuska ta ce "Na sani nima, fuskata sai ƙaiƙayi take yi, kuma an ce idan na sosa zan ɓata kwalliyar"
Abdallah ya ce "Ai abun ka da ba a saba bane ba, kuma fa kin yi kyau"
Mamaki ne ya kama ƴan wurin, me ya kawo maza wurin bridal shower, har da anko?.
Iman ce ya fara ganinsa ya shigo wurin, sai da hankalin da yawa daga cikin 'yan matan ya koma wurinsa, ciki har da iman, da take ta ƙara gyara cake ɗin da yake kan table.
Rumaisa ba ta taɓa tunanin mai sunan baba zai zo ba, zuwansa ya sanya suka cika su bakwai samarin gidan su kowa ya zo.
Gaban table ɗin ya ƙarasa, kusa da iman ya ɗauki ƴar ƙaramar wuƙar yanka cake ɗin, ya yanko cake, ya kalli rumaisa ya yi mata alama da ta buɗe bakinta, ta buɗe kaɗan ya saka mata a baki sannan ya ce "Happy marriage life ƙanwar maza, Allah ya sanya albarka" tafi aka hau yi ana shewa, rumaisa ta kasa tauna cake ɗin idonta ya cika da ƙwalla.
Ya girgiza mata kai, ya nuna mata mai hoto, ya ce "Smile, amarya ba ta haɗe rai ranar aurenta"
Kasancewar yayyenta a wurin ne, ya sanya ta saki jikinta, suka din ga ƙoƙarin yin abun da zai kwantar mata da hankali.
Sai dai mai sunan baba, ya rasa dalilin da ya sanya shi, son satar kallon iman, gaba ɗaya kamar ba bahaushiya ba, ta yi kyau sosai da sosai, a ɓangaren iman kuma, zuwansa wurin ya sanya duk ta takura, da ta motsa sai su haɗa ido, gabanta ya faɗi.
Ƙarshe dai da su aka gama partyn, suka ɗauki ƙanwarsu suka yi gida.
Mai sunan baba ne ya rage, zai tafi ya fito harabar wurin, in da zasu tafi shi da abokinsa, kasancewar abokin nasa yana da abun hawa.
Iman ya gani a tsaye, wani matashin sauryi ya tsareta, yana ta zuba mata surutu ita kuma da alama akwai abun da take jira.
Haka kurum ya tsinci kansa da tsareta da ido, wanda hakan ya sanya ta ji kamar ta fasa ihu, jikinta har rawa yake, gani take kamar ta aikata wani zunubi da bai kamata ba.
"Me ki ke jira baki tafi gida ba?"
A tsorace ta ce "Motocin ne suka cika, shi ne na ce su tafi zan taho".
"Wuce mu tafi" yayi maganar cikin command.
Babu musu ta wuce, ya sakata a gaba, zuwa motar da zasu tafi.
Ayshercool
08081012143
What's app only please
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
Bayan motar ta shiga suka tafi, sai da suka kai ta gida sannan suka wuce.
Ko da mai sunan baba ya koma gida, mama ya tarar a ɗaki tana rungume da rumaisa, tana ta rarrashin ta, su Aliyu duk sun zauna sun yi jugum suna kallonsu.
Ƴan uwa sai bawa rumaisa haƙuri suke yi.
"Meye haka?" Ya faɗa a kausashe.
Gwaggo ta ce "Ka san lamarin aure, dole za ta ji babu daɗi za ta yi kewar mahaifiyarta, kuka take yi"
"Saboda shirme, ku kuma ku ka zo ku ka sakasu a gaba babu mai tsawatar mata? Tana fama da tension da hayaniya na biki, ke kuma kin zo kin sakata a gaba kina kuka? Da wanne za ta ji? Tashi ki cire wannan kayan, ki yi wanka ki nemi wurin kwanciya"
Mama kasa cewa komai ta yi, rumaisa ta tashi tana kuka, ta shiga uwar ɗakan mama.
Su usman daurewa kawai suke yi, dan gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi da suka ga tana kuka, ba su ba shi kansa gogan jikinsa a sanyaye yake.
***
Samha har ta gaji da kuka, kowa da irin shawarar da yake bata, ta banza da ta arziki, tana kwance a kan gadonta ta yi rigingine, tana tunanin yadda za ta aiwatar da malamin da suke zuwa wurinsa ya bata, dan ta yi alwashin raba Adam da kowane irin farin ciki, in dai abun da ya shafi aure ne.
Ba ta san a karo na nawa wayarta ta yi ringing ba, cika mata kunnuwan da wayar ta yi ne ya sanya ta ɗaga, ta saka a kunnenta ba tare da duba ko waye ba.
"Babbar yarinya, ashe abun da ya faru kenan, yayanki zai angwance da wata ba ke ba?"
"Murna ka kira ni ka yi mini, ko kuma ci mini mutunci?"
"Babu ɗaya, jaje kawai na kira na yi miki, tare da mamakin abun da zai saka Adam kawar da kai a kan cikakkiyar mace mai aji kamar ki Samha, ban da so makaho ne, tuntuni nake jaddada miki, ki rufe ido a kan wannan son, mu yi duk mai yiwuwa mu ga bayan adam, amma ki ka dage a kan cewar ke ba za a cutar da shi ba, ai kina son sa, yanzu son wace ranar yayi miki?"
A hasale Samha ta ce 'Look wakili, i don't have time, for all this now allow to rest"
Khalifa ya ce "Ba ki da wani hutu samha, lokaci ne kuma zai cigaba da ƙure miki, kan ki farga yayi miki nisan da ko tafin ƙafarsa ba zaki hango ba, let's join hands together"
Kashe wayar ta yi ta ajiye, tare da faɗin "Shashasha kawai".
Iman ita kaɗai a ɗakinta, ta yi wanka ta sauya kaya, sai dai ta kasa manta fuskar mai sunan baba, yau yayi kyau sosai, sai dai yanayin muzuransa ko tunawa ta yi sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har suka kawota gida, ban da kwatance, ko abokin nasa ba ta ji yana yi wa magana, balle ita ya kulata.
Ɓangaren mai sunan baba ma, mamaki yake yi, yadda tsoronsa ke bayyana sosai a kan fuskar iman, ya san yana da kwarjini sosai, sai dai ita ya lura ba kwarjini kawai yake yi mata ba, tsoronsa take ji, tsoro kuma ba na wasa ba. Taɓe baki yayi ya cigaba da sabgoginsa.
Washegari ya kama ranar da za ayi dinner, rumaisa ta tashi da ciwon kai, saboda kukan da ta sha jiya, idanunta duk sun yi ja.
Ta wuni a uwar ɗakan mama, tun ƙarfe uku yayyenta suka tafi fara nasu shirin, a ƙarfe ukun kuma, aka aiko da motar kaita wurin kwalliya.
Maƙwabta na ta mamakin wani hamshaƙin ne haka zai auri rumaisa, sai abu ake yi kamar wata babbar budurwa.
A wurin kwalliyar ma, kuka take ta yi, Habiba da su hauwwaliya suna ta rarrashin ta, amma ta ƙi tsayawa.
Mai kwalliyar ƙawar nusaiba ce, dan haka ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki. Nusaiba ta gaya wa takawa, ya din ga mitar shi ba ya son a tsaya wannan shafe-shafen aje a ajiye mutane su na jira.
Ƙarshe dai da kansa ya tafi wurin kwalliyar da shi da bashir.
Ya je ya tarar duk an yi wa ƙawayenta kwalliyar ban da ita.
Ya kalleta ya ce "Zaki tsaya ayi kwalliyar ne, ko kuma mu tafi a haka?".
"Ni bana son auren nan na fasa, mama ta ce wai barin gidanmu zan yi, ni na fasa" ta yi maganar cikin kuka.
Bashir ya ce "Haba rumaisa, an gama tara mutane, ki bari idan aka gama sai ayi duk maganar da za ayi".
Adam dai ya ƙule ƙarshe, Bashir ne yayi ta bata haƙuri, sannan ta tsaya aka yi.
Mai kwalliyar ce ta fito da rumaisa reception, ta yi kyau kamar ba ita ba, kayanta iri ɗaya da na Adam.
Hauwwaliya har da tsalle, tana koɗa rumaisa.
Bashir ne ya din ga yi musu hotuna, sai dai daga ita har adam babu wanda yake walwala.
A harabar wurin bikin, suka tarar da su Aliyu, sun haɗe cikin shadda iri ɗaya, hatta huluna da agogo iri ɗaya suka saka, motar na tsayawa, ta buɗe ta fice ta nufi wurin su Usman.
Abdallah ya din ga ɗaukar rumaisa a hoto.
Usman ya ce "Allah sarki lantarkin gidanmu, zaki tafi ki barmu a duhu, zaki barmu da ɗan hasken da ba zai ishemu ba"
Rau-rau ta yi da ido, za ta yi kuka, ya girgiza mata kai ya ce "Yau ranar murna ce, da yi wa Allah godiya, ki bari mu je mu yi rawa mu ci kaji, idan an koma gidan kya yi kukan, dan kukanki ba zai hanani cin abinci ba na gaya miki"
Bisa ga al'ada, ƙawayen amarya da ƴan uwanta ne ke shigo da ita, sai dai wannan amaryar, yayyenta maza ne suka shigo da ita, ga ta ƴar mitsitsiya a gaban angon nata, kamar ƴa da uba.
Abun ba ƙaramin ƙayatar da mutane yayi ba, sai dai fa wasu surutu suka fara da raina wayon takawa, na auren ƴar mitsitsiyar yarinya.
Taken gidan sarauta aka saka wa shigowar ta su, ga maroƙa da suka biyo su suna yi musu busa, tare da kirari.
Rumaisa ta kalli yadda hall ɗin ya cika, dama tun daga haraba motoci ba a magana, manyan mata masu shiga ta alfarma, gaba ɗaya taga ido a kanta, ga takalmi mai tsini, take ta ji jiri na ɗibarta.
Adam ne ya fuskanci haka, dan haka ya riƙe hannunta, sai da ta ɗan waro ido, ta sake kallon mutane ta ga kowa sai ƙoƙarin ɗaukarsu a hoto yake yi, ta sake sunkuyar da kanta a cikin mayafi, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga na Adam amma ya riƙeta sosai.
Har kan high table suka raka rumaisa, suka zaunar da ita, kowa ya gansu sai ya ce Masha Allah, tare da jinjina rumaisa a matsayin ƙanwar zaratan maza har bakwai.
Iman ce ta fito stage, ta karɓi mic, tare da gabatar da addu'a, da fatan alkhairi ga amarya da ango.
Jabir ba ƙaramin mamaki ya yi ba, ganin rumaisa ita ce matar da takawa zai aura, ya din ga tunanin yaya aka yi hakan ta kasance bai sani ba?. Me Adam zai yi da wannan yarinyar ƴar talakawa mara kunya.
Sai da aka yi kamu, kan a fara gabatar da dinner, duk wani abu da ƙawayen amarya za su yi, yayyen rumaisa ne suka yi shi.
Dangin su Adam sun so su farfaɗi maganganu, da yin rashin mutunci a wurin, mussaman da kusan kowa ya san Samha tana son shi bai aureta ba, amma kasancewar su Abubakar da mai sunan bab a wurin, suka cika wa mutane ido, kowa ya riƙe gulmarsa.
Jabir ya rasa nutsuwarsa, ga tunanin auren adam,ga iman ta ɗau ado, sai shiga take yi tana fita, yayin da ita kuma hankalinta ke kan mai sunan baba, har fata take Allah ya sa ba kallonsa ake yi ba, dan dangin nan akwai tarin ƴan mata.
'To sai me ina ruwanki?' wata zuciyar ta tambayeta.
Aliyu habiba ya saka a gaba, yana yi wa dariya ƙawar amarya an sha ɗauri, ƴar baƙa kyakykyawa.
Iman ta ƙarasa ta cewa Usman "Yaya ban san sunanka ba, na san dai duk sunanku yaya, kuma duk kamarku ɗaya, koda yake na san yaya Aliyu"
Usman ya ce "Usman nake, ma'abocin haske, ƴar balarabiya ya aka yi ne?".
Ta yi murmushi ta ce "Dama ban sani ba ko kun zo da abokanku, ga in da aka yi muku reserving can, za a fara dinner ne, gara mu fita kunyar kowa".
Usman ya ce "Abokai kai, kin san mu yawa ne da mu, bari in tattaro su wuri ɗaya, dama zan zo mu zauna in baku amanar ƙamwarmu, dan Allah a kula mana da ita, ayi haƙuri da ita, idan aka taɓata zuciyar maza bakwai ce za ta girgiza "
Iman ta yi dariya ta ce "Wane mu mu yi mata ba dai-dai ba ma, ai sai mu sha duka" tun da suke zuwa gidansu rumaisa, maganar kirki ba ta taɓa haɗata da yayyen rumaisa ba, sai yau da Usman yake yi mata halin na sa.
Umar yana jin su, kasancewar yana kusa da su.
Jabir ya ƙaraso in da Iman ke tsaye a wurin usman ya ce "Sweetheart, ina son magana da ke fa, ina aka yi wa abokan aikinsa reserving, suna daf da ƙarasowa, na ga ke ki ke ta arranging mutane".
"Uncle J, ina wani aikin ne, ga uncle bashir nan, da shi muka zo wurin nan ɗazu, ya san yadda aka tsara komai fa" ta yi maganar cikin muryarta ta shagwaɓa.
"Yes na ji, zo mu je dai, ko na ɗagaki yanzu na yi waje da ke, idan ya so gobe a ɗaura auren da namu"
Usman dai murmushi kawai yake, iman kuwa ba a son ranta ba, ta bi bayan jabir.
Suna yin gaba ya hau ta da faɗan, dan me za ta je wurin maza ta tsaya. Ba ta iya bashi amsa ba, ta tsaya tana kallon sa kamar za ta fashe da kuka, babu tsammani mai sunan baba ya gifta ta bayansu yana waya, ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, da sauri ta koma cikin wurin dinner.
Kwaɓe fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya ɗan sunkuyar da kansa ya ce "Meye kuma?".
"Ni na gaji, sai kallona ake yi,