Showing 81001 words to 84000 words out of 199108 words

Chapter 28 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

827

abinci da mai da yaji, amma yarinyar nan ta ƙi yarda".
Asiya ta kalli baba uwani, suna ƙasa basu san ma me ruma ta girka ba, balle baba uwani ta hanata, amma ta ce ta hanata ba ta hanu ba.

A fusace ya koma saman benen, baba uwani ta lallaɓa ta bi bayansa, tana cigaba da salallami.

A falo ya tarar da rumaisa ta fito, cikin fushi ya kalleta ya ce "Muzuru ne ni da zaki dafa abinci da mai da yaji ki ajiye mini?".

"Papa meye a ciki, abinci ne fa?".

"Shut up! Na yi kama da wanda zai ci abinci da mai da yaji ne?".

Baba uwani ta ce "Ayi haƙuri mai gida, ba za ta sake ba, rashin sani ne, in sha Allah zan nunnuna mata abubuwan da yakamata ta sani, duk laifina ne, yarinta ce take damunta"

"Ba wani yarinta baba uwani, ai na ce girki ba huruminta bane ba, ta bari a din ga yi amma kasancewar, kunnen ƙashi ne da ita, ba za ta ji ba".

Kuka rumaisa ta saka ta ce "Kuma sai na gaya wa ammi kana yi mini faɗa, idan na yi abu gwaleni ka ke yi".

Taski ya yi ya , tafi ɗakinsa, yana barin falon rumaisa ta yi wa bayansa gwalo.

Ya fito da mukullin motarsa, ruma ta ce "Papa ina zaka?" Banza yayi mata ya sauka, baba uwani sai bashi haƙuri take yi.

Bayan ya sauka baba Uwani ta kalli rumaisa ta ce "Ranki ya daɗe, ai ba a...."

Rumaisa ta kasteta ta hanyar cewa "Idan mun yi faɗa, ba sai kin nema mini afuwa ba, yarinya ce ni ba mahaukaciya ba, kuma ina sane na yi hakan, na san ba ya cin abinci da mai, an gaya mini" galala baba uwani ta bi rumaisa da kallo, dama baki ne da ita haka? Kamar ba daga bakinta maganganun suka fito ba.

"Amma ƴar nan idan ki ka fusata shi, yana da larura fa".

Rumaisa ta kalleta ta ce "Wace larurar?" Sai kuma ta tuna katoɓarar da ta yi ta ce "A'a bakomai".

"Shikenan tun da ba zaki gaya mini ba , idan ya dawo sai na tambaye shi wace larurar ce da shi?".
Baba uwani ta ce "Na shiga uku, da wasa nake yi miki, ba ya son ɓacin rai ne dai, dan Allah kar ki gaya masa".

Rumaisa ta ce "Aini duk abun da aka gaya mini sai na bi diddigi, bana mantuwa" ta wuce ta bar baba uwani tana gumi da dana sanin maganar da ta yi.

***
Ƙishirwar son ganin Umar faruk, ta din ga damun zuciyar iman, hotunan biki din ga shiga, tana kallon hotunan duk da ya fito a ciki. Cikakken namiji mai cikar zati kamala, duk da ba fara'a yake yi ba, son kowa ne ƙin wanda ya rasa, namiji mai matuƙar jan ajinsa da tsare gida.
'Na shigesu, me yake damuna ne?'

'son wanda bai san kina yi ba, wanda ba ki da damar ki nuna masa hakan, wands tsantseninss da kamewarsa, da matsanancin kwarjininsa ba za su bari ma ya gane hakan ba' wata zuciyar ta bata amsa.

Tashi zaune ta yi ta ajiye wayar, tare da furta 'Allah ka iya mini" ga gefe guda Jabir yana ta hura wuta, wanda har Ammi ta fara ganewa.

Ta sake ɗaukar wayar, ta shiga what's app ɗin ta, da ta yi saving number sa, da Yaya Omar, ta shiga chat, sai dai ta rasa mai za ta rubuta, ta buɗe hoton ka dp ɗin sa, hotonsa ne shi da hassan ɗin sa, wato yaya Abubakar.

Ta sake ajiye wayar, tana ajiyar zuciya.

***
Baba uwani addu'a ta din ga yi, Allah ya sa kar rumaisa, ta tambayi Adam, dan sai yanzu ta fara lura, yarinyar a tsaye take, gata dai yarinya amma alamu sun nuna ba ta ji.

Sai da aka yi sallar isha'i, Adam ya dawo, sai dai abun mamaki, ya tarar da abincin a ɗakinsa, amma a wannan karon har da miya, da salad da komai aka shirya masa.

Bai kula abincin ba, dan ya ciko cikinsa a gidan ammi.

Ya zauna babu jimawa, sai ga rumaisa ta shigo da sallama.

Ya shareta, ya fara ƙoƙarin buɗe laptop.

"Sannu da zuwa"

"Zo ki kwashe abincin nan, ki fita da shi".

"Da miya ce fa yanzu".

"Ba na ci"

Ta yi dariya ta ce "Na sha gaya maka, ka daina yanke hukunci da zuciyarka, ka din ga yi da ƙwaƙwalwarka, na san ba ka cin abinci da mai da yaji, Iman ta gaya mini, to in gaya maka na yi miya, ina sane na baka da mai da yaji, na san faɗa za ka yi, ka yi zuciya, na san halinka ai tas, to ranawa na yi, soyanin da ka yi da ruwan zafi da safe" ta yi maganar tana haƙiƙancewa.

Yayi mata shiru, bai ce uffan ba.

"Kuma saura abubuwan da ka ke yi mini, duk sai na rama".

"To, idan kin gama, ki kwashe abincin ki je ki san yadda za ki yi da shi"

Ba ban haƙuri, ta kwashe ta fice abun ta

Ya dafe kansa, rumaisa gaba ɗayanta danger ce, yana duba nasihar ammi ne a kan yayi haƙuri da ita, duk abun da za ta yi masa, y din ga duba girman sadaukarwar, da ta yi masa. Gefe ga shawarar da bashir ya bashi kan Ya aure ta, a kan ya bi ta a hankali su saba, dan ya samu bayanan da yake son samu a wurinta, idan ya tsananta ba zai samu ba.

"Allah ka shiga lamarina" ya furta a hankali ya tashi ya bi bayanta.

Ya ganta tana hawowa sama, bai san me ta je yi ƙasa ba, ya ce "Ki shirya, gobe in Allah ya kaimu da safe, zan kai ki makaranta"

Ɓata fuska ta yi, dan sam ko zancen makaranta ba ta so. Ya juya ya koma ɗakinsa.

Da asuba ta yi wanka, ta yi salla, tana tantama dai-dai ma ta yi wankan, ko ba daidai ba, dan ba za ta iya tunawa complete yadda mama ta koya mata ba, kuma ita ba za ta tambayi takawa ba.

Haryanzu rumaisa tana ɗokin sababbin kayan kitchen, dan haka haryanzu ba ta gaji da shiga kitchen ta yi girki ba.

Ta dafa tea, ta fito da biscuit, ta nufo falo, takawa ta gani a kan dining, ga kayan karyawarsa a kan dining, baba uwani kuma durƙushe a gabansa, ba ta san me take ce masa ba.

Kai tsaye ta nufi dining ɗin, ba ta kula su ba, ta je ta hau saman dining table abun ta, ta fara ƙoƙarin haɗa tea.

Baba uwani ta yi shiru, ta daina maganar da take yi.

"Barka da safiya ranki ya daɗe".

Rumaisa ta ce "Yauwwa sannu".

"Meye haka, zaki hau saman dining?".

"Idan na zauna a kan kujera, bana jin daɗin zama a kan tebur ɗin, gara na hau sama, ya fi daɗi, ka san babu a house".

Ya girgiza kai ya ce wa baba uwani, "Je ki kawai, ma ƙarasa maganar".

Tunani rumaisa take yi, me baba uwani take gaya masa, da ba za a faɗa a gabanta ba.

"Haɗa mini tea zan karya, ki je ki ɗauki jakarki mu tafi"

"Ni na kawo maka da zan haɗa maka, ita wadda ta kawo makan ta haɗa maka mana"

Hannu ya saka ya janyo ta ta baya, ya jawota ta ƙeya tana kallo fuskarsa.

Ya ce "Da ni ki ke?".

"A'a da kaina nake" ya hankaɗata ta tashi zaune, tana ƙiƙƙifta id.

Ta janyo kayan tean, ta fara haɗa masa, tana yi tana tura baki ta miƙa masa.

Ita kuma ta yi ƙerere a kan table, tana karyawa.

Ba ta gama na ta ciye-ciyen ba, ta ji ta ƙoshi, ta tashi ta kwashe kayan.

Sai wurin ƙarfe tara da rabi, sannan suka fita, ya tafi kaita makaranta.

Tsari da ginin makarantar, ba ƙaramin burge rumaisa ya yi ba, ta tabattar wa da kanta, akwai banbanci a tsakanin makarantarsu, da wannan, hatta ajinsu, basu da yawa, ga kujeru masu kyau, ga fankoki ko ina ga kayan wasa, ajinsu har da projector, da ake haska musu komai, duk wani abu na koyo da koyarwa akwai makarantar nan, makarantar ta burge rumaisa.

Kan takawa ya tafi, sai da aka kai shi har ajin su rumaisa, ya kalli ruma ya ce "Yau ga ki a makarantar ƴaƴan ɓarayi da suke sace muku kuɗi suna karatu. Sannan ba zan lamunci ina biyan kuɗin makaranta in tarar ba kya karatu ba, kullum zan din ga tambayarki me aka koya muku. Ban da surutun banza, da ciye-ciye. Na bayar da ordern abinci a wani restaurant, za su kawo miki abincin break, tun da kin ce ke ba za a dafa a gida ki ci ba".

"To, kai zaka zo ka ɗaukeni, ko gida zan tafi?".

"Dama ke ki ka kawo kanki?"

"Ahh na san hali ne, kar ka tafi ka barni, ka ga kayan wasa a makarantar nan, zan sha lilo, idan na din ga hawa ina sufa...."

"Ba shi na kawo ki yi ba, karatu zaki yi, wuce ki shiga aji"

Rumaisa ta shiga ajin, tana ƙarewa ajin na su kallo.

***
Takawa kuwa da ya tafi hanya, Bashir ya kira a waya, ya ce masa zai shiga bamfai su haɗu su yi magana.

Haka kuwa aka yi, ya haɗu da Bashir, sai dai bai shiga ciki ba, a shiya fito haraba, suka haɗu.

"Allah ya taimake ka, ya amarya yaushe za a gayyaceni cin abincin amarya ne?" Yayi maganar cikin zolaya.

Adam ya ce "Idan ma da wasa ka ke yi, to ta iya girki".

"Ahha haba dai?"

"Ka bari kawai bashir, yarinyar nan caza mini kai kawai take yi, Ammi ta bata masu aiki, amma ta ce kar su kuma dafa abinci su kai mata, wai kar ayi mata asiri. Jiya fa horon yunwa ta yi mini, mun samu saɓani da safe, na fita aiki ta hana ayi girki, wai ta dafa mai da yaji ta bani, na yi magana, wai ramawa ta yi. Wallahi haƙurina na daf da ƙarewa, duk maganar da ta zo bakinta, idan zan mutu haka za ta faɗa mini"

"Adam, sai ka yi haƙuri, ka san yadda yarinyar nan take tun farko, kuma ka san ba shiri ku ke yi ba, dole ka yi haƙuri da ita, idan ka nuna mata halin muzurai, ba zaka samu abun da ka ke so ba".

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na gaji ne, gashi familynmu, sun fara yar mata da maganganu, ka san ba ta da kunya ba za ta yi shiru ba. Ga matar da take tare da ita tana yi mana aiki, baba Uwani na san zaka santa, ita ma sun fara faɗa, ita duk abun da yake dama to ita hagu za ta yi".

Bashir ya yi dariya ya ce "A dai ƙara haƙuri, zai wuce in sha Allah".

"To, Allah ya sa, gata can dai na kaita makaranta. Jabir ya gaya wa Jamil rumaisa ce yarinyar da ta tsinci sabir, ya kuma tayar da jijiyoyin wuya a kan, dan me na ɓoye masa yana jami'in tsaro kuma yayanta. Abun da nake so da kai shi ne, ko da zance zai zo, ya san tare da kai mu ke bincike, kar ka gaya masa komai".

Bashir ya ce "In sha Allah, ba zan bayar da wata ƙofa na kowane bayani ba, sai mun yi nasara in sha Allah".

"Allah ya amince, na gode sosai " suka yi sallama Adam ya tafi.

Da daddare bayan ta dawo, tana ta murna, ta sha lilo har ta gaji, sai dai ba ta gane turancin da ake yi, dan malamansu har da turawa.

Tana ɗakinta, ta baje textbooks ɗin aka bata tana kallon hotuna, Adam ya shigo hannunsa riƙe da wayarsa, rumaisa na ɗaga kai ta kalli takawa, ta yi sauri ta rufe idonta, da hannunta, saboda daga shi sai dogon wando babu ko riga a jikinsa.

"Gaskiya ka daina shigo mini ɗaki tsirara"

"Dalla karɓi" yayi maganar a kausashe, ta ɗan zame hannunta ɗaya ta karɓi wayar, ta duba ta ga kira ne, ta saka a kunnenta.

"Ƙanwar maza, ƙanwar maza".

"Yaya Aliyu, ashe baku manta da ni ba, tun ina kuka har na daina".

"Saboda kin samu duniya ko?".

Ruma ta ce "Ba wata duniya, ina mama? Ba za ta zo ba ko?".

"Mijinki sun yi waya da mama, ta ce kar a kawo ki"

"To Meyasa, bani ita".

Mama ta karɓi wayar ta yi sallama ta ce "Ƴar auta".

"Mama shi ne ki ka ƙi zuwa, kuma ki ka ce kar a kawoni".

Mama ta ce "Ke tafi can, ba gaki nan ba abun da ya same ki ba".

"Ni dai dan Allah ki zo, ko in ta yi masa kuka, tun da kin fi son sa"

Mama ta ce "Shi wa?".

"Mijina" ta bata amsa kai tsaye.

"Sannu mara kunya, ai dama ban ce nawa ba ne naki ne".

Ruma ta ce "Mama albishirinki".

"Goro"

"Kin ga haɗaɗiyar makarantar da ya kaini, kamar a turai, kin ga liluka kuwa? Ga fankoki har da malamai turawa, baki gani ba, baki taɓa zuwa gidana ba ma, gidana haɗaɗɗe, duk ya sai kayan daɗi ya zuba mini"

Mama ta ce "Sai ki je ki same shi, ki yi masa godiya, dan na san baki yi ba"

"Taɓ, mama yaushe zaki zo to?"

"A'a ni ba zan zo gidanki ba, amma dai idan ya kawo ki shikenan". Za ta yi wa mama taɓara, mama ta kashe wayar.

Rumasai ta share hawayenta, ta bishi ɗakinsa, ta tarar yana banɗakin, ta ajiye masa wayarsa ta fice.

Kwanci tashi asarar mai rai, yau juma'a rumaisa kwana biyar da fara zuwanta makaranta, kuma wata guda cif, da ɗaura mata aure.

Takawa ya ɗaukota daga makaranta, ta ga ya canza hanya, maimakon su tafi gida.

"Ina kuma zamu je?".

"Sayar da ke, na yi tsafi da ke, kamar yadda aka ce na yi da aisha" ya bata amsa.

"To ai dai bani na faɗa ba ko?"

Tana gane gidansu zai kaita ta ce "Yeee zan ga Ammi zan ga Sabir da Anty Iman".

Da haka suka ƙarasa, cikin murna ta riga shi shiga sashin Ammi.

"Oyoyo ga ruma"

"Ammi, kin ga na fara zuwa makaranta, kin ga jakata"

Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya sanya albarka"

Iman ta ce "Congratulations Anty rumaisa".

"Thank you anty iman"

Takawa ya shigo, ya tarar da rumaisa a kusa da ammi tana nuna mata litattafanta.

Wato rumaisa ko kumyar nan ta sirka ba ta da ita.

"Ammi ina Sabir?".

Ammi ta ce "Yayi bacci"

"To bari in gama nuna miki litattafaina, sai na je na ganshi".

Ammi ta dubi Adam ta ga yanayinsa, kamar mara lafiya, ta ce "Takawarka lafiya, ya aka yi ne? Na ga yanayin ka kamar akwai damuwa"

Ya ce "Bakomai" tare da kashingiɗa.

Ta kalli rumaisa ta ce "Rumaisa, ko akwai matsala ne?".

Ruma ta gyara zamanta ta ce "Eh, dama ƙararsa zan kawo miki tun rannan, dan dai bamu zo ba ne, na ce sai na gaya miki, kin ce duk abun da yayi mini na gaya miki".

Ammi ta ce "Subhanallah, meyafaru?"

Ya kalli rumaisa yana jiran ya ji me za ta ce "Wai cewa yayi zai ƙara aure, saboda ba ni da nono!!!"



Tirƙashi!.



Ayshercool

*Chat me on what's app, to subscribe yours 08081012143, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank*
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏


Sai da falon yayi tsit na wucin gadi, Adam bai taɓa tunanin wautar rumaisa ta tsananta har haka ba. Ji yake tamkar yayi layar zana ya ɓace daga wurin.

Ta kuma cewa "Ammi, kuma yana yawo babu riga a cikin gidan nan, kuma alhalin ni ba muharammarsa ba ce, Yaya usy ya ce yayyena ne kawai muharramaina, amma yake yawo ba riga, ina kallonsa, ko kunya ba ya ji".

Wani kallo ya yi wa rumaisa, amma ta share shi ta ce "Ai dama na rantse sai na faɗa mata, ammi ta ce duk abun da ka yi mini na rashin kyautawa na gaya mata. Hmm ni  ko za a shekara nawa idan aka yi abu bana mantawa, ina riƙe da shi a zuciyata, ina sane sai yau na ce bari na gaya wa ammi".

Ammi ta yi murmushi cike da dattaku ta ce "Haba dai, wace irin kishiya ana zaman lafiya, tsokanarki yake yi kawai, wanda yake da wannan zuƙeƙiyar yarinya, ina ruwansa da wani ƙara aure. Kuma in dai saboda wannan abun ne, rai dai an fille wa fara kai, muna zaune Allah zai kawo su".

"Ammi ai hijjabi zan koma sakawa, ya daina saka mini ido, dama na ce gara in gaya miki, ba zan gayawa mama ba, saboda na fuskanci yanzu mama ta fi son sa a kaina, cewa za ta yi ƙarya nake yi, kuma ita ta ce duk wanda ya gaya mini maganar banza, wadda ta saɓa da tarbiyyar da take yi mana, in je in gaya mata. Shiyasa nake gaya mata komai, amma na san a wannan karon da zan gaya mata abun da ya yi, ba zata yadda ba".

"Da gaskiyarki kam, mama ta yi iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar ku, bai kamata ta rushe ba, Allah ya cigaba da dafa muku, bar mini litattafan naki na cigaba da gani, duba ɗakina, ko Sabir ɗin ya tashi, zamu yi wani sirri da ke".

Rumaisa ta tashi ta nufi ɗakin Ammi, ka sa haɗa ido Adam ya yi da ammi, ji yake kamar ya zama guguwa ya bar wurin, saboda takaici da kunya.

"Takawa" ya ɗan ɗaga kai amma bai kalli ammi ba.

"Ka din ga sanin me zaka gaya mata, tun da ta ce ko za a shekara nawa ba ta manta abu, na ga hakan a cikin idonta, a hankali zaka nusar da ita abun da ya shafi sirrin aurenku naku ne, ta daina faɗa, na san kana haƙuri amma ka ƙara nan gaba zaka ci ribar hakan in sha Allah". Ya jinjina wa Ammi kai ya tashi ya nufi ɗakin ammi, bin bayan rumaisa.

Ammi ta ce "Dan Allah kar ka yi mata wani abun, Allah ya taimake ka, daga ni sai ku ta faɗa, Iman ta riga ta tafi amsa waya, kar ka ce zaka yi mata wani abu".

"Babu abun da zan yi mata, Sabir kawai zan gani, a nan za ta wuni, a haɗa masa kayansa, da shi zamu tafi, zan kaita gidansu gobe in Allah ya kaimu za su wuni a can, ba ta taɓa zuwa gida ba".

Ammi ta ce "Masha Allah, babu laifi"

Rumaisa tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login