Showing 51001 words to 54000 words out of 199108 words

Chapter 18 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

833

zai zo?"

Rumaisa ta ɗaga kai ta kalli Usman ta ce "Oho masa"

"Ke ina yi miki magana, kina amsa mini a haka, tashi zaune"

Rumaisa ta tashi zaune tana ɓata rai. Mama da ke gefe ta ce "Ai gara ku shiga cikin lamarin, tun da ni ba zan gaya mata ta ji ba".

Usman ya ce "Aikuwa da ni take zancen, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki yi masa rashin mutunci, ko wannan cin maganin, sai na yi miki bugun sakwara, ko ki zauna kina wannan ɓata ran, ki na kumbura baki zaki ga yadda zan yi da ke"

"To ni yaya usy ya zan yi? ku fa ku ka ce mini ba ruwana da maza, ni ban taɓa zance ba ban san me ake cewa ba, sai dai Huzaifa ya rakani, ni tsoro ma nake ji".

Usman ya ce "Au idan aka yi miki auren ma, huzaifa ne zai biki gidan mijin, ya tayaki zama da kula da mijin?".

"Ni ba zani gidan kowa ba, sai dai shi ya dawo nan gidan ya zauna, kuma bada Sabir kawai zan kula ba, shi ƙato da shi me zan masa?"

Huzaifa ya ce "Ki ce auren Bollywood za ayi, ayi aure miji ya tare a gidan su mata, yarinya sai dai kar ki yi zancen, idan ni zan rakaki".

Usman ya ce "Ni bari na koya miki abun da zaki ce, ya za ayi wani huzaifa ya raka ki, ya ji kalaman soyayya ya dawo yana tsokanar ki".

Ta kwaɓe baki ta ce "Soyayya kuma?"

Usman ya ce "Eh mana, au da ƙiyayya?" Ta yi shiru, tana kallon Usman.

Ya ce "Idan ya zo, ba ƙifi-ƙifi zaki yi da ido, kina kallonsa kamar fusatacciyar kyanwa ba, ya ga alamar girmamawa a idonki, idan ya zo sai ku gaisa, ki tambaye shi ya mamansa, da ƙannensa da Sabir. Cikin mutuntawa ba da zazzare ido ko harare-harare ba, ki na yi kina sunkuyar da kai, ban da tsyawa ki ƙure shi da ido, na sa cikin naki, duk abun da ya tambayeki ki bashi amsa, ba cikin tashin hankali da masifa ba, sai dai idan kin ga yayi miki wani abu da ya saɓa shari'a da tarbiyyar da aka baki, sai ki zo gida ki gaya mana".

A ranta ta ce "Saɓa shari'a da tarbiyya na nawa kuma, dan dai kawai kar na zubar masa da mutunci ne, amma da sai na gaya wa kowa abun da ya yi mini".

Muryar Usman ce ta dawo da ita hayyacinta, da ya ce "Kin ji abun da na ce ko kuwa?".

"Na ji" ta amsa da ƙyar.

"To tashi ki je ki yi wanka, zan din ga yi ina zagawa in ga yadda ki ke zancen, idan ki ka kuskura, ki ka aikata abun da na hanaki, a gabansa zan tuburbuɗaki".

"To yaya usy, ni fa na yi wanka da safe"

Huzaifa ya ce "Sokuwa, wannan wankan tarbar masoyi ne, wankan ganin baby".

"Allah ya kiyaye na ce masa wani baby, kamar wata ƴar iska, sunansa Adamu"

Usman ya saka hannu, ya talle mata ƙeya, sai da ta kusa kifawa. "Shashasha, ana koya miki abu kina iskanci, ki je ki yi shirme a auren, zaki gane baki da wayo, tashi ki je ki yi wanka" tashi tayi ta dafe ƙeya, ta fice daga ɗakin.

Mama ji take kamar ta yi dariya, yayyen sun zauna suna koyawa ƙanwarsu, yadda ake yin zancen.

Mama ta ce "Malam usman wannan lakcar, anya ba a zagaya zauruka da magariba? Ba a taɓa bani labarin sirikar tawa ba"

Usman ya sosa kai ya ce "Mama a wurin abokaina nake ji".

Mama ta yi murmushi ta ce "Ba zan hanaka ba, ni dai fatana aji tsoron Allah, kar a din ga zuwa rage dare wurin yaran mutane, alhalin ba aurensu za ayi ba".

"Mama kar ki kawo komai a ranki ma, ba wurin da nake zuwa"

"Idan ma ana zuwan dai, ai dole na yi kashedi" Usman ya din ga murmushi yana sinne kai.

****
Iman tana zaune a kan gadonta, ta sunkuyar da kai, gefe Nusaiba na zaune, sai kuma jabir da ya saka Iman ɗin a gaba da kallo, kamar zai haɗiyeta.

"Talk mana iman ko na ji daɗi, saboda an ce baki da lafiya ban gama abun da nake yi ba, na baro Germany, na zo na dubaki kuma kin ƙi magana, talk please"

Nusaiba ta ce "Please iman, stop treating our uncle J this way, ki yi magana mana".

Cikin sanyinta ta ce "Anty Nusaiba, maganar ce bana so in general, bana jin daɗi sam"

"Amma duk da haka bai kamata ya yi ta magana ki yi masa shiru ba"

Ta ɗan kalleshi ta ce "Am sorry".

"To ya zan yi da ke jarumata, bana son yadda ki ke yi mini wulaƙanci, idan wani abun na yi miki am so sorry for it"

Ta girgiza kai ta ce "A'a babu komai"

"Shikenan, na ga kamar ina takura miki, bari na je gida, Nusaiba take a good care of her please"

Nusaiba ta ce "To uncle J, but you have pay for the service"

Yayi murmushi ya ce "Biyoni mu yi ciniki, za a biyaki ko nawa ne" ta yi murmushi ta tashi ta bi bayansa suka fita.

A hankali iman ta furta "Ohh Allah, ka iya mini, Allah ka yi mini zaɓi na alkhairi, Allah kar ka saka Jabir ya gayawa wani yana sona, he has no space in my heart. Ni ba kowan kowa ba ce, duk zaɓin da ka yi mini ina so Allah, Allah ka iya mini" ta ƙarasa maganar tana kwanciya a kan pillowanta.
Sai dai tana kwanciyar, ta ji tamkar an sanys igiyar ƙarfe, an ɗaɗɗaure mata jijiyoyin kanta, ta sanya hannu ta dafe kan ta fashe da wani marayan kuka, ta rasa me ma za ta yi, lamarin nan ya fara bata tsoro, dan kuwa ji take tamkar zata haukace.

Jabir ya kalli Nusaiba ya ce "Nussy, see how your sister is behaving towards me, just because i have feelings on jer, me yasa ba ta so na, meye aibu na?"

"Uncle J, yakamata ka yi mata uzuri, this girl suffer alot in this family, kalli yadda take samun manema, suna tafiya saboda abun da mutane basu da tabbas a kan sa, kalli saboda yarima ya ce yana son ta, kalli wulaƙncin da fulanin yola ta yi mata da cin mutunci, har a gidan nan ma ba ta tsira ba, na waje ma idan sun biyota suna so, sai a samu mai zigasu su daina zuwa. A yanzu ta riga ta ce ba ta son kowa ya raɓeta da sunan soyaya, ba ta son kowa, ka san abu na ƙarshe da ya faru a gidan nan ai, ba wanda bai ji ba, shi ma aka din ga surutu a kai. Dan haka ta ce idan har mijin aurenta ya zo ko ba soyayya, ta ce za ta yi, amma for now, tana buƙatar hutu ne".

"Nusaiba, babu ɗan adam ɗin da baya faɗi tashi da gwagwarmaya da ƙaddara, amma hakan ba ya sanya wa a sare, this is not an excuse da za ta yi denying kowa ya ce yana son ta, ni da gaske ina son iman, amma wace shawara zaki bani a kan ta?"

Nusaiba ta numfasa ta ce "Uncle J, ga ka da takawa, ga ka da Ammi, ai a duniya babu abun da za su ce ta yi, ta ƙi yi muddin bai saɓawa shari'a ba, ka bi ta wurinsu kawai, ina fatan idan komai yayi daidai, zaka kula mini da iman, ka kuma ji tsoron Allah a kan riƙon ta".

"Nusaiba da zan cutar da iman, ba zan aureta ba, ina son ta so na gaskiya ne, abu na gaba ina ga ammi zan samu kawai, takawa zai iya yi mini wasa da hankali, kin san halinsa, bari na je kawai na gode, ki yi mata sannu"

"Za ta ji, ka gaida gida" suka yi sallama ya tafi, ita kuma ta koma.

***
Aiki ya samu ƴan maza fa, domin kuwa su Usman ne suka zaɓowa rumaisa kayan da za ta saka, sai cika take tana batsewa, wannan ya dungure mata ya ce "Ki yi dariya dan ubanki".

Wannan ya ce "Ki ka yi mana shirme dakuwa zaki yi".

Suka shiryata cikin doguwar rigar atamfa, ta sanya dogon hijjabi, Abdallah ya ce "Ina hoda a shafa miki?"

"Ni bani da hoda" ta amsa masa tana ɗan hararsa.

Usman ya ce "Jambaki fa?"

Ta ɓata fuska ta ce "Ni fa kun san mai kawai nake shafawa, shi ma ba kullum ba, bani da komai ni".

Usman ya ce "Ikon Allah, lallai kin cika deluwa, kina mace amma ba hoda ba Jambaki, kamar gardi, wallahi ki ka je gidan miji ba kya kwalliya, wahala zaki sha, to yaushe mutum zai ajiye mace, amma shi da ita ba maraba? Ai na ga mama tana da kwalli, shi zaki saka"

Rumaisa ta ce "Yaya usman, idona fa yaji yake idan na saka kwalli".

"Ai ko tsiyayowa zai yi sai kin saka, Abdallah ya riƙeta, Usman ya saka mata kwalli, tana kuka sai ka ce dole"

Mama ta riƙe haɓa tana "Yau nake ganin ikon Allah"

Abdallah har da lakato Vaseline, ya shafa mata a leɓenta.

Huzaifa ya ce "Ai dole idan ya tafi, a yau ba sai gobe ba, a sayo kayan kwalliya ta din ga yaɓawa"

Usman ya ce "Dolenta ma kuwaa"

Aka ɗauko turare aka fesa mata, Usman ya ce "Ranar kamu ni zan kamaki, an ce da turare ake yi ko? Idan na din ga fesa miki, sai kin fara hayaƙi"

"Sai ka ce wata ita ce"

"Koma dai menene, ina sake jaddada miki, ki ka yi mini kwaɓa, da takalmi zan ladabtar da ke".

Ta kalli kanta a mudubi, ta ce "Kalli yadda ku ka mayar mini da ido, kamar wata sheɗaniya"

Yasir da yake zaune yana kallonsu yayi dariya ya ce "Koma dai wacece, idan ya zo, baby ka zo, you are welcome ya aiki? Ya family, kamar dai yadda ki ke gani a film, mussaman bollywood".

Ta buɗe baki ta ce "Taɓ, Allah ya tsareni, Bollywood ba taɓa mata suke yi da maza ba, wallahi ya taɓa ni, sai na gantsara masa cizo, babu namijin da zai taɓa jikina in tsaya ina kallonsa, ko a wurin ƴan bindiga, bana yadda, wallahi faɗa ake da ni" ga mamakinta sai ta ga gaba ɗaya sun tuntsure da dariya, Usman ya ce "Wannan bawan Allah yana ruwa, mama akwai buƙatar ilimantar da yarinyar nan kan aure"

Mama ta yi masa shiru, kamar ba ta ji ba, wanda a ranta tunani take yi, ta yaya za ta yi wa rumaisa bayanin wannan al'amari mai girma, yarinyar da ta tashi a kan iya abun da aka nuna mata shine dai-dai a gida, kome za ayi ba zata yadda ta canza ba, yanzu da an ce mata wani abu, tsaf za ta ce kenan da ƙarya ake yi mata.

Wata zuciyar ta ce "Ko da yake, ai ina ga zai ɗan ƙyaleta ta ƙara wayo, tun da saboda karatunta ma mamansa ta ce ayi auren'

'Namiji ne fa' wata zuciyar ta tunatar da ita.

Ta ɗan dafe kai ta ce "Yarinya ce, lokacin da aka yi mini aure, shekara sha biyar, na fi rumaisa girma sosai da sosai, amma lamarin aure abu ne mai faɗi"

Yasir ya ce "Mama magana ki ke yi ne?"

Ta ce "A'a kallonku nake yi dai".

Mai sunan baba ya shigo, hakan ya sanya duk suka yi shiru suka nutsu.

"Ke ki zo, ga mutumin can yazo, ki ɗau abun zama ki saka muku a soro, kar ki sake ki tsaya a waje, balle wannan iyayen saka idon su ganki".

Cikin rawar murya ta ce "Mama ni fa tsoro nake ji, gabana faɗuwa yake yi"

Mama ta buɗe baki tana kallonta, har idonta ya ciko da hawaye.

"To cinyeki zai yi?" Mai sunan baba yayi maganar yana tsareta da ido. Ta girgiza kai alamar a'a.

"To kukan uban me zaki yi? Wuce dalla, sai kin tayar mata da hankali haka kurum".

Huzaifa ya ɗau turare da darduma, ya ce "Bari na yi maza, na je shimfiɗa dardumar na fesa turare a soron, sai taho kina taku kamar gimbiya, dan gidan sarauta ba sa son hauma-hauma" ya ruga yayi soron da gudu.

Ya shimfiɗa, ya feffesa turare, ya dawo da sauri ya ce "To fito, ki ce masa ya shigo".

Ta fito tsakar gida zari silifas, za ta yi waje, Usman ya riƙeta "Wai ke rumaisa wace irin ƴar baƙin ciki ce? Yasin gidan sarautar nan sai kin je shi, ba zaki mana buƙulun zuwa gida mai kyau ba, canza wannan ɗan iskan takalmin, ko na cire shi, na tsinke ki da mari da shi, kuma idan ya shigo mintuna biyar, ki zo ki ɗauki kayan abincin nan ki kai masa, dole mu koya miki soyayya, dan ba zaki yi aure ayi miki kishiya ba"

Tana cusa baki, ta sauya wani ta fita, bagazan-bagazan ta leƙa wajen, ta ganshi a tsaye a jikin motarsa yana amsa waya.

"In ka gama wayar, ka shigo" ta faɗa tana riƙe ƙugu. Kamar bai san ta yi maganar ba, ya cigaba da wayar, ita kuwa ta koma soron, ta zauna ta mimmiƙe ƙafafuwanta.

Ya kai mintuna goma, kan ƙamshin turaren sa ya mamaye ilahirin soron, brown ɗin yadi ne a jikinsa, kansa babu hula, sai zuba ƙamshi yake, ta ɗaga kai ta kalleshi, kamarsa da Sabir ta sake fitowa sosai da sosai.

Ya nemi wuri ya zauna a kusa da ita, ta matsa can ƙarshen sallayar, tana kaɗa ƙafa.

Jin shirun yayi yawa, ba shi da niyyar magana, ya sanya ta ce "Ina wuni?" Ya kalleta ya yi shiru bai amsa ba.

"Ai dama na san ba amsawa zaka yi ba, dan a gida an ce in gaisheka ne, amma idan na gaishe ka, ba amsawa kake yi ba, ai ni na riga na gama sanin halinka kaf, daga A har Z"

Nan ma shiru bai amsa mata ba.

"Taɓ kana da aiki wallahi" ta juya masa baya, ta kalli wani wurin. Ya kalli bayanta, yana jinjinawa tsiwa da rashin jin ta, wai ta san halin sa daga A har Z. Can aka kwashi wasu mintuna, sai ta tuna abun da Usman ya ce mata ta tashi da sauri ta ɗauko kayan abinci nan.

Gaba ɗaya suka taso suna tambayarta yaya aka yi?

Ta ce "ba komai"

Usman ya ce "To, wallahi ki ka dawo da kayan Abincin nan, bai ci komai ba, to tabbss rashin mutunci ki ka yi masa, kuma zaki daku" ta gyaɗa kai, ta tafi soron ta tarar da shi, ta ajiye masa kayan a gabansa ta zauna ta ce "Ga abinci nan" ya ɗago ya kalleta ya cigaba da taɓa wayarsa.

"To, ni dai zan juya maka baya, ka ci, dan ba zan yi wahalar banza ba, tun safe ake azabtar da ni a gidan nan saboda zaka zo, zan juya maka baya, ka ci idan ba zaka iya ci a gabana ba"

Ta juya masa baya, ta ɗauko goruba tana ci.

A ransa ya ce "Na ga ta kaina ni Adamu, wai wannan ce matar da zan aura?"

Ta waiwayo ta ce "Wai ba zaka ci ba? To wallahi ba zaka ja mini duka ba.

Ta ɗauki coca-cola, ta tsiyaya a kofi, ta shiga hijjabinta ta sha, ta buɗe meat pie, ta ɗauki ɗaya, ta  shiga hijjabinta ta ci, ta gutsuri wani ta ajiye ta ce "Yauwwa, dan ba zaka ja mini duka ba, an ce idan har na koma da shi ba ka ci ba, yaya usy zane ni zai yi"

Adam ya zubawa sarautar Allah ido, ita a rayuwarta ba ta san kara ba, idan ana neman mutum kai tsaye da ba ya rufi, to kowa ya bi bayanta.

Kamar wadda ta ci wani abun maye, ta takure abun ta, ta haɗa kai da gwiwa ta hau bacci, shi dai ikon Allah kawai yake kallo, wannan zance ya zo, ko kallon drama.

Ya mayar da hankali kan wayarsa, yana dannawa.

Usman da yake kaiwa yana komowa ya ce "Kai shirun nan yayi yawa, bari na duba"

Wata irin razana rumaisa ta yi "Iman!" Ta faɗa da ƙarfi, tare da faɗawa jikin Adam gaba ɗaya jikinta yana rawa, hakan yayi dai-dai da shigowar su Usman cikin rige-rige, domin ganin abun da yake faruwa, saboda ihunta da suka ji.

Ayshercool.
08081012143hi
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login