Showing 183001 words to 186000 words out of 199108 words

Chapter 62 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

821

abun da za ta yi wa Mahmud muddin bai saka an sakar mata ɗa ba domin kuwa ta san muddin asirin jabir ya tonu ba zai yi sarauta ba, kuma ta fuskanci kamar yanzu Mummy ƙoƙari take taga Mahmud ne ya samu sarauta.

Sai a yanzu Mummy ta tuna da furucin hajiya Lubabatu.

Tashi rumaisa ta yi ta fara tashin Mahmud.

Takawa ya ce "Ya samu bacci fa"

"Tashe shi kawai, daddy"

Ya buɗe ido a matuƙar wahale ya kalleta.

"Meya haɗaka da jabir?"

"Bakomai" ya furta yana numfarfashi.

Ta ce "To koma me ka yi masa, babarsa ta ce zaka gani"

Takawa ya ce "Mimi bana son rigima fa, ke a ina ki ka ganta?"

Ruma ta ce "Ɗazu da asuba ina bacci, na gansu su na faɗa, ban san a kan menene ba, amma ita ta ce zai gani, jabir yana police station ko?"

Ammi ta tashi ta kamo ruma ta zaunar da ita, ta ce "yi shiru da bakinki" shi dai takawa a iya sanin sa, suna tare da ruma, kuma ba wani wurin suka je ba, balle ace ta ji.

Mummy ta hau bala'in cewar mahmud sun yi faɗa da Jabir, amma ba wani abu da Hajiya Lubabatu ta yi masa.
Tayi maganar tana karewa saboda kar a gane sun samu saɓani da Hajiya Lubabatu, kuma muddin asirin lubabatu ya tonu, na ta ne ya tonu.

Takawa ya ce "Mimi ba ta ƙarya a cases irin wannan, zan yi bincike a kai, duk wanda na gano da saka hannunsa wani abu ya same shi, wallahi sai ya fuskanci hukunci ko waye shi".

"Matarka ba ta ƙarya ni nake yi kenan?"

Ammi da sauri ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ku yi haƙuri Takawa kar in sake jin bakin ka, rumaisa ku yi shiru mu yi masa addu'a".

Ruma ta ce "To ammi, amma wallahi ba ƙarya nake yi ba"

Mai sunan baba ne yayi sallama ya shigo, hankalinsa a tashe, "Subhanallah" yake ta maimaitawa saboda halin da ya ga Mahmud a ciki, dan kuwa sun yi waya jiya da safe, yake ce masa zasu haɗu yau.

Bai iya yi wa kowa magana ba, ya ƙarasa gaban gadon yana ambaton sunansa.

Gashi da an kira sunansa yake amsawa, ya buɗe idonsa ya kalli mai sunan baba.

"Mahmud, meyafaru haka ne? Wayarka na kira wata yarinya ta ɗauka ta ce mini wai kana Asibiti" ya cewa mai sunan baba "Ɗago ni"

Mai sunan baba ya sanya hannu biyu, ya ɗago shi, ya jingina da jikinsa.

Ammi ta din ga ajiyar zuciya ganin Mahmud a zaune.

"Ku yi haƙuri duk na tayar muku da hankali"

Mai sunan baba ya ce "Kar ka damu sannu ya jikin naka?"

"Da sauƙi, zan sha ruwa"

Mai sunan baba ya kalli Adam, Adam ya ɗaukko roba ya tsiyaya ruwa ya bawa umar, ya karɓa ya bawa Mahmud, ya karɓa ya sha sosai.

Ya ce "Alhamdilillah, ina ƙanwata tana lafiya?"

"Lafiya ƙalau, bata san me ke faruwa ba, na riga na fito sannan na kira wayarka, sannu Mahmud"

"Yauwwa yaya" kasancewar haka yake kiran umar.

Ammi ce ta ce "Mai sunan baba ya gida?"

Ya ce "Afuwan ammi, hankalina ne a tashe wallahi, ya gida ya mai jiki kuma?"

Ammi ta ce "Jiki da sauƙi Alhamdilillah"

Mummy kuwa sai cika take tana batsewa, Fauziyya ba ta taɓa ƙarewa mai sunan baba kallo ba sai yau, lallai Iman ta auri mai kyau, da cikar zati.

"Me zaka gaya mini ne ka ke nema na?"

Mai sunan baba ya ce "Ka ji da jikinka ka samu lafiya, kana tambayata me zan gaya maka" yayi maganar yana murmushi.

"Am curious about it" yayi maganar yana lumshe idanunsa, saboda allurar baccin ba ta sake shi ba.

"Zan gaya wa yayanka ya gaya maka"

"Wai Takawa? Ba zai gaya mini ba"

Mai sunan baba ya ce "Zai gaya maka mana, zaka ci abinci ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Bari sai na gama farfaɗowa, idan kuma na mutu....

"Shhhh, zaka farfaɗo in sha Allah, har aurar da kai sai na yi"

Ammi bakinta ya ƙi rufuwa dan murna, ita ba ta san ya aka yi ma ta sa ta zo ɗaya da Mahmud ba, saboda Mahmud akwai taurin kai da rashin mutunci, mai sunan baba kuma akwai izza da son girma, amma yadda yake yi masa zaka gane akwai mutuntawa da girmama juna a tsakaninsu.

Ya kwantar da Mahmud, ya ce "Ka yi bacci, zan je gida ƙanwarka ta yi maka girki, mu zo ta duba ka"

"Kar ka wahalar da ita, ga Mummy ga Ammi ga daughter duk na wanda na samu zan ci".

"Ba wata Mummy, na ammi zai ci" Rumaisa ta faɗa tana harare-harare.

Fauziyya ta buɗe baki za ta yi magana, amma kwarjinin mai sunan baba ya cika mata ido, dan ta san ƙarya take, ta zagi rumaisa a gabansa ya ƙyale ta.

Ya kalli Adam ya ce "Ina son yin magana da kai"

Mamaki ne ya kama Adam, amma ya tashi ya bi bayan mai sunan baba suka fita.

Fauziyya ce ta ɗora da rashin mutunci.

"An yi magana wani ammi ce za ta bashi abinci, sai ka ce ammin wahalar sa ta sani, uwarmu ce dai ta yi masa duk wata wahala ta rayuwa".

"Da tayi mata fashin ɗan? Kallon biri ku ke masa yake yi muku na ayaba fa. Uwar me ta tsinana wa rayuwar ta sa ban da masifa, uwar riƙon arziki ce za ta raba uwa da ɗan ta, ta raba jini da jininsa, ta raba shi da ɗan uwan sa, yanzu dai shi ma ya san gaskiya, gurbin ido ba ido ba ne, kuma wallahi ko bayan shekara dubu, tuwo sunan sa tuwo"

Ammi sai ƙoƙarin hana magana take yi, amma rumaisa tayi mursisi ta din ga gasawa Mummy da Fauziyya magana, ita kaɗai su biyu ba tare da kunya ko tsoro ba.

Duk abun nan da ake yi Mahmud yana jin su, amma yayi shiru kamsr mai bacci.

Mai sunan baba ya kwashe komai ya gaya wa takawa, game da Alhaji Aminu, jikin takawa har tsuma yake yi ya ce "To yanzu Lagos ɗin zamu je, ko yaya za a yi? Mu ga shi Alhaji Aminun, idan ta kama tambayarsa zamu yi, ko ma a tafi da ammi sai ayi "

Mai sunan baba ya ce "A'a ina ga gara mu mu je mu tabbatar, tun da yanzu tana cikin damuwar rashin lafiyar Mahmud, dama da shi na so mu je, to gashi ba shi da lafiya"

"Bakomai, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu, in dai ya ƙara warwarewa, sai mu je kawai, ina fatan Allah ya tabbatar ya sanya ƴan uwan iman ne "

Mai sunan baba ya amsa da Amin, har takawa ya juya zai tafi mai sunan baba ya ce "Na ce ba" ya juyo ya tsaya yana sauraren sa.

"Akwai buƙatar duk abun da ya faru a baya ya wuce, a fuskanci gaba.

A zamana da Mahmud babu abun da yake marari da so da ya wuce ka, you have to play your role as his senior brother, babu abun da yafi ɗan uwa daɗi. Ba zaka gane hakan ba sai ranar da babu shi a duniya"

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, na gode sosai" mai sunan baba ya jinjina masa kai ya tafi.

Samha sun je duba Mahmud a asibiti, dan tuni labari ya zaga masarautar, Mahmud ba shi da lafiya, ƴan dubiya sun fara kaiwa suna komowa.

Sai dai fa cacar baki taƙi tsayawa a tsakanin Fauziyya Mummy da rumaisa.

Muraran yau ruma take nuna musu asalin tantirancinta.

Samha za ta saka baki ruma ta ce "Yi mini shiru, ba dake nake ja gayyar mushirikai maƙiya Allah, ai wallahi a doron duniya ban ga bokan da zai yi asirin da zai kamani ba, sai dai ku yi wa wasu".

"Su waye mushirikan?"

"Gaku nan gaba ɗayanku, ban da yawon asiri da ƙoƙarin rusa rayuwar mutane me ku ka saka a gaba, azzalumai maƙiya Allah"

A rikice ammi ta fita neman Adam, suka yi kiciɓis a hanya, ta ce masa maza ya je ya ɗau rumaisa ya mayar da ita gida.

Sai dai suna shiga ɗakin, suka tarar Samha da Fauziyya tamkar za su rufe ruma da duka, ita ma ta tsaya ta riƙe ƙugu tana bala'i, Nusaiba sai ba su haƙuri take.

Babu abun da ya gigita Samha sama da ganin tirtsetsen ciki a jikin rumaisa bayan ta miƙe, ta riƙe ƙugunta.

Ruma ta ce "Mamaki ki ke yi ko Samha, kin ga ciki a jikina? Baba uwani ba ta gaya miki na cire layar da aka saka a cikin katifar ɗakunan mu ba?.
Ai tunda Allah ya sa na ritsuta, duk wani lungu da saƙo, sai da ta tone komai, na zauna na warware abun da ki ka ƙulla mini na tsiya, masifarku sai dai ta ƙare muku".

Cikin matsanancin tashin hankali Samha ta ce "Me ki ka nufi? Nima sharrin zaki yi mini?".

"Wallahi na fi ƙarfin in yi miki ƙarya, rufa miki asiri kawai na yi, amma tarkacen layoyi da kayan tsubbun duk da ku ka binne mana a cikin gida an tone su, na kuma tara su wuri ɗaya saboda sheda, duk bala'inki ke da Adam sai dai ido Samha"

Ba tare da sanin Adam ya shigo ba, ta yi ƙoƙarin hankaɗa Rumaisa.

Amma cikin zafin nama, ya hana faruwar hakan, ya ɗauketa da mari.

Tsit suka yi suna kallon Adam.

"Wallahi ko da makamancin wasa, ki ka sake ki ka yi wa rumaisa wani abu, sai na taka ki, sai dai zumuncin ya watse uban kowa ya kama gabansa wallahi. Kuma na gode da abun da ki ka yi mini, na mayar da ni mara amfani a gidana, sai dai Allah ba a azzalumin sarki bane ba, kanki ki ka yi wa samha"

Mahaifiyar Samha ta fara bala'i "Wane irin mutum ne kai? Duk abun da yarinya ta faɗa sai ka yarda da shi, kai ba ta laifi kenan. Saboda rashin ta ido, a gabana ka mari ƴa ta"

"Saura Jamil ma, wallahi sai na warware kowane munafuki, babban algungumi mara tsoron Allah"

Nurses ne suka shigo, suka ce su fa asibitinsu ba wurin hayaniya ba ne ba, dan haka a tafi a bawa mara lafiya damar hutawa.

Adam ya maze ya ce kowa ya tafi Shi da Ammi za su zauna, ruma kuma anjima zai mayar da ita gida. Mummy ta ce bai isa ba.

Likita ya zo da kansa, ya ce wace mahaifiyar Mahmuda ta zauna da shi, ita da mutum ɗaya, ruma ta nuna Ammi ta ce "Ga mahaifiyar sa nan" Mummy na ji tana gani aka sallame su, ya rage sai ruma Ammi Nusaiba da takawa.

Mahmud ya kalli ruma ya ce "Daughter kina ganin bai yi wuri ba?"

"Bai yi ba daddy, yakamata komai ya zo ƙarshe, enough is enough"

Adam ya ce "Ban gane me ku ke nufi ba"

"Zaka gane very soon, amma kar ka matsa Please"

Ammi ta ce "Mahmud, a kawo abincin? Ya ka ke ji yanzu?"

"Alhamdilillah da sauƙi, Yaya zai kawo abincin"

Da azahar takawa ya tafi sallar juma'a, bayan ya dawo ne Iman suka zo tare da mai sunan baba.

A lokacin Mahmud yana zaune, har yayi salla jikin da sauƙi.

Iman ta din ga jera masa sannu, mai sunan baba ya ce "Deeja zuba mana abincin tare da shi, ko zai samu ya ci da yawa".

"Cikina dai babu daɗi, kar a ɗura mini abinci da yawa".

Mai sunan baba ya yi murmushi, ya ajiye abincin a kan gadon, ya ce "Ko a baki zan din ga baka ne? Na iya ɗura ka tambayi deeja ka ji"
Iman ta sunkuyar kai, saboda ammi na wurin a zaune da nusaiba.

Takawa kuwa ya cewa ruma ta tashi ya mayar da ita idan sun gama cin abincin.

Iman sai tsokanar ruma take yi, wai yau abun ɓoye ya fito fili, sabir zai yi ƙani.

Ta din ga tura baki, tana harar su.

Ko da suka je gida gaba ɗaya takawa ya hau yi wa rumaisa faɗa.

"Why are you making things complicated rumaisa?"

Cikin rashin fahimta ta ce "As how?"

"Ni da ke idan kin gaya mini abu ina yarda da ke, sauran mutanen fa? maganganu sun fara yawo, mahmud ya daki Jabir ya rufe shi ba wanda ya san dalili, mahaifiyarsa ta je an ƙi sakin sa an ce sai mahmud ya je. Kin ce Samha na asiri, a dalilinki na daketa, komai ya hargitse na ma rasa ya zan yi, wambai ya ce lallai in zo da ni da ke, kun hargitsa al'amura, babu wanda ya san me ku ke ciki, kina ɓoye mini wasu abubuwan"

"Wait" tayi maganar tana ɗaga masa hannu.

"Duk cikin wannan maganganun naka, marin Samhan da ka yi ne ya fi baka haushi kenan? To sai ka koma ka bata haƙuri ai. Ka san dai ba zan yi mata ƙarya ba, tun da lokacin da na zo gidanka ba uwar abun da na sani, balle in san an yi maka wani asiri baka da lafiya, ko in yi wa Samha ƙarya. Kuma ba wambai ba ko gaban waye idan na je ina da gaskiya kuma zan faɗeta.

Ta ƙarasa ta saka mukulli, ta buɗe wata wardrobe, ta ɗaukko wata Viva bag, cike da takaici ta watsa masa.

Ta ce "Ga kaɗan daga binne-binnen da aka yi a hanani zama, daga ni har kai, da yake Allah ba azzalumin sarki bane, duk in da nake rayuwa in dai da sihiri, sai na sani. Ka duba a ciki har da abun da Samha ta yi, ta saka aka sanya a cikin katifarka da tawa, banda abun da aka binne"

Jikin takwa yayi sanyi, tsigar jikinsa ta tashi, saboda uban tarkacen da suka zubo daga cikin ledar, sai uban wari suke, ƙoƙarin rumaisa ya gani, da ta iya ajiye wannan tarkacen a ɗakinta.

"Kuma ka sani ban ɓallo ruwa ba tukuna, dan wallahi abubuwan da zan faɗa a gaban wamban nan da yawa, dan sai dai ka sake ni ko a kashe ni, dan Jamil shi ne mutumin da anty aisha ta gaya mini ta gayawa cewar ta zo kano, za ta je dubiya. Kuma lambar ƴan bindiga suka kira, suka sanar da cewa ta rasu, na haddace ta, Yasir yayi tracking ɗin ta, Jamil ne, kuma shi ne yake haɗa kai da wakili yake ko waliyyi oho muku dai. Kuma duk abun da na faɗa ina da cikakkiyar hujjata, kuma ba wanda ya isa ya hana ni magana"

A gigice cikin tsawa ya ce "Me ki ke nufi rumaisa? Me ki ke faɗa ne? Jamil fa ki ka ce"

"Malam sake ni, ba gaya maka nayi dan ka yarda ba, amma ko ka so ko ka ƙi, Jamil ne ya bayar da bayanan da aka sace anty aisha, kuma har da shi aka je aka ɗauki gawarta, duk da a cikin kaya yake ya rufe fuskarsa, amma na gane shi"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un " ya din ga maimaitawa jikinsa yana rawa.

Banza ruma tayi masa, ta fice daga ɗakin ta bar shi.

Wata irin rawa jikin Adam yake yi, yana fatan Allah ya sa abun da ruma ta faɗa ba gaskiya bane ba.

Jikinsa yana rawa, ya ɗaukko wayarsa da take vibrating, Sunan Bashir ya gani, ya ɗaga amma ya kasa magana.

"Adam, maganar madam fa ta zama gaskiya, Wakili su ne Smoke, kuma ba su kaɗai ba ne ba, manyan ƙusoshin ƙasar nan SMOKE! Sai dai magana mara daɗi, DSS fa na Kano sun je Abuja sun kama Jamil, an kama shi da laifin fitar da sirrin hukumar ga marasa gaskiya, yanzu haka yana tsare"

Ba tare da ya katse wayar ba, ya ajiyeta yana jin yadda kansa yake wata irin bugawa, zuciyarsa sai harbawa take yi da saurin gaske.

Ruma ta dawo ɗakin ta tarar da shi ya haɗa gumi, sai tsuma yake yi.

"Ka tashi ka bar mini ɗakina, ɗakin maƙaryaciya mai haddasa muku husuma a dangi, ka je ka bawa wadda ka ke so haƙuri, kuma ka kwashe wannan kayan tsubbun da aka binne mini, duk saboda kai".

Kallonta yake yana sake jinjina yadda abubuwa suke gudana, tashi yayi ya bar mata wayarsa da kayan tsubbun, ya fice ya bar ɗakin.

Ta kwashe kayan ta ɓoye, ta ɗauki wayar sa, ta buɗe pin ɗin, ta kira Iman.

Iman na ɗagawa ta ce "Kun tafi ne?"

"Eh, amma yanzu su mama suka shiga"

Ta ce "Ok".

Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga "Mama ya jikin daddy, ya tashi kuwa?".

"Eh, a zaune muka tarar da shi, jikinsa da sauƙi sosai".

"Mama dan Allah ba shi wayar"

Mama ta miƙawa Mahmud, da yake zaune yana hira da su mama da Ammi.

"Hello daughter"

"Jikin ka da sauƙi daddy?"

Ya ce "Sosai Alhamdilillah"

"Get ready, an ce gobe in Allah ya kaimu za a kawo ƙarshen wannan lamarin, zamu haɗu a gaban wambai, kuma ba zamu yi magana ba sai a gaban ƴan sanda"

Ya ce "Am ready in sha Allah, ku yi magana da su Yasir, dama komai na sa ya zama ready, zai tafi Canada, next week"

"Shikenan daddy, na gode sosai".

Hankali kwance ruma ta sha baccinta yau, sai ƙarfe uku da rabi ta tashi, ta na sallar dare, tana roƙon Allah ya basu sa'a.

Shiru tayi tana tunani, lokacin da take mamakin yadda mama ke katse bacci tana sallar dare, yau sai ga abun ya zo kanta.

Takawa kuwa bacci ya gagari idonsa, yana sake nanata Kasancewar Jamil a cikin mummunan aikin nan, to idan rumaisa ƙarya take yi, binciken su Jamil da kama shi da aka yi fa?.

Ammi kuwa ta wani fannin a iya cewa, rashin lafiyar Mahmud gaba ta kaita, domin kuwa sun fi ƙarfe biyu suna hira.
Ta yi iya ƙoƙarin mantawa da abubuwan da suka faru a baya, ya bata labarin makaranta, da yadda ya samu kansa a wurin aiki, amma a cikin hirar ya din ga haɗawa da abubuwan alkhairin Mummy.

Sai dai ga marasa gaskiya, ciki ya ɗuri ruwa, Samha ta din ga kiran wayar baba uwani, dan tabattar da abun da rumaisa ta faɗa a bakinta, amma wayarta ba ta shiga. Gashi ba tare da saninta ba, maman su, ta je ta sanarwa da turaki komai, cikin bala'i da tashin hankali, kuma ta kira wambai ta gaya masa, cewar takawa ya mari Samha, kuma ya ce a kan matarsa ba abun da ba zai yi ba, sai dai zumuncin ya watse.
Ga gefe guda, Hajiya Lubabatu ta kai ƙarar Mahmud, wai Mummy ta saka shi, ya yi wa Jabir duka, ya saka an rufe shi, ba tare da ta san wani station ɗin aka kai shi ba.

Samha ta san muddin aka yi zaman nan, to fa kashin su ya bushe, domin wannan matar ta takawa, ba mutunci ne da ita ba.

Suna tsaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login