Showing 90001 words to 93000 words out of 199108 words
meye, ya yi mata abun da yayi mata, ba zata goya mata baya ba, faɗa za su yi, a bata rashin gaskiya, kuma a kirsheta ace sai ta faɗi abun da ta sani, bayan ta riga ta ce ita ba ta san komai ba.
'Subhanallah, na fasa faɗa, bari na yafe masa, wataran ya na da kirki, amma wallahi ko zai kasheni ba zan faɗa masa komai ba, sai lokacin da na ga dama, bari na lallaɓa na san yanzu ji yake kamar ya kashe ni' sai kuma ta ɗan yi shiru ta ce "To da ya shaƙe ni kuma sai na yi bacci, oho dai? Ta gama abun da Allah ya nufe ta da yi, ta yi salla ta fito dan yunwa take ji.
Adam ya tashi ya nufi ɗakinta, domin ya duba ko ta na lafiya ta gama wartsakewa, sai dai ya jiyo motsi a kitchen.
Ya leƙa kitchen ɗin, ya hango ta taka kujera, tana saka ɗan wake, kamar babu abun da ya sameta.
Abun har mamaki ya bashi, kamar ya yi mata magana, sai kuma ya fasa ya fita.
Baba Uwani na ganin fitar Adam, ta lallaɓo ta hawo benen.
"Sannu ƴar nan, ina fatan bai yi miki komai ba?"
Rumaisa ta waiwayo ta kalli baba uwani ta ce "Yayi mini me?".
"Ai ganin yadda ya janyo ki ɗin nan, abun ya tsoratani, ke ma da ko me yake buƙata kin bashi kin wuce wurin, idan ransa ya ɓaci hankalinsa gushewa yake wasu lokutan, zai iya yi miki illa. Ko dai hakkinsa ki ka hana shi ne?"
Rumaisa ta juyo gaba ɗaya ta kalli baba uwani ta ce "Wane irin haƙƙi kuma?".
"A'a haƙƙin aure mana".
"Meye haƙƙin aure kuma?"
Baba uwani ta ce "Ahh shikenan, bari maganar kawai".
Har baba uwani za ta fita ta ce "Kenan papa da gaske maye ne?"
A razane baba uwani ta waiwayo ta ce "Me ki ka ce?"
"Kin ji me na ce ai".
"Ke waye ya gaya miki?"
Rumaisa ta ce "Ke ce ki ka gaya mini yanzu"
Baba uwani ta ce "Ke, yaushe na gaya miki? Ki ji tsoron Allah"
"Ke ki ka faɗa, wannan ne karo na biyu ki na gaya mini, zan kuma tambaye shi".
"Dan girman Allah ki rufa mini asiri, da wasa nake yi ma fa, dan Allah kar ki gaya masa"
Rumaisa ta juya ta cigaba da saka ɗan wakenta, baba uwani kuwa ta toshe baki ta na fatan, Allah ya sa kar garin neman gulma, ta janyo kwaɓarta ta yi ruwa, domin kuwa ta lura bayan ƙuriciya, har da wauta ke damun rumaisa.
***
"Hajiya Lubabatu, ki na free gobe in Allah ya kaimu". Mummy ta yi maganar da waya a kunneta.
"Ya aka yi ne?".
Mummy ta ce "wurin malam na gidan dutse, zaki rakani, akwai case ne".
Hajiya Lubabatu ta ce "Wane irin case kuma?".
"Ɗan maje ne ya turo mini saƙo, wai ya ji mai martaba zai wakilta turaki, zuwa taron bunƙasa al'adu da harsunan afrika, rainon burtaniya, wai ya ɗauki mutum biyu a matasan yaran nan ya tafi da su, kuma da alama za a samu cigaba, wai ya ji turaki ya ce har da Adam za ayi tafiyar".
Hajiya Lubabatu ta ce "To ba sai su yi ta yi ba"
"Ina ba fa zai yiwu ba, wai ke meyasa ki ke ɗaukar al'amuran nan da sauƙi, komai sai dai shi, duk wannan miyagun fentin da suke tare da shi, komai sai dai a saka shi, ke me zai hana a tafi da Jabir, ga mahmud, ga Jamil nan, ina su yarima jikokin mai marataba, duk ba a ɗau kowa ba sai shi? A dalilin me?".
"Kuma fa da gaskiyarki Jamila"
"Dan Allah ki shirya, na ga da yadda zai tafi ai".
"Ke dole ma, zan shigo da wuri ma yi maganar, ni Jabir ne yadda ki ka san an yi masa asiri,gaba ɗaya hankalinsa ba ya kan harkar sarautar nan, mussman idan abu da adam a ciki, sai ka ce ya yi masa asiri".
"Ni ma na fuskanci kamar aikin da ake yi wa Mahmud ba kamar da ba, zamu haɗu kawai".
***
Ko da Adam ya dawo da yamma, ya iske ruma, tana kwance a doguwar kujera, tana kallon cartoon.
Ya kalleta ya na jiran ya ji ko za ta ce wani abu, suna haɗa ido ta galla masa harara, bai dai tanka mata ba, ya wuce ɗakinsa.
Adam dai hatta abincin sa bai iya ci ba, yadda aka kawo su, haka ruma ta ɗauka ta mayar musu.
bacci sai ɓarawo, kwana ya yi ya na juyi, kuma yau sai ya kasa tashi ya yi sallar dare kamar yadda ya saba, tasbihi ma sai ya kasa saɓanin da, sai ajiyar zuciya da istigfari, ji yake komai ya yi masa zafi, ba ya jin daɗin komai, ko abinci ya kasa ci, ya rasa ta ina zai fara.
Sai gefin asuba barcci ya ɗauke shi, ana kiran salla shi ma ya tashi.
Ko da ya dawo daga sallar asuba, neman wuri ya yi ya zauna, ya cigaba da Adduoi, sai da rana ta ɗaga, sannan ya tashi ya shiga wanka.
Har ya kammala shirinsa, bai ji motsin ruma ba, gashi yau Monday.
Gaba ɗaya ba shi da kuzari, balle karsashi, ya nufi ɗakinta.
Ta na tsaye a gaban mudubi, yau ta fara saka uniform ɗin ta, ta saka skirt ɗin ya zauna a jikinta cif, da taimakon jigidar da ke ɗaure a ƙugun na ta.
Ta saka ƴar cikin, ta ɗaga kai tana ƙarewa wuyanta kallo, ta na shafa wurin da ya yi mata rauni. Uniform ɗin sun yi mata kyau sosai.
Ɗan gyaran murya ya yi ya ce "Haryanzu ba ki shirya ba, balle ki karya yau monday fa"
"Na gama shiryawa, uniform nake ƙarasa sakawa".
Ya juya ya tafi dining ya zauna, da niyyar ko yaya ya ci wani abu, dan ya na jin yunwa, amma ya ji bakinsa babu ɗanɗano.
Ta fito ta ajiye jakarta a kan kujera, ta nufo dining ɗin.
Ta buɗe food flask ɗin abincin, soyayyiyar doya ce da miyar ƙwai.
Ta ce "Bari na yi bisimillah, na ci abincinka, yau ban yi girki ba, ko sallar asuba ba ka tashe ni ba, da safe na yi salla kuma alhaki a kan ka".
Ta kama kujera, ta haye saman dining ta zauna.
Kallon ta yake, yana jiran ta yi maganar abun da ya faru jiya, amma ya ga ba ta yi ba, ta haɗa shayi ta tura masa kofin gabansa, ta ɗau na ta.
Jujjuya cokali ya din ga yi, amma ya gaza kai wa bakinsa ya sha.
"Wai da zafi ne shayin?" Bai ce mata komai ba, ya cigaba da kallon shayin.
"To in ƙara maka madara?" Sai a wannan karon ya girgiza mata kai alamar a'a.
"To ka sha mana, ka ci abincin"
A hankali ya kai kofin bakinsa, sai dai zuƙa ɗayan da ya yi, sai da yayi ta fama sannan ya haɗiye shi, ƙarshe ya tashi ya ce mata, ta same shi a mota.
Kasancewar rumaisa tana son shayi, haka ta haɗe nasa da nata ta shanye abun ta, ta ɗauki jakarta, ta ga tasa jakar ma ya bar ta a wurin, ta ɗauki jakarta da tasa, ta fita.
Ta tarar da shi, ya kifa kansa a sitiyarin motar, sai da ta buɗe motar, sannan ya ɗago. Idanunsa sun yi ja, kamar am zuba masa abu a cikin su, har sai da ta fara fargabar ko hayaƙin ne zai fara fitowa, amma ta ga idon ya tsaya a haka, ya fara jan motar a hankali.
"Wai zazzaɓi ka ke yi ne?" Bai amsa ba, sai lumshe ido da yake ya na buɗewa.
"Yauwwa papa ka san me? Na san ba zaka amsa ba, haka mai sunan baba yake yi, shiyasa bakomai ka ke yi mini na ji haushi ba, na san ka na ji na. Dan Allah ka sai mini lunch box mana, in din ga zuba abinci ina tafiya da shi makaranta".
"Lunchbox na ƴan primary ne"ya faɗa a hankali.
"Eh, ni shi nake so, ƙarami mai kyau" tana cikin maganar traffic ta tsayar da su, sai ga mai alawar madara, rumaisa ta tsayar da shi ta kalli Adam ta ce "Papa ɗan sai mini". Ya kawar da kansa gefe, yana kallon wajen window.
Ta saka hannu ta zuge jakarsa da ke hannunta, ta ga kuɗi a ciki, ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Allah ya kama ka, ga jakarka a hannuna ai, na ranci dubu ɗaya, idan na gama makaranta, na samu aiki, salaryna na farko zan biyaka" sai da Adam ya kalleta jin abun da ta ce, ta bawa mai alwar madara, ta ce ya bata ta duka.
Gaba ɗaya ba shi da kuzarin da zai biye mata, dan haka bai ce mata uffan ba.
Ita kanta ta lura shirun nasa ya yi yawa, shi kuma mamaki yake yadda duk surutunta, da mitar tsiya amma ta yi shiru, ba ta ce masa komai ba, a kan abun da ya faru.
Suna tafe ta cika masa kunne da waƙoƙin indiya, ga abun da yake damunsa, ga waƙarta da ta addabe shi, kuma ya san da ya kuskura ya ce ba ya so, za ta tsiri wani abun.
Sai kuma ta koma waƙe-waƙe, masu kama da habaici "Idan mutum ma bashi da lafiya, shan kunu ba magani bane ba. Idan kuma wani abu ne yake damunsa, rashin cin abinci ba maganin matsala bane ba. Cikin mutum ne zai gaya masa, ulcer ta kama shi na ruwan rumaisa, lalaaalallaaa, alawar madara da daɗi".
Duk ta yi ta gama ya na jin ta, ya kaita ƙofar makarantarsu, ta sauka ta ɗau jakarta, ta shiga.
***
Ya na tsaye ya na saka lense ɗin rigarsa, sai kokowa yake ya saka, amma ya kasa sakawa saboda hankalinsa ba a kan abun da yake yi, yake ba, jin zuciyarsa yake tamkar a kan wuta, wata ƙishirwar baɗini ce ke addabar ruhinsa, abun da yake ji a jikinsa, zai iya rantsuwa da abun da zai kashe shi, tun da Allah ya sa mama ta kawo shi duniya, bai taɓa jin irin sa ba, duk yawon zuwa makaranta da yake yi, da yadda ƴan mata, ke kaiwa suna komowa a gabansa, bai taɓa damunsa ba, amma yau ba gaira ba dalili ƴar mutane ta tsaye masa a tunaninsa.
Mussman jiya da ya ga status ɗin ta, ta yi video ita da sabir, ta ɗora, ya kalli status ɗin nan, bai san adadi ba, sai da ya fara bawa kansa haushi. Kuma ya kwanta bacci ya din ga mafarkinta, mafarkin da sai ya kai shi ga danganawa ya tsarkake jikinsa kan ya yi salla.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya mayar da hankali, ya gama abun da yake yi, ya fita ya yi wa mama sallama ya tafi.
Sai dai a ƙasan zuciyarsa ya na jin, da zai samu dama ya ganta, wataƙila atleast, zai rage abun da yake ji a tsakanin ƙirjinsa zuwa zuciyarsa, amma ta yaya?.
***
Sanin halin rumaisa na rashin isasshen saiti, ya sanya ba ya wasa da abun da ya shafeta, duk da halin da yake ciki, da lokacin tashi ya yi, haka ya tafi ɗaukota.
Sai dai ya shafe mituna goma sha biyar, a tsaye, bai ganta ba bai ga alamarta ba.
Sai da ya ɗan tsorata, ya fara addu'a Allah ya sa ba tafiyarta ta yi gida ba, saboda abun da ya faru.
Har zai shiga mota, ya shiga cikin makarantar yana duddubawa, can ya hangota, a cikin liluka, ta ajiye ɗan ƙaramin hijjabinta, sai fama take yi kai ka ce wata ƴar primary 2.
Sai da ta hango shi, sannan ta saukko, ta ɗauko jakarta da hijjabinta, ta zo ta wuce shi, ta tafi mota, ba tare da ta ce masa uffan ba.
"Wallahi idan ka kuma daɗewa ba ka zo da wuri ba, sai na tafi gida, idan na ɓata a hanya shikenan"
Ganin ya zame mata tamkar kurma, ya sanya ta ɗan fara tsorata, shirun na sa yayi yawa, dan kafin su yi aure ne yake da yawan shiru, da suka yi aure ta fuskanci yana da baki, amma daga jiya zuwa yau, shirun ya wuce hankali.
Ta yi shiru ta zuba masa ido, damuwa kwance a fuskarsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi, ta daina yi masa surutun, da neman magana.
Har suka je gida, tana tunanin, ko dai wani abun ta yi masa, yake jin haushinta, har ya daina cin abincin?.
A karo na farko tun da ya kaita makaranta, ya tarar da ita a falo, ta duƙufa ta na rubutu, bai san me take rubutawa ba, ya nufi in da take ya tsaya a kanta, takardar kifi ce, da wani math a jiki, da gani question paper ce, take ta fama sai ta yi soloving, ko a ina ta samo takardar oho mata.
Ƙafarsa ya saka ya daki ƙashin bayanta, take ta banƙare tare da ɗan yin ihu, dan ta ji zafi.
Ya zauna a kan kujera, ya ce "Samo mini abun da zan ci".
Sai da ta ɗan tura baki, a ranta kuma ta ji daɗi da ya kulata, har ya nemi cin wani abu.
Bayan ta tashi ya zauna ya na duba litatafan ta, maths dai gashi nan, ta na cin abun ta, daga assignment har classwork.
Sauran subjects kuwa, har 2/10 ruma ci take.
Assignment ɗin ma ba yi take yi ba, babu wanda ya fi kunna shi, har haushi ya saka shi dariya, irin subject ɗin basic technology, an basu assignment a kan cewa, a matsayin ka na matashin ɗan makaranta, wani abu ne zaka iya ƙirƙira, da ka ke ganin zai amfani al'umma da ƙasa baki ɗaya.
Shafi guda ta ware, ta zana malamin nasu, riƙe da maka a hannunsa, yana bayani, sai dai a real portrait of him, kai ba ka ce ita ta yi zanen ba, very accurate, a matsayin amsar tambayar.
Ya yi shiru yana shafa haɓarsa, wasu lokutan yarinyar kamar bil'adama ba.
Ta dawo da plate a hannunta, ta ajiye masa a gabansa.
"Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata litattafanta"
"Me na yi?"
"Karatun ne ba kya ganewa, ko kuma meyafaru ki ke cin wannan makin".
"Ni fa bana gane turancin da ake yi, kuma ba za ayi wa mutum bayani da hausa ba, wai ba a hausa a makarantar, yanzu haka kuɗin vanacula ya kai dubu uku ake bi na, wai idan ka yi hausa ɗari biyu, ina zan iya na ce idan ka zo a gaya maka zaka biya".
"Saboda ke ki ke nemo mini kuɗin ko? Kin taɓa ce mini ga abu baki gane ba, in koya miki?"
Ta yi shiru, ta kawar da kanta gefe, matsawa ya yi kusa da ita, yana kallon wuyanta, ciwon da ya ji mata, ya fara baƙi.
Ya kai hannunsa wurin, amma ta riƙe hannun ta ce "Meye haka?".
"Ciwon zan gani, haryanzu ban ji kin yi mini magana a kai ba".
Ta sunkuyar da kanta ba ta ce komai ba.
"Kin rantar mini dubu ɗaya, kuma kin ce zan biya kuɗin vanacula da ki ka yi, amma yaushe zaki biyani??
Ayshercool
08081012143
Ban da kira please, what's app only 🙏 masu jiran document, idan sai an kammala 1k ne document.
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Shiru ta yi masa, ta kasa magana, saboda yadda take jin wani iri a jikinta.
Ya janye hannunsa ya kalleta ya ce "Ba a bani abinci a plate".
Ta kwaɓe fuska ta kalleshi, ta lura adam akwai saka aiki, ba gaira ba dalili.
Ta tashi ta ɗau plate ɗin, sai da ta zubo a flask, da cokali, da ruwa ta kawo masa, ya ce mata ta kunna masa tv.
Sai da ta ji kamar ta yi tsaki amma ta fasa, ta kunna ta dawo ta zauna, sai dai ta lura da yanayin sa, abincin ba wai daɗi yake yi masa ba, ci kawai yake yi.
"Papa maiyasa idonka yake hayaƙi, idan ka yi fushi?"
Yayi dariya ya ce "Sai ka ce generator, ko wani murhu, saboda gani jarababbe"
Ganin ya mayar da maganar shirme, ya sa ta yi shiri.
Kaɗan ya ci, ya rufe, a lokacin ta fara ƙoƙarin mayar da litatafan ta, ya ce "Ban gama da litattafan ba".
Ya karɓa ya cigaba da duddubawa, a hankali ya din ga bi ɗaya bayan ɗaya, ya na sake yi mata bayanin darussan da aka koya mata, sai a lokacin ta ƙara ganewa ta kalleshi ta ce "Ai da za a din ga yi mini da hausa, da sai na fi ganewa".
"No, da turanci suke magana, ni ma da turancin zan din ga yi miki magana".
"Ashe za ayi zaman kurame, dan bai fi kalmomi, sha biyu na sani da turanci ba"
Bai bata amsa ba ya cigaba da cewa "Zan saka a ki islamiyya, ko ba na nan, sidi zai din ga kai ki yana ɗauko ki, sannan wannan zanen da ki ka yi, ki goge shi, ki rubuta wani abun".
"Ba ka san ma'anar zanen nan ba, duk makin da na ci zan zo na nuna maka" ta ƙarasa maganar tana tattare litattafan ta, a cikin jakarta, daga nan ta mayar da hankali kan abun da yake kallo.
Film ne na Hollywood, sai dai yadda ake nuno matan, bai yi wa rumaisa ba, ta din ga kawar da kanta gefe, ba ta yi aune ba ta ga ana kiss, da sauri ta saka hannu ta rufe idanunta, ta sunkuyar da kai.
Sai dai ta ɗaga kanta, ta gefen ido, ta ga takawa ko a jikinsa, ya cigaba da kallo.
"Ka canza mana wannan tashar"
Ya ce "Saboda me?".
"Ba ka ga abun da ake yi ba?".
"A ina?".
Cikin ƙulewa ta ce "Ka na gani ana abun da bai kamata ba, amma ka ke kallo, mama ta ce ba kyau, a gida ba a bari mu kalli irin wannan film ɗin ma fa, ka daina gani za ka makance".
Ya kalli cikin ƙwayar idonta, iya gaskiyarta take gaya masa, bai ga alamar wasa a abun da take faɗa ba.
"Ko zamu gwada?" Yayi maganar yana tsareta da ido.
"Waro masa ido ta yi ta ce "Mu gwada me?".
"Kiss ɗin"
Miƙewa tsaye ta yi, ta ce "Na shiga uku" har da haɗawa da gudu, ta bar masa falon.
Shi a zahiri ma ba film ɗin yake kallo ba, yanzun ma fitowa ya yi, domin ragewa kansa damuwa, da kaɗaici, atleast ya ɗan ji releif kaɗan, ya saka a ransa zai yi mai