Showing 48001 words to 51000 words out of 199108 words

Chapter 17 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

800

masa, yayi gaba rumaisa ta bishi a baya.
Sai da suka je ƙofar ɗakin sannan ya tsaya, ya kalleta ya ce "Ƙwanƙwasa ki fara shiga"

Ta matsa gaban ƙofar, ta ƙwanƙwasa sannan ta buɗe ta shiga da sallama babu kowa a ɗakin, sai iman da ke kwance, hannunta ɗauke da cannula, an rataye robar ruwan da aka gama saka mata a drip stand.

Shiga ya yi shima, sai dai babu kowa a ɗakin sai ita kaɗai.

Da sauri rumaisa ta ƙarasa gaban gadon tan faɗin "Subhanallah, Anty Iman, baki da lafiya ne?" Sai dai ta tarar bacci take yi.

Ta kalli mai sunan baba ta ce "Amma ya naga babu kowa a wurinta" shirun da yayi mata ya sanya, ta tuna ta yi tambaya ba a gurbinta ba.

Da sauri ta ce "Bari na duba waje, ko zan ga wanda yake zaune tare da ita". Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya a tsaye, ya sake kallonta tana kwance cikin doguwar rigar material, dogon gashin nan ya sha ribbon, duk da ya ɗan hargitse, ga farar fatarta gwanin sha'awa, babban abun burgewa da jikinta, bai wuce wuyanta ba, duk da ba ta da ƙiba, amma tana da irin wuyan nan, mai guru-guru.

Da sauri ya sunkuyar da kansa yana a'uzubil'ahi.

Zagayawa rumaisa ta shiga yi a cikin asibitin, tana mamakin waye yake zaune da iman a asibiti, ya bar ta ita kaɗai babu kowa?

A hankali Iman take furta "Ammi, Ammi ruwa, ƙishirwa nake ji" yana jin ta, yayi shiru, kamar babu kowa a ɗakin.

Tun bayan farfaɗowarta, kasancewar ciwon kan baya sauka, ya sanya likitocin, suka yi ta yi mata allurar barci, da sai yanzu ta saketa ta tashi.

Duk da tana cikin ciwo, sai da ta razana da ta ganshi, a tsaye yana danna wayarsa.

Tunani take yi ko a mafarki take, ta miƙa hannu jikinta yana rawa, tana ƙoƙarin ɗaukko robar ruwan da ke kan side bed.

Sai a lokacin ya motsa, ya ƙarsa, ya ɗau kofi, ya zuba ruwan ba tare da ya kalleta ba ya ce "Tashi ki sha"

Cikin tsananin tsoro ta ce "Bani in sha a kwance, ba zan iya tashi ba"

Miƙa mata ruwan yayi, ya ga iya gudun ruwan ta, ta fara ƙoƙarin sha a kwance, ya karɓa kofin ya ce "Tashi!"

Kamar zata fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri kaina ciwo yake yi"

Haushi ne ya kama shi, gani yake kawai tsabar langwai ne, da iskanci. Ya saka hannu ya ɗagota gaba ɗaya, hakan yayi dai-dai da shigowar nusaiba.

Wani irin ihu ta saki, ta riƙe hannunsa, hawaye na bin fuskarta, sabodaa ji ta yi, kamar kanta ya rabe biyu.

Da gudu Nusaiba ta ƙaraso tana faɗin, "Wanene wannan, bawan Allah lafiya?" Tayi maganar tana yi masa kallon sani, amma ta manta a ina ta san shi.

Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Wane irin shirme ne zaki tafi ki bar mara lafiya ita kaɗai, wace irin jinya ce haka?"

Gaba ɗaya ruɗewa nusaiba ta yi, ba ta san waye ba, amma kwarjinin sa ya razanata, ta ce "Likita ne ya ce a bani jininta na kai gwaji yana buƙatar result yanzu, ammi kuma ta riga ta tafi gida ta je ta huta, shine na je lap ɗin asibiti, suka ce ba sa yi, shi ne na fita waje, da takawa nake jira ya zo ya kai, likita ya ce lallai yanzu yake so"

Tsaki yayi, ya kalli iman ya ce "Ke kuma cikani" wata irin kunya ce ta kamata, dan ba ta san ta riƙe shi haka ba.
Ta sakar masa riga, ta karɓi ruwan ta fara sha.

"Ita kuma wannan ma shiririciyar ko ina ta tafi oho mata".

Rumaisa kuwa lungu da saƙo na asibitin take ta bi, har ta gaji ta kama hanyar komawa ɗakin, kawai ta hango motar takawa, yayi parking ya fito daga motar, hannunsa riƙe da leda.

Aikuwa ta nufe shi, babu tsammani ya ganta a gabansa.

"Dama kai ne a wurin Anty Iman? Haka ake jinyar mutum dama, ka yi tafiyarka ka barta? Kai idan aka yi maka haka zaka ji daɗi ne?"

Sororo yake bin ta da kallo, yadda take yi masa haƙilon masifa kamar babarsa.

"Ya ina magana kana kallona, sai wani abun ya sameta? Kawai ka ɗau mota ka tafi yawonka, ka bar mara lafiya ita kaɗai? To wallahi sai na gaya wa ammi" banza yayi mata, ya nufi cikin asibitin, rumaisa kuma ta bishi tana cigaba da mita.

Cike da shiga taitayi, Nusaiba ta bawa mai sunan baba haƙuri, ita dai ba ta san waye ba, amma ta tsinci kanta da shakkarsa.

Ta kalli iman ta ce "Iman, me zan baki ki ci to, tun jiya baki ci komai ba, an ce lallai ki samu ki ci wani abun, ga abinci ga fruit wanne zaki ci?"

Iman ta girgiza kai ta ce "Na ƙoshi, bana son cin komai" mai sunan baba a ransa yake jinjina halin mata, su a rayuwarsu ta duniya komai sai an lallaɓasu? Abincin ne ba zata ci ba, sai an yi ta rarrashinta, alhalin ta san kanta zata cuta idan ba ta ci ba.

Takawa ne yayi sallama, ya shigo hankalinsa a kan iman, ya ƙarasa gaban gadon ta.

Nusaiba ta ce "Maman sabir, yaushe ki ka zo?"

"Tun ɗazu muka zo ni da mai sunan baba, ashe wannan ne yake jinyarta, ya tafi ya barta ita kaɗai" tayi maganar tana nuna Adam.

Nusaiba ta ce "Eyya, ni ce tare da ita, jininta na tafi kai wa a gwada, ba yadda zan yi ne shiyasa na tafi na bar ta".

Rumaisa ta ce "Au na zata shi ne ai".

Ta ƙarasa ta leƙa fuskar iman ta ce "Anty Iman ya jiki?".

Cikin ƙarfin hali ta ce "Da sauƙi Alhamdilillah ".

Adam ma lallaɓata yake yi, ko za ta ci wani abun, amma ta ce ita ba ta cin komai, ya din ga rarrashin ta, ta ce tuffa take so, takawa ya tashi ya ce bari ya je ya duba, ya sayo mata.
Daga mai sunan baba har Adam babu wanda ya kula wani, takawa na tafiya, iman ta fara ƙoƙarin kwanciya, mai sunan baba ya kalli Nusaiba ya ce "Ke, zuba mata abincin nan" gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa.

Rumaisa ta jinjinawa Nusaiba kai, dan ba ruwansa da baƙunta yanzu sai ya balebalesu da masifa.

Romon kifi ne da dankalin turawa, sai ƙamshi yake yi, idon iman ya cika da hawaye, dan ko ƙamshin abinci ba ta so, ya karɓa ya je gaban iman ya ajiye shi, ya tsaya mata ƙiƙam a ka, ba tare da ya furta komai ba, ta kama cokali, ta fara cin abincin nan, jikinta yana rawa, saboda tsoro da fargaba, ga wata irin Muguwar kunya, dan ba ta saba cin abinci a gaban maza ba, ko a taron mata ba iya ci take ba.

Sai da ta ci sosai sannan cikin faɗa  ya ce "Kuna sane kuke wahalar da iyayenku, dan kun ga suna ta taku. Ke kuma tashi mu tafi" yayi maganar yana kallon rumaisa.

Ta tashi, kamar ta tuntsire da dariya, daga Nusaiban har iman ɗin kamar ka ce kyet su zura da gudu, saboda tsoro.

Ruma ta ce "Anty iman, Allah ya ƙara afuwa".

Cikin sanyin jiki ta ce "Amin maman sabir na gode".

Bayan tafiyarsu Nusaiba ta ce "Ke iman, wannan jarabbaben mutumin fa?"

"Yayan rumaisa ne" ta bata amsa.

"Kam bala'i, yau na ga wanda ya taka takawa iya tsare gida, daga zuwa ya hau ni da masifa"

Iman ta sunkuyar da kai ta ce "Mhmm, baki ga komai ba"

Babu daɗewa takawa ya dawo da tuffa, Nusaiba ta bashi labarin abun da ya faru, bai ce komai ba yayi shiru, dan shi kansa jin kan mai sunan baba yana bashi mamaki.

***
Iman jikinta yayi sauƙi, mama ma ta je asibitin ta dubata, ta warware, sai dai lokaci lokaci, kan ya kan matsa mata da ciwo, aka sallameta daga asibiti. Sai dai tun da ta koma gida, washegari ta sake tashi da ciwon kan, sai dai ta yi ƙoƙari ta jure, saboda ba ta san sanya ammi a damuwa.
A ranar da aka sallameta daga asibiti ranar Jabir ya dira Nigeria, daga wurin duba mahaifinsa.
Hajiya Lubabatu ta yi mamakin ganinsa ya dawo, dan sun yi da shi zai yi sati uku a can kan ya dawo.

"Wai kai Jabir, menene ya dawo da kai tun a yanzu?"

"Bakomai, ji na yi an ce iman babu lafiya, shiyasa na dawo ita ma na dubata".

Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Iman ɗin, kai a wa? Meye haɗinka da ita?"

"Bakomai zumunci kawai".

"Ban gane zumunci ba? Jabir kar na zo na ji wata magana saɓanin wadda nake son ji, ka san halina dai ban da kyau"

"Babu wata magana da zaki ji, kawai dai ina yi ne saboda Adam" tsaki tayi, ta shiga wata sabgar daban ta ƙyaleshi.

***
Yau tun da safe ammi ta kira mama, ta sanar mata da Adam zai zo wurin rumaisa, domin idan da wani abu da take buƙata ta gaya masa na game da shirin biki.
Amma mama ta ce "A'a hajiya, a ƙyaleta kawai, duk abun da aka yi Allah ya amfana"
Ammi ta ce "Ai da ni da ke, babu ruwanmu, namu ido abu ne na ma'aurata, dan haka yakamata su din ga tattaunawa domin su fahimci junansu!.


Ayshercool.
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*



Mama ta ce "Ai kin san masu sarauta ba sa son wauta, ita kuma ƴar taki sai fatan shiriya"

Ammi ta yi dariya ta ce "Rabu da su, namu addu'a da ido, ai rumaisan ce dai-dai shi".

"To, Allah ya iya mana ya jikin iman kuwa?"

Ammi ta ce "Jiki yayi kyau mun gode Allah, har tana iya barci yanzu, in da nake ta yi wa Allah godiya, an ce zuciyarta lafiya ƙalau wannan karon, ciwon kai ne dai da razana take yi".

Mama ta ce "Allah sarki, sai a dage da addu'a, a haɗa da na islamic, kin san kana da ido ba na ganin gari ba, mussaman ita da take tubarkallah Masha Allah, kyau kamar ita ta yi kanta, sai ana dagewa da addu'a"

"Wallahi maman rumaisa ana yi dai-dai gwargwado, kin san sabgar iyali ce, sai dai ka yi iya yin ka ka bar wa Allah sauran, idan wannan ya ce wash anjima wannan ya ce wayyo, kuma duk kai kaɗai ranka, sai fatan ɗaukin Ubangiji"

"Haka ne wallahi, dama shi ne mai tafiyar rayuwar gaba ɗaya, ba dan haka ba idan an kira ka, ba zaka amsa ba, ko yaya ace kula da ragamar gida a kan mace itakaɗai, akwai ƙalubale, Allah ya raya mana su yayi musu albarka".

Ammi ta ce "Amin ya Allah, dan Allah maman rumaisa idan da abun da take buƙata kar a saka ta yi ƙwauron baki, duk ta gaya masa, tun da rayuwa za su yi inuwa ɗaya, a ƙyaleta ta faɗi abun da take so".

Mama ta yi murmushi ta ce "Na lura son kan ku yayi yawa, kin fiye son ƴar nan taki, babu mai takurawa ɗana nima ehe".

Ammi ta yi dariya, cikin jin daɗin hirar ta su, suka shiga tattauna yadda yakamata abubuwa su tafi game da auren.

Kamar an jefota rumaisa ta faɗo ɗakin mama, mama ta ɗaga kai ta kalleta ta ce "To madiga, yau babu sallama?".

"Na yi fa, baki ji bane ba, yunwa nake ji"

"Kai rumaisa ni wannan ci naki yana bani mamaki, gidan miji zaki tafi, maza ba sa son mace mai shegen cin tsiya, kuma ba ma cin kirki ba, kina ci kina wasa ba zaki zauna ki mayar da hankali ki ci lokaci guda ki tashi ba".

"Taɓ, aikuwa mama sai in din ga dawowa gida ina cin abincin, Allah ya halicci bawa da ciki, wani ya ce wai baya son mace mai ci"

"Ke tafi can ki bani wuri, yauwwa sirikarki ta ce, in an jima mijinki zai zo"

Rumaisa ta yatsune baki ta ce "Waye mijina kuma?"

"Ban sani ba" Mama ta bata amsa.

"Mama to ni kawai sai ki wani ce masa mijina"

Mama ta ce "Ke, nutsu ki saurareni, bana son wannan shirmen da wautar taki, dole ki shiga hankalinki, aure ba abu ne na wasa ba, wallahi idan ya zo, ki ka sake ki ka yi wani abu na shirme ba dai-dai ba, wallahi ni da ke ne.

Namiji duk in da yake, ko ba mijinki ba abun girmamawa ne, balle shi da zai aureki, ki ka sake ki ka yi masa wata wautar ko fitsarar, sai kin ga yadda zan yi da ke".

Rumaisa ta yi shiru ta sunkuyar da kai, tana tunanin shi meyasa ba ayi masa faɗan ya daina yi mata abun da yake yi mata, ko dan tun farko ba a san ita me yayi mata ba?.

"Yanzu me ki ke ganin za ayi masa wanda za'a tarbe shi da shi?"

Kai tsaye ta ce"Ruwa"

Abdallah da yake jiyo maganar ta su daga tsakar gida ya shigo, ya ce "Mama, ita fa wannan yarinyar taki, kamar namji take ba ta san komai na rayuwa ba, sai an karanta mata yadda yakamata".

Ya kalleta ya ce "Ke, ki nutsu malama, aure zaku yi, so muke idan ki ka tafi kin tafi kenan, ba zaki dawo mana gida ba, dole ki din ga yi wa mutane abun da ya dace, har zancen ma zan koya miki. Yanzu mama ki kawo kuɗi, mu sayo kayan meat pie, in taya ta mu yi, sai a haɗa masa da lemon roba da abinci"

"Duk shikaɗai? Gaskiya ni ba zan iya aikin wani meat pie ba, bacci zan yi, ni idan ya zo ma ban san me zance masa ba? Sai dai Huzaifa ya rakani, ko Yasir"

Abdallah ya ce "Ka ga shashasha, tashi ki je ki yo cefanen meat pie ɗin nan"

Gaba ɗaya rumaisa ga rasa gane dalilin da ya sanya, kowa laifinta yake gani a kan Adam, kowa so yake lallai sai ta kyautata masa, haka mama ta saka baki, aka aiketa sayen kayan meat pie da za a karɓi Adam.

Abdallah da Huzaifa suka sakata a gaba, a kan aikin, amma ta ƙi mayar da hankali, ƙarshe su suka yi aikin suka ɗai.

Yaya Usman ne ya dawo, ya tarar da su Abdallah suna ta kai kawo, an yi girki, kamar dai wani abu mai muhimmanci na shirin faruwa.

"Wai lafiya na ga ana ta wani shiri, ko bikin aka fara tun Yanzu babu labari, abu na masu hannu da shuni"

Huzaifa ya yi dariya ya ce "Yaya Usman, sirikin ne zai zo, yau zai fara zuwa zance, shi ne ake shirya masa abinci, kar azo a ji kunya. Gara mu  kankaro kanmu, sai dai ita yarinyar ce ba ta da hali, ana saita ta a hanya tana fizgewa".

Usman ya nufi ɗakin mama yana faɗin, "ubanta kuwa za ta ci wallahi, dole a saita ta. ke kina ina?" Yayi maganar yana shiga ɗakin mama, rums ta yi ɗai-ɗai tana kallon Tv, tana cin kantu mai gishiri.

"Ba zaki tashi ki fara shiri ba, yaushe ya ce miki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login