Showing 150001 words to 153000 words out of 199108 words

Chapter 51 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

835

katsewa sannan ya ɗaga.

"Yaya umar"

"Na'am".

"Ashe kuɗin auren zaku kai, na zata kawai zuwa kayi ka amsa kiran da mai girma turaki yayi maka?".

"Na yi garaje ko, na kai kuɗin auren ba tare da kim ce mini kin amince ko a'a ba. Tun da rumaisa ta ce mini, akwai wanda ki ke so".

Iman a ranta ta ce 'Kai ɗin ne dai, kai nake so yaya umar'.

A zahiri ta ce "Ni ba wanda nake so fa"

Har cikin kansa ya ji shagwaɓar da tayi masa, ya sake gyara zaman wayar sannan ya ce "To ya aka yi?"

"Bugowa na yi, na maka ya ka je gida, Allah ya ƙara buɗi".

"Masha Allah, ayi haƙuri abun talaka na san kin fi ƙarfin hakan"

Iman ta ce "A'a ban fi ƙarfin haka ba, Allah ya yassare maka".

"Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, thanks" ya katse wayar.

Nothing romantic mai sunan baba ya sani, kawai ayi abun da ya dace, dan soyayya in dai irin yadda Aliyu da Abubakar suke me
Jabir kuwa tamkar zai yi hauka, haka ya ji da aka ce, wai an kai kuɗin auren iman, bai taɓa tunanin da gaske yana son ta ba sai yanzu.
A baya matsananciyar sha'awarta ce take addabarsa, tun ranar da ciwonta ya tashi, yana nan shi ya ɗauketa ya kaita mota.
A baya bai taɓa tunanin jin son ta ba, saboda tana girmama shi a matsayin yayanta, shi kuma ƙanwarsa, tun daga ranar da ya ga jikinta, ya sanyawa ransa lallai sai ya mallaki iman, ko ba komai, idan ka samu irinta a yaranka, ka samu kadara, saboda kyakywar bafulatanar yarinya ce.

Washegari, ammi ta bayar order yin girke² snacks, ta ce a kai gidansu rumaisa, ruma ta ce gida za ta je, ayi sabgar nan da ita, saboda wauta ta cewa Iman ta shirya, su tafi tare, laila ta ce ya za ayi ta je kai tukuicin kuɗin aurenta, ban da wauta irin ta ruma.

Ammi ta ce laila da sidi sai su kai, sai su tafi da rumaisa, ruma ta ce ga Mahmud, ba sai sidi ya je ba.
Ammi har mamakin yadda Mahmud yake yi wa rumaisa biyayya take yi, duk abun da ta ce masa yayi, ko musu baya yi yake aikatawa.

Hakan kuwa aka yi, da shi da laila, da rumaisa, suka kai kayan nan, mama ta din ga mitar wannan kayan sun yi yawa, dan sun kusa kai ɗaya da kuɗin auren, banda uban lemuka da naman kaji.

Laila sun gaisa da mai sunan baba, sai dai sama-sama, yaya Abubakar ne mai sakin fuska, sai usman sarkin tsokana.

Laila ta daɗe a gidan, suna hira, take bawa mama labarin yanayin zamanta a canada, da iyalinta, take gaya mata a cikin watan, mijinta da yaranta suma zasu zo hutu.

Laila ta yi wa mama sallama, ta cewa rumaisa, za ta je ziyarar ƙawayenta da ke Kano, idan Mahmud ne ya zo ɗaukarta, ko sidi sa biya su ɗauke ta.

Rumaisa kuwa baki yaƙi rufuwa dan murna.
Yasir ya samu ruma ya ce "Ke, zo mu yi shawara, nifa zan saiwa mai sunan baba akwatunan biki".

Ruma ta ce "Da wani kuɗin?".

"Ke baki san na kusa fara shigo da wayoyi, da computer daga china ba, ni da abokina muke tara kuɗin, yayansa ne zai tsaya mana, mama ma ta san zancen, amma a kuɗin dole ni zan saiwa mai sunan baba akwatunan lefe"

Rumaisa ta din ga bayar da shawarwari, na arziki da na shirme.

Bayan la'asar, Mahmud ya dawo ya ɗauki rumaisa, suka biya suka ɗauki laila, albarkacin rumaisa, duk da ko a baya, laila da Mahmud ba a ga maciji, amma suka din ga hira yau sosai, hirar da ba su taɓa yi a baya ba.

Jabir kuwa, Kasa jurewa yayi, ya ɗauki mota, ya tafi gidansu takawa, wani irin kishi, da zafin zuciya yana ta azalzalarsa, ya shiga part ɗin su, sai dai kai tsaye da ya shiga babu kowa a falon, ya tafi ɗakin iman.

Tana zaune a kan gadonta tana danna waya, kawai sai ganin mutum tayi a tsaye a kanta, yana huci.

Sai da ta tsorata, ta ce "Uncle J, lafiya kuwa?".

"Ban sani ba, tsohuwar munafuka, ni zaki yaudara? Wato dama wancan banzan talakan matsiyacin ki ke so? Ya rasa abun da zai kawo kuɗin aurenki sai dubu ɗari da hamsin, ko da yake babu mamaki, tun da kema tsatson tsiyar ce, ƴar masu kiwo ƙafa babu takalmi duk da babu wanda yake da tabbacin hakan ma, munafuka mayaudariya".

"Uncle j ya zaka din ga zagina ne?, Nifa ban taɓa cewa ina sonka ba, na sha gaya maka a baya".

"Dalla rufe mini baki, har ke wani zaɓi ne da ke, kina wulaƙantacciya"

Iman tayi murmushi ta ce "Tun da ni wulaƙantacciya ce, sai ka bari mai sona saboda Allah, ba dan jikina ba, ya aureni".

"Ni kike gayawa haka ko? To ayi auren mun gani, zaki gane kurenki ne".

Ya juya ya fita fuuu, ta zuba bishi da ido, a falo yayi kaciɓis da ammi, ammi cikin tuhuma ta dube shi ta ce "Ahh jabir daga ina kuma?".

"Wallahi baki yi wa kanki adalci ba, a da ne ake aibata ki, nake karewa, ashe haka kike, waccan ƴar matsiyatan ta zigaki kin hanani ƴa, ƴar ma da ba wanda ya san tushenta, balle a san daga gidan uban wa take, nayi jihadi na ce zan aureta amma aka wulaƙanta ni".

Ammi ta ce "Jabir, ni ka ke gayawa haka?".

"Na faɗa, ai kema kin san baki yi mini adalci ba, mun gama magana da ke, ki je ki canza magana, har da yi wa mahaifiyata sharri, saboda tsabar mugunta da son zuciya, ban sani ba ko dan ba ƴar ki ba ce ba, ya sanya kika zaɓa mata talaka matsiyaci".

Ji yayi an ja shi baya da ƙarfin gaske, an sauke masa zazzafan marin da ya kasa gane daga ina marin ya fito.

Mahmud ya fuskance shi sosai ya ce "Idan kana cin ƙasa ka kiyayi ta shuri, babarka ce babbar annamimiyar da ta haɗa komai, ita ta zo ta ce ba ta son auren, ta koma kuma ta ce ba haka ta ce ba, idan ka kuma yin mummunar magana a kan ta, sai na yi maka dukan tsiya wallahi".

Duk kallon mamaki suke yi wa Mahmud, banda rumaisa da ta dubi Mahmud ta ce "Ai wallahi duk ɗa nagari abun da zai yi kenan daddy. Kuma mun ji, ni da yayana talakawa ne, amma masu mutunci da sanin darajar kai.
Kuma idan har za a bawa mutum aure saboda nagartar da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya faɗa, wallahi sai an bawa mai sunan baba sau dubu ba a baka ba".

Jabir ya kalli Mahmud ya ce "Ni ka mara?".

"Waye kai ɗin da ba zan mareka ba?"

Jinjina kai yayi ya fita, yana huci, sai dai ya san ko a ido, ba zai iya dukan Mahmud ba.

Kasancewar baba uwani tuni mummy tayi bikonta, domin kuwa ta gane cewa dole-dole tana buƙatar baba uwani a cikin al'amuranta, domin sai ta na sanin halin da ake ciki a sashin ammi, sannan za ta san ta ina za ta dinga ƙulle-ƙullenta.
Ita ma baba uwanin Kasancewar ta rayu da mugun son abun duniya, ya sanya babu tunanin komai, ta komawa mummyn.

Dan haka ko da wannan al'amarin ya faru, ita ta lallaɓa ta kira Mummy a waya ta labarta mata.


Ammi kuwa ta rasa meya kamata ta yi ne? Farincikin ɗan da aka rabata da shi, aka cusa masa ƙiyayyarta ya damu da ita, har ya shigar mata faɗa? Ko kuma fargabar abun da ka iya biyo bayan abun da ya aikata ɗin?

Washegarin da abun ya faru, shine lokacin da suka shirya tafiya gombe, wanda tafiyar har da ammi, har da laila da rumaisa, nusaiba iman da kuma sabir.

Rumaisa taga karamci, kamar su cinyeta, ko ina ta shiga ayi ta nunata ga matar takawa, ga kuma ɗan sa ɗan marigayiya Aisha.

Haka zalika sun yi murnar zancen auren iman, da yayan rumaisa, da ammi tayi musu, maman laila ta daɗe rasuwa, sai mahaifinta da ƴan uwanta, kasancewar saukar su iman an ƙara sati guda, ya sanya ammi ta kashe wayoyinta, dan kar ma a kirata a ɗaga mata hankali, a kan abubuwan gidan nan, sai da suka kwana uku, sannan suka dawo kano.

Rumaisa ta samu abun arziki kashi-kashi.

Mummy kuwa ta rasa in da zata saka ranta ta ji daɗi, domin kuwa alkadarinta ya tasan ma karyewa, tun da labari ya isaketa cewar Mahmud ya mari  jabir, saboda ya kare ammi, abun ya dungunzuma hankalinta ainun, me hakan yake nufi kenan? Asirin giwa ya fara cin sa? Zai karkata ya koma wurinta, domin shishshigin da yake yi a sashinta yayi yawa, dan ko kai kuɗin auren iman, labari ya isketa, shi ne ya jagoranci ƴan uwan su rumaisa har gidan turaki.
Sai dai ta lura, kamar rumaisa ke taka muhimmiyar rawa, wurin rusa mata shirin da take yi, ta hanyar ziga Mahmud, sai dai ta rasa ta ina yakamata ta yi maganin rumaisa. Sannan ta ƙudiri yadda ta ƙwace Mahmud, ba zata bari ya koma ga ammi ba, dan ba zata gama wahalarsa ba, sannan rana tsaka ya koma wurin uwarsa ba, dan idan haka ne, gara ta nakasta shi yadda ba zai moru ba.

Mummy na tsaka da tunanin meye abun yi, Hajiya Lubabatu tayi mata dirar mikiya, ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba, a kan marin da Mahmud ya yi wa jabir.

Aka yi sa'a kuwa yana nan, mummy ta ce "Haba lubabatu, mutuwa ma na kunyar idon mahaifi, ya a gabana zaki zo kina zagar mini ɗa? Ai sai ki haɗa su ki yi musu nasiha, tun da duk ƴaƴanki ne".

"Ba wani ƴaƴana, kema ki daina Wannan ƙumbiya-ƙumbiyar, ki fito kan ki tsaye ki daina wannan munafuncin, kina riƙon Mahmud ne da cikar naki muradin".

Mummy ta ce "Ni tsakani da Allah na riƙe shi, sai ma dai tayaki da nake yi, naki muradin ya cika"

"Jamila, wallahi kar nake kallonki. Kai kuma zaka ga abun da zai biyo ba, ban da tsabar wulaƙanci, uwar me uawar taka binta ta tsinana maka a rayuwar, da har zaka mari jabir saboda ita? Ƙarya yayi an kama an cuce shi, a kan wannan banzar yarinyar to wallahi ahir ɗin ka, shi da yake jiran gadon sarauta, ai mace ma sai wadda ya zaɓa".
Mummy ta ce "Lubabatu yakamata ki san abubuwan da ki ke faɗa fa".

"Ba wani, ni ki ƙyaleni, kashedi nayi da babbar murya, idan kallon uwa yake yi miki, to ki ja masa kunne, ya kiyayi ɗa na" Mummy tayi mamakin abun da hajiya Lubabatu ta zo tayi mata, wato hakan yana nufin ita ma tunanin da yake ranta, shine a nata ran, na lokaci yayi da kowa yakamata ya kama gabansa, tun da haryanzu kusan za a iya cewa ita hajiya Lubabatu ba wani benefits da ta samu a tafiyar nan ta su.

'Aikuwa ba zaki samu ba, a hakan zan ƙara zage damtse, ka samu kujerar nan Mahmud, kuma na kawo ƙarshen duk wannan abun, ta hanyar nisanta ka da giwa da ahalinta'.

Ta kalleshi ta buɗe baki za ta yi magana, amma ya tashi tsam ya bar mata falon.
Wanda a da, ko gyaran murya tayi jikinsa na tsuma, yake saurarata.

Koda rumaisa suka dawo, kamar yadda ammi tayi tsammani, ana ta surutun kuɗin auren iman, wai dan ba ƴar ta ba ce, ta hanata auren jabir, za ta aura mata talaka, tun da laila ƴar yayarta ce, ai mai kuɗi ta aura mata.

Ammi dai ta toshe kunnenta, kwanansu uku da dawowa, aka yi saukar Alqur'ani na su Iman, an ci an sha an yi walima sosai da sosai, sai dai mai sunan baba bai je ba, wanda hakan bai yi wa iman daɗi ba sam.

Kayan saukar ma da ta ware masa, sai sidi ne ya kai masa gida.

Sai daga baya yaje gida, ya ga allon saukar ta ta.

A ranar ruƙayya ta ga iman tare da mai sunan baba, ta koma sashinsu, tana koɗa kyawunsa da tsananin kwarjininsa.

A haka rayuwa ta cigaba da juyawa, matsaloli suka ƙara tsananta a tsakanin gidajen sarauta, kowa ya ba za komar cimma burinsa, ko ta halin ƙaƙa ko a mutu ko ayi rai, kowa burinsa ya ga ya samu abun da zuciyarsa take muradi.

Mijin laila ya zo hutu da shi da yaransu, sai dai yaran gaba ɗaya hausa ba ta ishesu ba, sun fi magana da turanci, ga mijin lailan kansa wani fari sol da shi, kamar ba ya jin hausa, laila sai zuba taɓara take kala-kala, suka tattara zasu koma gidansu na Kano, laila ta ce sai rumaisa da iman sun bita gidanta, ammi ta ce ba za ta kwashe mata 'ya'ya ba za dai su din ga zuwa.
Ƴaƴan laila kansu, tamkar black Americans, mata biyu sai namiji ɗaya, kyawawa sosai, ranar da Yasir suka kaiwa rumaisa ziyara gidan laila, yarinyar laila ta biyu, ta liƙewa Yasir, hira kala-kala, ta din ga yi masa tambayoyi, mussaman ganinsa da computer, har mamakin yadda yarinya ƙarama take da ilimin computer sosai haka.
Haka mijin laila babu ruwansa, hirar da suka din ga yi da su huzaifa, da yasir, mijin laila ya cewa Yasir idan za a bar shi a gida, zai tafi da shi canada, ya ƙara karatu idan ya kammala diploma da yake yi a kan computer science.
Ya cewa Huzaifa, "kai kuma gashi an ce tela ne, baka cika alƙawari kai ya zmu yi da kai"

Huzaifa yayi dariya ya ce "Sharrin yasir ne, ina cika alƙawari, shi da yake hacking ma"

Dariya suka yi, ya ce "To kaima zaka bi mu canadan ko kuwa?"

Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Mama ba zata bari a tafi da mutum biyu ba, shi dai ya tafi"

Su duk basu zaci da gaske yake ba, laila take bashi labarin rumaisa kuma zane-zane take yi, nan ya dinga bayanin yadda masu zane-zane suka da muhimmanci a ƙasashen ƙetare.

Rayuwarsu very simple, iya zaman da suka yi a ranar, sun ƙaru da mijin laila sosai da sosai, ya kuma cewa laila, idan har Yasir ya kammala diploma, tayi masa magana ayi wa Yasir visa.

***

A ranar da rumaisa ta tsaya a gaban kalandarta, ta soke kwana na ɗari da saba'in da uku, a ranar yayi dai-dai da saura kwanank bakwai cif-cif mijinta ya dawo, ji take tamka ta zuƙo sauran kwanakin, dan gani tayi kwanakin ma sun daina yi mata sauri.

Duk wani gyaran jiki da laila take yi wa iman na aure, da wanda ta saka ake yi mata, tare da rumaisa ake yi mata su.
Rumaisa kuwa daga ita har iman yadda suka koma ba a magana, domin kuwa sosai ba kaɗan ba, sabayar maman Khadija ta karɓi rumaisa, da maganin girman nono na maman ilham, duk wanda ya san rumaisa a baya, ya ganta yanzu sai ya sake kallonta, ta cika abun ta dai-dai gwargwado, mujewar da ta yi, tayi ƙiba gwanin sha'awa ƴar caraf da ita, ga wani irin kyau da fatarta tayi.

Dama iman ba a magana, gata fara tas, ta ƙara da kunun maman Khadija, gashi ita ma ba a barta a baya ba, wurin amfani da maganin maman ilham, abun sai wanda ya gani.


(Ga mai buƙatar ya murmure, yayi kyau gwanin sha'awa kamar rumaisa, iman da kuma anty laila, sai ku garzaya inbox ɗin maman Khadija, domin mallakar na ku garin kunun sabayar, ku tuntuɓeta kai tsaye ta lambar wayarta 08033411249, tana zaune a bayan Federal Palladan Zaria, haka zalika tana aika kayanta ko ina a faɗin ƙasar nan, da kuma maman ilham mai tula-tula, domin tsantsamw jiki sa kama mutuncin nai, ga masu aure, ƴan mata zaurawa da masu yaye, suma suna iya garzayawa inbox ɗin ta ta wannan lambar 08135613021, tana nan zaune a no. Ai kawo road Kaduna, haka zalika ita ma tana aika kayanta ko ina a Nigeria)

Ita kanta mama, sai da tayi mamakin yadda rumaisa ta koma, dan bar sai da ta fara tunanin ko ciki ne da ita, saboda yadda tayi kyau abun ta.

Laila da kanta, da masu aiki, suka je gidan rumaisa, suka yi masa gyara sosai da sosai, aka gyara komai, ta cigaba da jaddada mata, ta riƙe abubuwan da ta koya mata, ta kula da kanta.

Turarukan rumaisa na aure, ta bayar aka haɗa da na iman, aka ƙara tsuma su, sannan aka yi mata wasu.  Banda sabbin ɗinkuna na kece raini da aka yi wa rumaisa.
Babu babban abun da ya ƙara birge ruman, irin yadda aka yi mata riguna masu breast cut, kuma suke zama cas a jikinta, gashi ta fara saka brezia, murna har da taka rawa, ta sha gyaran gashi, ga lallenta ja da baƙi. Ƴan makarantar bokon su na mamakin yadda wasu lokutan rumaisa ke cin karenta babu babbaka, an hana kowa yin lalle, amma rumaisa ana bari tayi abun ta.

Ƙarfe goma sha ɗaya na safe, jirginsu ya sauka a aminu kano international airport.
Sannu a hankali yake tafiya, yana jan akwatin sa, wayarsa yake dannawa yana neman layin laila, dan a wayarta suka yi magana da rumaisa jiya, ta ce za ta turo a ɗauke shi, so yake yaji waye zai zo ɗaukar ta sa.

Sai dai yayi turus, da ya ga Mahmud a tsaye, da sabir a hannunsa.

Da ƙarfi Sabir ya fara kiram "Papaaa. !paaapaaa" yana miƙe masa hannu, ya tattaka har da ɗan gudunsa na yara masu koyon dabo, ya nufi in da mahaifinsa yake!.


Ayshercool.
*SHIN YAR UWA KIN SAN ILLAR DAKE TARE DA INFECTION KUWA?, TO BARI KI JI KAƊAN DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE DA SHI? KIN SAN CEWA INFECTION YANA HANA HAIHUWA?, YANA HANA MA'AURATA JINDADIN MU'AMALA, YA NA SAKA  WARIN GABA KOWANE IRIN TURARE KI KA YI AMFANI KO GYARA KI KA YI, BA ZAI HANA WANNAN WARIN FITA DAGA JIKIN KI BA FITAR FARIN RUWA, TARE DA ƘURAJE. ƘAIƘAYIN GABA, TUSAR GABA, DUK SUNA DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE WA LAFIYARKI
INA MASU FAMA DA ULCER, ASTHMA, SICKLA, INA MATAR DAKE FAMA DA MATSALAR FIBROID, MATSALAR RASHIN HAIHUWA KO BUSHEWAR  JIKI DA FATA, KU GARZAYO KU GWADA MAGUNGUNANMU MA GHT SUPPLEMENT, KU GANI DA  IKON ALLAH DA IZININ ALLAH, MAI BUƘATAR ƘARIN BAYANI YA NEMI WAMN 0703 527 5119*
Ko ku danna wannan link ɗin, domin kasancewa da mu, ku ji yadda

https://chat.whatsapp.com/COM8NE7rDs8HAG0Oqfr9wm



*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login