Showing 75001 words to 78000 words out of 199108 words
da hayaƙi, kuma hayaƙin daga kitchen yake fitowa.
A sukwane ya nufi kitchen ɗin, ya na zuwa ya tarar da rumaisa tana suyar wainar fulawa tana tari, Saboda ƙaurin manja.
"Ke meye haka? Me ki ke yi?"
Ta waiwaya ta ce "Girki nake yi"
Da sauri ya ƙarasa yana ƙoƙarin kashe gas ɗin, dan tuni suka haɗa baki da iman, direbanta ya ɗuro mata.
Tarewa ta yi ta ce "Girki fa nake yi na iya"
"Matsa, ban ce kar ki kuskura ki ce zaki yi girki ba?" Buɗe masa flask ta yi ta ce "Ka ga fa, na iya" wainar fulawa ce ta yi saƙa mai kyau, sai ƙamshin attaruhu take.
Ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, amma a fili ya ce "Idan ki ka yi mini gobara a gida, sai na casaki".
Ta ce "Eh na yadda" ya gyaɗa kai ya fice.
Kusan awa guda, ya ma manta da batun rumaisa ya tuna kar ta yi wata aika-aikar, ya leƙa falo, ya hangota tana ta suɗar baki tana cin yaji.
Ganin tana lafiya, ba wani abu da ya faru, ya sanya ya nemi wuri ya kwanta, dan a gajiye yake sosai.
Sai dai bacci ya gagare shi, tunani daban-daban ya addabi kwanyarsa, ya rungume pillown sa, ya rintse idanunsa, ba ya son tuna yana da tarin matsalolin da ya kasa soloving ɗin su. Ga wani abu da yake bijiro masa ba gaira babu dalili.
Tashi ya yi ya kunna fitilar ɗakinsa, ya tafi kitchen, sai dai ya tarar da rumaisa ba ta yi bacci ba, tana ta gyara abubuwan da ta ɓata, tana tsaye a gaban sink tana wanke-wanke.
Bai ce mata uffan ba, ya ɗauki heater, ya zuba ruwa ya jona, ita ma ba ta kula shi ba, ta cigaba da aikinta.
A ransa yake yabawa mahaifiyar rumaisa da yayyenta, dan a ƴan kwanakin da suka yi, ya fuskanci tana da ƙoƙarin tsafta.
Tea yake son haɗawa, ga ruwa ya tafasa amma sai duru-duru yake yi.
Ta kalleshi ta ce "Rumaisa, dan Allah tun da na ga kin iya girki, dafa mini tea, zan sha. Shi ne abu mai wahala a wurin ka, bari dai na taimaka maka, ai tun da na ga ka ɗauko kofi na san shayi zaka sha, a gida ma kusan kullum sai su Yaya Aliyu sun sha shayi da daddare".
Ta taka kujera, ta buɗe wata drower, ta ɗauko Lipton, da kayan shayi, wanda bai san a in da ta same su ba.
Ta zuba a cikin ruwan zafin, ta sake tafasawa, ta ɗauki ƙaramin flask ta juye masa, ta haɗa masa da kofi a kan tray, sannan ta ce "Gashi nan, kar ka damu ba sai ka yi mini godiya ba, dan na san ba za ka yi ba, muna da irinka a gidanmu. Idan ka gama shan shayin, ga omo da soso, ka wanke kofunan, kar ka bar mini kwanuka wani abun ya bi".
Kamar soko haka yake kallonta, ta ɗauki wani ɗan bowl, ta zuba uban cabin da madara da sugar, ta fice.
Washegari ta tashi da safe, tana aikace-aikacen ta, barira ɗaya daga cikin hadimanta, ta kawo abinci ta ce na takawa ne.
Ta karɓa ta ajiye masa, dan da baba uwani ta gaya masa rumaisa ta ce a daina kawo abinci, cewa yayi su ƙyaleta su cigaba da kaiwa.
Ɗakinsa ta shiga da kayan mopping, ta tarar yana banɗaki yana wanka, ta karkaɗe masa gadon, ta gyara ta kalli gadon bai gyaru sosai yadda yakamata ba, ta ce "Oho, ni a gidanmu babu gado sai katifa, hakan ma na yi ƙoƙari ai".
Idonta ne ya sauka a kan side bed, in da ya sha shayin, nan ya bar kwanukan, "Kam bala'i, Wa ya bar wa kwanukan nan a nan?" Ja ta yi ta tsaya tana jiran fitowarsa.
Rigar wanka ce a jikinsa, sai dai gaban rigar a buɗe yake, gashin ƙirjinsa ya kwanta saboda ruwa, da sauri ta kawar da kanta gefe.
"Ya aka yi?".
Ba ta kalleshi ba ta ce "Eh kwanukan da na ce idan ka gama shan shayin ka wanke na gani a nan".
Ya ce "Eh, idan kin gama ki fita da su ki wanke"
"Ni na sha maka da zan fita da su in wanke?"
Ya kalleta ya ce "Me ki ka ce?" Ta girgiza kai ta ce 'Bakomai".
"Oya kwashe su ki fita da su, ki je ki wanke, sannan kan na gama karyawa, ki shirya, zamu je gidan turaki".
Ta ji daɗi za su fita, amma babban abun da ya bata haushi, bai wuce sakata fita da kwanukan da shi ya mora ba ita ba.
Wata turkey abaya ta saka, blueblack fuskar nan fayau babu ko kwalli, ta yi ta shafa turare, dan akwaisu available a kan mudubinta, dan ko a gida ta saba, dan Abdallah har ɓarauniyar turare yake ce mata.
Suna tafe a hanya, tana kallon titi, tana son gane hanya, dan so take wataran ta ɓalle ta tafi gida.
A gidan turaki suka tarar da Jabir, da shi da Jamil ga kuma Zainab da Mummy, Samha ce ba ta nan.
Rumaisa ta gaishe su, sai dai ba wanda ya amsa mata da mutunci sai Zainab.
Adam ya ce "Zainab nema mana iso wurin mai girma turaki" ba musu Zainab ta tashi.
Rumaisa da sun haɗa ido da Jabir take galla masa harara, haka Jamil da yake ta kallonta a wulaƙance.
Aka yi musu izinin shiga wurin turaki, turaki yana ganin rumaisa ya fara murmushi.
Ita ma Murmushin ta yi ta ce "Barka da wannan lokaci ranka ya daɗe".
"Barkanmu dai ƴar albarka, ya gidan ya ƙoƙari?"
Ta amsa da "Alhamdilillah"
Adam har leƙa fuskarta yake, ya ga ko ita ce ta nutsu haka.
Shi ma suka gaisa da Adam, Adam ya ce masa sun zo su yi godiya ne, tare da yi musu bangajiya na hidima da aka yi.
Turaki ya yi musu nasiha sosai, mussaman ma Adam, a nasihar rumisa ba komai take fahimta ba, mussaman da ta ga da Adam ake.
Bayan turaki ya gama, yayi musu addu'a sosai, Adam yayi ta godiya, ya ce masa za su je wani wurin daga nan.
Rumaisa ta ce "Babana, yaushe zaka zo gidanmu, na iya abinci in dafa maka duk abun da ka ke so?" Yayi murmushi ya ce "Za a zo ne in sha Allah".
Gudun kar ta fara sakin layi kamar yadda ta saba, ya sanya adam sakata a gaba suka fita, sai dai a wannan karon sai suka fita ta ƙofar da zasu fita haraba kai tsaye, ba tare da bi ta falon gidan ba, sai dai suna fita suka yi kiciɓis da Samha!
Ayshercool.
08081012143
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Adam yayi ta maza ya ce "Au dama kina nan? Mun wuce su mama a falo ban ganki ba ai".
Cikin matsanancin takaici ta ce "Meye na borin kunya kuma? Ai ba ka so ka ganni ɗin ba ne? Tun da har ka shiga ta falo, ka biyo ta nan za ka tafi".
Rumaisa ba ta kula Samha ba, dan ba zata manta fuskar ta ba, ta mayar da hankali wurin tsinkar furanni da ke wurin, sai dai tana jin duk abun da suke faɗa.
"Yanzu da ma adam a kan wannan abar ka wulaƙanta ni, ka ƙi ka aureni? Yanzu wannan abar wani abu ta fi ni da shi, yarinyar da ba ta kai a kirata mace ba ma, an ya ka yi mini adalci kenan? Soyayyar da na nuna maka tsawon shekaru shikenan ba ni da wata makoma?"
"To ni idan ba mace ba mace ba ce, namiji ce ni?" Rumaisa ta yi maganar tana riƙe ƙugunta.
Adam ya kalli rumaisa ya ce "Wuce ki je mota ki jirani"
"To saman motar zan hau ko ƙarƙashin tayoyi? Tun da a rufe take".
"Duk in da ya yi miki" kallon banza ta yi wa samha ta wuce.
Samha tana ta tunanin a ina ta san fuskar rumaisa ma, ta kasa tunawa, ta ma fi cika ido a hotunan bikinsu, a zahiri kuwa ƙwaila ce ta gaske.
"Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta Samha? Da auren wuri aka yi miki, ko baki haifeta ba kin kusa, wannan ai salon ki janyo wa kanki raini ne".
"Ban damu ba adam, ba raini ne a gabana ko akasin haka ba, ni batun soyayyaya ta ce a gabana, wallahi ka cutar da ni Adam".
Adam ya ɗan yi shiru, sannan ya ce "Ban cutar da ke ba Samha, abun da nake son ki gane shi ne, komai muƙadarri ne na Allah. Daga haɗuwata da rumaisa, zuwa lokacin da na aureta, da zan gaya miki zaki gane aurena da ita ƙaddarar Allah ce".
"Ba ka son ta kenan?"
"Ba zan ce eh ba, kuma ba zan ce a'a ba, ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, idan da rabo sai in aureki, idan kuma babu ko yi haƙuri, ki auri wani, kar ki ce zaki cigaba da zaman jirana samha".
Rumaisa kuwa ranta a ɓace, ta ƙarasa in da motarsu take, tana zuwa ta ga Jamil da Jabir a tsaye a wurin suna magana, ba ta kula su ba ta tsaya, tana hura hanci.
Jamil ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce "Lallai, Adam sai ka ce makaho, dan Allah ina mamora a tare da wannan yarinyar? Me wanna za ta tsinana masa a zaman aure? Yanzu wannan ya zaɓa ya bar Samha? Saboda wannan abar?".
Jabir ya ce "Kai ba ka san komai ba ai, ba ta da kunya ne yarinyar nake gaya maka, kai ka ga wahalar da ta din ga bashi, ka san ita ta dawo da jaririn fulani, kan ta faɗi fulanin ma ta rasu, sai da aka kai ruwa rana, ba ta da kunya"
Zabura Jamil ya yi ya ce "Kana nufin da gaske wannan yarinyar ce, ta dawo da yaron wurin aisha?".
Jabir ya ce "Tambayeta ka ji"
Juya musu ƙeya rumaisa ta yi, tana wasa da ƙasa da ƙafarta.
"Ke, da gaske kin ga fulani, kin ganta a hannun ƴan bindiga, suwaye? Ya aka yi suka kasheta?" Yayi maganar cikin rikicewa yana kallon rumaisa,ya na jin tamkar yanzu A'isha ta rasu.
Ɗaga kai Rumaisa ta yi ta kalleshi, ta yi guntun tsaki.
"Magana nake yi miki, aisha ƙanwata ce, jami'in tsaro ne ni, ki gaya mini abun da ya faru, ko kuma ƙarya ne kawai haɗin baki ne?" Yayi maganar kamar zai kaiwa rumaisa duka.
Sheƙeƙe rumaisa ta ce "To mijinta ma shi Adam ɗin ban gaya masa komai ba, balle wani kai, ba ruwanka da ni kuma, wallahi ka sake ce mini wannan abar, sai na yi maka rashin mutunci, mai na yi muku, ni na ce kar ya auretan? Wannan masifaffiyar matar na na ɗauka ma babar wasu ce".
Daga nesa da ya tunkaro su, ya hangi rumaisa tana zazzaga masifa, Jabir ya riƙe hannun Jamil, ya ce kar ya yi magana.
Adam ya ƙaraso ya ce "Lafiya kuwa?"
Rumaisa ta ce "Ce mini yayi wai wannan abar, ni na ce kar ka auri waccan matar, da za su din ga ce mini wai wannan abar, shi kuma wannan har da ce mini mara kunya, me na yi masa na rashin kunya".
Adam ya buɗe motar, ya ce wa rumaisa "Shiga ki jirani"
Buɗe motar ta yi ta shiga ta zauna, tana cigaba da tura baki.
Adam ya kalli Jamil ya ce "Sannu Jamil, kirkin ka har ya yi yawa, shikenan ita rayuwa ba za a karɓi ƙaddara ba, ka ƙi halartar ɗaurin aurena, kuma ka ƙi yi mini Allah ya sanya alkhairi".
"Allah sanya alkhairi saboda ka auri wannan abar?" Yayi maganar yana nuna motar adam.
Adam ya sauke hannun Jamil ya ce "Ko dan albarkacina, yakamata ka tausasa harshe a kan ta, matata ce, kuma bana son zumuncinmu ya samu matsala saboda son zukatanmu".
Jamil ya ce "Adam ka na da ƙwarin gwiwar yin wannan maganar? Dama yarinyar nan ita ce ta zo da jaririn aisha, ka ce aisha a hannun 'yan bindiga ta mutu, ya aka yi ita ta kuɓuta, wani mataki ka ɗauka, na san dole ba za a rasa wani information daga bakinta ba, menene dalilinka na ɓoye mana?".
Nan da nan Adam ya hasala ya ce "Kai ma kana zargin ni na kashe fulani na yi tsafi da gawarta ko? To na yi, idan wani bayani ka ke da buƙatar ji daga bakinta, ka je ka tambayi mai girma turaki".
Cikin sauri Jabir ya ce "Jamil, bai kamata ka faɗi irin wannan maganganun ba, da na san haka abun zai zama, da ban gaya maka ba, takawa dan Allah ka yi haƙuri"
Bai ko tsaya ba, ya wuce mota, ya buɗe ya shiga, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi.
Sai da suka ɗan yi nisa sannan ya cewa rumaisa me suka ce miki?.
"Su wa?" Kallonta yayi, ta ga alamar babu wasa a idonsa, ta ce "Tambayata yayi, wai ya aka yi na san anty aisha, ni kuma na ce ban sani ba"
Jinjina kai kawai ya yi, ya cigaba da tuƙinsa.
Wani store yayi parking, ya ce ta fito su shiga. Ta fita ta bishi tana kallon wurin.
Suka je ɓangaren jakunkuna ya ce ta zaɓi jakar makaranta.
Haushi ne ya kamata, dan ko zancen makaranta ba ta so.
Ya sai mata kayan karatu da rubutu, da takalma, jakar ma uku ya saya mata, sannan ya sakata a mota suka tafi.
Gidajen ƴan uwansu ya din ga zagayawa da ita, suna gaishe su, sai dai rumaisa ta ƙule da yadda wasu suke karɓarta, tare da nuna ita yarinya ce, ta yi masa ƙarama da aure.
Babu wanda ya sake ƙona mata rai, kamar hajiya Lubabatu, wato mahaifiyar Jabir, matar Galadima mai ci a yanzu.
Ban da tana ganin girman matar, ta yi sa'ar mama, da babu abun da zai hana ta zageta, dan ma Adam yana ta kareta, amma matar ta ci zarafinta, duk da bakomai take fahimta ba.
"Ragowar ƴan bindiga aka kawo mini kenan, lallai takawa, ka yi jihadi sai fatan Allah ya biya ka".
Adam ya ce "Ba ragowa ba ce ba, kuma aurenta ba ni na yi jihadi ba, ita ta yi, tun da kun san waye ɗanku, amma ta amince da aurensa".
Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Yo ba dole ba, ai ko a turu kake ɗan mu yana da arziki da sarautar da za a aure shi domin sa, kuma a zauna da shi, kwaɗayin abun duniya ne kawai".
Ba dan Ammi ta matsa, lallai ya zagaya da rumaisa, ya nuna mata familynsa ba, ya kuma yi musu bangajiya ba, da babu abun da zai sanya ya zo gidansu Jabir, wurin mahaifiyarsa.
Adam ya ce "To Hajiya, ina ga bari mu koma, akwai in da zamu je".
"Ahh haba dai, na saka a ɗora muku girki ai".
"A'a Alhamdilillah, a ƙoshe muke".
Hajiya Lubabatu ta ce "Gaskiya ban ji daɗin wannan zuwan ba, yakamata a kawo mana ita ta wuni, da haka tana shiga cikinmu, za ta san yadda matan sarakai suke rayuwa, dan na san ba sani ta yi ba".
Adam ya ce "Bakomai ana koya mata"
Wata hadimar Hajiya Lubabatu ta ƙaraso, ta bawa hajiyar wata leda. Ta karɓa ta miƙawa rumaisa ta ce "Amarya ga wannan ba yawa, kya sai tsintsiya, sai na sake kawo ziyara, tun da rabona da gidan, tun washegarin kai ki, mun ce a bamu ƙyalle mu tabattar da abun da aka auro mana, an yi mana wala wala".
Rumaisa ta sha kunu, ta ƙi karɓar ledar.
"Ki karɓa mana" rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a"
Hajiya Lubabatu ta ce "Takawa, ba ka gaya mata, masarauta ba ma kyauta ace a'a ba, rayuwar masarauta, ba kamar ta sauran gama garin mutane ba ce".
Ya kalli rumaisa da ke kusa da shi ya ce "Ki karɓa, ba a mayar da kyautar matan sarakai".
"Bana so" ta faɗa yadda shi kawai zai ji.
Ya saka hannu ya karɓi ledar ya ce "Godiya take, kin san amaryat ta wa akwai jan aji, da gudun raini, kyauta ko da ga ni take, sai ta tantance, gaku sarakai, amma ta fi ku sarauta" yayi maganar a baibai, cike da mayarwa da Hajiya Lubabatu martani.
"Ikon Allah, da alama auren haɗi zai koma na soyayya, ai labarin zuciya a tambayi fuska takawa".
Adam ya ce "Eh to, ba zan musa miki ba, amma hausawa suka ce ɗan hakin da ka raina.."
Murmushi kawai hajiya Lubabatu ta yi, tana yi musu su gaida gida. Rumaisa tuni ta yi waje, dan idan ta cigaba da tsayuwa, matar nan tana washe baki, tana gaya mata magana, ba abun da zai hana ta zageta.
Shi kansa adam mood ɗin rumaisa ya gani, ya san a ƙule take kamar ta fashe dan takaici, la'asar ta riga ta yi sosai, ya ga idan suka koma gida, shi ficewa zai yi, ya san zama za ta yi, tayi ta ƙunci a gidan, dan haka ya wuce da ita da ita gida.
Ammi ba ta nan, sai Nusaiba da Iman, da kuma Sabir, ganin Sabir ya sanya ya manta wani ɓangare, na fushin da take yi.
Ba ta fiye shiri da Nusaiba ba, ta fi yi da Iman, dan haka da ita suke ta hirarasu.
Iman ta saka aka kawo musu abinci, nan iman take bata labarin, bayan ta dawo gida mai sunan baba ya kirata, ya ga missed calls ɗin ta, a lokacin take gaya mata, yadda suka yi da shi, da ta kira shi tana tambayar sa, ina take.
Ruma ta din ga dariya ya ce "Baban mama, sa ba ka dariya sai hamma, kirarin da mama ke yi masa kenan, shi dai kar a raina shi".
Iman ta ce "Anty rumaisa gara haka fa, ina son in ga namiji mai aji, rashin kintsi ko ga namiji bai yi ba ai". Suka cigaba da dariya, iman na nunawa rumaisa hotunan biki.
Nusaiba kuwa kallon iman take, yadda fuskarta take nuna jin daɗin hirar mai sunan baba da suke yi.
Nusaiba a ranta ta ce "Iman, wannan ba irin mutumin da ya dace ki so bane, ya fiye zafi, larurarki kuma tausasawa take buƙata, kuma wataƙila ba zai amince da ke ba, idan ya san ke wacece, uncle J ɗin dai, shi ya san k wacece, shi zai iya zama da ke, wannan wahalar sarrafawa zai yi miki'.
Ana idar da sallar magariba, Adam ya dawo, ya ce rumaisa ta tashi su tafi, ta