Showing 192001 words to 195000 words out of 199108 words
dai, ana yi miki abun arziki kina na tsiya"
Haka rumaisa suke faɗa da gwaggo, komai sai ruma tayi raki.
Yanzu ma Adam ne ya je ya tarar da ita gwaggo na ta masifa, kamar ta ari baki, a kan rumaisa ta tashi ta je ayi mata wanka, tun yamma ake dafa ruwan, amma Rumaisa taƙi yadda ayi, ta maƙale tana kuka, wai wallahi fatarta duk ta dahu saboda ruwan zafi.
Takawa ya shiga ɗakin suka gaisa da gwaggo, ya dubi ruma ya ce 'Mimi meyasa ki ke da gardama ne?"
"Saboda ba ka ga uban tururin da ruwan zafin yake ba, da wanne zan ji, zafin haihuwa ko mutuwar ɗa na, ko na ruwan zafi?"
"Ai ni kin san bana jin zafin ruwa, zo mu je" yayi maganar yana miƙa mata hannu, ba kunya ta zagaye gwaggo ta bi takawa.
Gwaggo ta saki baki tana kallon ikon Allah, daga rumaisa har mijinta ba su da kunya ko kaɗan.
A banɗakinsa ya haɗa ruwa zafin dai-dai jikinta, ya taimaka mata, ta gyara jikinta ta yi wanka, sai dai rumaisa akwai langwai.
Suka fito ya bata abinci ta ci, sannan ya ɗauki magungunan ta ya bata ta sha.
Ya kalleshi ta ce "Na gode sosai papa, ya ku ke ciki a abujan ne, yaushe Abdallah zai dawo?"
Takawa ya kwashe komai da ya faru ya gaya mata.
Tayi ta rarrashin sa, tare da bashi tabbacin, Allah baya barin zalunci, amma kar ya ce zai cigaba da dagewa sai ya ga bayan wakili, saboda yana da goyon bayan manyan ƙasar.
Ya ce "Haka ne, in sha Allah na bar wa Allah"
Cikin dare rumaisa nono ya cika, ya takura mata da ciwo, saboda ba ta shayarwa, dan haka kwana tayi kuka, har da zazzaɓi.
Gaba ɗay tausayinta ya cika takawa, su mata komai na su abun tausayi ne, ta haihu ta rasa ɗan, amma akwai wani pain ɗin na daban.
Anty laila ya kira directly ya sanar mata, ta ce su yi haƙuri, da safe su kira maman ilham a waya, su sai maganin ta na gyaran nono, mace ko yaye tayi yana hana mata jin zafi, kuma baya bari nono ya lalace.
(0813 561 3021zaku iya neman maman ilham kai tsaye ta lambar wayarta. Haka zalika kar ku manta da haɗin maman Khadija na sabaya
0703 777 7442)
Da safe har wurin ƙarfe goma, sanna suka tashi ita da takawa, Gwaggo har ta gaji da jiran fitowar ruma ayi wanka, sai ganin ta tayi tsaf, ta sha wankanta sun fito ita da takawa. A kunyace gwaggo ta gaisa da takawa yayi musu sallama ya fita.
Yana tafiya Gwaggo ta din ga yi mata faɗa "Saboda rashin gado, kina jego ki ka bi miji ku ka kwana tare ko? Ki cigaba da biye masa wani cikin zai yi miki ya bar ki wahala, tun jikinki bai gama ƙwari ba, dama gashi kin ƙi bari ayi miki jegon kirki, ki je ki ƙarata".
"Ni fa gwaggo ke ba kya lallaɓa ni kamar yadda yake yi mini, jiya har ranƙwashi na ki ka yi"
"An ƙi a lallaɓa ki, ku ƙara ina yin sati biyu zan gudu, ba zan iya baɗala ba" haka gwaggo ta cigaba da mita, ruma kuwa ko a jikinta.
Turaki tun da aka watse daga taron nan kuwa, kwanansa biyu ya rufe kansa a turakarsa, yana jinyar zuciyarsa daga raɗaɗi da ɗacin abun da iyalinsa suka aikata.
Wanda ya ɗora alhakin hakan a kansa, da kuma rashin jajirtacciyar uwa ga yaransa, kodayake auren biyayya ne na haɗi, duk cikinsu sharif ne kawai yayi tutsu, ya ce shi sai wadda yake so.
A kwana na uku, aka sanar da jikin galadima ya tsananta, dan haka ya shirya ya tafi jamus.
Mahaifiyar su Jamil kuwa ta sha kuka, duk wanda ta san zata kira, ta roƙi a saka baki a bayar da belin jamil, kowa yaƙi.
Samha ba ta taɓa zaton Jamil ne mutumin da wakili ya samu yake taimaka masa ba.
Ko da ta kira shi a waya, ya ci mata mutunci ya ce kar ta sake kiransa, shi yanzu ya samu biyan buƙatar sa ya san koba koma, yanzu Adam ya san su ba sa'anin yin ba ne ba!.
***
Su mahmud kuwa, basu wahala ba wurin kwatancen da aka basu, nan da nan suka isa gari da Ade take, kuma gidan ƙanin nata sam bashi da ɓaci.
Ras ta gane mai sunan baba, ta din ga murna da zuwansa, sai dai ta din ga kallon mahmud, kamar ta san shi a wani wurin.
Babu ɓata lokaci mai sunan baba ya wassafa mata abun da yake tafe da su, da kuma dalilin da ya sanya yake ta bibiyarsu tun a lagos, har biyo ta nan.
Ba tare da ya gaya mata waye mahmud ba, jiki a sanyaye ta ce "Adamu ne?"
Umar ya ce "Kin gane shi? Kin san Ammi?"
Tayi murmushi mai ciwo ta ce "Na san Bintu, bintu ƴar ɗakina ce sosai da sosai, lokacin da tayi aure tana goyon yaronta na biyu, muka bar garin, nayi kewarta sosai da sosai, sai dai wasu dalilai ya sanya ko da muka bar garin ko sunan garin bana ƙaunar ji"
Mahmud ya ce "Kin tuna jikar ki mairamu?"
Ade ta fashe da kuka, ta ce "Yarinyar da aka bar amanarta a wurin jauro, da dabbobin mu, muka yi gaba, ya iskemu ya ce: wai ƴan fashi ne suka kai musu farmaki, an kasheta ita da mijinta, dabbobinmu ma duk an tafi da su, kamar wanda ya rufe mana baki, babu wanda ya ƙaryata shi haka muka sha kuka. Bayan wasu shekaru yara suka fara fita neman ilimi, wasu suka zauna a riga, muna katsina a ka kai mana farmaki shekara uku baya, aka sake kashe mana ƴan uwa, muka sake yin hijira, shi kuma jauro ya ce a can zai cigaba da zama, sai daga baya labari ya iskemu, ashe jauro ɗan fashin daji ya zama, kuma shi ya kashe mijin mairamu ya gudo shi da matarsa, yayi asiri ya rufe mana baki. Wai sojoji sun kashe shi kwanan nan".
Mahmud ya ce "Kar ki ce mini mutumin da rumaisa ta zana ta ce yana kama da Iman kawunta ne? Shi ne ya kashe mahaifin ta?"
Ade ta ce "Waye kuma ima?"
Sai a lokacin suka warware mata abubuwan da suka faru bayan barin su garin.
Jiki na rawa ta ce "Kuna nufin Bintu tana raye? Ita ta riƙe ƴar mairamu?"
Mahmud ya ce "Ƙwarai kuwa wannan mijinta ne ma?"
Ade ta rikice da kuka, tare da yi wa Allah godiya, da kuma sanya wa Ammi albarka.
Ta ce "Wallahi yaro Bintu tana zuciyata, ka ga dai gani a cikin garin gombe, amma har yau ko tuna rigar da muka zauna bana yi, ko in hanyar garin take bana son ji, gaba ɗaya tsoron mutane nake ji, Jauro bai yi mini adalci ba, dan Allah ku tashi ku kaini na ga Bintu, naga abun da mairamu ta bari" nan ta din ga basu labarin kyawawan halaye irin na mairamu, na rashin magana da haƙuri, yadda ta rayu a gidan jauro, ana azabtar da ita, tun tana yarinya saboda kawaici suka baro ta, suka sauya riga, an yi mata aure sun taso tare suka ya da zango, ta haihu tukuna, amma jauro ya cuce su.
Ade ta din ga murna tana cewa amma ta ji daɗi da malam umar ya zamana mijin jikarta.
Nan da nan ta saka a kira Alhaji Aminu, tare da ce masa duk in da yake ya dawo, ko kuma yazo ya tarar ta tafi kano, an ga jikirta a birnin kano, tun da ba a kaita kano dan Allah ba, yanzu dalili ya samu dan haka babu mai hanata tafiya.
Nan da nan riga ta ɗauka, an samu ƴar mairamu a raye, ashe kan ta mutu ta haihu, aka din ga zuwa ganin mai sunan baba da mahmud. Sun sha karramawa kala-kala.
Washegari da wuri Alhaji Aminu ya sauka a garin, tare da jin batun tamkar almara, abun da ya faru shekaru kusan goma sha tara baya, yaya za ayi ace, wai an ga ƴar mairamu.
Sai dai ya tsinke da lamarin, bayan saukarsa mai sunan baba ya nuna masa hoton iman.
Alhaji Aminu ya ce "Malam Umaru, amma ka kasa gaya mini wannan abu, duk da ban wani san mairamu ba, amma wannan kamarta ɗaya da ade, kuma ba shakka jininmu ce, yanzu meye abun yi?"
Mai sunan baba ya ce "Idan ba damuwa, sai mu taho da iman ɗin da amm...
Ade ta ce "Wane mutum, da ƙafar nan tawa ko a ƙafa zan taka na je kano, na ga Bintu"
Alhaji Aminu ya ce "Da wace ƙafar? Ƙafa duk sai saura? Ki zauna a shirya tafiya, sai a tafi gaba ɗaya "
Nan ya sake warware musu irin zaluncin da jauro yayi musu, ya din ga haɗa kai da ƴan bindiga ana cutar da su, wanda hakan ya sanya da yawansu suka tarwatse, da farko basu gano shi ba, sai daga baya amma an ce sojoji sun kashe shi.
Da daddare takawa ya ceea rumaisa, ta zo su tafi su kwanta, ta ce "Ba zani ba gwaggo ta ce idan na biye maka wani cikin zan samu, kuma wallahi haihuwa da wahala"
Dariya yayi ya ce "Ai shikenan"
Gwaggo ta kawo wa ruma abincin dare, ta ce "Yau ba zaki bishi ba?"
"Ai na gaya masa kin ce bamu da kunya, kuma idan na cigaba da biye masa wank cikin zan samu da suri"
Gwaggo ta ɗora hannu a ka ta ce "Rumaisa ba ki da hankali? Ki ka ce ni na faɗa, ashe halinki na wauta na nan, da wani idon zan kalle shi? Wallahi dole in tattara kayana in bar gidan nan"
Ruma ta ce "Ashe kuwa zaki maimaita masa abun da ki ka faɗa mini, dan sai ya bi ba'asi"
Ta samu ɗan kwali ta kwaɗawa ruma a baya ta ce "Shashasha uwar wauta, shikenan zai daina ganin mutuncina".
**
Mahmud ya kira Ammi a waya, ya ce "Su shirya, su haɗu a wuri guda, suna tafe da manyan baƙi zuwa kano shi da mai sunan baba.
Ba yadda ammi ba ta yi ba, amma yaƙi gaya mata ko suwaye, ya ce amma muhimmancinsu ya kai ace har mai girma wambai ko turaki yana wajen.
Ammi ta ce "Turaki baya nan, ya je Germany wurin galadima, jikinsa ya tsananta, sai dai wambai"
Mahmud ya ce "Baƙi ne masu muhimmanci, har mimi muna buƙatar ta a wurin" Ammi ta din ga mamakin wane irin baƙi ne kuwa haka?".
Da ta sanar da wambai kuwa, ya ce babu laifi, a jira ƙarasowar ta su, aji wani irin baƙi ne, ya ce idan sun iso a kira shi.
Ammi ta sanya aka yi ta ɗorawa da saukewa, duk da bata san wane irin baƙi ba ne, amma akwai buƙatar ayi girki.
Duk nacin ruma da iman, a kan son sanin suwaye baƙin, ammi ta ce musu ita fa ba ta sani ba.
Duk suna falon mai sunan baba ya yi sallama, iman ta tashi da sauri ta ce "Hero suwaye baƙin?"
Ruma ta gwale baki ta ce "Su hero manya"
Takawa ya ce "Umar kun bar mu a duhu kai da ƙaninka, ku muke ta jira"
Yayi murmushi ya ce "Yanzu za su shigo" ya kalli iman ya ce "My yellow, yakamata ki bani tukuici kan ki ga baƙin nan fa" yayi maganar yana jan karan hancinta, a gabansu.
Kunya ce ta kamata ta ce "To me zan baka?"
"Saniya zaki sai mini" gaba ɗaya suka hau dariya, Ammi ta fito ta ce "Mai sunan baba kun sauka? Ina baƙin?"
Mahmud ne yayi sallama, sai Alhaji Aminu a bayansa ya riƙo ade, sai ƙannenta guda biyu.
Sakin carbin hannunta ade tayi, ta ce "Ade" da ƙarfi.
Jiki na rawa saboda tsufa Ade ta ɗago ta kalli Ammi ta ce "Bintuna"
Da sauri Ammi ta ƙarasa ta riƙo hannun Ade, hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Dan Allah gaske ne ba mafarki nake ba, Ade ke ce a gabana? Ade ba irin neman da ban yi miki ba"
Suka rungume juna ita da ita.
Alhaji Aminu ya ƙurawa iman ido, ya ce "wannan ce ƴar ta mu?" Kamar sokuwa haka iman ke bin su da kallo.
Mahmud ya ce "Hajjaju ga ƴan uwanki, mijinki ya nemo"
Jiri ne ya fara ɗibar iman, saboda ba ta san mafarkin nan ya cigaja da yaudararta.
Umar ya riƙe ta ya ce "Iman, calm down mana menene"
"Dan Allah ka tashe ni daga baccin, kamar ba zai faru a gaske ba fa?"
"Ba mafarki bane ba fa" yayi maganar yana zama tare da ita, saboda har numfashinta ya fara sama.
Alhaji Aminu ya ƙaraso gaban iman, ya riƙe hannunta, ya ce "ƴa ta ba mafarki bane ba, mu ne ahalinki" bayan gama kukan ammi ta ce Aminu haka ka girma sosai? Iman ga Ade da nake baki labari, wannan su ne ahalin mairamu"
An sha koke-koke, Ɗan aike ammi ta tasa, aka kira wambai, sai dai yaji kunya da nauyin abubuwan da suka din ga yi wa Ammi da iman, a kan rashin sanin wacece, wanda hakan yana da alaƙa da zigar Mummy.
Nan Alhaji Aminu ya gaya musu cin amanar da jauro yayi musu, da ƙiyayyar garin da ya sanya musu, suka kasa komawa, balle su binciki abun da ya faru gaske ne ko ƙarya.
Takawa ya ce "Tabbas wannan mutumin shi ne rumaisa ta zana mini, ta ce da wa yake kama? Na ce mata iman, ta ce a yanayin da ta ganshi ne ya sanya ba zata taɓa cewa ta ga wani mai kama da iman ba, kasancewar sa mutumin banza, dan har tattaunawa da shi ta yi"
Iman ta rasa mai zata cewa mai sunan baba saboda murna, sai kuka take yi.
Bayan an nutsa, ammi ta saka aka kawo abinci, takawa ya ce "Shi da matarsa zai ci abinci, mai sunan baba ya ce shi ma haka. Mahmud ya ce "Ni za a yi wa gori? Sai in ci da ammina"
Haka suka wuni cikin raha da dariya, iman ta rasa in da zata tsoma dan farinciki.
Labari ya bazu, Mijin iman da Mahmud sun gano iyayen Iman.
Hankalin Mummy ya ƙi kwanciya, sai da ta zo ta ganewa idonta, Ade ga jikarta, amma ta yi ram da rumaisa, saboda yadda yarinyar ta yi mata.
Da yamma ammi ta ce ruma ta tafi gida, tun da jego take yi, takawa ya ce ta ƙyaleta, duk tare za su zauna, su taya iman murna.
Mai sunan baba ma barin iman yayi a gidan, ya tafi gida dan ya huta.
Iman da rumaisa gami da nusaiba, sun kewaye Ade, sai dariya take basu, suna yi mata tambayoyi, har bacci ya kwashe su.
Takawa dama yana ɗakinsa na sashin Ammi, fitowa yayi, kusan sha ɗayan dare yana nunawa ammi wayarsa, ya ce "Ammi ina mimi, a taso mini ita"
A daren aka wallafa labarin kama Khalifa wakili a Mexico da cocaine.
Ammi ta ce "Bacci take yanzu, ka bari da safe"
Ya ce "Ammi ba zan iya jira ba, a taso mini ita dan Allah"
Haka Ammi ta je ta taso masa ruma, ya ja ta ɗakinsa ya nuna mata.
"Ban gaya maka ba papa, duk wani azzalumi da ya fi ƙarfinka, bai fi ƙarfin Allah ba, ka zuba ido zaka ga yadda Allah zai ɗaiɗaita azzalumai, yanzu ma ga ta in da ɗan nasa zai yi takara, kuma wannan abun da aka kama ɗan sa da shi, ya isa ya saka baban nasa ma su faɗi zaɓe".
Alwala takawa yayi, ya din ga salla yana godewa Allah, ko wannan tashin hankali ya isa hana wakili sukuni, ɗan sa yayi laifi da ƙasar da bashi da halin yin cuwa-cuwa.
Ruma kasancewar jiya ba ta yi bacci da wuri ba, ya sanya take ta bacci da safe.
Ammi ta saka aka ɗorawa ruma ruwan zafi.
Ade ta ce lallai a kai su su gaida iyayen mai sunan baba ma, Ade ta yi wa Ammi addu'a da iyalan ta da fatan alkhairi, bisa jajircewa kan riƙe amana.
Takawa ne ya je yana tashin ruma, ta buɗe ido ta tashi zaune, ya ce "Ammi ta ce ki tashi haka, ki yi wanka sabuwar kakar ki ma tana nemanki".
Wani irin zilllo ruma ta yi tana haki, ta yakushi takawa a wuya ta fita da gudu daga ɗakin, bayan ta ya bi yana kiran sunanta, ta baya ta ɓulla in da ake girki idan da baƙi a gidan, ta kefa wani abu a cikin murhu.
Kan ya ƙarasa wurin kuma ta faɗi, cikin tashin hankali ya ɗauke ta, ya kaita ɗaki, sai dai a sume take.
Ammi ya je ya gayawa abun da yake faruwa, hankali tashe suka nufi ɗakin da take.
Kasancewar iman nursing take yi, ta dudduba ruma, amma babu wani abu da yake nuna akwai matsala a vitals ɗin ta.
A hankali ta yi juyi, ta ta da kai da hannunta kamar mai bacci, Ammi ta ce "Alhamdilillah, iman ku ɗaukko mp a kunna karatun Alkur'ani, ko wani abun ne ya sameta" iman ta jinjina kai ta aiwatar da abun da Ammi ta ce.
Mutane na ta zuwa ganin dangin iman, su Ade sai godiya suke yi musu na riƙe musu ƴa.
Ade ta dame su da tambayar ina rumaisa, iman dai ta fito ta gaya mata halin da ake ciki.
Har kan rumaisa Ade ta je, ta dafa kan rumaisa ta ce "Wannan ai kamar shaiɗanu ko sihiri"
Tun sanin da Ammi ta yi wa Ade, mace ce mai ibada da yawan addu'a, duk da kasancewar ta ba wata mai ilimi mai zurfi ba.
Ta dafa kan rumaisa tana ta yi mata addu'a, a hankali ruma ta ce "papa"
"Na'am mimi"
"Wata mage ce za ta sha maka jini a wuyanka, ta kasa"
"Babu wata magge fa, tsorata ki ka yi, bacci ki ke yi"
"A'a ta yakushe ni a hannuna, idonta hayaƙi ma yake yi" ta nuna musu hannunta, in da aka karta mata farata.
Ade ta ce "yarinya na jego kun barta tana yawo ko ina, gashi ba ta son ɗan kwali, idonta ne ya buɗe take gane-gane ai". Aka samu dai ruma ta farfaɗo, sai dai ba ta magana sosai.
A yammacin ranar su Ade har gida suka je, suka gaida mama, dan a washegari suke son komawa.
Mai sunan baba ya tabattar musu da yardar Allah, zai kawo musu iman, ta ga dangin ta.
Har gida suka sake bin mai girma wambai, suka sake yi masa godiya, turaki kuma a lokacin yana Germany.
Hajiya Lubabatu wani irin ciwon kai ta din ga fama da shi, mai tsananin gaske, da har ta kai ba ta gane mutane sosai, kuma ba ta son haske sai duhu, tayi ta surutai