Showing 99001 words to 102000 words out of 199108 words

Chapter 34 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

818

ta tarar da iman, ta na kuka.

Ruma ta ce "Gaskiya kin ba da ni, wai shi waye Jabir ɗin nan ne? Ya san waye mai sunan baba kuwa? Ke ma kin wani zauna ki na yi masa kuka, ni ma ina da saurin kuka amma kin ga ina yi? Meyasa ba a yi wa Nusaiba abun da ake yi miki?".

Iman ta share hawayen ta, Sabir sai jijjiga iman yake yana cewa Iman, dan ya iya sunanta raɗau, kamar shi ya raɗa mata.

Ruma ta ce "Gidanku, Anty zaka ce ko Mummy"

Iman ta yi murmushi ta ce "Anty Nusaiba ta su ce, kuma ta na da bakin da idan aka yi mata za ta rama, ni bana son tashin hankali ne, baki ga komai ba ma, dan su Fauziyya sun daina zuwa ne, baki ga abun da suke yi mini ba".

Ruma ta ce "Wallahi ko a kan bola aka haifeni, ba zan yadda da wulaƙanci ba, amma cika mini alƙawarina. Meyasa papa ba sa shiri da daddyna, meyasa kuma ba ya shiri da ammi, Meyasa ki ke cewa kan ki, ƴar tsintuwa?".

Iman ta ɗan yi shiru, sannan ta numfasa, a dai-dai lokacin da wani hawayen yake zubo mata.

***
ASALIN LABARI.....
1972 Kano state emirate palace, a zamanin sarki Adamu Abdullahi.

Masarautar kano na ɗaya daga cikin manyan masarautu, da ake ji da su a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta turawan mulkin mallaka, suna ji da wannan masarauta.

Sarki Adamu Abdullahi, mutum ne mai adalci, karamci da kuma yakana, kuma jarumi, hakan ya sanya soyayyarsa a zukatan al'ummarsa.

Ya na da tarin dukiya, ƴaƴa, barori da sauran hadimai.
Yana da tarin ƴaƴa, daga matansa da kuma ƙwarƙwarorin sa.

A wannan lokacin, ya na kimanin ƴaƴa goma sha tara, maza da mata, a cikin mazan Allah ya jarrabe shi da ƙaunar ɗan sa Muhammad, da suke kira Sharif, tun ya na iya ɓoyewa har ya gaza, yake nuna masa soyayya muraran.

A lokacin turawa sun kawo harkar karatun boko, wanda a lokacin dama sun tarar da hausawa da karatunsu na allo da tsangayu.

Galibi ƴaƴan sarki a wannan lokacin, suna da sarautunsu, a lokacin da suke ƙallafa rai a kan sarauta, shi kuwa Sharif sam hankalinsa ba ya kan sarauta, ya fi karkata ga neman ilimi, na addini da kuma na zamani, da turawa ne suke koyar da su.

Sharif ya na da zafin zuciya, Mai marataba ne da mai babban ɗaki, wato kakarsa kawai ke iya sarrafa shi, kasancewar mahaifiyar sa ta bar duniya. A wurin mai babban ɗaki yake, sai kuma mahaifiyar Jafaru, wato turaki a yanzu, dan kamar uwa ya ɗauketa ita ma.

Bayan ya kammala karatun sakandare, turawa suka ba shi gurbin karatu a ƙasar Ingila, mai martaba ya ce bai san zance ba, babu mai raba shi da ɗan sa, Sharif ya ƙallafa rai a kan ya na son tafiya. Sai da mai babban ɗaki ta sanya baki, da wasu manya sannan ya amince.
Sai dai mai martaba ya na tsoron rayuwa cikin turawa, ga ƙanƙanin yaro kamar Sharif a wannan lokacin.

Bayan tafiyar sa, ya kammala degreensa na farko, a kan fannin tattalin arziki, ya ji daɗin zaman ƙasar waje, ba takura, babu kana tafe ana take maka baya, duk a hanaka sukuni da kaɗaici, a cewarsa.

Da ƙyar mai martaba ya saka aka dawo masa da Sharif, sai dai da ya dawo duk ya yasar da wasu al'adun, harkar gabansa ce kawai ta dame shi.

Ko zaman fada ba ya zuwa, idan ya shilla ya tafi na sa yawon, sai an ganshi.

Hakan ya fara damun mai martaba, ya fara tunanin yi wa Sharif sarauta, ko zai nutsu, sai dai ya na cikin yaransa ƙanana.

Sharif ya tsiri cewa zai tafi master's gombe, nan ma sai da aka kai ruwa rana, mai martaba ya ce ya na da sharaɗi, abokin sa wazirin daura, ya bashi ƙanwar matarsa ya aura wa ɗaya daga cikin ƴaƴansa dan ƙarfafa zumunci, dan haka ya ce Sharif ne zai aure ta.

Sharif da fari ya ce "Shi ba ya son ta, daga baya saboda yana so karatu, ya amince, amma sai ya gama master's ɗin sa, mai martaba ya ce bai yadda ba, lokacin ya yi tsayi, wazirin daura ya ce a saka shekara, ba damuwa kan nan ta ƙara girma ita ma.

Ko da Sharif ya tafi gombe, ya samu abokai ya cigaba da rayuwarsa, yadda yake so, duk da mai martaba ya na turowa, ana saka masa ido a kan sa, duk da akwai manyan mutane da suke bibiyar sharif, saboda karamci ga mahaifinsa.

Ɗalibai ba kowa ya san Sharif ba, yayi ta kashe musu kuɗi, suna bin sa, har sabon babur ya saya, yake yawonsa a garin gombe.

Ana haka yawo ya kai shi wani ɗan ƙaramin gari, nesa da cikin gari kaɗan, ya kusa buge wata yarinya, ya yi ta bata haƙuri, ya kafe babur ɗin sa ya rakata gida.

Tun da ya haɗu da yarinyar nan ya samu wurin zuwa, kusan kullum suna tare, ita kuma a lokacin yarinya ce sosai, yadda yake biye mata suna shirme, yake bin ta gona ya sanya ta saba da shi sosai.

Sunanta Bintu, ƴar wani babban malami ce a garin, shigaban manoma na wannan yankin, dan haka ya na da rufin asiri.

Babanta ya na ƙaunar fura da nono, akwai wata riga da take zuwa sayo masa, duk juma'a, a titi suke haɗuwa da Sharif, ya ɗauke ta a babur su tafi cikin rigar nan, Bintu ta saba da su sosai, bafulatanar da take sayen nonon a wurinta, ta mayar da bintu kamar ƴar ta, haka Sharif ma sun saba sosai, dan kakar bintu ma yake ce mata.

Kwatsam aka je aka gaya wa baban bintu abun da yake faruwa, ya din ga yi mata faɗa, aka hanata fita, hakan ya damu Sharif, ya kasa jurewa, ya bita har gida.

Yayyen Bintu suka kore shi, amma yaƙi tafiya, sai da ya haɗu da mahaifin Bintu, ya ce masa idan har son ta yake ya turo manyansa ayi magana.
Baban bintu yayi haka, dan ya kori sharif.

Sharif ya koma gida ya sakawa mai martaba rigima, shi fa baya son wannan jamilar, Bintu za a aura masa an ce ya tura iyayensa.

Mai martaba da fari ransa ya ɓaci, mai babban ɗaki ta taushe shi, ta ce dama ai so ake yayi auren, a fara aura masa bintun, sai ayi aurensa da Jamila, tun da dama shekara aka saka.

Matan mai martaba suka din ga ƙanan maganganu, suna cewa ya na biye wa yaro, kimar sa na zubewa.

Ya tashi tawaga daga Kano, aje a yi masa bincike a kan Bintu, idan ba su da wani aibu, a nema wa Sharif aurenta.

Mai martaba ya ji daɗin bayanin da ya samu, a kan Bintu da iyayen ta.

Da yawa sun yi mamaki, yadda kamar ɗan sarki daga kano, zai auri ƴar talaka.
Aka yi shagali sosai, aka yi auren.

Daga Bintu har Sharif, yarintar su kawai suke zubawa, dan a lokacin ba ta wuce shekara sha uku ba.

Mai martaba ya tura mutane, da ban haƙuri a kan abun da ya faru, tare da tabattar wa waziri, idan lokaci yayi ba fashi, za ayi auren Sharif da Jamila.
Jamila da yayarta, da mahaifiyarsu, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, dan haka suka din ga bin malamai, Allah ya tabattar da auren Jamila da Sharif.

Jin akwai wadda ake so Sharif ya aura, Bintu ta din ga murna, za a kawo mata ƙawa.

Wasa² sai da Sharif ya shekara biyu, kan ya auri Jamila, yau ya bayar da wannan uzurin, gobe ya bayar da wancan.

Ana haka Galadiman wannan lokacin ya rasu, bayan shafe zaman makoki, mai martaba ya sanar da naɗin Sharif a matsayin Galadima.

Ƴaƴan mai martaba da matansa, suka ɗaga hankalinsu, saboda gani suke rashin adalci ne, a bawa wannan yaron da ba shi da cikakken kai wannan babbar sarauta, bayan ga yayyensa.

Mai martaba ya yi burus, kuma bayan naɗin sarauta, aka ɗaura masa aure da Jamila.
Maimakon Bintu ta damu kanta, ita murna take yi, shi uban gayyar ne yake ta takaici, dan har ga Allah ba ya son jamila, ga wannan sarautar da aka bashi, ya na da shekaru ashirin da biyar. Jamila ta ƙudiri aniyar, ɗaukar fansar abun da aka yi mata a kan Bintu.

Rayuwa ta cigaba da garawa, son da Sharif yake yi wa Bintu, ya sanya mai martaba da mai babban ɗaki suma suke son ta, saboda tana da tarbiyya da nutsuwa.
Hakan ya ja mata baƙin jini a cikin facalolinta. Da an yi maganar sirikai, sai mai martaba ya ce "Ƴa ta bintu".

Sharif da kansa yake koyawa bintu karatu, daga baya ya sakata a makarantar boko.

Sai dai ba ayi shekara da auro Jamila ba, abubuwa suka fara sauyawa a gidan.

Jamila ta fi Bintu wayo sosai, dan ta ba ta shekara biyu ma, kuma ta rayu a gidan wazirin daura, hannun yayarta, dan haka ta san abubuwa, da munafunci na gidan sarauta. Saɓanin Bintu, da neman ilimi kawai ta taso ta na yi a gidansu, dan ita a gidansu ma, ba a banbance ɗan wannan ɗaki da wancan.
Dan haka da bin malamai, da makirci, Jamila ta fara haɗa Sharif da Bintu faɗa, kuma ta din ga shishshigi a wurin facalolinsu, tare da nuna musu ita ta Allah ce, Bintu ba wayo sosai, sai dai ta yi ta kuka.

Tsawon shekaru uku, da aure, sannan ta fara al'ada ma a gidan miji, wataran ta je garin su, ta tarar yayarta ta yaye jaririyar da ta tafi ta bari tana goyo, mai suna laila, ta saka rigima sai an bata ita.
A duk lokacin da ta je gida, sai ta je rigar nan, wurin Ade, wato bafulatanar nan, idan har ta je kamar kaka da jika, za ta tarar ta ajiye mata tsintsiya, man shanu, da sauransu, kuma ita ma Bintu da na ta alkhairi take tafiya ta yi mata.

Bayan ta dawo da laila, sharif bai ce mata komai ba, dan ya na son yara shi ma, mai babban ɗaki ta bata hadima, Uwani, domin ta din ga tayata kula da yarinyar.

Sai dai ba Bintu ba, Jamila ma ba ta taɓa ko ɓari ba, suka kasa zaune suka tsaye ita da ƴan uwanta, Bintu kuwa ko a jikinta, sabgarta kawai take da karatun ta.

Ana haka mai babban ɗaki ta rasu, wanda hakan ba ƙaramin tayarwa al'ummar masarautar hankali ya yi ba, mussaman Sharif da Bintu.

Kwatsam Bintu ta din ga rashin lafiya, babu ƙaƙƙautawa, duk ta rame, Aka kaita asibiti aka tabattar ta na da juna biyu. Saboda tsabar ƙuruciya da murna, Sharif ya je ya gaya wa jamila, wai ta taya su murna.
Aikuwa ta ƙwafe abun nan a ranta, da alwashin ganin bayan cikin, a cewarta tun da aka fara auren Bintu, sai t jira ta fara haihuwa. Dan muraran jamila ke nuna wa Bintu ƙiyayya.

Dan haka maimakonsa bin malamai, Jamila ta fara shiga bokaye, da tsubacce-tsubacce iri-iri, domin ganin bayan cikin nan.

Allah mai jarraba bawa, sai da Bintu ta yi ɓari uku a jere, kowanne sai ta sha wahala kamar ba ta rayu ba.
Hankalin Sharif ya tashi sosai, ya damu, mai martaba ne ke kwantar masa da hankali, ya saka ake yi wa Bintu rubutun Alqur'ani.

Sai a karo na huɗu, sannan cikin ya zauna, sai dai ta azabtu saboda laulayi, dan ƙarshe ba dan Sharif ya so ba, aka mayar da Bintu gida, ya din ga jin haushi, dan ba ya son ta yi nesa da shi, hakan ya sake ƙular da jamila, ta yi amfani da duk wata dama, ta asiri, wurin ɗauke hankalin Sharif daga kan Bintu, tun da ta je gida bai taka ya je dubata ba, sai da ta haihu, aka aiko.

Jin haihuwar ya fi komai saka shi farinciki, ta haifi ɗa namiji, sai a lokacin ya din ga murna, ya je garinsu, abun ka da mutan da, ko da wasa bai ga alamar ta yi fushi da shi ba, sai dai bayan suna yaro ya ci sunan Abdullahi. Aka ɗauki soyayyar duniya aka ɗorata a kan yaron nan.
Watanninsa shida, yayi zazzaɓin wuni ɗaya ya rasu.

Mutuwar nan ta girgiza Sharif, da ƙyar aka shawo kansa. Still sai da Bintu ta sake ɓari, sannan ta samu ciki ya zauna.
Da aka haife shi, aka saka masa Adam, wato sunan mai martaba, mahaifin Sharif. Ake kiransa da takawa, saboda gidan sarautar dabo ba a faɗar sunan saboda girmansa, sunan mai martaba ne, kuma a lokacin Sharif ya yi wa Bintu srautar giwar galadima.

Jamila ba ta sake shiga tashin hankali ba, sai da ta ga, hankalin kowa ya koma kan Adam, ba a kansa aka fara yi wa mai martaba takwara ba, amma an fi nuna masa so, duk soyayyar da mai martaba yake yi wa Sharif ya mayar da ita kan Adam.

Adam na da watanni bakwai, wani cikin ya ɓulla a jikin Bintu, da yanzu ake kira da ammi.

A lokacin laila ta tasa, ba shi da wata ƴar raino, sai Laila da baba uwani, idan baba uwani ta zo ta gama aikace-aikacen ta, sai ta tafi gida ta bar sauran hadimai, laila kuma ta cigaba da raino, dan Ammi ba ta iya komai.

Sharif duk ya shiga damuwa, yana murna zai sake samun ƙaruwa, amma yana jin tausayin Bintu.

Ƙannen Jamila na yawan zuwa gidan, su yi ta faɗa da laila, ko su din ga cin zalin Adam, sai dai laila a tsaye take, ba ta da haƙuri, haka za su yi ta dambe, Ammi ta yi ta mata faɗan ta rage faɗa.

Wannan cikin shi ma ya tsaya wa Jamila, ta yi duk mai yiwu wa ta salwantar da shi, amma abu ya gagara, sai da aka haife shi, shi ma namiji.

Aka sakawa yaron Mahmud, sunan galadiman da ya rasu. Adam ba shi da wayo sosai lokacin, dan bai cika shekaru biyu ba, amma yana son sabon yaron da yake gani a wurin amminsa mai kyau, yana matuƙar kama da Adam da sosai da sosai, tamkar an raba kara biyu, duk kamarsu ɗaya da galadima.

Zigar facaloli, da soye-soyen zuciya, ya tunzura Jamila, ta rasa in da za ta saka kanta, ta din ga jin idan ta samu dama,
tsaf za ta iya raba yaran nan da rayuwarsu.

A hakan, Sharif ya cigaba da tsaya musu, akan karatu, duk da ammi na fuskantar ƙalubale, kowa ya juya mata baya, an fi tausayin Jamila, shi kansa Sharif gaba ɗaya ya canza mata.

Sai dai Mahmud ma, bai fi wata bakwan ba, ta sake fuskantar tana da ciki, dan idan ta haihu ta gama biƙi ba ta al'ada sai dai ta ga ciki.

Ayshercool.
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏



Hankalin Jamila ya yi mummunan tashi fiye da da, kasancewar idan mutum ya na aikata abu, gani yake kowa ma haka yake, ya sanya ta ce Ammi ce take yi mata asiri, ta hanata haihuwa, dan haka ta ƙuduri aniyar wani abu a ranta, bayan yin shawara da Lubabatu, wato matar wan Sharif, wadda ta zame mata aminiya, a lokacin ita kuma mijinta ba shi da sarauta, yarima ne kawai.

Sai bayan da suka bi gari-gari, yawon asiri, sannan Jamila, ta bijiro wa da Sharif cewar tun da ba ta taɓa haihuwa ba, a bata Mahmud ko Adam, tun da giwa ta na wani laulayin, ba iya kula take da yaran ba, sai dai laila da masu aiki.

Babu musun komai, dan a lokacin ya na tausayin yadda take damuwa da rashin haihuwa, ya ce wanne take so a cikinsu.

Cikin ragon azanci, da ganin yadda ammi ta fi son Mahmud, fiye da takawa, saboda takawa na kowa ne, Mahmud kuwa ƙarami ne, amma jamila ta ce Mahmud take so, a lokacin ko yaye shi ba ayi ba.

Ammi ta yi kuka, ta yi kuka, har wurin mai martaba ta je a kan ya taimaka ya karɓar mata ɗan ta, amma ya ce ta yi haƙuri, da ita da Jamila duk ɗaya ne, ta tausaya wa jamila, tun da ita ba ta taɓa haihuwa ba.

Rashin ɗan ta, ga laulayi, ya sanya duk ta jeme, ƙarshe tana ji ta na gani, sharif ya tattara ya koma wurin Jamila, saboda ita kullum babu lafiya, ta daina cin abinci duk ta rame.

Da fari Jamila ta so azabtar da Mahmud ne, dan ta fara, kuma labari ya na iske Ammi, amma daga baya ta canza shawara, take ganin bari ta yi abun da har giwa ta mutu, zai fi yi mata ciwo, dan ta rama abun da aka yi mata, na fara auren Bintu maimakonta.

Dan haka ta koma nuna wa Mahmud so, a gaban mutane, da mahaifinsa, hakan ya saka kowa Addu'a yake yi mata, a kan Allah ya bata na ta ita ma.

Laila ce ke satar jiki, ta ɗaukko wa ammi Mahmud, ta kawo mata shi ta ganshi, duk yadda laila ta shaƙu da Sharif, sai da yayi mata rashin mutunci a kan ɗaukar Mahmud ta kai wa Ammi, ya ce kyauta halak ya bawa Jamila Mahmud.

A haka Ammi ta haihu, wannan karon ta samu ƴar budurwa, ta yi ta murna, aka saka mata suna Khadija sunan mahaifiyarta, sai dai duk da haka tana kewar ɗan ta, Adam tun yana kuka, yana tambayar ammi Mahmud, har ya daina.

Jamila ta toshe duk wata kafa, da zata sada Ammi da Mahmud, Ammi ta yi wa Sharif kuka, ta yi masa magiya a kan a din ga bari ta na ganin ɗan ta, amma ya ce wai Jamila za ta tambaya.

Sai dai jaririyar nan ma ba ta yi tsawon rai ba, ta koma ga Allah.

Abubuwa suka yi wa ammi yawa, depression ya nemi kamata, amma a lokacin ba a waye da ciwon ba, aka mayar da ita gida, wai aljanu ke damunta.

Kamar wasa, Jamila ma ta samu juna biyu, wanda tun da ta same shi take iyayi, da sanabe da feleƙe, ranar kwanan Bintu, sai galadima ya bata haƙuri, wai zai kwana da Jamila ba ta da lafiya.

Ammi ba ta taɓa tanka masa ba, dan a lokacin ta miƙa wa Allah lamarinta, ta rungumi laila da Adam, ta cigaba da riƙon abun ta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login