Showing 69001 words to 72000 words out of 199108 words

Chapter 24 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

809

yi haƙuri kin ji, zaki saba ne haka aure yake, ki yi haƙuri, duk abun da yayi miki wanda bai yi miki ba ki gaya mini. Sannan su nusaiba sun gaya mini abun da ya faru washegarin kai ki, shi ma ki yi haƙuri ki kawar da kanki, na san zaki fuskanci ƙalubale, amma ki dake. Kar ki yadda da duk wata mata da zata nuna tafi kowa ƙaunarki ko ta shiga jikinki, kuma kar ki sake ki gaya wa wani sirrin aurenki, duk abun da zai yi miki, ba zai yi wanda zai cutar da ke ba, na ja masa kunne sosai da sosai, idan yayi miki abun da ba dai-dai ba, ki gaya mini. Kar ki saki jiki da kowa, sai mijinki ko kuma ni da ƙannensa zama a masaruta sai ka iya allonka, ki yi haƙuri kin ji rumaisana".

Ruma ta ce "To Ammi, in sha Allah "

Har gaban mota ammin ta rakasu, suka shiga suka tafi.

Tun kan su yi nisa ta fara sana'arta ta barcci, ya taɓata ya ce "Idan ki ka yi bacci, sai dai ki kwana a mota, dan ba ɗaukar ki zan yi ba" da haka suka ƙarasa gida ta yi sallar isha'i, ko abincin ba ta ci ba ta kwanta.

Washegari da safe, ta tashi tana ɗan goge gogenta, ta fito falo tana ta goge tiles ɗin.

Adam ya fito cikin suits da jakarsa, da alama aiki zai tafi, ta yi masa ƙuri da ido, ba ta yi magana ba.

"Baki iya gaisuwa bane?"

Ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ce "Ba amsawa ka ke yi ba"

"Yes, ba kya gaisheni yadda ya dace ne, ki bar wannan aikin babu wanda ya saka ki, anjima masu aikin da ammi ta ce za su zo, idan da wani abu su gyara miki.
Ga breakfast can a kan dining, in anjima zasu fara aiki, zan sayo kayan abinci, ko kina buƙatar wani abu?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki zauna wuri ɗaya, banda taɓe-taɓen abun da ban saka ki ba".

"To sai yaushe zaka dawo?".

"Lokacin da Allah ya yi".

"Ni dai ka dawo da wuri, tsoro nake ji"

***
Gidansu rumaisa kuwa, mama ce ta hana kowa zuwa gidan, saboda ta san halin rumaisa, ta ce idan suka je kuka za ta yi ta ce zata biyosu. Sai dai ba a cikakken awa guda, ba ayi zancenta ba a gidan.

Kasancewar bayan mai hoton da ɓangaren su Adam suka ɗauko, Abdallah ma ya ɗauko mai hoto, aka turo masa hotunan bikin rumaisa, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tura su group ɗin su, na ƴan gidan.

Mai sunan baba yana kasuwa, da yake bayan makaranta ya kan ɗan shiga kasuwa, hotunan suka shigo.
Suna da yawa ya sauke su, ya fara buɗewa yana kallo, yana kallo yana murmushi yana jin yadda ya yi kewar ƙanwarsa.
Babu tsammani ya ci karo da hotonsa shi da iman, rumaisa kuma a gefensu, ya wuce hoton da sauri, amma ya kuma karo da hoton iman ɗin, na ranar bridal shower, ta yi wani irin kyau na musamman.
Zuciyarsa ta tsananta bugawa, kuma ya kasa wuce hoton nata, ba shiri ya rufe wayar, ya saka a aljihunsa yana ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi gudu.

***
"Wallahi Adam na yi mamaki da har ka iya ɓoye mini al'amari mai girma kamar wannan, menene a ciki idan na san wannan yarinyar zaka aura" Jabir yayi maganar cike da ƙorafi.

Adam ya ce "Koma menene bai kamata ka ji haushi ba, yanzu ba gashi ka ji ba, ko da yake gara kai a kan Jamil, ni Jamil zai ɗauki gaba da ni, yaƙi zuwa wurin ɗaurin aurena, ni na karɓi ƙaddarata dan meyasa shi ba zai ɗauka ba".

Jabir ya ce "A'a takawa, so so ne fa, amma son kai ya fi, Samha ƙanwarmu ce ga ta gida, amma ace ka auro wata a waje, wadda ba ta kaita komai ba, babu daɗi".

"Amma har ya kai ayi gaba da ni saboda hakan? Meye aibun rumaisa idan aka kamanta shi da abun da ta yi mini na sadaukarwa, bai kamata gaba ɗayanmu idonmu ya rufe ba, idan akwai rabo a gaba sai ka ga na aureta, amma a yanzu ban zaci haka daga Jamil ba, amma zan shiga wurin aiki, zamu haɗu da shi mu yi magana"

Jabir ya ce "To shikenan, har ka gama amarcin kenan ka fito, bai yi wuri ba komawarka aiki ba kuwa?"

Adam ya yi murmushi ya ce "Bai yi ba, ita ma sai a bar ta ta huta. Kai ni har mamaki nake yi yadda kai  ba a saka maka ido ba, ko auren fari ba ka yi ba, amma ba ruwan wani da kai, duk mu aka sanya wa ido"

Jabir ya yi dariya ya ce "Bayan ka ce ba zaka bani iman ba, ai ni na zaci kai zaka aureta"

Adam ya ɗan ɓata fuska ya ce "Please mu bar wannan zancen"

Jabir ya ce "Shikenan, tun da baka so"

***
Rumaisa ta rasa abun da yake yi mata daɗi, zaman shirun nan duk ya isheta.

Ta saman benen take kallon harabar gidan, da gidajen da ke maƙwabtaka da nata, duk manyan gidaje ne, sannan kowane gida a rufe yake, ko gilmawar mutane ba ka gani, sai dai a cikin mota.

Mai gadin ta ga ya tashi ya buɗe gate, nan da nan ta fara murna ta yi baƙi.

Ta koma ɗakinta da sauri, ta saka hula a kanta, ta fito, sai dai ta yi turus lokacin da ta ga baba uwani, da wasu matasan mata guda biyu.

Jiki a sanyaye ta ce musu "Ina wuni?"

Baba uwani ta yi murmushi ta ce "Ranki ya daɗe ai mu zamu gaisheki, barka da wannan lokaci? Mun same ki lafiya?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa a ɗan tsorace.

"To kamar yadda giwa ta yi miki bayani jiya, ga ma'aikatanki nan, sannan kuma ni ce cikon ta ukun, zamu zauna tare da su a nan, na din ga lura da yadda zasu gudanar da aikin".

Rumaisa ta ce "To sannunku".

Baba uwani ta ce "Yauwwa, wani ɗakin zamu zauna, da kayanmu muka zo".

"Ku zaɓi duk wanda ku ke so" rumaisa ta yi maganar tana kallonsu.

Ta nemi wuri ta zauna a falo, baba uwani ta zaƙe ta fara dudduba ɗakunan da suke saman benen.

Ta shiga ɗakin rumaisa, ta ƙare masa kallo, ta fito tana faɗin "Allah ya taimake ki, ashe an shirya miki kayan, ko takawan ne ya shirya miki su?"

Rumaisa ta ce "A'a ni na yi"

"Masha Allah, to bari ɗauki wancan ɗakin, tun da na ga ɗayan kamar babu kowa a ciki"

Ita dai rumaisa ba ta ce komai ba, ta ƙare ta shiga kitchen tana dudduba kayan kitchen ɗin Rumaisa.

Ganin sun isheta da kallo, sauran mata biyun da ko sunayensu ba ta sani ba, ya sanya ta tashi ta koma ɗakinta.

Ta buɗe window ta cigaba da kalle-kallenta, ta hango baba uwani a bayan gidan, tana waya. Ba ta jin mai baba uwani take cewa, sai dai da alama kamar wayar ta ta ta sirri ce.

Baba uwani kuwa cikin ladabi take waya da Samha.

"Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, bana son a samu kowane irin akasi a kan aikin nan, ki zuba mini ido sosai, duk abun da yake faruwa ki din ga sanar da ni, ina fatan kin gane?"

"Na gane ranki ya daɗe, duk abun da ki ka ce in Allah ya yarda zan yi, zan zuba ido sosai da sosai"

Samha ta ce "Yayi kyau".


Da la'asar Adam ya dawo, rumaisa ma sam ba ta san ya dawo ba, saboda wunin ɗaki ta yi, ko haɗa hanya ba ta son yi da baba uwani.

Gyaran murya ya yi, hakan ya sa ta waiwaya ta ganshi a tsaye.

Ya shiga ɗakin ya ce "Me ki ke yi ke kaɗai a ɗaki?".

"Bakomai"

"Ke ki ka ce wa baba uwani su zauna a ɗakin saman nan?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce "To na ce su koma ƙasa, ba haka ake yi ba. Ga kayan abinci can na sayo, na zuba a kitchen ɗin ƙasa, zasu din ga girki suna kawo mana, sannan zasu din ga yin duk wani aiki na gidan nan, banda gyaran ɗakina, ke zaki din ga wannan ai kin iya ko?" Ta jinjina masa kai.

"Bana son body language, amsa mini zaki yi"

"Eh na iya".

"Good, ki fito zan nuna miki abu".

Ta tashi ta bishi, zuwa kitchen ɗin saman benen.

Ya nuna mata kayan tea, manyan gwangwanayen madara da na milo, kayan biscuit na ciye-ciye da sauransu.
Sai cartons na lemuka, da kayan marmari ya ce "Gashi nan, wanda zaki kai ɗaki ki kai, wanda za su saka miki a fridge kuma sai ki nuna musu".

"To an gode" ta faɗa a sanyaye.

Gani yake yi kamar an sauya rumaisa, duk wannan tsabar rashin jin da tsaurin ido, duk ta yi sanyi, sai dai a ransa ya ce ba a yabon ɗan kuturu.


Kasancewar tun a yau su baba uwani suka fara gudanar da ayyukansu, sun yi abincin dare, suka kai wa su rumaisa sama.

Ruma ko kallon abincin ba ta yi ba, ta din ga cin kayan marmari, sai da ta ji ta ƙoshi.
Ta haɗa madara da milo, fal a kofi ta tafi da shi ɗaki, ta din ga sha ta gaji ta ajiye sauran ta yi bacci.

Ba ta san ma Adam ya dawo ba, sai da asuba ta ji yana babbuga mata gefen gado ta tashi ta yi sallar asuba.

Ta buɗe ido ta kalleshi ya ce "Ke ba kya iya tashi salla dole sai an tasheki ne? Kuma haka ki ke kwana da fitila a kunne?"

Ba ta ce komai ba shi kuma ya fice. bayan ta yi sallar, ta ɗan yi baccin safe ta tashi, ta shiga banɗakinta, yanzu duk ta san yadda ake amfani da kayan toilet ɗin, da idan za ta yi alwala, sai ta kunna hot water ta fara, tana tsaka da yi, ta ji ruwan zafi yana ƙona ta, yanzu kuwa duk ta gane kansu.

Wankanta ta yi a nutse, ta fito tana goge jikinta da ruwa, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta.

Baba uwani ta yi sallama, da kayan mopping a hannunta.

Rumaisa ta razana tana neman hijjabi ta saka, kasancewar daga ita sai towel.

Baba uwani ta ce "Haba ranki ya daɗe, ai na haifeki, meye na damuwa kuma, gyara miki ɗakin zan yi".

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ki bar shi kawai zan gyara da kaina, kaya zan saka".

"Ki saka kayanki kawai, aikina zan yi".

A ɗan hasale rumaisa ta ce "Ki bar shi kaya zan saka".

Ta kalli rumaisa, ba wata uwa a jikin nata sai tsirfa. Ta juya sumi-sumi ta bar ɗakin.

Guntun tsaki rumaisa ta ja ta ce "Wannan mata meye damuwarta ne? Bana son shishshigi", rumaisa ta saba yawonta a gidansu, babu suturar kirki ba ta damu ba, amma ba ta yadda wani na waje ya ganta ba. A gaggauce ta saka kayan, tana son ta yi magana da adam Kafin ya fita.

A falo ta tarar da adam yana danna system, babu alamar zai fita yau.

"Ina kwana" ta faɗa ba dan ta na tsammanin ya amsa ba, aikuwa bai amsa ɗin ba.

Ta ɗora da cewar "Dama, tambayarka zan yi, yau tun da juma'a zaka ɗauko mini Sabir ɗin, ammi ta ce za a din ga kawo shi, juma'a zuwa ranar lahadi, sannan dan Allah ka kira mini yaya Aliyu a waya, dan Allah su zo".

Ya kalleta ya ce "Da ni ki ke ko da system ɗi na, ko akwai wani bayan ni a nan?" kallonsa ta yi da mamakin rainin hankalin da ya yi mata ta ce "Da kai nake mana".

"Bani da suna ne ko yaya?"

Rumaisa ta ce "Ka na da shi".

"Ok, ya sunana?" Yayi maganar yana tsareta da ido.

Har ta buɗe baki za ta ce Adam, sai ta ji sunan yayi mata nauyi a bakinta, gashi ya tsareta da ido, yayi mata kwarjini sosai.

"Papa" ta faɗa a hankali.

Adam ya ce "Waye hakan?"

"Saboda Sabir, na ji ya fara koyar faɗan sunanka"

Ɗan rausayar da kai ya yi, a ransa ya ce "Ashe kina da hankali wasu lokutan '.

A zahiri kuma ya ce "Me ki ka yi wa baba uwani, na ga ta fito daga ɗakinki, kamar ranta a ɓace?".

Ta ɗan tura baki ta ce "Ba abun da na yi mata"

"Bana son ƙarya"

"Ba ƙarya nake ba, zuwa ta yi wai za ta gyara mini ɗaki, ni kuma daga wanka na fito ban saka kaya ba, kawai cewa na yi ta bar shi zan gyara da kaina shikenan fa"

"Ba ta haifeki ba, me za ta gani?"

Da sauri ta kalleshi ta ce "Taɓ, ni wallahi ba zata ganni ba".

"To me za ta gani?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba.

Ya girgiza kai ya ce "Kasancewar ta na yi miki aiki, ba ya na nufin ki rainata bane, ita ce babbar hadimar ammi, muma muna girmamata. Ga abinci can sun girka, ki je ki karya".

"Na ƙoshi" ta faɗa cikin jin haushi, dan ita ba ta ga abun da ta yi wa baba uwani ba.

"Kin ƙoshi saboda me?"

"Ni so nake na din ga girka abincina da kaina, ammi ta ce kar na yarda da kowa, kar na je ayi mini aisiri a cikin abincin"

Tattara hankalinsa ya yi a kan rumaisa sanannan ya ce "Waye zai yi miki asirin?"

Ta ce "An ce a gidan sarauta ana asiri, dan haka ni ba zan ci wannan abincin ba".

"Ai dama me hali baya fasa halinsa, kin huta, sai dai idan ba zaki ci abinci a gidan nan ba, idan ki ka sake na ganki a kitchen da sunan zaki yi girki, sai na saɓa miki, ba zaki haɗa mini gobara a gida ba, kuma ki cigaba da ina magana ki na yi mini gatsali, zaki ga yadda zamu yi da ke"

Ya mayar da hankali a kan system ɗin sa.

Jin sa kawai take yi, amma ta yi wa kanta alƙawarin ba za ta ci abincin nan ba.

Ya tashi ya shiga ɗakin sa, ya fito da mukullin motarsa, ya fice ba tare da ko kulata ya yi ba.

Yana fita ta sauka ƙasan benen, ta tarar da su baba uwani suna aikace-aikace.

Tana ganin rumaisa ta saki fuska tana faɗin "Uwar ɗakina, sannu da fitowa, kina buƙatar wani abun ne?"

Rumaisa a ran ta ta ce, ji matar nan kamar ba yanzu ya ce ta fito ranta a ɓace ba.

"Bakomai, Takawa ne ya ce mini, kin fita daga ɗakina ranki a ɓace, kamar baki ji daɗin abun da na yi miki ba, ki yi haƙuri dan Allah. Sannan zan din ga yin aikin saman, zan din ga gyara komai".

Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar ɗakina, ai zamanki muke yi, kar ki damu dolenmu mu gyara miki, ai ke hutuwarki kawai zaki din ga yi"

Ruma ta ce "A'a na iya aiki, zan din ga yi da kaina". Baba uwani ta bi rumaisa da kallo, ta shiga cikin kitchen ɗin, ta ɗebi indomie, da abubuwan da take buƙata.

"Indomie zaki ci? Ko in turo barira ta dafa miki".

"A'a na iya girki" ta juya ta nufi stairs.

Mamaki ne ya cika baba uwani, sai a yau ta fuskanci yanayin rumaisa fetsararriya ce.

Ko da rumaisa ta je kitchen ɗin ta na saman bene, babu gas a cylinder ta, dan haka a kan electric ta dafa indomie da tea ta zauna a kitchen, ta ci kayanta, ta yi wanke-wanke.

"Ke amarya kina ina ne" ta ji muryar Aliyu a bazata.

Da gudu ta fito falon, ta ɗane jikin Aliyu tana murna.

Shi da mai sunan baba ta gani, ta saki Aliyu ta nufi mai sunan baba.

Murmushi yayi ya riƙeta da hannu ɗaya ya ce "Ya kike?"

Take ta fara kuka ta ce "Yaya shi ne ku ka ƙi zuwa"

"To yanzu ba gamu ba, idan kuka zaki yi zamu koma".

Ta share hawayen ta ce "na daina"

Zama suka yi Aliyu yana ta kallonta yana "Inyee amarsu ta ango, to yanzu ma mama ba ta san zamu zo ba, wai kar mu saka ki kuka, yaya Umar ya ce mu zo mu ganki"

"Aikuwa kuka na din ga yi, yau ne kawai ban yi kuka ba".

Aliyu ya ce "Ke, na ga wasu mata a ƙasa su waye?".

Rumaisa ta ce "Wai hadimai ne, su suke aikin gidan".

"Saboda me, ke baki iya bane?".

"To ya zan yi, ammi ta ce gidan yayi mini girma ba zan iya aikin nikaɗai ba".

"Ke, wannan dattijuwar za ta yi saka ido, kamar mara gaskiya kin ga yadda ta din ga binmu da kallo, wai su waye mu daga ina muke?"

Rumaisa ta ce "Ni ina ruwana, tun da ba a kaina suke ba".

Mai sunan baba ya ce "Da ruwanki mana, ki dai kula da kan ki sosai ".

Sallamar iman ce ta kaste musu hirar, rumaisa ta ce "Yeee, yau baƙina da yawa"

Idonta bai sauka a na kowa ba, sai cikin na mai sunan baba.

Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau " ya amsa yana kawar da kansa.

Ta gaida Aliyu ma, ya amsa mata cikin sakin fuska.

Rumaisa ta karɓi Sabir tana murna.

Kamar kullum, tsoro da fargaba ya mamaye iman, kasancewar, mai sunan baba a wurin.

"Anty iman, na zaci ba za a kawo shi ba fa".

"A'a za a kawo shi, amma ba bar miki za ayi ba, sai an haɗa masa kayansa tukuna".

Zuwan Iman ya sanya mai sunan baba tashi ya cewa Aliyu su tafi.

Kamar rumaisa ta yi kuka ta ce "Mai sunan baba baku daɗe ba fa".

"Eh, ai mun zo dai, tafiya zamu yi sauri muke yi "

Iman ta ce "Idan saboda ni ne, bari in tafi, takawa ya mayar da sabir ɗin".

Ta yi maganar tana tashi.

"Meyasa zamu tafi dan kin zo? Nemi wuri ki zauna ba zama zamu yi ba dama" ya mayar da idonsa kan rumaisa ya ce "Take care"

Daga haka yayi wa Aliyu alamar su tafi, rumaisa ta ce zata rakasu, amma ya ce ta yi zamanta, ya ajiye mata kuɗi, suka fice.

Kuka rumaisa ta yi ta yi, iman tana rarrashinta, ita kan ta tana mamakin irin halina bawan Allah nan.

Kasancewar iman na nan, ga kuma Sabir, ya sanya rumaisa ta haƙura, suka shiga kitchen ita da iman suka yi girki, iman ta tayata ta ɗebo wasu daga kayan abinci daga kitchen ɗin ƙasa zuwa na sama.

Iman ta din ga mamakin yadda rumaisa ta iya girki.

Rumaisa ta ce "Hmm, tun ba a barina na yi a gida, in yi in jagwalgwala har na iya, yaya Abdallah tare muke girki, har a YouTube yake ganin girki mu gwada, daga baya na gane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login