Showing 108001 words to 111000 words out of 199108 words

Chapter 37 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

811

ya ce mini mai martaba ya tura mu wakilcin taro, kuma da na dawo zan je course ɗin nan ta watanni shida, kin ga ba zan wani daɗe tare da ita ba".

"To sai ta zo ɗin dai tukuna".

"Ammi, ina Jamil ne? Ban ƙara ganinsa ba fa, tun da ya tafi ɗaukko Rumaisa".

Ammi ta ce "Ni ma dai na yi mamaki, ka san da ta zo ta ce wai ƙin hawa motar ta yi, saboda ta san yana jin haushinta, ina ga saɓani suka samu, ya ji haushi, mukullin motar ma, Sidi ya bawa ya kawo".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "To ai ba da ni suka yi ba, ni kaina ba na son surutun nan na ta, ita ba ta iya kara ba ko kaɗan".

"Ai ƙuruciyar kenan, sai dai ayi ta sakata a hanya, ni maganar da ta faɗa ne a kan Jamila, nake jin tsoron kar ta koma kunnenta, bana son tashin hankali da masifarta, in da na gode wa Allah ma, ba a gaban wani ta faɗa ba"

Takawa ya ce "Ina tsoron wannan bakin na ta a cikin masarautar nan, sai dai Allah ya shirya".

Can ɗaki kuwa, suka gama koke-koken su, ita da Iman, kamar wata babba haka ta yi ta rarrashin iman.

Can Iman ta ce "Anty rumaisa ba zaki kira mai sunan baba ki yi masa godiya da ya ya je gida ba?".

Ta yamutsa fuska ta ce "Godiyar me kuma?"

"Dubiya da ya zo mana".

"Ba ki san halin gayen nan ba, ba lallai ya gode, kina ganin yarfani ya yi dan na ce zan raka shi, wai na je na kula da mijina, yanzun ma zai iya yarfa ni".

Iman ta ce "Ba haka bane, yakamata ki yi masa godiya, idan yana gida ma sai ki gaisa da su mama, ko yana zama yayi dare a waje?".

Rumaisa ta kalleta ta ce "To mai sunan baba da mace ne, da an shigesu, ba shi da wasu abokai fa, daga makaranta sai kasuwa, sai gida, su wani ball su wani abubuwan abokai, ko yawo duk ba ya yi, da dai yaya usy ne ko gadanga na mama yaya Aliyu, mama da kanta take fita yawon nemansu wataran"

Iman ta yi murmushi ta ce "Kowa da halinsa kenan, ga wayar ki kira shi"

"Sai dai ke kira shi"

"In kira shi in ce masa me, na gaya miki ya ce na daina kiransa".

Rumaisa ta ce "Gaskiya idan na kira shi, ya yi mini wulaƙanci sai na rama a kan ki".

Iman ta bata wayar ta ce "na yarda".

Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga, alhalin wayar na hannunsa, yana kallonta, ya din ga fatan Allah ya sa muryar iman zai ji, ba ruma ce ta kira ta dame shi ba.

"Hello mai sunan baba"

Sak yayi da ba Muryar iman ya ji ba.

"Ya aka yi?"

"Amm dama, kiranka na yi na ji ya ka je gida, na gode sosai"

"Yayi" ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin kashe wayar.

Ruma ta ce "Dama Iman ce ta ce, na kira ka na tambayi ya ka je gida?"

Da sauri Iman ta ce "Kai Anty rumaisa" ta yi maganar tana karɓe wayar ta kashe.

"To me na yi kuma?".

Cikin shagwaɓa iman ta ce "Meyasa zaki gaya masa haka, kar ya zaci wani abun fa".

"Wani abu kamar me?"

Iman ta ce "Bakomai" ta tashi tsaye ta ce "Ki kwana a kan gadon, ni sai na kwana a kan katifa a ƙasa".

Rumaisa ta kwanta ta ce "Ai ba kara zan yi miki in ce a'a zan kwana a ƙasa ba" Iman ta yi dariya, ba ta sake cewa komai ba, ta yi shirin baccinta ta kwanta.

Har kusan ƙarfe biyun dare, rumaisa idonta biyu, rabon da ta ci karo da abun da zai hanata bacci, tun farkon shigarta hannun kidnappers, daga baya kuwa baccinta take yi, sai lokacin da ta kuɓuta da Sabir.

A hankali ta tashi zaune, ta na jin kanta duk ya yi mata nauyi, tausayin wa ma yakamata ta ji ne?.

Ta kalli in da iman take barci, ta girgiza kai 'Allah sarki Iman, a yadda ki ka bani labari ke yanzu gaba ɗaya ba ki da uwa ba ki da uba, sun rasu ba zaki taɓa ganinsu ba har abada, ba a san in da za a ga dangin su ba, ba ki da wa ba kuma ki da ƙani ga larura. Ashe ni kukan daɗi nake, na ban san babana sai a hoto, wannan ke ce marainiya.
Allah sarki ammi, ashe da gaske mama take da take cewa aure ɗan haƙuri ne, ni na zata kawai abinci ake ci ayi bacci, amma a ƙwace mini ɗa a bawa kishiyata, wallahi sai dai ayi masifar da za ayi kowa ya huta.
Ga ɗan ta ba shi da lafiya, ɗayan kuma an raba shi da ita, kamar yadda dai mama take sonmu a ƙwace mata ɗaya daga cikinmu, ko kuma kamar ni a ƙwace Sabir ya auri ƙanwar anty aisha ya bata. Kam bala'i wallahi da sai dai kowa ya rasa'.

Ta dafe kanta, abubuwan ba da ita suka faru ba, amma ta ji sun dameta, ammi tana da kirki fiye da tunani, amma meyasa aka tsaneta?.

Ta tashi ta sauka daga kan gadon, ta zauna a ƙasa ta yi shiru, abun duniya duk ya dameta, ƙarshe a nan ƙasa ta yi bacci.

Mai sunan ba tun da ruma ta ce masa Iman ce ta ce, a kira shi, yake jin wani irin nishaɗi a ƙasan zuciyarsa, dan ƙoƙari yake ya hana hakan tasiri a zuciyarsa, dan yaƙi yadda ya sallama cewar ya faɗa soyayya, haryanzu tantama yake yi.

Da asuba bayan sun yi sallar asuba, rumaisa ta je ta gaida ammi, ta tarar da ammi na salla, ga sabir ya farka, yana kuka. Ta hau kan gadon, ta ɗauke shi, ta bashi ruwa ta kwantar da shi ta hau yi masa wasa, daga haka kuma suka yi bacci gaba ɗaya.

Wajen ƙarfe bakwa, ammi ta tashi rumaisa, ta ce ta je ta yi wanka, ta shirya ta je ta duba takawa da ya kwana a ɗakinsa, ta zo a kaita makaranta.
Gaba daya ba ta sanya ran zuwa makaranta ba, a zaton ta tun da bashi da lafiya, ba bu zuwa makaranta.

Ta je ta yi wanka, ta karya, sannan ta tafi ɗakin nasa.

Ciwon kwana ɗaya, amma idanunsa sun yi zuru-zuru.

Ta ƙarasa kujerar da yake zaune, sanye da ashe ɗin jallabiya ta ce "Sannu ka warke?".

Ya kalleta ya ce "Ina kwana?" Gatse yayi mata, amma cikin ko in kula ta ce "Lafiya ƙalau, ya jiki?"

Jawota ya yi ya zaunar da ita, ya tsura mata ido sannan ya ce "Baki san gatse ba ko? Ban isa ki gaisheni ba?"

Ta ce "Auu, wai dan ban gaishe ka ba, na ɗauka kawai gaisheni ka yi, to ina kwana?"

Yayi shiru bai amsa ba yana bin ta da kallo.

"Ai ka ga matsalar, mutum ya gaisheka, ka ƙi amsawa wai sai an yi maka irin taka". Bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta.

"Barka da wannan lokaci ranka ya daɗe, na sameka lafiya?" Ta yi maganar tana risunar da kai, kamar yadda ake yi masa.

"Ki tashi ki je, sidi zai kai ki makaranta".

Ta tashi ta amsa masa da to, tayi waje.

Sai dai a harabar gidan, ta haɗu da Mahmud, yana shirin fita.

Gaisawa suka yi, ya ce "Ya mai jiki?".

"Ai ba zan amsa ba, sai ka je ka duba shi"

"Anya zuwa dubiyar nan kuwa? Taho mu je in kai ki makarantar, ya sunan makaranta"..

Sunan kawai ta gaya masa ya gane, ta buɗe motar ta shige.

Sidi ya taho da sauri, ya ce "Ranka ya daɗe, jiranta nake giwa ta ce zan kaita makaranta ne".

Mahmud ya ce "Mayar musu da mukullin, zamu tafi tare" ya ja motar suka tafi.

Suna tafe a hanya, tana zuba masa shirme, yana biye mata.

Can ta ce "Kai ina son mama a rayuwata daddy, a duniya bayan Allah da Manzonsa, ba abun da nake so kamarta, dama ban san babana ba, amma mama dai kam, Allah ya tsundumata a aljanna. Allah ya bani abun da zan shagwaɓa ta, in ta sai mata abubuwa".

Ya ce "Amin, sai ki yi ta mata biyayya da addu'a".

"Ai ina yi mata, har da ammi ma dukkansu yi musu nake yi, mutane su yi ta hantarata wai ba na ji, har da yayanka ma hantarata yake yi wataran amma dai ya na da kirki wasu lokutan, idan na yi masa laifi sai ya yi mini banza. Ammi ka ga da mama da Ammi, da yayyena, da Anty Aisha da Sabir, da mai girma turaki, da gwaggo, da iya, da malam habibu na islamiyyarmu, da barde ɗan bindigar da yake bani abinci, da Bashir abokin takawa da ya tsinceni, da Iman kai duk wanda suke yi mini mutunci a rayuwa, kullum sai na yi musu addu'a da fatan alkhairi"

Ya ce "wonderful, gaskiya nima a taimaka a sakani a ciki".

"Eh zan saka ka, amma kai wa ka ke yi wa addu'a, tsakanin Ammi da wannan matar?" Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi ya kalli rumaisa.

"Daddy, duk yadda nake son Sabir, da anty aisha na raye, duk wahalar nan da na sha, ba shi da kamarta, kuma dole ne ya bita, to kamar haka ne fa, kai da wannan matar, duk rashin ji na, Mama sai dai ta yi ta cewa Allah ya shiryeni, amma kai har ka saka Ammi ta yi maka kuka, kana da kirki amma ita ba ka yi mata meyasa?"

A dai-dai nan, ya iso ƙofar makarantar su, bai amsa mata ba, yayi shiru.

Ta ce "Yauwwa, ya batun baba uwani, ta je kuwa?"

Ya girgiza mata kai ya ce "A'a, kuma ban ji mummy ta yi maganar ba, ina ga ba ta kai ga faɗa mata ba"

Ta buɗe motar ta ce "Shikenan sai an jima, na gode sosai Daddy" ta nufi cikin makaranta.

Sosai maganganun rumaisa suka ratsa shi, baya samun wanda zai din ga tattauna maganar nan da shi, yana ji a jikinsa abubuwan nan da suke faruwa, tamkar juya sama ne a ƙasa, gaba ɗaya abubuwa basa tafiya daidai, amma jin sa yake, tamkar an ɗora masa dutse, kuma kamar a cikin wata kurku yake da ruhinsa ya kasa samun salama.
Ranar da ammi ta zubar da hawaye, saboda ya ƙi auren iman, ji yayi kamar zuciyarsa tana ci da wuta, ya daɗe yana ganin abun a idonsa, amma ya ji farincikin mummy shi ne a gaba, dan haka wannan bakomai bane ba.

Sosai Adam yake masifa, jin wai mahamud ya ɗauki rumaisa zai kaita makaranta.

"Takawa, ka sakawa zuciyarka salama, dan Allah ka yi haƙuri mana".

"Ammi kin san ba shiri muke ba, idan ya kitsa mata wani abun fa? Ko ya bugi cikinta ta saki baki tana zuba, meye haɗinsa da matata? Yarinyar nan ba cikakken saiti ne da ita ba, kar a cutar da ita*.

Ammi ta ce "Kana da gaskiya, amma na ga ta su ta zo ɗaya, in sha Allah babu wani abu da zai faru, tun da ka ji sauƙi ma, sai ku tafi amma dan Allah kar ka ce zaka yi faɗa, kaga ba ka da cikakkiyar lafiya. Kuma ka sani ko a dalilinta komai ya dai-dai ta tsakaninka da ɗan uwanaka?"

Kallon idon ammi yake, tuni har hawaye sun cika mata ido.
"Shikenan ammi, ba zan yi magana ba, ki yi haƙuri, amma dole in raba shi da iyalina".

***
Da aka tashi daga makaranta, Adam ne ya zo ɗaukar ta, saboda ya ji sauƙi sosai, ciwon bai kuma tashi ba.

Tana ganinsa ta hau dariya "Ka warke ne ka zo da kanka, da adaidaita sahu zan hau na tafi ai".

Fuskar sa babu walwala, yayi mata banza, ya ja motar suka tafi, sai dai ta ga ya nufi gidansu, maimakon na Ammi, ganin ya na ta cika yana batsewa, ya sanya ba ta kula shi ba, ta cigaba da harkokinta.

Ko da suka je gida, su Asiya suka din ga yi musu sannu da zuwa, suna yi wa Adam sannu, dan baba uwani ta gaya musu, maigidan ne babu lafiya.

Ya wuce ɗakinsa ta wuce nata, ta yi wanka, ta kwanta baccin da ba ta samu yi jiya ba.

Sai da aka yi la'asar, sannan ta tashi, taje kitchen ta haɗa shayi, ta zuba madara fal da milo, ta dafa ƙwai ta ci abunta, sannan ta ɗau littafinta, ta tafi ɗakin Adam.

Yana zaune a kan kujerar ɗakin sa, yana dudduba wasu takardu, ta yi sallama ya amsa mata a ciki, ba ta damu ta je gabansa ta tsaya, ta ce "Albishirinka?"

Ya kalleta ya ce "Ya aka yi?".

Ta nuna masa littafinta, na assignment ɗin da ta yi, ta zana malaminsu, ta ci 10/10.

Ya ɗan kalli littafin da mamaki, sannan ya kalleta, alamar yana jiran bayani.

"In gaya maka har malamin ya kirani gaban allo, zai yi disgracing ɗina, ya ɗaga littafin ƴan ajin suna dariya, ya tambayeni da turanci wai meye wannan? Ni kuwa na ce ni ban iya ƙirƙirar komai ba, amma idan malamai suka yi kyau kamar zanen nan nawa, to za a samu ɗalibai masu ƙoƙari da tsara zane kamar nawa, koma fiye da nawa, Aikuwa aka dinga tafa mini,ya ka ji azancin nawa"

Ɗan murmushi gefen baki ya yi, dan ya fuskanci ita fa dan kana fushi da ita, kai ta shafa.

Ya ce "You try".

"Yauwwa, sai ka saya mini kyauta, teddy bear nake so, da kuma ƴar tsana babba, sai lunch box ɗina"

Yayi mata kallon ba zaki girma ba.

"Ya naga kana kallona?"

"Mahmud, Alaƙarki da shi bana so, kar ki kai ni bango a kan haka".

"Wai meyasa zaka saka ni a cikin faɗa ku? Ni meye nawa yana yi mini kirki, shikenan dan kuna faɗa nima sai na din ga jin haushin sa. Jamil, Jabir, Samha alaƙar ka da su bana so, Jamil da Samha, sun wahalarsa da matarka, su meyasa ba ka gaba da su?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.

Rasa bakin magana yayi, duk yadda kake tunanin rumaisa ta wuce nan, a zahiri tana da ƙuruciya da wauta, but she have a very sharp brain, ba shi da amsar bata a yanzu dan ta ƙure shi.
Amma saboda kar ta ga ta yi nasara ya ce "Ni ne shugaba, a gaba nake da ke, dan haka duk hukuncin da na yanke dole ki bi".

Ta ɗau littafinta ta ce "Babu biyayya ga abokin halitta wurin saɓawa mahalicci, duk daƙiƙancina a makaranta, na san wannan, kuma Allah ya yanke rahamarsa ga mai yanke zumunta, Annabi ma ba ya tare da mai yanke zumunci, sai ka din ga jin tsoron Allah wurin yanke jiki kai ma" ta fice ta koma falo ta bar masa ɗakin.

Mintuna kaɗan ya fito ya fice daga gidan gaba ɗaya, ya dafe kanta ta ce "Na shiga uku wannan wane irin abu ne, anya kuwa zan iya, ni duk na gaji" tayi tsaki, ta tashi ta je ta ciko roba da gugguru, ta ɗaukko lemo, ta zo ta saka a gaba tana ci, tana kallon cartoon.

Hayaniya ta ji ana hawowa sama, ta tsaya tana jiran taga waye zai shigo?

Samha ce da Fauziyya, da kuma ruƙayya sai zee ƙanwar Samha, baba uwani biye da su, hannunta riƙe da foodflask.

Babu ko sallama suka zo suka zazzauna, baba uwani ta ajiye kwanukan, ta ja gefe.

Samha ta kalli rumaisa ta ce "An samu duniyar da babu a gidan tsoho, an yi ɗai-ɗai a katafaren gida, da duk dangi babu irinsa" rumaisa ta yi mata banza, ya cigaba da kora lemonta.

Ruƙayya ta ce "Allah wadaran naka ya lalace haryanzu ban ga technology a auren wannan busashiyar yarinyar ba, da ko rantsuwa na yi babu kaffara, ragowar masu garkuwa da mutane ce, sun gama lalata ta" ɗan shiru ruma ta yi tana tunanin, me take nufi.

Fauziyya ta ce "Ba wani technology, wulaƙanci ne kawai, dan Allah dubi Samha ki dubeta, ita ta isa ta kira kanta mace ma wallahi wannan ko a mai aikin samha ba ta isa ta zo ba, kalli bakin shegiya yadda take auna madara, saboda samun wuri, ga ƙirjinta fayau kamar faifai ba wata mamora, amma wai ita ya aura".

Rumaisa ta yi gyatsa ta ce "Gidan miji daɗi, mussman irin gidan papa, auren mai kuɗi daɗi ba, na samu promotion, gida babu, na samu a gidan miji" tayi maganar tana lashe madarar hannunta.

Fauziyya ta ce "Ke dalla rufewa mutane baki, tashi ki kira mana ɗan uwanmu, mun zo duba shi"

Cikin tsawa rumaisa ta ce"Ba zan kirawo shi ɗin ba tun da ke ba uwata ba ce"

Samha ta ce "Ke, uban wa ki ke yi wa tsawa".

"Uban duk wanda ya tsargu, ba sunana Aisha ba, sunana rumaisa Mahmud, ƙanwar maza, ku tambayi yayan naku wace ni, kawai ku zo ku cika mini kunne, wai ko a  ƴar aiki ba zan zo ba, ai Allhan ba naku ne ku kaɗai ba, da ban zo a ƴar aikin ba, sai na zo a matar gida, antynku ce ni, tun da matar yayanku ce ni, ke kuma da ki ke cewa ke ce mace, na ji ni namiji ce, ni duk wadda ta yi mini, wallahi sai ta ci ubanta, babu wata barazana da tashin hankali da ban gani ba, dan haka ba zaku ɗaga mini hankali ba, ke kuma da ki ke cikakkiyar macen, kin san idan ki ka gama cikar, zubewa zaki yi ki fara tsufa, kin ga ni kuma a lokacin da ki ka fara tsufa na cika ko? Banza kawai"

"Ke! Kina ƴar matsiyata ni ki ke gayawa haka? Kina da hankali kuwa, waye ubanki a ƙasar nan, har ni ki ke cewa ubana zaki ci?"

"Eh na faɗa, sai na ci ubanki, da ke da duk wanda ya ce zai zageni, ƴan fashin daji ma, ba su razana ni ba, balle ku shashashai, gwalagwaje, marasa mutunci, idan tunaninku gayya, ku taron mata ne, ni kaɗai dai-dai nake da tunanin maza bakwai".

Ayshercool.
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏



Ruƙayya ta riƙe haɓa ta ce "Kan uban nan, wannan wace irin yarinya ce, mara tarbiyya Binta ta aurawa ɗan ta?"

Jin maganar rumaisa ta yi wani iri,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login