Showing 180001 words to 183000 words out of 199108 words

Chapter 61 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

796

ƙure mai sunan baba da ido, har ya ƙarasa gabanta ya zauna.

"Ade, ga wanda yake ta yi mini ƙoƙari a kan kayana, shi ya ce a baki haƙuri, dan Allah kar ki koma ƙauye".

"Au jibo gulmata ka ke yi kana yamaɗiɗi da ni kenan, yaro na bar shanu da dabbobina a ƙauye, an zo nan ƙwam an ajiyeni, sanyi na neman yi mini illa, ga wannan yaran da suka addabe ni, ai zaman ƙauye yafi daɗi".

Mai sunan baba ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffara ba, wannan matar na da alaƙa da matarsa, duk da tsufanta, tsananin kammaninta da iman ba su ɓuya ba, sai a yanzu ma ya ga Iman ba kama take da Alhaji Aminu ba.

Ade ba ruwanta, ta din ga zuba tana bashi labarin yadda take son shanunta, tun da a cikinsu aka haifeta.
Kayan marmarin da ya zo da su, ya din ga ɗauka yana ɓarewa yana bata, tana karɓa tana ci.

Ta ce "Kaga yadda ka ke yi mini ɗin nan, shi ba ya yi mini, kullum cikin rubutu yake da lissafin kuɗi, Euro ya leƙo mun gaisa, sai ya kama hanya ya tafi yawonsa"

Alhaji Aminu ya ce "Sai ka ce a ƙauyen hakan suke yi miki"

"Eh amma dai idan na ga nagge, zuciyana na sanyi sosai"

"Yallaɓai kai baka da ƴan uwana ne?"

Alhaji Aminu ya ce "Kowa ya kama gabansa, ka san ainihi daman mu fulanin tashi ne. To ƴan uwan nawa galibi wasu suna wasu garuruwan, wasu ma wasu ƙasashen. Ni ne ɗan autan ta, ƙauyen fa a gidan wani ƙaninta take, wai an rabata da ɗan uwanta, kamar ɗan uwanta ya fimu"

"Ya fika mana, shi yana zama mu yi hira, kai sai shegen son kuɗin tsiya".

"Ni zaki tozarta a gaban baƙo ko, saboda ya baki ayaba, da lemo, to yasin a daina yin ƙosai a gidan nan, tun da ba kya so na"

Alhaji Aminu kamar kakarsa ya ɗauki Ade, su yi ta faɗa wasu lokutan, saboda shi ne ƙaramin ɗan ta.

Mai sunan baba ya ɗan jima a gidan, sannan baba ya ce zai tafi, Ade ta din ga tambayarsa yaushe zai dawo, idan bai dawo ba, za ta ƙulle takalmanta a zaninta, ko ta katanga ta bi, ta gudu ta koma ƙauye.

Mai sunan baba ya ce "Ai ba za ayi haka ba"

"Ka rabu da ita, karen nan zan kawo ɗakinta na ɗaure, na ga ta wurin fita"

Ta galla masa harara ta ce "Tashi ke je ɗakina, ka samo masa ɗan biskit ɗin nan"

Alhaji Aminu ya ce "Biskit kuma? Ade kyautar nagge zaki bashi, me zai yi da wani biskit"

Mai sunan baba ya ga ƙoƙarin ta ma, rikicin taufan na ta ba na zage² bane ba.

Mai sunan baba har ya koma gidan da yake, yana al'ajabi, kuma ya yanke shawarar zai yi wa Mahmud zancen, koma ya zo lagos ɗin, ya je su ganewa idonsu, su san ta in da za a ɓullowa lamarin.

Dan baya son yayi gaggawa, a zo a gane cewar ba su da wata alaƙa.

***
Ammi ta kasa mantawa da matsananciyar cin amanar da babu uwani ta yi mata, har ta kai ba ta iya sakin jiki tayi magana a gaban kowa yanzu, saboda tsoro da tunanin kowa ma ba son ta yake yi tsakani da Allah ba.

Ranar da mai sunan baba zai koma, Iman gyara kala-kala, aka ƙalƙale ko ina, ta shirya girke² ta sha kwalliya.

Dama har kirari yake yi mata da ɗawisu sarkin ado, Iman akwai ado da kwalliya.

Sosai suka yi missing ɗin juna ita da shi, sai dai da ya kalleta, Alhaji Aminu yake tunawa da mahaifiyar sa.

Ya din ga jin tamkar yayi mata zancen, amma ya kasa.

Washegarin dawowarsa, da yamma ya shirya su ka yi wa mama siyayya, suka je gida gaisheta.

Mama tayi ta yi masa faɗa a kan yanzu yana da iyali, yakamata ya mayar da hankali a kan gidansa, ƴan samarinta sun ɗauke mata komai, kuma dubu ɗarin ma da ya turo tayi yawa, jiransa take yi ya dawo dama.

Ya ce "Ni fa ba ruwana, ƴar ki ce ta ce ayi haka"

Mama ta ce "Kuma sai ka biye mata?"

Iman ta ce "Mama idan bamu yi muku ba, wa muke da shi? Ayi ta saka mana albarka kawai".

Mama ta ce "Albarka da addu'a kullum cikin su muke, amma dan mun haifeku ba ya nufin, mu takura rayuwarku, ina fatan dai kun je wurin hajiyar?"

Iman ta ce "Gobe in Allah ya kaimu za mu je ammi, a can zan wuni, shekaranjiya na koma gida, idan na kuma zuwa faɗa za ta yi mini".

Mama ta ce "Ai faɗan na gyara ne, mun kai ku ɗaki amma kullum ku ba kwa gajiya da zuwa gida"

Iman ta yi dariya ta ce "Mama kenan".

Kasancewar umar akwai kyauta, haka ya din ga bayar da kuɗi, ga bikin Abubakar saura wata ɗaya kacal ya rage.

Mai sunan baba suka yi waya da Mahmud, ya tabbatar masa da shima zai shigo kano, dan haka umar ya ce idan ya shigo yana son su haɗu za su yi magana.

Nusaiba har ta shirya tafiya makaranta, sun yi sallama da ammi, ammi tana ta fama Sabir, ya isheta da fitina, tana ta mita ta ce makaranta za a kai mata shi, ta huta.

Barira tana mata dariya ta ce "Anya ranki ya daɗe, kin hana mamansa shi ma balle kai shi makaranta, idan aka kai shi, sai kin fi kowa damuwa"

"A'a ba wata damuwa gara a kai shi, tun da yayi baki"

"Ammi, ammi" Nusaiba ta shigo tana ƙwalawa ammi kira.

"Lafiya baki tafi makarantar ba?"

"Ammi wai yaya Mahmud ne ya dawo shekranjiya, wai ya je har gida ya yi wa Jabir dukan tsiya, ta ƙarfin tsiya ya saka shi a mota a fita da shi, ya kai shi ofishin ƴan sanda an rufe shi. Yau shi kuma ya wayi gari da ciwon ciki, a asibiti ma ya kwana bai san waye a kansa ba".



Ayshercool
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*



Miƙewa Ammi ta yi cikin sauri ta ce "A ina ki ka ji?"

Nusaiba ta ce "Yanzu su musa suke faɗa, wai a asibiti ya kwana ma, tun cikin dare aka kai shi"

Rikicewa ammi tayi, ta nufi ɗakinta, Nusaiba ta bita ta na cewa "Ammi me zaki yi?"

"Nusaiba asibitin zan tafi, ni babu wanda ya gaya mini ai"

Nusaiba ta ce "A'a Ammi, kar ki je su yi miki wani rashin mutuncin, ki fara kiran takawa ki gaya masa"

"Yaron ya kwana a asibiti, ki ce sai na kira takawa na gaya masa?"

"Dan Allah ammi ki bari ya zo tukuna, sai ku tafi tare ma, kar su cutar da ke" da ƙyar Nusaiba ta shawo kanta, ta amince a kira takawan tukuna".

Juma'a ce, dan haka rumaisa ta ce ba zata makaranta ba, dan jikinta babu daɗi ko ina ciwo yake yi mata.

Takawa sai lallaɓata yake yi, yana son ya fita aiki, sai sangarta take yi masa, da shagwaɓa kala-kala.

Wayar Ammi ya gani, dan haka ya ɗaga tare da yin sallama.

Cikin ruɗewa ba tare da ta iya amsa sallamar ba ta ce "Takawa, kana ina ne? Mahmud aka kwantar a asibiti, wai ya kwana yana ciwon ciki jiya, so nake na je"

Takawa ya ce "Dan Allah ammi ki kwantar da hankalinki, ki bari na je wurin aiki, idan aka saukko daga masallacin juma'a zan zo na kai ki ki duba shi".

"Baka da hankali ne? Ka san ciwon ciki kuwa? Yaron ya kwana a asibiti amma ka ce sai an idar sa sallar juma'a awa nawa? Idan zaka kaini ka zo yanzu, idan ba zaka zo ba zan yi tafiyata ko me za su yi zan jure tun da ni na kai kaina"

"Kiyi haƙuri gani nan" rumaisa ta zuba masa ido, bayan ya kashe wayar ya ce "Duk ta rikice a kan ɗan da bai san darajarta ba, nan zai yi ciwo ta je duba shi, ta hanata ganinsa ta ce bacci yake, ko baya son hayaniya amma za  taje duba shi, ammi ba ta gudun abun da zai ɓata mata rai sam"

Ruma ta ce "Dan Allah zuciyar mutum ce a jikinka? Ka san me ake nufi da uwa da ɗa kuwa? Kai banda dalilin sihiri da nake da tabbacin shi ya raba ammi da daddy, kai kana zaton akwai dalilin da zai sanya ta zuba ido ta barwa wata mata ɗan ta.
To ai ko ni da abun da ke cikina bai zo duniya ba, da shi da Sabir, ban ga wanda ya isa rabani da su ba, kai idan aka ce za ayi asirin ma, sai na haɗa asirin da bokan na ci ubansu wallahi.
Dan Allah papa kaima ka sassauta wannan ƙiyayyar, yanzu bari in saka kaya in bika".

Ya ce "No, ki zauna a gida, zan je kawai"

Ruma ta ce "Hankalina ba zai kwanta ba, ka tafi da ni dan Allah, idan ba haka ba zan biyoka idan ka fita".

"Mimi kina da matsala, cikin nan ne bana son a gani".

Ta kalleshi ta ce "Saboda me?"

"Kin fi kowa sani ai, ba na son wani abu ya samu cikin nan naki, kullum cikin Addu'a nake yi Allah ya sa ki haihu lafiya, kin san komai ai"

"Babu abun da zai faru sai ikon Allah, ka tafi da ni saboda zatin Allah, hijjabi zan saka, ba wanda zai gan shi ai" kasancewar rumaisa ta ƙware a iya magiya, tamkar ƴar maroƙa, haka ya sanyata a gaba suka tafi.

Da shi da Nusaiba, da Ammi, haka suka rankaya asibitin da aka ce Mahmud yana can.

Gaba ɗaya Ammi ba ta cikin nutsuwarta, takawa ya ce "Ammi dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin San ki na da high bp".

A rikicen dai Ammi ta ce "Kai ka san sani high bp, ka tambayar mini ɗakin da yake dan Allah "

Ruma ta din ga kallon ammi cikin tausayawa, haka ta shafe shekaru da soyayyar nan da tausayi suna nuƙurƙusa zuciyarta, ruma ta jinjinawa mugunta irin ta mummy.

Ba ƙaramin razana ammi tayi ba, ganin Mahmud a kwance ba ya motsi, ga ruwa an saka masa, ga kuma oxygen da take taimaka masa yana numfashi, gefensa kuma mummy ce a zaune.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Mahmud meya sameka haka?" Ammi ta yi maganar cikin rawar baki.

Jin muryarta ya sanya shi ya motsa, ya fara yi wa ammi nuni da hannunsa ta zo.

Cikin hanzari ammi ta ƙarasa, idonta na ta zubar da hawaye.

Ya miƙa hannunsa ya riƙe nata, sai dai ba baki, sai hawaye da yake zuba ta gefen idonsa.

Ammi ta riƙe hannunsa tana jejjera masa sannu.

Ya ɗora hannun a kan cikinsa.

Ruma ma ta ƙarasa gaban sa cikin kuka ta ce "Daddy meyafaru? Meya sameka?"

Wata irin miƙa yayi bakin sa yana zubar da kumfa, cikin sarƙewar numfashi ya ce "Daughter mutuwa zan yi. Ammi. Amm....Ammi na faɗa yau rumaisa, Ammi ki yi mini Addu'a cikina" yayi maganar tamkar numfashin sa zai bar gangar jikinsa.

Daga rumaisa har Ammi kuka kawai suke, Nusaiba ma kuka take.

Cikin kiɗimewa Mummy ta tashi cikin azama, ta ce "Mahmud ciwo ba mutuwa bane ba, kar ka sake cewa zaka mutu, haba Mahmud kar ka yi mini haka dan Allah " tayi maganar tana fashewa da kuka.

Ya buɗe ido a galabaice ya kalli Mummy, ya zare hannunsa daga na ammi, ya riƙo nata "Mummy na gode, na gode Mummy"

Ya sake zare hannunsa daga na Mummy, ya miƙawa adam, sannan ya cewa ruma "Ki ce masa ko sau ɗaya ya riƙe hannuna Daughter" ya yi maganar yana sake mimmiƙe wa.

Cikin matsanancin kuka da tashin hankali rumaisa ta kalli Adam ta ce "Papa dan Allah"

Adam da tuni ya karaya, kuma ya tsorata da lamarin, A  hankali  ya tako, ya zauna a kusa da rumaisa, ya saka hannunsa a na Mahmud ya rungume shi.

"Ina son ka ɗan uwana, Ƙaddara ce"

Mummy ta rasa in da zata sanya kanta, dan lafiya ƙalau Mahmud ya kwanta, idan har ta ce ba ta ƙaunar Mahmud ƙarya take yi. Saboda yayi mata biyayya fiye da yaran da ta haifa, kuma ta saka an ƙwace shi an bata shi, dan mugunta, amma kuma sai ta fara son sa daga baya.

Likita ne ya shigo, ya din ga yi wa Mahmud wasu allurai.

Bayan fitar likita, duk sun yi shiru sun zuba masa ido, Adam yana rungume da shi, rumaisa ta miƙe zumbur, dan tamkar ana mata raɗa ta ji komai.

"Me ya haɗa shi da jabir ne?"

Takawa ya ce "A ina?" Duk suka tsaya suna kallonta.

"Meyasa ya daki Jabir ya kulle shi?"

Duk suka zubo mata ido.

ganin da Mahmud yayi Mummy, tana cikin damuwa, ya sanya ya sakata a gaba, a kan ta gaya masa meke damunta, ta kasa ɓoye masa ta gaya masa komai. Ba ƙaramin girgiza yayi ba da jin abun da Jabir ɗin ya yi ba shi da ruƙayya, tun da ya fita a fusace, sai wayar Hajiya Lubabatu ta gani, ta tabattar mata da zata ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login