Showing 153001 words to 156000 words out of 199108 words

Chapter 52 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

805

DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)





Durƙsawa takawa yayi, ya ɗauki sabir yana juyi da shi, yana murmushi, ya ce "I so much miss you darling, how are you?" Yayi maganar yana sumbatar goshin sabir.

"Paapa, daddy kaga" yayi maganar yana nuna masa in da Mahmud yake tsaye.

Kallon in da Mahmud yake yayi, yana mamakin saurin wayon sabir, ya ɗaga kai yana dubawa ko zai ga su ammi, amma babu kowa sai Mahmud.

Ya kira laila a waya, ta sanar masa da cewa Mahmud ya zo ɗaukarsa, zai fara masifa, ta kashe wayarta.

Mahmud kuma yayi banza bai ce masa komai ba, bashi da wani zaɓi, illa ya je ya saka akwatinsa a boot, sannan ya buɗe bayan motar ya shiga.

Har suka fara tafiya, babu wanda ya tankawa wani, sabir ne dai daɗi ya isheshi na ganin mahaifinsa, ya kasa zama wuri ɗaya, sai ya taka cinyar adam ya miƙe yana taɓo Mahmud "Daddy ka ga papa"

Mahmud yayi murmushi,yana shafo kan sabir da hannu ɗaya.

Takawa ya riƙe hannun sabir ya ce "Ina mimi?"

"Mimi, iman, baba" ya din ga jero wa adam sunaye, adam yana ta murmushi, yana jin yadda yayi kewar ɗan nasa.

Tun daga bakin gate, security suke yi wa adam barka da zuwa, aka ɗauki akwatinsa zuwa cikin gida.

Cike da ɗoki da son ganin mimi ya ƙarasa sashin ammi, ammi ce ta fara taro shi, ta rungume shi, ya durƙusa ƙasa yana gaisheta.

Ammi ta yi masa alamar ya tashi, ta sake rungume shi tana faɗin "Barka da sauka, ya hanya ya makaranta?"

"Alhamdilillah ammi, na same ku lafiya?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah"

Laila ta ce "Ƴan makarantar bokoko, sannu da zuwa"

"Yauwwa big aunty" yaran laila safiya, anam da haidar, suma suka taho da gudu, suka rungume takawa suna faɗin uncle.

Nusaiba da iman ma duk sannu da zuwan suke yi masa, fuskokinsu, ɗauke da tsantsar farincikin ganin dawowar ta sa, sai dai ya gama rarraba idonsa bai ga mimi ba.

Ya kalli iman ya ce "Amarya ba kya laifi, ya shirye shirye? Kodayake dole a zo a sake wani shirin, tun da na dawo".

Dariya suka yi gaba ɗaya, yana ta son ya tambayi rumaisa, amma kunya yake ji, kuma dai ya san suna cikin hutun makaranta.

Nusaiba ta kai masa akwatinsa ɗakinsa da yake sashin ammi, takawa ya ce "Nusiaba ina mimi ne?".

"Wallahi ban sani ba takawa, anty laila zaka tambaya" ya jinjina mata kai. Ya shiga yayi wanka, ya fito falo, an shirya masa abinci a dining, sai dai ammi kanta ta lura yadda yake ta leƙe-leƙe, ta san ba kowa yake nema ba sai rumaisa.

Laila kuma ta zauna ta saka shi a gaba da surutu, ya dubi laila ya ce "Yanzu a gidan nan a rasa wanda zai iya zuwa a cikinku ya taro ni?"

Laila ta ce "To yanzu a ƙafa ka taho? Ba ɗaukkoka aka yi ba?".

"Amma shi ne yakamata ya je ya ɗaukko ni?"

"Wannan kuma matarka za ka tambaya, da ta shirya hakan".

Ya kalli in da ammi take, ya ga ba ta jiyo su, ya ce "Yauwwa, wai tana ina ne?"

"Ita wa?"

"Meye haka ne, matata mana".

Laila tayi murmushi ta ce "Tana nan ƙalau tana gaisheka"

Ya tsuke fuska ya ce "Wai meye haka ne? Dan Allah tana ina, ina son ganinta"

"Zaka ganta ne, kai dai ka kammala cin abincin ka huta"

Ya dire cokalin ya ce "ya haka ne? Watanni shida ba ma tare, na dawo kuma kin ɓoye ta".

"To wai me za ta yi maka ne? Sai mun gama jan aji tukuna". 

Yayi dariya ya ce "Jan aji, wane ajin kenan, ina fatan ba wata rigimar ki ka koya mata, in the name of jan aji ba?"

"You will see" tayi maganar tana dariya.

Mirsisi anty laila taƙi faɗa wa takawa, in da rumaisa take, sai da ta kai ga ya cire kunya ya cewa ammi "Ammi wai ina maman sabir ne?"

Ammi ta ce "A'a bani zaka tambaya ba, ai dama da zaka tafi laila ka bawa riƙo, kuma da zaka dawo ta ce ba ruwana da abun ku, dan haka babu ruwana".

Wasa² har la'asar, tun yana tambayar har ya haƙura, sai daf da magariba, laila ta ce masa jeka gida, zan kawota.

Da fari bai yadda ba, sai da ta rantse masa tukuna, sannan ya amince.

Da ya je ya tarar da gida ko ina tsaf, duk an sauya fasalin zaman furnitures ɗin, ko ranar da aka kai masa rumaisa, gidan bai haɗu har haka ba.

Yana zaune a falo, yana kallon ƙwallon dole, saboda ya ma rasa abun yi.
Ya ji maganganu ana hawowa sama, da sauri ya tashi tsaye, yana jiran isowarsu.

Laila ce da Iman, sai nusaiba, rumaisa ta duƙunƙune da mayafin lafayarta.

Murmushin sa ya faɗaɗa, suka matsa daga kusa da rumaisa, ta ɗaga kai ta kalleshi, ta sake rufe fuska tana murmushi, ƙarasawa yayi gabanta ya rungumeta, yana murmushi.

Rumaisa ta rintse ido, saboda wata irin kunya da ta kamata, ganin yadda ya rungumeta a gaban su laila.

Nusaiba kuwa video take yi musu, tana cewa bari muyi ƙara'i tun da bamu yi a lokacin biki ba.

Ya ɗagota yana son ƙare mata kallo, amma ta hana shi damar hakan, sai cukuikuye jikinta take yi, mayafin gashi sai wani irin ƙamshi ne kala² yake tashi daga jikinta.

Laila ta ce "Ku zo mu tafi, kar ya saka mini duka, saboda jan ran da na yi masa, ga ta nan ku cinye juna, ƙarewar ƙauna".

Adam ya ce "Eh ɗin, Allah ya bada lada, amma an wahalar da mu haba".

"Da ƙafarka zaka zo nemana, zan rama ne" tayi maganar tana dariya, su iman suka bita suka tafi.

Suna tafiya, ya tsuguno dai-dai tsayinta, ya sake rungumota jikinsa, ya ce "I miss you little mimi"

Kasa magana tayi, kawai taji hawaye na zubo mata, jin tana sheshsheƙar kuka, ya sanya ya ɗagota, ya ce "Yaya aka yi?" Kasa shiru tayi, ta cigaba da kukan.

Ya zauna da ita a jikinsa a kan kujera, ya ce "Gaya mini menene?".

"Ba kai ne ka daɗe ba, kuma kwanakin suka ƙi cika ba?"

Takawa yayi dariya ya ce "To ni na hana su cikar?. Allah sarki, duk murnar ganina ce har da kuka? I so much miss you dear"

Lafewa tayi a jikinsa, tana cigaba da kuka, cike da shagwaɓa, ganin dawowar ta sa take yi, tamkar a mafarki.

"Mimi, meye sirrin ne? Kin ga yadda ku ka yi kyau kuwa, kalli skin ɗinki, duk da dare ne, kin yi fresh ga wani ƙamshi mai daɗi da ki ke yi, i like it baby"

"Baby kuma, kamar wata mijin anty laila, gursumemen dattijo wai baby, ni in dai zaka ce mini baby, sai ka sayo mini feeder, da kayan wasa"

"Ai na sani, ko shekara ɗari za ayi, ba zaki canza halinki ba mimi"

Hira suka sha sosai, rumaisa ta din ga bashi labarin wasu daga abubuwan da suka faru, sai dai tafi karkata ga laabrai masu daɗi da suka faru.

Haka shima ya din ga bata labarin makaranta, sai da suka raba dare a falon, ya ce suje ɗakinsa su kwana, amma ta kada baki ta ce Ba zata kwana a gado ɗaya da shi ba, sai ka ce Anty laila.

"Au kina nufin laila ce mara kunya ko, sai na gaya mata. Kuma banda gulma ba sau biyu kina kwana tare da ni ba?"

"To ai wannan tsautsayi ne, Anty laila dai kama rayuwar turai ta ratsata, take gaya mini ita ɗaki ɗaya take kwana da mijinta, wai tare a kan gado ya rungumeta, ni dai wannan karatun nata ba ɗauka nake yi ba. Dan ba iyawa zan yi ba"

Yayi murmushi tare da shafar sumar kansa, ya ce "Shikenan a sauka lafiya, tsarabarki sai Allah ya kaimu da safe"

Babu kunyar komai, ta wuce ɗakinta.

Sai dai da ta tafi ɗakin, ta kasa manta rungumar da yayi mata, haka ta shirya ta kwanta bacci, tana sake ganinsu a tare a cikin idonta, yana magana yana yi mata dariya.
Rungume pillown tayi, ta furta "papa a hankali"

Washegari da wuri ta tashi ta hau aikace-aikace, ta gyara ko ina duk da babu datti.
Ta shiga kitchen ta haɗa abincin karin kumallo, ta leƙa ɗakin Adam.

Ya lulluɓe jikinsa da bargo, saura fuskarsa kawai a ya bari a waje, baccinsa yake yi hankali a kwance, kai da gani ka san a gajiye yake.

Ta kalli agogon ɗakin, tara da rabi na safe, a hankali ta ce 'Papa baka jin yunwa ne?'

Sai kuma ta tuna lecture malamarsu da ta laila, wai yadda ake tashin miji daga bacci.

Ta rife bakinta da hannunta ta ce "Ni, haka kurum in je in wani kama shafa shi, ina cewa ya tashi, kamar wani mage, ko ɗan jariri, ai gara in daki ƙofa da ƙarfi irin yadda mama take yi wataran a gida, idan haka ne abun, meyass a gida ba a haka ake tashin su Yaya usy ba? Kai anty laila bata da kunya, zaman turai duk ya canza ta'.

Ta gama soki burutsunta, ta koma kitchen tayi wanke-wanke.

Daga nan ta tafi ɗakinta, yin wanka.

Sai dai ko da ta fito daga wankan, bisa mamakinta adam har ya tashi, dan ya ma biyota ɗakin.

"Wai daga zuwana nayi wanke -wanke har ka tashi?" Tayi maganar a ɗan tsorace tana rufe jikinta.

Maimakon ya amsa, kawai ya hau dariya, ta tsaya cak ta ce "Menene?".

Purple ɗin brezia da ta bari a kan gado, ta shiga banɗaki, ya ɗaga mata ya ce "Meye wannan?"

Kame-kame ta fara tana son faɗar abun da zata kare kanta da shi.

Ya ce "Inyeee mutuniyar, ai kamata yayi a nuna mini, ni dama tun da nayu hugging ɗinki jiya, i feel it but i thought na scam you wanta scam me, ashe na gaske ne, come let me see inyeee".

Shan kunu tayi ta ce "Papa bana so"

"Meye ba kya so kuma? Ganin kawai"

Ƙarasowa tayi zata karɓi breziar, amma ya riƙeta yana dariya, ta saka hannu ta riƙe towel ɗin ta gam, tana ihu.

"Ni wallahi da baka nan, nafi sakewa"

"Abun har da sharri, kamar ba jiya ki ka gama kuka ba, saboda kin ganni. Anyway, shirya ki zo mu yi breakfast, zamu yi magana"

Sai da ya bar ɗakin sannan hankalinta ya kwanta, ta shirya, ta fito tana wani haɗe rai.

Shi kuma ya ƙureta da ido, har ta zauna.

Taƙi kula shi, tayi serving ɗin sa, ta ja nata ta fara ci, duk yadda ya so ya maze kasawa yayi, dan yana jin daɗin tsokanar rumaisa yaga ta haɗe rai.

"Papa dan Allah ka daina kallona kana dariya, Allah zan tashi".

"Allah da iko yake, abun ne da mamaki, six months back, a ƙwailarki na tafi na barki, amma in just six months ace lamari ya kankama haka, kuma kin ƙi yarda na tabattar kar in je acuci ake yi mini.
Abunki ras da ke, ai ni yanzu kuma na daina takara da ke, na yarda yafi nawa nesa ba kusa ba, wane ni ma? Ai ni yanzu babu suaran jayayya, zaki iya rainon baby yanzu sosai, kai congratulations mimi, kamata yayi fa mu yi party, tare da celebration, mimi is no more ƙwaila, she's now a big girl, she can bear a baby, she even wore brezia size nawa ne ma ki ke sakawa, mu je mu sayo dozens of it" ƙarshen ƙuluwa rumaisa ta ƙule, ta jefa masa guntun ƙashin da yake hannunta, ta tashi za ta tafi. Ba dan ya iya shanye dariyarsa ba, ya riƙe ta yana cigaba da ƙyaƙyatawa.

Duk da tsiyatakun da yake tayi mata, ta kasa fushi da zuciya, watannin nan da yayi, ba ƙaramin missing ɗin sa tayi ba, amma dawowarsa ya sakata a gaba da tsokana kamar tayi kuka.

Ta tafi kitchen yin wanke-wanke ya bita, ba abun da yake tayata, ya sakata a gaba da tsokana.
Ruma ta kalleshi, kamar ba shi ne idan ya kamile ya tsuke fuska, ko fara'ar kirki ba ya yi ba, yayi ta muzurai, mussman idan yana cikin shigarsa ta sarauta, amma yadda ya sakata a gaba sai ka ce yaya usy saboda tsokana.

Ya ƙaraci dariyarsa ya koma falo, ya cigaba da kallo, lokacin sallar azahar yayi, ya tashi ya fita masallaci.

Sai dai da ya dawo, har ta kammala girki, ta yi salla ta canza kaya, amma ta kima uban hijjabi, tana so ta ganshi sosai, amma tsiyar da yake mata duk ya takurata.

Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Budurwar, meye haka kuma?".

"A ina?".

"Meye na wani saka hijjabi ana zaune ƙalau, wannan abu na farinciki da ya same mu, gaskiya ban yadda ba".

"Allah papa zan tafi ɗaki na daina fitowa"

Ya ce "Sorry, ke kin san yadda na yi kewarku kuwa, tsokanar da na daɗe ban yi miki ba nake fanshewa. Ya ƙarasa wurinta ya cire hijjabin, tana riƙewa amma ya cire shi.

Kasancewar ba a dining za su ci ba, suka zauna a ƙasan carfet.

Ta janyo kwanukan abinci, da plate biyu, ya ce mata "an daina raba plate, a ɗaya zamu ci" ta tuna anty laila ta ce mata cin abinci kwano ɗaya da miji, yana ƙara soyayya, amma ita ba wannan ya dameta ba, sai tambayarta da tayi, to ba zai yi mini kishiya ba, laila ta ce sai kin kula da abubuwan da na koya miki tukuna.

Ta zuba abinci ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login