Showing 57001 words to 60000 words out of 199108 words

Chapter 20 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

1170

ta ce "Ok, size ɗin phant fa?" Ruma ta buɗe baki, tana kallon fuskar Adam ko yana jin me iman ke tambayarta.

"Wannan kuma mama za'a tambaya"

"Brezia fa, ko ita ma a tambayeta?"

Rumaisa ta ce "Amma dai anty iman kawai dai tsokanata ki ke yi, idan aka saka wannan ai sai dai yayanki ya saka, tun da da nace a bani sabir, cewa yayi bani da abun bashi nasa ma yafi nawa girma, sai dai idan shi zai saka, ni bana saka komai, bani da su"

Dariya Iman ta yi ta ce "Allah ya baki haƙiri. Akwai kaya da zai baki, kalar da ki ka zaɓa ne, wanda zaki rabawa ƙawayenki, zamu saka ranar bridal shower, sai kuma na dinner, kayan lefenki na ji su mama sun yi magana sun ce kawai a kai miki gidanki, idan kin tare sai ki gani, kayan da zaki saka ma duk ya taho da su"

Rumaisa ta ce "To, sabir fa wanne zai saka?"

Iman ta yi murmushi ta ce "Iri ɗaya da babansa"

Rumaisa ta yi murmushi ta ce "To ki gaishe mini da ammi". Ta miƙa masa wayar, ba tare da ta kalleshi ba.

Mayafin kanta ne yake zamewa, gashinta baƙi ƙirin, har gaban goshinta, tamkar zai haɗe da yalwatacciyar baƙar jagirarta.

"Me ki ke cewa na ce nawa yafi naki?"

"Au kasa kunne ka yi ka ke jin me ake faɗa? To me ka ji iman ta tambayeni?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.

"Size ɗin brezia take tambayarki, kuma tun a gida na gaya musu, baki da abun sakawa"
Buɗe baki ta yi tana kallonsa da mamaki, shi ko nauyin faɗar brezia ba ya ji a bakinsa, a haka sai ka rantse da Allah ba ya magana.

Ya ce "Ba kin ce mata, na ce nawa yafi naki ba, ai ba ƙarya na yi ba, ko baki gani ba"

'Wallahi na kusa daina rufa maka asiri, zan fara faɗar maganganun da kake gaya mini na batsa, bana so ni ba ƴar iska ba ce ba"

Guntun tsaki ya ja, ya tashi tsaye ya ce "Mu je ki karɓi kayan nan, ina da wurin zuwa" tashi ta yi ta bishi tana haɗe rai, saboda kar ya kuma kawo mata maganar banza.

Ko da suka fito ƙofar gidan, ɗan ƙare mata kallo ya yi, mayafi ne a jikinta yau, ɗan ƙarami, siririya ce mai matsakaicin tsayi, ƙirjin nan fayau babu komai, sai dai daga ƙasa ƙugunta ya buɗa, ko ta zama cikakkiyar budurwa, zata kasance a cikin mata masu diri daga ƙasa.

"I just wish you are that big enough, a kece raini tsakani na da ke, in ga ƙarshen fitsara, unfortunately look at you, ƙwaila mara jin magana, ban san ma iya adadin lokacin da za a ɗauka kan ki zama mace ba, baki da magana sai ce mini ɗan iska, ba zan manta ranar da ki ka gaya mini haka ba, amma zaki ga ɗan iska ganin idon ki, zo ki kwashi kayan nan zan tafi "

What's app only please.
Ayshercool
08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*


Sororo ta yi tana kallon sa, sam ba ta fuskanci in da ya dosa ba, abun da ta iya ganewa kawai shine ƙwaila, wato wadda ba ta da nono.

"Am talking to you kin tsaya kina kallona"
Cikin tsuke fuska ta ƙarasa gaban booth ɗin, manyan ledoji ne a ciki.
Ya dubeta ya ce "Gasu nan, iman ta ce yadin wanda zaki rabawa ƙawayenki, sauran bayanin ban riƙe ba, idan kun yi waya ta yi miki.
Akwai invitations da wurin da za ayi events, sai kayan sawarki".

Maimakon ta ce Ta gode, sai cewa ta yi "Ni ta yaya zan iya ɗaukar wannan kayan masu nauyi, kuma fa an sai mini kaya a gida, nifa kar ka zo daga baya ka din ga yi mini gori, idan ka san ba da zuciya ɗaya ka bani ba, ka riƙe abunka, ƙawayena za su saka abun da suke da shi" ɗagowa yayi ya kalli rumaisa, sai dai maimakon ya ji haushin abun da ta faɗa, sai ma ya yaba da yadda take taka tsan-tsan, ita dai kar ayi mata gori, tana da gudun abun wani.

Amma a zahiri, sauke mata kayan ya yi a ƙasa, ya rufe booth ɗin motarsa, ya saka hannu ya ɗauko wata babbar ledar a motarsa, ɗora mata a kan kayanta ya ce "Idan da wani abun ki saka Aliyu ya kirani" daga haka ya shiga mota ya ja ya tafi.

Gida ta shige ta ce wa su Huzaifa su je waje su kwaso kaya, idan ba haka ba a sace. Sun zata da wasa take yi, ashe da gaske take.
Gwaggo tuni ta zo kano, ita da lawisa, da zaliha, aka baje kayan da takawa ya kawo wa rumaisa.

Iya leshin da zata saka na dinner, ka san ba ƙarami bane ba, an ɗinka shi da jakarsa da takalmi da komai, an haɗo mata kayan fitar biki, ga kuma invitations, rumaisa ta yi ta kallon invitation ɗin tana mamakin wai sunanta ne a jiki.

Ledar nan da ya bata kuwa, babbar envelope ce a ciki wata dubu ɗari biyar ɗin ce a ciki.

Mama ta kalleta ta ce "Rumaisa tambayarsa ki ka yi?"

"Haba mama, to ni ce masa ma na yi, idan ya san zai yi mini gori wataran, ya ɗauki kayansa, ni za a sai mini a gida".
Gwaggo ta yi salati ta ce "Shi mijin naki ki ka gayawa hakan?"

Rumaisa ta ce "Mijina kuma taɓ".

Usman ya ce "Ke fa banza ce, yanzu ya kawo miki wannan uban kayan ki kasa yi masa godiya, saboda ke dai baki da alƙibla?"

Ta yi shiru tana muzurai. "Bari Aliyu ya dawo, ya kira shi a waya, ki yi masa godiya tun da ba ke ki ka nema masa kuɗin ba"

Haɗe rai ta yi, saboda zuwa yanzu yaya usy yana takura mata a kan mutumin fiye da kima.

Can kuma ta hau murna, tana lissafin ƙawayenta da zata bawa ankon da zasu ɗinka, ga uban kuɗi kuma tana gani.

Mama dai shiru tayi tana bin kayan da kuɗin da kallo, ita ba tarin kayan alatun ba, fatan ta Allah ya sa rumaisa ta shiga a sa'a ya sanya mata albarka.

***
Bin invitations ɗin yake da kallo, yana tuna lokacin da yayi auren fari, tun saura wata guda biki ya fara ɗoki, yana murna yana rabon invitation card, a wannan karon da shi da amaryar bai san wanda ya fi wani anti serious ba.
Rumaisa Mahmud, ya din ga kallon sunan nata, da kuma nasa Adam Sharif Galadima.

Bashir ne yayi sallama a falon, Adam ya amsa masa, ya ƙarasa suka gaisa sannan ya zauna ya kalli Adam ya ce "An kammala komai na gidan, zasu iya kai kaya a kowane lokaci".

Adam ya ce "Masha Allah, that's good ina godiya sosai, ina sidi?"

"Na ajiye shi, shima ya sha aiki ya gaji"

"Na gode sosai bashir, zan shiga na je na gani, daga nan sai na ɗauki ko mutum biyu a yayyenta, mu je su ga gidan".

Bashir ya ce "Hakan yayi, Allah ya sanya albarka, amma haryanzu fa ba ka fara rabon invitation ba, ko a social media ba a saka ba".

Adam ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Wallahi Bashir sam bana ɗokin auren nan, bana son duniya ma ta san zan yi shi, ni da za a shafa fatiha ma ba wannan events ɗin da na so hakan, rainon yarinya kawai za a kawo mini"

Bashir ya yi murmushi ya ce "Ka yi haƙuri, ammi ba zata zaɓa maka abun da zai cutar da kai ba. Sannan ba zai yiwu ka ɓoyewa duniya zaka yi aure ba, idan ta fasu aka sani, za a iya yi maka wani sharrin"

"Haka ne, haka zalika idan aka ga Yarinyar da zan aura, shi ma ba zan tsira ba, mussaman idan aka san ita ta zo da ɗa na daga hannun ƴan bindiga".

Bashir ya ce "Mafita ɗaya ce, duk yadda zaka yi ka ɓoye wa duniya cewar ba son auren ka ke yi ba, dole a ga farinciki da ɗoki a fuskarka".

Adam ya yi murmushi ya ce "Yadda za a ji daɗin cewa, saboda na auri yarinya ƙarama na kashe matata ko?"

"Ai dama dole sai an faɗi wani abu, amma yafi ace ka yi amfani da ƙaramar yarinya ka ɓoye wa duniya laifinka, na kai kashe matarka, ka turasasata ta aureka, dan kar a cigaba da surutu da zargin ya za ayi yarinya ƙarama kamarta ta kuɓuta da jariri a hannun 'yan bindiga"

Adam ya yi ajiyar zuciya, ya ɗan murza goshinsa ya ce "Duniya gidan rikici, Allah ya iya mana".

"Amin ya Allah"

Wayar takawa ce ta fara ringing, ya ɗauka ya duba ya ga sunan Aliyu.

Ya ɗaga ya saka a kunnensa tare da yin sallama, Aliyu ya amsa ya ce "Barka da wannan lokaci, ya hidima?".

"Alhamdilillah, ya taku hidimar?"

"Mun gode Allah, dama rumaisa ce za ta yi magana da kai"

Adam ya ce "Ok, ba ta".

Rumaisa ta karɓi wayar, Usman ya sakata a gaba ya tsareta da ido.

Ta karɓi wayar ta saka a kunneta, amma ta tsaya tana kallon Usman, ta kasa magana.

Ya daki ƙafarta ya ce "Ba zaki gaishe shi ba?"

"Ina wuni?"

Maimakon ya amsa ya ce "Ya aka yi?"

"Gaisheka fa na yi" ta yi maganar a ƙule.

"Ba a yi wa basarake irin wannan gaisuwar, babu ladabi a gaisuwarki, dan haka ko sau nawa zaki yi ba zan amsa ba, riƙe kayarki, ina jin ki"

Rumaisa ji ta yi kamar ta yi zagi, meye aibun gaisuwar ta, idan ba neman bala'i ba.

"Idan kin shirya yin magana, sai ki sake kirana".

"Su yaya ne suka ce dole sai na kiraka na yi maka godiya, na gode, kuma wai kuɗin da ka bani sun yi yawa, sannan......"

"Lokacin da ki ka san abu yakamata, ba sai wani ya saka ki ba, sai ki neme ni, yayyenki na ƙoƙari wurin baki tarbiyya, Allah ya biya su, kuɗi kuma ki zubar" ya kashe wayarsa.

Dungurar da wayar ta yi a ƙufule, ta ce "Yaya usy kalli abun da ka janyo mini"

Dungure mata kai yayi ya ce "Ki ka jawa kanki dai, ke a rayuwar duniya baki iya siyasa ba? Ji yadda ki ke gantsara masa magana, kamar kashi ba tausasa lafazi, ba ɗan karya murya, wai ke ma namiji ce irinmu ne? to ko mu muna kashe murya, ranar da na kama malam habu yana waya, kamar ma nutse dan kunya, amma ke kina ta wani shirme.
Ke, tashi mu je ɗaki, na yi miki bayanin me auren ya ƙunsa, in fayyace miki komai in gaya miki, na ga mama ba ta da niyyar gaya miki, daga ita har su gwaggon.

Aliyu ya ce "Kai fa wasu lokutan baka da kamun kai, uban me zaka gaya mata?".

"Komai ma gaya mata zan yi, yo haka za ta je ta zauna masa a gida kamar gardi, idan ka ga tana tausa murya to wani abun take nema, tashi mu je na fayyace biri har wutsiya".

Aliyu da dariya ta ƙwace masa ya ce "Mama, wallahi usman ya zama abun da ya zama, zai juyawa yarinya tunani, saboda bashi da kamun kai".

Usman ya ce "Eh, bani da kamun kan, ni ina ma ni za ayi wa auren nan, wai muna zaune ƴar da aka haifa a gabanmu za ta rigamu girma Allahu Akbar wata shekarar sai ta fara ƴa ƴa kuma".

Aliyu ya ce "Wani irin ta fara ƴaƴa wata shekarar, kamar wata bishiyar lemo, wannan yarinyar ko nan da shekara biyar albarka"

Wani irin kallo Usman ya yi masa ya ce "Haba, a banza za ku kaita ya din ga bata abinci, yana biya mata kuɗin makaranta ko? You don't get sense. Ko kaza dan a cinyeta ake killace ta a  sai mata dusa, kar ka yaudari kan ka".

Aliyu ya ce "kai haba, she's too young for it, and the man is very decent and calm, bana tunanin haka".

Usman ya yi dariya ya ce "Uban calm da decent ɗin, that thing don't get sense, don't fool yourself, if not ku fasa aurar da ita, hauka ake mutum zai kashe kuɗi ya auri ƴa ya sakata a gaba yana kallonta, Allah ya sa jaririya ce"

Aliyu ya yi tsaki ya ce "Zaka ɓata mini rai "
Rumaisa da ba gane kan hirar take ba, ta din ga bin su da kallo, Usman ya ce  "To Algume, sai kallon bakinmu ki ke, ƙila kin san komai, ki ka yi wani kasaƙe da kai".

Aliyu ya ce "A hakan ta san komai? Tana wannan gidadancin".

Usman ya ce "Kuma fa haka ne, to jeki na fasa gaya miki komai, duniya zata gaya miki, Allah ya shiryeki".

"Nuraini, Allah ya baka abun yi na aurara da kai, ina ga daga rumaisa kuma sai kai, tun baka wuce in da nake tunani ba" a guje Usman ya faɗa ɗakinsu, dan sam bai san mama ta ji hirarsu ba.

***
Jabir ya din ga juya invitation ɗin, sannan ya kalli Adam ya ce " da gaske Adam saura kwanaki a ɗaura maka aure, amma ban sani ba?"

"Am sorry, abun ne ya zo cikin gahgawar gaske fiye da yadda na yi zato, sai haƙuri".

Jabir ya sake kallon invitation ɗin, sannan ya ce "To ita kuma wacece, a ina take? Kamar na san sunan nan".

Adam ya ce "Zaka ganta very soon".

"Da jamil ya gaya mini maganar auren nan, na zaci da wasa yake yi, ashe da gaske ne, Allah sarki samha ina tausayin yarinyar nan sosai".

Adam ya ce "Please, don't raise that issue here, ku daina ganin laifina, ƙaddara ce ta zo a haka".

Jabir ya ce "Na yadda, ban ce wani abu ba, kawai dai ina jin tausayinta ne, sai dai na yi mamakin yadda har ka nemi aure, har ka samu ban sani ba, yaushe muka fara haka da kai".

"Jabir, this is an arranged marriage, ku yi mini uzuri".

Jabir ya ce "Arranged marriage, to Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu".

"Amin, addu'arku nake buƙata dama, yanzu ka tashi mu je gidan mai girma turaki, zan kai masa nasa katin, da zai bawa mutanensa, da na jamil da gidan gaba ɗaya".

Jabir ya ce "Ok, ba damuwa bari mu yi salla tukuna"

Bayan sun idar da salla, suka tafi gidan turaki, kai tsaye sashinsa suka shiga, bayan sun tarar da babu kowa a falon.

Yayi murna sosai yayi addu'a da fatan alkhairi, sannan ya yi wa adam nasiha sosai mai shiga jiki. Sai dai kamar haɗin baki suka tarar da mama da Samha, har ma da zainab a falo.
Samha jikinta har tsuma yake da ta ga Adam, ga soyayya ga kuma kishi, ya gaida mama ta amsa masa sama-sama, ta saki jiki ta amsa gaisuwar Jabir.

Su Samha suka gaishe shi ya amsa, ya ajiye wa mama katuna, ya ce "Gashi nan, ammi ce ta ce in kawo miki, na taron wunin da za ta yi, na bawa mai girma turaki nasa".

Da ƙarfi Samha ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login