Showing 168001 words to 171000 words out of 199108 words

Chapter 57 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

817

yadda take jin zuciyarta tamkar tana ci da wuta, saboda ɓacin rai.

Adam bai ga rumaisa ba sai bayan sallar magariba, ya faɗo ɗakin unexpectedly ya tarar da ita a zaune tamkar zata fashe, gashin nan ya sha gyara, ya kwanta sai ƙyallin mai yake yi. Gashi ta wani ƙara fresh, dan gyaran jiki suke sha tare, an yi mata lalle kamar ita ce amaryar, ɗakin kansa sai ƙamshin turare yake yi.

Cikin sanyin jiki ya ƙarasa, ya ce "Mimi dan Allah ki saurareni, i will explain to you"

"To hell with your explanations, bana son ji" ta yinƙura za ta tashi, ya sha gabanta.

"Rumaisa kin fi kowa sanin ni ba mutumin banza bane ba, wallahi bani na gayyato Samha gidan nan ba, kawai ganinta nayi unexpected".

"Dama na ce kai ka gayyato ta, idan ma gayyato tan kayi ina ruwana? Dan Allah ka rabu da ni, bana son jin duk wani bayani naka"

"Kiyi haƙuri dan Allah"

"Ai ni baka yi mini komai ba, ƙarewa saura tayi tsirara ka kalleta, shi ma duk cikin kuskure ne" Duk yadda ya so ta tsaya ta fahimta ta ƙi, tayi mursisi ta din ga yi masa rashin mutunci.

Tun da ake faɗar fitsararta, bata taɓa gwada masa tijara muraran ba kamar yau, sam tayi burus taƙi fahimtar sa.
Ƙarewa ma, yana fita ta kulle ƙofarta.

Gaba ɗaya Adam ya rikice, ya rasa abun da yake yi masa daɗi, rarrashin duniyar nan, ruma tayi burus da shi, da sassafe ta fita ta tafi gidan ammi, aka cigaba da shirin biki, tamkar babu abun da ya faru.
Rashin ganinta a gidan bayan ya tashi, ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, ya fara zuwa gidansu, amma ya tarar da ita tamkar ba abun da ya faru, tana ta hidimominta, ƴan uwan su ammi na gombe, duk sun hallara. Daga nan gida tayi tafiyarta gidansu, nan ma gida ya cika mutanen katsina duk sun hallara.

Ana ta shirin biki, da daddare su habiba suka zo ita da mamanta, idan da aikin da za a kamawa su mama, ga su Hauwwaliya, ai tuni ruma ta manta da damuwarta, ta shiga cikinsu suka cigaba da taɓararsu.

Aliyu tun da yaga Habiba yake shiga yana fita.

Ruma ta ce "Habiba baki da mutunci fa, ki ke soyayya da yaya Aliyu ba labari, kuma ko gaisheni ba kya zuwa yi"

Habiba ta ce "Sannu mama" suka tuntsire da dariya.

Habiba ta ce "Kamar in janyo lokacin candy rumaisa, ina ƙaunar Yaya Aliyu kamar me, Ruma aure da daɗi dan Allah?"

Hauwwaliya ta ce "Eh ɗan gaya mana"

Ruma ta ce "Eh to, ba nace babu ba, bana ce akwai ba, idan kun je kwa gani, idan ku ka yi sa'a ku ka auri irin mijina, to kun dace, ni da mijina bani da matsala, sai danginsa 'yan bala'i. Ku san kowa da kalar jarrabwarsa a gidan aure".

Hauwwaliya ta ce "To, Allah ya sassauta mana"

Suka amsa da Amin.

Da Adam ya koma gida, aka ce masa ruma ta tafi gidansu, dan haka ya tafi yana fatan Allah ya sa ba ta faɗi wani abun ba.

Wayar mama ya kira, suka gaisa ya ce mata rumaisa ta zo, zasu tafi.

Ba ta son tayi musu ko wani abu da zai sanya, a gane saɓani suka samu, dan laila ta gargaɗeta sosai a kan haka, ta ce mata duk wata matsala, in dai za su iya warwarewa a tsakanin su, kar ta bari wani ya ji, balle ya shiga. Galibin aure yana samun matsa a dalilin sako mutum na uku a cikin matsalolin auren.

Bayan motar ta buɗe ta shiga, ko kallonsa ba ta yi ba.

Har suka je gida ba ta kula shi ba, shi ma kuma bai iya ce mata komai ba, duk da ƙasan zuciyarta har ta fara jin tausayinsa, dan a kiɗime yake sosai da sosai.

Da suka je gida ma, a buɗe ta bar masa motarsa ta yi shigewarta cikin gida.

Ko tayi niyyar daina fushin, da ta tuna yadda ta ga Samha a tsaye a gaban sa, ta turo ƙirji sai wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta.

Wanka tayi, ta je kitchen ta damo kununta, ta koma ɗaki tana sha. Ita kanta missing ɗin sa take yi sosai da sosai, saboda sun yi wani irin sabo sosai da sosai.

Kamar mara gaskiya haka yayi sallama a ɗakin, ta amsa masa ƙasa-ƙasa.

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Rumaisa".

"Na'am" ta amsa a daƙile.

"Yanzu kina tunanin zan iya aikata abun da bai kamata ba kenan? Yakamata ki fahimce ni, ya ci ace kin san halina, wallahi rumaisa babu wani abu da ya faru, abun da ki ka gani ma is not intentionally ban san me ma zan ce miki ki yarda da ni ba. Amma dan Allah kar ki kawo komai a ranki".

"Amma fa tsayawa ka yi kana kallonta, fisabilillahi".

"Rumaisa a rayuwata bana tunanin akwai wanda na taɓa bi ina bawa haƙuri, kamar yadda nake binki a yanzu, dan Allah ki yi haƙuri, ko sai na durƙusa ɗin a kan gwiwoyina?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki dube ni mana, kiyi haƙuri Please" yayi maganar yana riƙe hannunta cikin nasa.

"Na haƙura amma dan Allah kar ka sake kulata, wallahi ji na yi kamar na je kitchen na samo taɓarya na zo na rotse mata kai. Kawai ta wani tsaya ta gantsare a gabanka, wallahi na ji haushi"

Ya ce "Subhanallah, duk ba ta kai ga haka ba, nima ban ji daɗi ba amma ki yadda da ni, ai ni namu sun isheni, me zan kalla a na wata"

"Abun da bai fi murfin jarkar faron ba?"

Yayi murmushi ya ce "Har laifukana na baya za'a tayar kenan?".

"Eh ɗin, ka je ka kalli naka ko na Samha"

Yayi murmushi ya ce "Allah dai ya bada haƙuri"

Ta amsa da "Amin"

Ya rungumeta ya ce "I so much miss you, smile please"

Ta lashe cokalin hannunta ta ce "ba zan iya ba yanzu, idan na ce zan yi murmushi yanzu, yaƙe kawai zan yi. Ka ci abinci kuwa?"

"A ina zan ci, tun da baki bani ba?"

Ta ce "To mu je na sama maka abun da zaka ci"

"Yauwwa my dear, ana so na ana kaiwa kasuwa, an damu da ni amma ana ta wahalar da ni"

Ta kalleshi ta ce "Ka ke dai so na"

Ya ce "Na yadda".

Ta ce "To amma sai dai ka goya ni, ka kai ni kitchen ɗin"

Ya durƙusa ya ce "Zo ki hau"

Aikuwa ta miƙe ta hau bayansa tana dariya, ya goyata a bayansa, har kitchen.

A ranar dai suka shirya, rumaisa tayi iyakar ƙoƙarin ta wurin bin shawarar da anty laila ta bata, na cewa idan har namji zai iya yi miki laifi ya baki haƙuri, to ba ƙaramin kimarki yake gani ba, ba kowann namiji ne zai yi ba dai-dai ba ya nemi afuwarki, sai ma yayi ƙoƙarin nemo wani laifin ya jingina miki, duk dan kar ya nemi afuwarki.

Sosai aka shiga hidimar biki, ka'in da na'in, mai sunan baba kai ya ɗau caji sosai da sosai, abunka da wanda bai saba da hayaniya ba, nan da nan sai ciwon kai.

Gidan marigayi galadima Sharif ma, ya cika ya tumbatsa, mutane sai kaiwa suke suna komowa.

Mummy kuwa ba gaira ba dalili take tsinewa auren, tare da mummunan baki a kan haka.

Rumaisa kuwa ba ta a nan bata a can, takawa sai mita yake a kan ta nemi wuri ta din ga hutawa, kar sai an kammala biki, ta zo tana ciwon jiki.

Ranar da aka yi dinner rumaisa tayi kyau, haka amarya Iman da mai sunan baba, shi gaba ɗaya ma kunya yake ji, ko ɗaga kai baya son yi ya kalli taron jama'ar nan.
Yazo wurin nan ne kawai saboda iman ta matsa. Kamar da bikin rumaisa a wannan karon ma, kaiwa da komowa zaratan samarin gidan maman suka din ga yi, sanye da kaya iri ɗaya a jikinsu gwanin sha'awa ango ba shi da wasu abokai, sai classmates sai ƙannensa.

Ƙawayen ammi sun yi mata kara sosai da sosai, suka din ga liƙi suna kaiwa da komowa, duk wanda ya ga couples ɗin sai ya ce masha Allah, saboda kyau ne ya haɗu da kyau, duk da bai kai iman haske ba, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka ce kyakkyawa ne.

Bayan an kammala dinner suka taso, Mahmud ne ya ɗaukko su a motarsa, Iman sai hamma take yi, saboda ta gaji.

"Kin gaji ne?" Ya tambaye ta lokacin da ta kashingiɗa da seat ɗin motar.

"Eh yaya umar, ko ina ciwo yake mini"

Yayi murmushi ya ce "To sannu, idan kin je gida ki kwanta ki huta sosai"

Ta ce "To ango"

Yayi murmushi, suka fara kaita gida, sannan suka wuce Mahmud ya kai mai sunan baba gida.

Washegari aka ɗaura aure, turaki ne yayi wa Iman waliycci. Aka ɗaura auren Umar Mahmud da Khadija Muhammad Galadima.

Ayshercool
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*




Mai sunan baba jin sa yake yi tamkar ba shi ba, wai yau shi ne yayi aure, abun da bai taɓa kawowa nan kusa cikin lissafin rayuwarsa ba.
Ya san iya karamci, an yi masa wurin bashi iman, sai addu'a yake yi, da fatan Allah ya bashi ikon riƙe amana.

Ƴan unguwarsu suka din ga gulma, daga rumaisa ta auri basarake, sun liƙe sun nace musu, saboda tsabar kwaɗayi da son abun duniya. sun ga bushashar da aka yi, da irin manyan mutane da suka halarci taron ɗaurin auren Umar.

Yayin da ƴan uwa da abokan arziki, ke ta yi wa mama barka, da cewar gidan sarauta sun ji daɗin auren ruma, shiyasa suka bawa mai sunan baba ƴa.

Iman ta rasa wanne za ta yi tsakanin farinciki da akasin sa, bayan duk turka-turakar, faɗi tashi da ƙalubalen, yau Allah ya yanke mata, sai dai akwai tsananin soyayya da shaƙuwa tsakaninta a amminta da su nusaiba da rabuwa da su take jin wani babban giɓi ne a tare da ita.

Manyan mutane ne suka hallaci bikin shaida auren, har da sarakunan maƙwabta, da manyan mutane masu faɗa aji.

Gaba ɗaya jikin Iman yayi sanyi, tana tunanin sabuwar rayuwar da za ta shiga, ko da wane kalar ƙalubale za ta zo mata sanin gaibu sai Allah.

Jin an ɗaura wa Iman aure kuwa, Jabir kamar ya haukace, saboda ya tabattar da ya riga ya gama rasata.

Ƙarfe takwas na dare, anty laila ta shirya Iman cikin lafaya, aka ɗora mata alkyabba, maroƙa sun cika sashin ammi, suna ta faman koɗa ammi.

Iman ta riƙe ammi tana ta uban kuka.

Duk yadda ammi taso ta daure ta kasa, ta din ga kukan ita ma.

Mai sunan baba kuwa shi ma kamar mace, Abubakar sai masifa yake masa ya shirya, azo a raka shi mutane su huta.

Bayan yayi wanka ya shirya, jiki a sanyaye ya shiga wurin mama, ya durƙusa a gabanta, ji yake kamar ya ce ya fasa, har ga Allah bayan Allah da ma'aikinsa yana ƙaunar mahaifiyarsa matuƙa.

Mama tayi murmushin ta cire hular kansa, ta shafa sumar kansa ta ce "Allah ya yi maka albarka, Allah ya albarkaci rayuwar aurenka, ya sanya ta zame maka sanyin idaniya. Na sanka babana amma zan sake jaddadawa a kula da amana, a kula da marainiya, ba a yi wa mace muzurai, mace uwa ce, abokiyar shawara ce. A kula mini da ita. Yadda ka tallafi rayuwar ƴan uwanka ka kula da su, Allah ya baka masu yi maka, mun gode mun gode Allah ya saka maka da alkhairi babana, Allah ya kula mana da ku Allah ya yi maka albarka"

Ya sanya hannu ya kama hannun mama a cikin nasa, amma ya kasa magana, zuciyarsa ta kai matuƙa wurin yin rauni, yayi shiru ya sunkuyar da kai.

Su hajiya Iya kuwa sai rafka guɗa suke yi, Gwaggo sai masifa take tana neman rumaisa, aka ce mata ai direbanta ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita can gidansu mijinta.

Gwaggo ta cigaba da masifa "Rumaisa ba zata nemi wuri ta nutsu ta zauna ba, wannan kyan da take yi da sheƙi, da ƙyar idan ba ciki ne da ita ba, a garin wannan rawar kan sai ta zubar da shi tukuna, nayi magana ta ce ita ba ta da ciki, manya ne suke haihuwa, wai ita kunun gaya take sha ko na sabulu? Ita dai ta sani"

Hauwwaliya ta ce "Gwaggo kunun sabaya ta ce miki bana sabulu ba, ta ce ni ma zata bani na din ga sha. Ni yanzu jira nake ta ce za ta saka azo a ɗauke mu a tafi da mu gidan amarya".
"Oho muku dai, daga ke har ita".

Abubakar ne ya zo ya janye mai sunan baba suka fito, a mota ya kalli yadda umar ɗin yayi jugumm ya ce "Wai kuka zaka yi ne?" Yayi maganar yana dariya.

Mai sunan baba yayi masa shiru.

"Ango mai kuka, duk na gulma ne, da an ga Khadija za a ware, inyeee ango na mama". Ya din ga tsokanarsa, yayi shiru ya ƙi kula shi.

Takawa da kansa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login