Showing 123001 words to 126000 words out of 199108 words

Chapter 42 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

829

ta, za ta fita, ta ganta a damuwa, ta dawo ta ganta cikin annashuwa, ba tare da ta san menene ya sanya ta cikin farin cikin ba.

Sai da ta je kwanciya sannan ta janyo wayarta, ta shiga what's app, cikin fargaba ta turawa mai sunan baba saƙo "Yaya umar ya ka je gida?"

Kallon message ɗin ya din ga yi, yana shafa kan message ɗin amma yaƙi reply.

Kusan mintuna talatin, tana ganinsa online, amma bai reply ba.

Tunani tayi meyasa ma ta tura saƙon, sai ta yi sauri ta goge.

Ta na gogewa ya yi replying da 'Me ki ka goge?'

"Bakomai" ta bashi amsa.

"Send it again"

Tsuru-tsuru tayi kamar tana gabansa, sannan ta sake rubuta masa ya ka je gida.

"Wayata yakamata ki kira, idan kin damu ki ji ya na je"

Ta yi masa replying da "Yi haƙuri"

"Kin yi laifi ne ki ke bayar da haƙuri?"

"A'a na ga kamar ka ji haushi ne"

"Ba haka nake ba, masifaffe kamar yadda waccan yarinyar take baki labari ba".

Iman ta ce "Eyya ba haka ta ce mini ba wallahi"

"Umar ba masifafe bane, na dawo lafiya ƙalau, na gode sosai" tashi zaune iman ta yi tana yarfe hannu cikin murna.

Offline mai sunan baba shi ma yayi, ya na murmushin da bai san dalilinsa ba.

Yau juma'a akwai makaranta, amma ruma ta ƙi shiryawa, ta sha baccinta.

Takawa ma bai takura mata ba, bai ce sai ta je ba.

Sai sha ƙarfe goma na safe, sannan runaisa ta fito, ta shiga kitchen ta haɗa abinci ta dawo falo ta zauna.

Ta zauna ba jimawa, sai ga shi ya shigo, ashe ma ba ya gidan ba ta sani ba.

Ta wani sake tsuke fuska, ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Ba gaisuwa yau?" Ta matsa daga kusa da shi. Ya sake matsawa ya ce "Mun yi faɗa ne?".

"Gaskiya papa bana so, Allah ka taɓa ni sai na yi ihu da ƙarfi"

"Me zan taɓa?" Yayi maganar yana kallon ta.

"Oho ai ka san me kayi mini".

"Ba wannan ba, tun da yau kin ƙi zuwa makaranta, zan je na ɗan yi bacci ne, an jima zaki tayani haɗa kaya, gobe in Allah ya kaimu zan tafi"

Da sauri ta ce "Haba dai?"

"Ba kya so na tafi ne? Ai gara na tafi, na je na yi aure, tun da ihu ki ke yi mini. And turaki ya ce mini Mummy ta samu mai girma wambai ya ce magana ta wuce, Weldon little Mimi, aikinki yayi kyau"

Kallo ta bi shi da shi, har ya shiga ɗakinsa.

Ta kalmashe ta kunna Tv, tana kallo, ta ji sallamar wata mata, wani irin ƙamshi ya daki hancinta.

Ta ɗaga kai ta kalli matar, matar fara sol kamar ka taɓa jini ya fito, wata ƴat gayu, ta sha baƙin glass, da English wears.

Ta nemi wuri ta zauna, ta kalli rumaisa ta ce "Hey, ina mutanen gidan?"

Rumaisa ta kalleta, tare da jinjina rainin wayo irin na matar,  ta ce "Mutan gida kamar wa kenan?".

Matar ta ce "Matar gidan, da kuma takawa"

Cikin rainin hankali ruma ta ce "Matar gida ni ce, takawa kuma is not available"


Ayshercool.
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏


Matar da mamaki take kallon ruma, "I don't get you, he is not available like how?".

Maimakon rumaisa ta amsa, sai ta sake kashingiɗa ta ce "Elizabeth ma ta ci ubanta, haka ta gama turancin ta mutu".

Cikin isa matar ta cire gilashin fuskarta ta ce "Kin san wacece ni kuwa?".

"Ina ruwana da ke wacece? Ko da ban san ki ba, na san ba zai wuce kema a danginsu ki ke ba, masu zuwa su ci mini mutunci, ni kuwa dai-dai nake da kowa, wallahi duk wanda ya zageni ramawa zan yi ehe".

"To yanzu zagin ki na yi?"

"Ai na san tatsuniyar gizo, ba ta wuce ƙoƙi, kun saba zuwa ku yi mini wulaƙanci, na sani ko kema abun da ya kawo ki kenan, daga shigowarki sai kallon banza ki ke yi mini, kuma dan raini ki ke tambayata wai ina matar gidan. To ban sani ba ko nayi kama da ƴar shara da wanke-wanke"

Matar ta riƙe haɓa, sannan ta jinjina kai ta ce "Anyway, na ji kece matar gida, kuma ban zo na ci mutuncin ki ba, i want see ma brother please"

Rumaisa ta ce "Ban iya turanci ba"

"Ohh ikon Allah, ina son zan ga ɗan uwana ne, wurinsa na zo".

"To bacci yake yi, idan zaki jira shi to, bai daɗe da kwanciya ba, amma ina fatan ke ba ƴar uwar wannan samhan ba ce ba?"

Matar ta yi murmushi ta ce "No, am not" ta saka hannu a jakarta, ta ciro waya, cikin harshen Ingilishi take magana, da accent ɗin da rumaisa ba ta iya fahimta, ta ajiye wayar.

Bai fi mintuna takwas ba, sai ga takawa ya fito.

Da sauri matar ta miƙe, ta nufe shi, kamar zasu rungume juna, suka yi musabaha, ta sumbaci hannunsa ta ce "Takawarka lafiya ranka ya daɗe, gaba salamun baya salamun"

Adam yayi murmushi ya ce "Ke dan Allah yaushe ki ka sauka? Kuma da safen nan na je gidan mai girma turaki, na ji kasala nake ji, ban ƙarasa gidan ba, kuma jiya fa har 5pm muna gidan.

"Around 11 na ne gida, na cewa ammi kar ta gaya maka, yau na ce ammi ta saka a kawoni, na zo na ganka na ga amarya, and i met this little arrogant creature, screaming at me that why should I ask for you. She even claims that she's your wife, but i doubt  she is the one in the pictures. She looks innocent and matured in picture".

Takawa yayi dariya ya ce "She's the one, rumaisa kenan maman sabir".

Jiki a sanyaye ta ce "Adam, na ga yaron fulani, so cute, yaron kyakykyawa da shi".

Rumaisa da ba ta kula su ba, ta ce "Tubarkallah".

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ruma ya ce "Mimi, ga Anty Laila, cousin sister ɗina, da muka tashi tare, kuma uwar ɗakina. Tana aure a canada da mijinta da yaranta".

"Au ai ban santa ba, kuma da ta zo ba ta gaya mini ita ce ba, na zata kawai ƴan uwanku ne masu zuwa gida, su yi mini wulaƙanci, shiyasa ban kulata ba".

"To ai ba duka ƴan uwan mu ne, masu yi miki wulaƙancin ba, ku gaisa mana".

"To ita kuma ya ake gaisheta, kar in yi ba dai-dai ba ta ƙi amsawa, ba zan sake gaisheta ba"

Yayi murmushi ya ce "Ita wannan baturiya ce ai, kowace irin gaisuwa ki ka yi mata zata amsa".

Rumaia ta sake kallon laila sannan ta yi murmushi ta ce "Sannu da zuwa, ina wuni? Ya hanya ya iyali, sannu da zuwa"

Ta ce "Yauwwa thank you"

Ta tashi tsaye ta je ta kawowa laila ruwa da lemo, ta kawo mata kayan shayi ta ajiye, ta haɗo da cornflakes duk ta ajiye mata.

Laila ta ce "Ya zan yi da duk wannan kayan, kar ki takura kanki, na ƙoshi ni".

"A'a kar ki je ki ce, kin zo gidana ba a baki abinci ba. Na san lokacin breakfast ya wuce, amma dai ki sha shayi, ko cornflakes, akwai fruit ma, yanzu zan je na ɗora girki".

Laila ta ce "Girki kuma? Ba naga akwai maids ba, na ga baba uwani ma na nan, kar ki ciwo a kitchen fa".

Rumaisa ta ce "Ai da yake a unguwar ɗorayi nake, na iya duk wani girki da yakamata, ni ba ƴar masu kuɗi ba ce, kar ki damu da yarinta ta, na iya abinci gidanmu ba ƴar aiki".

Adam ya ƙunshe fuska yana dariya, rumaisa kuma ta nufi kitchen, tayi ƙasa da murya ta ce "Yenyenyen, ta wani shaƙe murya tana turanci, har da saka wando, babba da ita wai ita baturiya, Elizabeth ma ta gama saka wandon da mini skirt, aka haɗa da ita da turancin aka binneta".

Laila kuwa ruma na barin falon ta ce "Bros yanzu da gaske this is your wife?"

"Yeah, ta canza miki ne, ita ce dai ki ka gani a hoto".

Laila ta ce "Taɓɗijan, amma ba ta da kunya, a tsaye take, amma tayi ƙarama takawa".

"Haba dai, yanzu ai ta ciko, ta yi ƙiba, rigima kam akwai ta har da ta sayarwa ma, sai dai duk da haka bamu fi wata ɗaya ba, na fara jin daɗin zama da ita. She's very intelligent, fiye da yadda ki ke zato, wauta da ƙuruciya ne dai damuwarta".

Nan ya bata labarin yadda rumaisa ta dawo da sabir, da yadda aka yi har ya aure ta, zuwa yanzu da suke tare, da abubuwan da take ta hasaka masa, a zamansu.

Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Well, amma ba ta da kunya gaskiya, a haka ku ke zaune?".

Ya ce "Ya ki ke zagar mini mata ne, zaki shiga sahun Black list ɗin mu fa".

"Am serious matarka ba ta da kunya takawa"

Sai ya tuna abun da ya faru jiya, ya ce "Kin san family ɗin mu sai a hankali, gida suka zo suke yi mata rashin mutunci, ta rama. Kin san ƙanwar maza ce ba tsoro. Haka nan muke lallaɓawa muke tare, ake rainonta kan Allah ya sa ta gama hankali, ko me za ta yi, ta cancanci ayi mata uzuri, kuma in kula da ita, abun da ta yi mini, ko duniya na bata ban biyata ba"

"Haka ne, amma ban gane ake lallaɓawa ake rainonta ba, haka ku ke zaune kana kallonta tana kallonka"

Yayi dariya ya ce "Ina ruwanki ne?"

"Babu, amma tun a hotonta nayi mamakin yadda ka auri ƙaramar yarinya haka, na sam baka da ra'ayin auren ƙaramar yarinya, na san plan ɗin ammi ne, ban da haka wannan guda nawa take? Me ta sani?"

"Ai fa, in dai ɓangaren zamantakewar aure ne, ba ta san komai ba, sai kaifin basirar sanya ido da gane mara gaskiya, shiyasa na yi mata registration na islamiyya matan aure, ta ce dai ba zata ba, ita yara zan sakata, ba zata shiga cikin matan aure su rainata ba, wannan kuma da ammi zan bar ta, dan sun fi kusa"

Laila ta ce "Well, tun da ba tare zaku tafi ba, ka bar ta a hannuna, zaka ga canjin kafin ka dawo in sha Allah".

Ya dubi laila ya ce "Like how kenan?".

"Kai ina ruwanka, tun da tafiya zaka yi, ta zo mu zauna a gidan ammi tare, she needs to learn so many things, ko kuma you are taking another wife ne, wannan tayi ƙwaila da yawa".

"Allah ya sa ta ji ki na ce mata ƙwaila, zaku yi faɗa da ita sosai, nikaɗai ne idan na faɗa take ƙyaleni, ni ɗin ma sai da tayi mini abun da na daɗe ina jin kunyar kallon ammi, ta gaya mata wai na ce zan ƙara aure saboda bata da nono"

Rufe baki laila ta yi tana dariya, ta ce "Lallai wannan yarinyar ɗanya ce sharaf, ka bar ta a hannuna kawai".

Hira suka cigaba da yi, ya din ga bata labarin abubuwan da suka din ga faruwa, tun bayan komwarta canada daga hutun ƙarshe da ta zo.

Laila ta sha mamakin ganin yadda rumaisa ta kawo mata abinci da ta girka, komai nata tsaf, hatta falonta a gyare yake, dan har ƙamshin turaren wuta yake, a tunaninta ko masu aiki ne suka yi mata, sai da adam ya ce mata ita take abun ta.

"Mimi ina nawa abincin?" Adam yayi maganar yana kallon ta.

"Au, dama zaka ci? Ya ƙare saura ƙanzo, ko in dafa maka taliya da manja da yaji"

Yayi murmushi ya ce "zan kama ki ne, da ke da taliyar.

Rumaisa ta koma ɗakinta, ta bar musu falon, wanka ta yi, ta fito da nufin ta shirya, ta ga takawa a ɗakin nata. Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Ya na ganka kuma, ina baƙuwar?".

"Haka ake yi, kin yi baƙuwa kin tafi kin bar ta?".

"To ba wurinka ta zo ba, ko zuwa zan yi na saka ku a gaba ina kallon bakin ku?".

"To, yanzu dai ba wannan ba, dan ta tafi ma, taho mu yi magana".

Rumaisa ta ce "Taɓ, kaya zan saka, ka je idan na kammala shiryawa, zan zo"

Ya janyo hannunta ya zaunar da ita a kan gadon, ya ce "Yanzu zamu yi, baki da isasshen lokacin cigaba da ganina. Idan na tafi gida zaki koma wurin ammi, zuwa lokacin da zan dawo, lokaci-lokaci kuma, zaki iya zuwa gida, shima sai kin nemi iznina tukuna"

Jiki a sanyaye ta ce "To meyasa ba zan koma gidanmu ba, ni fa ba zaman gidanku ne bana so ba, wannan ƴan rainin hankalin ƴan uwan naka ne ba zan juri wulaƙancinsu ba"

"Rumaisa kin iya cewa bani da haƙuri, ke haƙurin ne da ke? Babu ruwanki da su, gobe in Allah ya kaimu da azahar zamu tafi, idan na kammala wakilicin mai martaba, zan wuce in da zan yi course ɗina na watanni shida. Dan Allah ki nutsu ki zauna lafiya da kowa, ban da rigima, ga Anty Laila nan, zata kula da ke tana da kirki sosai".

"Wannan ɗin ce mai kirki, bayan daga zuwan ta ta fara gaya mini magana, dan dai kawai ka ce yayarka ce".

"Dai-dai take da ke ai, idan ki ka yi mata rashin kunya, ta san yadda za ta yi da ke"

"To yanzu idan ka tafi, wa zai cigaba da aikin binciken da kake yi?".

Ya ce "Ga Bashir nan, akwai group ɗin mu da duk tare muke yin ayyukanmu, ki sanya ni a cikin addu'ar ki mimi, matsaloli sun yi mini yawa".

Rumaisa ta ce "Allah yana tare da bayinsa masu tawwakali da haƙuri. Allah yana tare da mu papa, zan din ga yi maka in sha Allah"
"Thank you dear" yayi maganar tare da sumbatar hannunta.
Tayi dariya ta ce "Kai, sai ka ce abun indiyawa, kiss a hannu"

"To muyi a baki?" Da sauri ta saka hannu ta rufe bakinta, ta tashi. Murmushi yayi ya tashi ya bar ɗakin.

A ranar takawa ya je ya yi wa mama sallama, ya sanar da ita batun zai bar ruma, a wurin ammi. Cikin kara mama ta nuna bakomai, tare da yi masa fatan alkhairi, sai dai bayan tafiyarsa ƴan mazan mama, duka din ga mitar, dan me ba zata dawo gida ba, za ta tafi gidan sirikai ta zauna, kamar mara gata.

Ruma ba ta ɗauki tafiyar takawa serious ba, sai da ta ga da gaske yana haɗa akwatinsa a daren yau.

Tana tsaye ya ce ta miƙo masa wannan, ta ɗaukko masa wancan.

"Papa, ya batun anty iman ne, ba wani abu da zaka yi a kai kan ka tafi? Kar wannan jabir ɗin ya aureta fa".

"To ke ina ruwanki?" Yayi maganar yana duba wani turare.

"Da ruwana mana, ni fa na bana son jabir ɗin nan".

"Ita ta ce miki ba ta son sa ne? Kin fiye damuwa, ko so ki ke in tayata mu bijirewa ammi?"

Rumaisa ta ce "Wallahi ba ta son sa, taɓ gaba ɗaya kalar munafukai ne jabir ɗin nan, da gani yana aikata wani laifi a ɓoye da Allah yake rufa masa asiri. Ko dan halin babarsa ma dole ya zama shaiɗani".

Ƙurii yayi da ido, yana kallon rumaisa, zuwa yanzu ya daina mamakin abubuwan da take faɗa da aikatawa, dan idan ta faɗa, ko ɗari-bisa ɗari bai zama dai-dai ba, kashi saba'in dai-dai ne.

"To, haka ta ce miki, kin san ba zamu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba, mu cigaba da yi mata Addu'a, idan shi ne alkhairi......

"A'a ba alkhairi bane ba ma, kuma ba zata aure shi ba" ta katse shi.

"Tun da kece waliyyinta ko? Wai ke kin fi ni son ta ne? Kin ƙwace mini ɗa, kin ƙwace mini ammi, kuma ƙanwartawa ma da nake ji da ita, kin ƙwace ta, haka ake rayuwa ne?"

Rumaisa ta ce "Eh ɗin, tana da wanda take so yake son ta, amma ba wani jabir"

Takawa ya ce "To wa take so? Dan bani da labari"

"Ban gayawa kowa ba dai, saura ka faɗa kaima, mai sunan baba take so, kuma yana sonta shima"

Da sauri takawa ya ɗago ya ce "What?! Umar ɗin gidanku?"

"Eh mana".

"Amma iman ba ta da da hankali, ina ita ina wannan yayan naki?".

Rumaisa ta haɗe rai ta ce "Saboda talaka ne ko?".

Shi ma ya ɗan tsuke fuska ya ce "Bana son bahaguwar fassara. Amma kin san halinsa dai sai dai ki gayawa wani, iman kuma is very simple and cool, ta yaya?"

Rumaisa ta ce"Ta yadda aka yi ka aureni, kai ba ruwanka, sai dai idan saboda talaka ne ba zaku ba shi ba, yaya umar bai taɓa damuwa da halin da wani yake ciki ba, ko zai shekara dubu bai ga mutum ba, in dai ba mama ba ce ko ni, ba ruwansa, amma zuwan da muka yi ya ce mini ina ƙanwar mijinki, to dan Allah ba soyayya ba ce haka? Ai kai dai ka san soyyaya ko, ka san ya ake ji?".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ke baki santa ba?"

"Ina na sani, ni fa sau ɗaya wani ya taɓa cewa yana sona, su yaya Aliyu suka ce, idan suka ƙara ganinsa, sai sun zane shi. To sam ban san ya soyayyar take ba, in ta so in ga ina zance".

Ya kwashe da dariya, rumaisa ba ta rabo da wauta.

"Ni ba daga zuwa zance, ki ka haɗa kayan zancen ki ka cinye ba, ki ka faɗo jikina, ki ka sani neman kalaman kariya. To yanzu tun da baki taɓa saurayi ba, zan zama saurayinki, mu gani, idan na tafi sai mu din ga waya, irin na saurayi da budurwa".

"Eh ayi haka, Allah ya sa na ji ya soyayya take, in din ga yi maka waƙoƙin soyayya, irin na Indiya"

Dungure mata kai adam yayi yana dariya, ya ce you won't kill me.

"Papa ni fa da, mai sunan baba wani tsoho zai aura mini a unguwar mu, malam ladan, mutumin nan ya taɓa zaneni da carbi, wai daga na tambayi mama wani abu, wai sai yayi mini aure, ya sai mini tabarma da buta. Wai ko a aura mini wani Ɗan ladi mai kan sirdi, kansa kamar plate, ka ga baƙinsa Astagfirullah, tsoro yake bani, gashi ɗan ƙarami, shi ba wada ba gashi nan dai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login