Showing 171001 words to 174000 words out of 199108 words

Chapter 58 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

814

saka Iman a mota laila da ƙawayen ammi a motar suka je suka kai iman.

Hatta su Fauziyya sai da suka je gidan iman, domin ganin ƙwal uwar daka, sun kukkushe abubuwan da dama, sai dai duk yadda suka so gano makusa a jikin angon basu gano ba.

Gidan Iman ɗan madaidaici, dai-dai zaman amarya, sai dai an zuba mata dakakkun kaya, na gani na faɗa.

Zuwansu babu daɗewa, su mai sunan baba suka ƙaraso, har da Mahmud a tawagar angwaye.

Aka yi adduoi, ƙawayen ammi suka yi musu nasiha sosai da sosai suka tafi.

Takawa ya kalli mai sunan baba ya ce "Kamar yadda ka kawo mini taka ƙanwar ka ce amana, nima ga tawa nan, amanar marainiya ce a hannunka"

Ya kalli in da ruma take zaune kusa da iman, suke ta kuka, ya kalleta ya ce "Mimi tashi mu tafi" yayi maganar yana jan hannunta, da ƙyar ta tashi, iman sai kuka take suka tafi.

Takawa sai da ya zazzarewa Nusaiba ido, sannan ta tashi, saboda tare suke faɗuwa suke tashi da Iman a gida.

Kowa ya watse, daga shi sai iman, sai dai sun shafe lokaci, ba tare da wani ya ce uffan ba, mai sunan baba ya tashi, ya je ya rufe gidan.

Ya dawo falon, ya tarar da ita a in da ya bar ta a zaune, ya ƙarasa gabanta ya miƙa mata hannu ya ce "Ranki ya daɗe bisimillah"

A hankali ta kalli hannun nasa, amma ta kasa motsi, ya ƙara miƙa mata hannu.

A hankali ta miƙa masa nata hannun, ya riƙe ta, ta tashi tsaye ya ja ta zuwa ɗaya daga cikin bedroom ukun da yake falon.

Ya taimaka mata ta cire Alkyabbar jikinta, ya saka hannu ya ɗago fuskarta, fuskar tayi pink saboda kuka, sai jan mayafin take, tana rufe baƙin gashinta wuluk, da ya sha gyara.

Kallonta yake yi, wai wannan zuƙeƙiyar yarinyar ta sa ce, Alhamdilillah ala kulli halin.

Ya ɗan lumshe idonsa sannan ya buɗe su ya ce "Kukan me ki ke yi ne?".

Tayi shiru ba ta ce komai ba.

"Mu je mu yi alwala" ta jinjina masa kai, toilet ɗin cikin ɗakin suka shiga, ya kunna mata famfo ya ce "Bismillah" tare suke alwalar, sai dai da ya kai hannu idan hannunsu zai haɗu, sai ta janye nata.

Ya shammaceta ya ɗan watsa mata ruwan hannunsa, ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Salla suka yi raka'a biyu, yadda mai sunan baba ya din ga kwararo addu'a ba ƙaramin burge Iman yayi ba, dan a rayuwarta tana ƙaunar namiji mai addini.

Bayan sun idar sun shafa, ya koma falo, ya shiga kitchen in da Mahmud ya ajiye kaji, da lemuka ya ɗaukko ya dawo ɗakin.

Gaba ɗaya a takure take, sai sunkuyar da kai take kamar mara gaskiya.

"Yaluwa, me zaki iya ci a nan?"

Murmushi ta yi ta ce "Yaya umar yaluwa kuma?".

Shima Murmushin yayi mata ya ce "Yeluwa mana, balarabiya a Nigeria".

"Idan Larabawa sauka ji ka babu ruwana".

Yayi murmushi ya tura plate ɗin gabanta ya ce "Bismillah"

"Na ƙoshi" ta faɗa a hankali.

Wata hamma ta kamata, tayi a hankali tana lumshe ido.

Ya ɗan ƙare mata kallo ya ce "Bacci ki ke ji zaki kwanta ne?" Da sauri ta ce"A'a".

Ya sake cewa "Bacci ko yunwa, wanne ne dalilin hammar?"

"Yunwa"

"Oya ci abinci" tamkar za ta nutse, haka take ɗan mintsunar naman tana kaiwa bakinta tana sunkuyar da kai.

Tashi yayi ya bata wuri, ya tafi gaban wardrobe ya buɗe, an shirya mata kayan sawarta, kuma duk ciki ba wanda aka ɗauka na lefenta aka ɗin ka.

Ya sauya kaya zuwa wata jallabiya, ya cire agogon hannunsa ya ajiye.

Ta nannaɗe sauran da ba ta ci ba, ta ajiye, ta tashi zata fita, ya ce "Ina zaki?"

"Can ɗakin zan je na kwanta"

"Mhmm, Ashe da bayan ɗaurin aure, sai ki yi zamanki a wurin ammi, nima na zauna a wurin mama. Dan na kusa yin kuka nima ɗazu kamar ke, bana son yaran nan su raina ni ne" tayi gajeriyar dariya.

Ya ce "wanko hannun ki zo"

Ta ce "To" ta shiga ta wanko hannunta, ta fito.

"Ki kwantar da hankalinki, ba abun da zan yi miki nima tsoro nake ji kamar ke, a gajiye ma nake kaina ciwo yake, i know what you are scared of, am scared too, ki shirya ki kwanta" wata irin Muguwar kunya ce ta kamata.

Har ƙoƙarin tuntuɓe take yi, ta nufi gadon ta kwanta.

"In baki bargo ne?"

"A'a yaya umar ai zafi ake yi "

"Shi hijjabin da kayan jikinki iska suke baki?"

"A'a"

"Trust me, ba abun da zan yi miki yanzu, nima tsoronki nake ji, ki sassauta kayan mana"

Da ƙyar ta canza kaya, zuwa wata doguwar rigar bacci, mai balance, ta raɓa da ƙyar da kwanta a bayansa.

Ba tare da ya waiwaiya ba ya ce "Kiyi Addu'a"

Ta amsa da "To"

Sai da ta tabbatar da gaske ba abun da zai yi mata, sannan ta yi bacci.

***
Rumaisa a gidan ammi ta so kwana, amma takawa ya ce bai yadda ba, tun da suka koma gida tayi wanka, take mitar ta gaji sosai.

"Papa ka yi mini sannu na gaji fa"

"Lokacin da nake cewa ki nemi wuri ɗaya ki zauna, ai baki ji ba"

"Mhmm, dan Allah kayi mini tausa to, ƙafata ciwo bayana duka jikina ma"

Takawa ya ce "Maganinki kenan"

"Wayyo mama na gaji, ka ce mini sannu"

"Ke ni tausayin ƙanwata ne ya dameni yanzu, ta shiga sabuwar Rayuwa Allah ya bata ikon jure ibada"

"Wai Iman, ai mai sunan baba ba irinka bane, na san ba zai mata abun da ka ke yi mini ba"

"Allah ko, saboda ga shugaban waliyyan ƙarshen zamani ko?"

Ruma har cikin zuciyarta ta ce "Allah da gaske nake, shi fa mai sunan baba babu ruwansa".

Ba ƙaramar dariya ta bawa Adam ba, kuma ita har ga Allah take gaya masa iya gaskiyarta.

"To ai shi idan ba ruwansa ke da ruwanki" da sauri ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah wallahi bani da lafiya, gashi kuma na gaji".

"Lokacin da nake hanaki ai ba kya ji, maganin mara ji kenan" ba yadda ta iya da papa, haka ta ƙyale shi.

Bayan komawa bacci bayan sallar asuba, ringing ɗin wayarta ya sanya ta farka, murya ƙasa-ƙasa tayi sallama.

Nusaiba ta ce "Amarsu ta ango, baccin gajiyar ne haryanzu baki tashi ba?"

Iman ta ce "Bari Anty Nusaiba, gajiya fa akwaita"

"Ko a taho da ruwan zafi"

Kallon in da mai sunan baba yake kwance tayi, sai dai ya juya baya ta ce "Anty Nusaiba sai ka ce wata mai jego".

"To idan ba mai jego ba ce yanzu, nan da 9months dai an zama"

"Ina ammi?"

"Tana can tare da sauran baƙi, ita ta ce na kira ki ma, zaki yi baƙi wanda ba su samu zuwa jiya ba, za a taho miki da abinci"

Iman ta ce "To, Allah ya kawo su lafiya, ke ba zaki zo ba?"

Nusaiba ta yi dariya ta ce "Ai ruwan zafi na ce zan kawo miki, tun da kuma ba kya so shikenan"

Tayi dariya ta katse wayar ta ce "Allah ya shiryeki Anty Nusy"

"Ai da kin gaya mata ba ayi komai ba, tun da shi take son ji"

Gabanta ne ya faɗi, ba ta san idonsa biyu ba, ya juyo gaba ɗaya ya zuba mata ido, ta saka hannu ta rufe fuskarta.

Yayi murmushi ya janye hannun ya ce "Da kin gaya mata, duk a tsaroce ki ke, nima haka, duk tsoron juna muke ji, amma zamu iya nemanta da ruwan zafinta nan kusa ko nesa kaɗan".

Wato ba ƙaramin mamaki abun da mai sunan baban yake faɗa yake bata ba, bata taɓa zaton Wannan maganganun daga bakinsa ba.

Hular kanta da ta zame, ta bawa gashinta damar bayyana, ya shafa gashin ya ce "My pretty yellow. Tashi mu kintsa kan baƙin naki su ƙaraso".

Ta tashi zaune ta ce "In haɗa maka ruwan wanka ne?"

"Kar ki damu da ni, yi wankan ki"

Kafin Iman ta fito, cif ya ɗame gadon, gidan babu wani datti dama.

Kasancewar baya ɗakin, ya sanya ta saki jikinta, ta shirya ta fito ta same shi a falo, yana ta ƴan dube-dube.

"Yauwwa ƙaraso ki ga gidan naki, ɗan abun da talakan mijin naki yayi miki"

Ta ƙarasa ta ce "Ni wannan gidan ya fi mini kowanne kyau da tsari".

"Really?"

"Yeah"

"Jazakillah khair for appreciating it, Allah ya yassare mini in yi miki wanda ya fi wannan"

"Amin ya Allah" tare suka zazzagaya, ta din ga yabon gidan, da yabawa ƙoƙarin sa.

Aka ƙwanƙwasa gate ɗin gidan, Umar ya je ya buɗe, ya ga Usman da Abdallah, da ledar viva a hannunsu.

"Mai sunan baba ko mu koma ne na ga kana kallonmu, mama ce ta bayar da abinci mu kawo" buɗe musu yayi, ya juya ya koma falon.

A kujerar da iman take ya je ya zauna, cikin murna Iman ta ce "Yaya usy sannunku da zuwa"

Usman ya ce "A'a ai mu yakamata mu gaishe ki, ina kwana antynmu"

Iman ta ce "Kai dan Allah har ka bani kunya"

Ya ce "Ai girmanki ne, dole a baki"

Ta shiga yi musu bangajiya, tare da tambayarsu ya mama.

Abdallah yayi ƙasa da murya ya cewa Usman "Ka tashi mu tafi, gulma ce a bakina, kar na yi misbehaving a samu akasi"

Usman ya ce "To mu tafi, nima ita nake son yi"

Suka tashi Abdallah ya ce "Bari mu tafi".

"Haba yaya Usman, daga zuwanku, ko ruwa ban baku ba"

"Bakomai ma sha a waje, tun da mai gida ya haɗe rai, baya buƙatar mu ne sai anjima"

Bayan sun fita ta ce "Yaya umar ka din ga dariya mana, ko smiling ne"

"Ban iya ba, tun da ke kina yi ai shikenan deejangala, bari mu karya ko, dan ni na fara jin yunwa".

Tare suka karya, duk ita duk a ɗarare take, tun da suka fara baƙi ya fice ya bar gidan.

Usman kuwa gulmar mai sunan baba suke yi, wai yadda ya wani zauna a kusa da Iman, wai shi mai gida.

Suna tafe rumaisa ta kira Usman, ya ɗaga ya ce "Ke kuma meye zaki dame ni?".

Ta ce "Daga kira me nayi maka to?"

"Ke rabu da ni, nima aure nake so rumaisa, ke kin yi aure, mai sunan baba yayi, Aliyu da yaya Habu suna hanya, jiya dan abun takaici, rige-rigen katifar mai sunan baba muka din ga yi, da tsofaffin kayansa. Kin ga yadda yake wani basarwa yau da muka je, wai shi maigida. Ke ma kina ta ƙarshe a gidanmu, amma ƙiri-ƙiri daga sunanki rumaisa an mayar da ke mimi, saboda aure, kallemu ni da Abdallah aka bawa kwanukan abinci muka kai musu. Allah ka aurar da ni, ko babyn nan a din ga ce mini"

Rumaisa dariya har da tuntsurawa, "Zaki yi dariya ne, wato ke kin tsallake, mijinki na ta lallaɓa ki, zuwa zan yi mu dai-daita da Hauwwaliya, daga baya mu yi kuɗi a tare, dama mutuniya ta ce, tun da yanzu mata sun fi son mai kuɗi muyi tuwona maina, kar na je na lalace"

Shi har ga Allah yake maganar, takawa da yake jin su ya ce "Usman idan ka lalace ina muka kama? ka samo mata, in dai aure ne zan yi maka na baka jari"

Usman ya ce "Subhanallah, Allah ya taimake ka dan Allah ka ce ba ka ji abun da na ke cewa ba, har kunya ta kama ni".

Suka yi tayi masa dariya.

***
Baƙi suka fara watsewa, saboda an kammala biki.

Gidan Iman ma mutane suka yi ta sintirin zuwa gidan ta, mai sunan baba yayi burus da ita, har ta ɗan sake daga tsoronsa da take ji.

Yau kiran sallar farko na asuba, ya tashi yayi nafilfilinsa da karatun Alkur'ani, ana daf da fara kiran sallar asuba, ya tashi da niyyar tashin Iman ta yi alwala.

Sai dai zancen ya canza, maimakon first night shi first asuba yayi, ƙarshe sai da hasken rana ya hudo, sannan sallar asubar nan ta yiwu.

Mai sunan baba kenan, komai nasa daban ne, sai dai kamar wanda ya yi laifi, duk ya diririce, mussaman ganin tana kuka.

Bayan ta idar da sallar asuba, ta kifa kanta a kan sallaya, a hankali ya kira sunanta "Khadija"

"Na'am"

"Ki tashi ki kwanta mana".

"A'a bakomai, ai gari ya waye ma"

"A'a ki kwanta dai ki huta, kina buƙatar wani abun ne?".

Ta ce "A'a"

"To tashi ki kwanta"

Ya ɗagata ya rakata kan gadon ta kwanta.

Har zai tafi ya ce "A cewa Nusaiba ta zo tayi aikin nata, ta kawo ruwan zafin duk da ma dai na yi da kaina".

Rufe fuska kawai ta yi ta, lumshe idonta tana murmushi.

Ƙiri-ƙiri mama ta kira mai sunan baba, ta ce masa maƙwabta za su zo, amma ya ce kar su zo, ba ta jin daɗi.

Abun da Iman tayi tsammanni, da kuma wanda mutane suke jiye mata, ba shi ta tarar a gidan mai sunan baba ba, mutum ne matuƙar kulawa.

Aikace-aikacen gidan kuwa ba ruwansa, tashi yake yayi abun sa, da ta motsa sai ya ce ta zauna ta huta, shi tausayin ta yake ji.

Ranar da zai koma kasuwa kuwa, shagwaɓa iri-iri a wurin Iman, kamar kar su rabu.

***

Ihun da rumaisa take yi ne tana salati, ya sanya takawa fitowa daga toilet a hargitse, ya nufota.

"Menene lafiya?"

Ya tarar da ita bacci take yi, tana ta fizge-fizge tana son ta tashi, ta ɗaga murya tana "La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin".

Da sauri ya ɗagata ya din ga karanta mata adduoi, yana tofa mata, ko da ta buɗe ido ta ganshi, ta saka ihu ta ƙwace tana haki.

"Mimi lafiya kuwa? Menene?"

"Ba kaine ka zo idonka na hayaƙi ba, zaka huda mini cikina da faratanka ba".

Gabansa ne ya faɗi ya ce "Ni kuma mimi?".

Eh mana tayi maganar hawaye sharkaf fuskarta.

Jiki a sanyaye ya ce "Mafarki fa ki ka yi, ni ina banɗaki".

"Da gaske mafarki ne, ba ka fasa mink cikin ba?"

"Duba ki gani".

Ta shafa cikin ta ta ce "Ni fa tun ina gida nake mafarkin idonka na ci da wuta, zaka soka mini farce a wuy, har a gaske fa watarn idonka yana yin hayaƙi"

Ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Ki yi addu'a ki cigaba da baccinki mafarki ne"

Ta ce "Ba zan iya ba tsoro nake ji"

Ya rungumeta ya ce "Ki yi ta Addu'a"

Yayi shiru yana tunanin kenan rumaisa ciki ne da ita? In dai Aisha tayi irin wannan mafarkin, to ɓari take yi, amma rumaisa ta ce masa tun a gida take irin mafarkin.

Wata guda da auren su Iman.
Mai sunan baba bai taɓa zaton zai iya zagewa ya yi soyayya haka ba, babban abun da yake ƙara masa son Iman bai wuce matuƙar biyayyarta ba, da soyayyar da take yi wa mama, da ƴan uwansa ba, dan haka yake ƙara iya ƙoƙarin sa wurin ganin ya kyautata mata.
Tuni ta cigaba da zuwa makarantar ta, wasu lokutan kan ta dawo ya zo gida ya rage mata aiki, ranar kuwa da zata kai shida a makaranta, har makarantar yake zuwa kai mata abinci babu ruwansa.

Ƙawayenta suna yawan faɗa mata, tayi dacen miji mai son ta. Idan za ta tafi makaranta idan ba zai samu kai ta ba, shi ne yake bata kuɗin mota.

Tana zaune a falo da daddare tana shige -shigenta a system ɗin sa, tana typing ɗin wani assignment, ya fito daga bedroom ya kwanta a kan kujerar da yake, ya ɗora ƙafafuwansa a kan cinyarta ya ce "Me ki ke nema a computer ta?"

Ta shagwaɓe ta ce "Dubawa nake ko zan ga hoton ƴan mata"

Dariya yayi ya ce "Ni ina ruwana da wasu ƴan mata, ke ma dan kin liƙe ne ki ka same ni"

"Ko kuma mun liƙe ba" tayi maganar tana tura baki.

Tashi yayi zaune ya rungumota jikinsa ya ce "Na yadda ni na liƙe, tun a kallon farko da na ganki, na zata ma da aljana ce za ta aure ni, ashe ƴar autar ammi ce"

Tayi dariya ta ce "Ni fa da tsoro ka ke bani my, i just felt for you, ashe duk fasa aurena da ake a baya rabonka ce ni, Alhamdilillah for having a good husband like you my faruk" tayi maganar tana shafa sajensa

Murmushi yayi yana jin wata annashuwa, da soyayyarta na ratsa shi, ya sake rungumeta ya ce "Deejana, my pretty yellow girl, gaskiya kina so na da yawa".

"To ka ce kana so na nima"

Wata ƴar dariya ta bashi, ya ce "Ɗaukko carbi, ina faɗa kina lissafawa, har sai kin ji kin gamsu da ina son ki"

Iman ta sake narke masa ta ce "Ni waƙar soyayya ma zaka yi mini"

"Taɓɗijan, ai muryata ba ta waƙa ba ce, ban ma iya ba deeja"

"Muryar ka ta tsorata mutane ce" tayi maganar tana yi masa dariya.

"Eh ai an fi son haka, monster haka ba raini, tashi mu je mu kwanta, zaki school gobe in Allah ya kaimu"

Ta ce "To, bari na kashe system ɗin"

"Ahh, Baby an yi maka Gmail"

Mai sunan baba ya ce "Ba zaki daina babyn nan ba ko? Baby kamar ɗan daudu, gara ki ce mini faruk ɗin ai".

"Ai a waje ne ake maka kallon monster, ni a wurina babyna ne"

"Daɗinta ke ma a da monster ki ke gani ai".

"Eh yanzu kuma baby ba" tayi maganar tana duba Gmail ɗin.

Message ne a kan ana nemansa a Lagos zai je interview.

Ya ce "Anya wannan message ɗin nawa ne? Bana tunanin nawa ne"

"To na waye, naka ne mana"

Zai yi magana sai ga message ɗin Mahmud.

"An kiramu interview lagos, ban sani ba ko ka ga message ɗin, ranar Sunday zamu tafi, za ayi interview Monday, mun samu aikin nan"

Nunawa Iman yayi yana cigaba da mamakin abun, tamkar dai mafarki.

Iman ta din ga murna, tana addu'a, tamkar tun farko ba ta san zancen ba.

***
Duk da haryanzu bai gama komawa cikin nutsuwarsa gaba ɗaya ba, amma yayi ƙiba sosai abun sa, da gani ya samu nutsuwa sosai yanzu.

Sallama da aka yi a office ɗin ce ta sanya ya ɗago, ya amsa sallamar.

Jamil ne ya shigo fuskar nan babu annuri, shi ma Adam ya haɗe fuska yana jiran ya ƙaraso.

"Wurinka na zo"

"Ina saurarenka"

"Zuwa na yi na ji ina ka tsaya"

"Ina tsaye a in da ka sanni"

Jamil ya ce "Magana nake so mu yi ta fahimta, zuwa yanzu yakamata ace ka kammala binciken da zaka yi, ka wanke ni daga zargi da kuma zullumin da ka jefa ni a ciki kai da matarka".

"Jamil a kan me zaka yi zullumi, idan har ka na da gaskiya? Ka cigaba da harkokin ka kawai"

"Ba zai yiwu ba Adam, ya zama dole ku wanke ni, kuma ku tabattarwa duniya, bani da laifi".

"Jamil kana bani mamaki fa, ni da na dawo ban tayar maka da hankali na cigaab da bibiyar matata a kan lallai ka samu wasu bayanai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login