Showing 117001 words to 120000 words out of 199108 words

Chapter 40 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

815

san duk halin da ake ciki"

Ras! Gaban Iman ya faɗi, mussaman ganin yadda ammi ke murna da al'amarin.

"Ya ki ka yi shiru, ba ki ce komai ba?"

Iman ta ce "Ammi tsoro nake ji, kin san mamansa ba za ta amince ba"

Ammi ta ce "Iman addu'a zamu yi, Allah ya sa ta amince ya shige mana gaba, na san babu yadda za ayi"

Jiki a sanyaye Iman ta ce "To Ammi" daga haka ta tashi ta tafi ɗakinta, ammi ta nuna goyon bayanta a kan lamarin, gashi ita ko kaɗan, ba ta ra'ayin Jabir, hasali ma zuciyarta na tare da wani daban, da bai san tana yi ba.

Mai sunan baba yana ɗakinsu yana cin abinci, yana jiyo tsalle-tsallen ruma a tsakar gida, takawa kuma yana tare da mama suna hira.
Haka kurum ya ji gabansa ya faɗi, har sai da ya ji tamkar abincin da ya haɗiya ba zai wuce ba.
A take tunaninsa ya kai kan iman, ya janyo wayarsa, ya shiga What's app ɗin sa, sai dai ba ta online, to idan tana online ma me zai ce mata?.

Ya taso ya fito tsakar gida, rumaisa ta zauna ta saka Yasir a gaba, suna magana ƙasa-ƙasa.

"Yasir, kai ka san ta kan waya, na san kai gwani ne, hacker ne kai, hacking nake so ka yi mini"

Ya harareta ya ce "Ni ne hacker?"

"Yi haƙuri, wani abu zaka yi mini, wayarka zaka ara mini, zan haɗaka da wanda zaku yi aikin tare, sirri muke so".

"Ke, bana son iskancin banza, haka kurum ki ja mini masifa, ke idan kin nemo magana mijinki zai fitar da ke, ni kuwa fa?"

Ruma ta ce "Ba irin wannan aikin bane, yaya usy ya san komai, tare muke shawara ma, papa zaku tayani mu taimakawa, amma bana son ya san halin da ake ciki, bari ya usy ya dawo, zan baka lambar Mahmud ɗin, ƙanin mijina ne" gyaran murya suka ji a bayansu. Ruma ta waiwaya taga mai sunan baba a tsaye.

Da sauri ta tashi ta ce "Laa mai sunan baba ina wuni, ban san kana nan ba ai"

Alama yayi mata da ta je, ta ƙarasa zuwa cikin ɗakinsu, ya kalleta ya ce "Ina yarinyar nan, ta warke?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wace yarinyar?"

"Ƙanwar mijinki?"

Ruma ta ce "Auu, Anty Iman, dama ba ta da lafiya ne?".

Ya ce "Never mind, je ki kawai".

"Tana lafiya ƙalau, shekaranjiya ma mun je gidan, kusan kullum idan muka je, sai ta ce mini ina yaya Umar, ko ta bani wayarta ta ce....

"Fita ki bani wuri" ya katseta, saboda yadda ta fara zuba.

Sum-sum ta fice, ya nemi wuri ya zauna, yana tuhumar kansa meye ma na tambayar rumaisa.

Tamkar mata, haka suka din ga shewa da Usman ya dawo, ta baje musu abincin da ta zo da shi, ta haɗu a cikinsu, suna ci.
Idan da sabo, takawa ya riga ya saba, dan haka ba ya damuwa ma yanzu, ya riga ya fuskanci irin alaƙar da ke tsakanin su, shiyasa a rashin su, take sauke masa duk wani kwandon rashin ji da take yi musu.

Sai ƙarfe goma suka bar gidan, suka tafi gida.

***
"Jamila ina cikin damuwa, wai ni Jabir zai tunkara, ba tsoro ba kunya wai yana so in bashi dama ya auri ƴar da giwa ta tsinto iman?"

Mummy ta ce "Ni na san wannan maganar tuni, ba wannan ne ya dameni ba, lamari ya fara jagulewa, na fuskanci kamar aikin malam na kan dutse ya fara sanyi"

Cikin mamaki ta kalli Mummy ta ce "Kin sani fa ki ka ce? Amma baki gaya mini ba"

"Ban zaci abun har zai kai haka ba, ban ɗauka da gaske zai yi maganar aure ba, amma na san ba wata matsala ba ce ba, zaki iya jajircewa a kan hana faruwar hakan".

"Lallai ma jamila, ke kin fi kowa sanin, ba zan haɗa alaƙa da giwa ba, ya auri ƴar ta idan Allah ya sa ya samu sarauta, su mallake mini ɗa?"

"Lubabatu naki fa mai sauƙi ne, nifa abubuwa sun fara sakwarkwacewa, dole a nemo sabon boka, duk da na bayar da aikin da aka bani na ƙarshen nan, amma dole na nemi abun yi, akwai matsala".

Hajiya Lubabatu ta ce "Kin ga ni yanzu bana gane komai, sai anjima ma yi magana daga baya kawai"

Mummy ta ce "Dole in motsa in sauya taku, ban taɓa samun matsala a abubuwan da nake ba sai a wannan karon, saboda zuwan wannan matsiyaciyar yarinyar, ƴar wannan abar daga zuwanta za ta hargitsa komai, Allah ya sa uwani ta yi abun da na sakata, yadda yakamata".

Wayar Mummy ta fara ringing, ta duba taga baba Uwani ce, ta ɗaga ta ce "Ya aka yi?".

Cikin kuka baba uwani ta ce "Ina cikin bala'i ranki ya daɗe, yarinyar nan wai ashe tana sane ta ce kina yi wa takawa asiri, dan ta gane idan ina kai miki maganar giwa, wallahi a sashinki ma akwai munafukinta, wallahi yarinyar nan ba yarinya ba ce aljana ce ranki ya daɗe, dan Allah kiyi wani abu a kai".

A fusace Mummy ta ce 'Kuma ki ka samu ƙwarin gwiwar kirana ki gaya mini wannan shirmen? Yayi miki kyau, ki mayar da hankali ki yi mini aikin da na saka ki, na san matakin da zan ɗauka a kanki"

"Na shiga uku, hajiya wani irin mataki?" Katse wayar Mummy ta yi, ta jefar a kan gado ta ce "Aikin banza"

**
Kamar kullum takawa ya je gaida ammi, ya tarar da kaya a ɗakinta, har da ƙaramin keke na yara.

Ya ce "Ammi, wannan kayan fa?"

"Mahmud ne ya saya wa takwaransa"

Har zai yi magana, da ya kalli fuskar ammi sai ya fasa.

Ammi ta ce "Yauwwa, ban gaya maka wani abun arziki ba".

"Wane abun arzikin?".

"Ina ranar da jabir ya zo, muka fita ka ke tambayata fara'ar me nake yi?"

Ya jinjina kai alamar ya tuna.

"Wata magana ya zo mini da ita, da ta faranta mini rai"

"Maganar me kenan?"

"Cewa yayi ya na son Iman, kuma aurenta zai yi"

Adam ya yi Jimmmm sannan ya ce "Yaushe kuma ya fara sonta?"

Ammi ta ce "Ban sani ba, ya ce mini dai zai je ya lallaɓa hajiya Lubabatu, ba ka ji daɗin da na ji ba, idan ta amince ai na ji daɗi, tun da ɗan gida ne, kuma na yaba da shi, jabir ɗa ne a wurina"

Adam jinjina kai kawai yayi, ya tashi ya ce "Bari na je wurin aiki, ina da idan na taso zan biyo, sai na dawo"

Ammi ta ce "Allah ya tsare".

Abun ya din ga damun Adam, baya son tonawa Jabir asiri, amma sam bai dace da auren Iman ba, salihar yarinya kamar wannan, duk da kashedi da gargaɗin da yayi masa, bai ji ba, bai kuma janye maganar son auren Iman ba.

Ga wanccan batu da rumaisa ta ɗaukko masa a kan Jamil, gaba ɗaya sai abubuwan suka ƙara rikice masa. Sosai yake son saka pressure a kan Jamil, dan har yayi maganar da Bashir ma, sai dai gefe ɗaya yana tunanin anya haka zai yiwu kuwa? Kar ya ɓata zumuncinsu, tayaya Jamil zai saka hannu a ɓatan aisha, bayan babu wanda ya san ma ta zo ƙasar sai shi, kar ya biyewa shirirtar rumaisa ta rufta shi, amma duk da haka akwai ƙamshin gaskiya a maganganunta.

Ƙarfe sha biyu ya kira sidi a waya, ya ce ya je ya ɗauki rumaisa, ya mayar da ita gida.

Ƙarfe biyu ya tashi, daga wurin aiki, ya tafi wurin aikin su Jabir.

Fuskar Jabir babu yabo babu fallasa, suka gaisa.

"Jabir, zuwa na yi na ji dalilin da ya sanya ka je ka samu ammi, ka ce mata kana son iman, baya ka san yadda muka yi da kai?".

"Tambayar da ka zo ka yi mini kenan Adam? Ka watsa komai kana neman ka ɓata zumunci, saboda kana auren wannan ƴar yarinyar, gaba ɗaya kanka ya juye, abun da ta ce kawai shi kake yi babu bincike? Ka je ka cewa Jamil yana da saka hannu a ɓatan matarka, ta yaya ƴar uwassa ce fa, ta yaya zai yi hakan? Ta ce Mummy tana yi maka asiri, magana ta koma kunnenta, ka je ka yi wa ƙannenka wulaƙanci dan su je gidanka duba ka, dan rashin ta ido, a gaban Mummy, yanzu kuma ka zo kana maganganu dan na ce zan auri Iman, kai ka san aurena da iman shine rufin asirinta, kuma ka sani Mummy sun kai ƙararka wurin mai girma wambai, dan yau da safe ya kira Ammi a waya, lallai yana nemanka, kuma zama za ayi na mussaman a kanka da matarka, dan da yiwuwar har gaban mai martaba, ba zai yiwu dan ka yi aure, ka hargitsa mana family ba.

Duk da gaban takawa ya faɗi, amma cikin jarumta ya ce "Jabir, gaban mai martaba ba gaban Ubangiji bane ba, daga nan a kaini duk in da aka ga dama, shi ciki da gaskiya, wuƙa ba ta taɓa huda shi" ya fita ya bar office ɗin.

Yanayin yadda ya zo ya wuceta a falo, ya sanya ta gane, akwai damuwa, har zata basar da shi, sai ta ji ba zata iya ba, ta bi bayansa.

"Papa, yau ba cin abinci, ba magana, iya sanina ban yi wani laifi ba"

Ya ɗan lumshe ido ya ce "Bakomai, ki je bacci zan yi".

"Ba bacci ka ke ji ba, wani abu ne yake damunka",  ta yi maganar tana murza zoben hannunsa. A hankali ya buɗe idonsa ya kalleta.

Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Bari na yi maka ta Yaya usy, ya ce gist me masoyiya ya ake ciki, to gist me aboki ya ake ciki?"

Ita duk tsananin situation, ba ka rabata da wasa.

Sai ya samu kansa da gaya mata halin da ake ciki.

Ta kwashe da dariya ta ce "Ohh, ni ƴa su, yaro bai san wuta ba sai ya taka, to kar a fasa kaini wurin mai martaban mana, idan ban warware kowa a gabansa ba me nake, ni fa bana tsoron kowa sai Allah, kuma wallahi duk abun da na faɗa gaskiya na faɗa. Sai in faɗi komai a gaban mai martaban".

Cikin rashin fahimta ya ce "Me zaki faɗa?"

"Ba zan gaya maka ba, daga gaya maka abu a kan Jamil ka je ka gaya masa, dama na san zuciyarka ba zata bari ka danne ba, shiyasa bana gaya maka wasu abubuwan, sai ka ɓata mini aiki, ni bana ƙwaina sai da zakara, ka san wanda ya gaya wa Mummy na ce tana yi maka asiri?"

Ya ce "A'a"

"To baba uwani ce, kuma ina sane na faɗa, dan daga ita sai ammi da iman a wurin na faɗa, baba uwani na kwasar sirrin ammi, ta je ta gaya wa Mummy. Saura kuma ka faɗa so muke mu kama ta red handed, Daddy ya tabbatar mini da ya ganta sau biyu a sashin Mummy cikin dare".

A sukwane ya tashi zaune, yana kallon rumaisa kamar ya ga abun tsoro, ya fara tsorata da lamarin rumaisa, kamar wata mai rauhanai.

Ta tura baki ta ce "Meye kuma? Saura ka gayawa wani, idan ka faɗa ba zan sake gaya maka abu ba, yanzu in anjima mu je gida, ina son in ga Mummy, na tabattar maka da babu wanda zai wani kira ka ya tuhume ka".

"Kin fara bani tsoro ne, don't make things complicated, tayaya za ki ce baba uwani tana cin amanar mu?"

Rumaisa ta ce "Ai ban ce ka yarda ba dama, amma zan tabattar maka da hakan, yanzu dai zo mu ci abinci, mu yi wasan gudu a backyard, in anjima in je wurin Mummy".

Ya ce "Am not in mood, je ki yi wasanki"

"To buɗe mini wayarka na yi game" shiru yayi mata, ya tsunduma kogin tunani.

Ta ɗau wayar, ta kama yatsansa ta buɗe, ta jingina da jikinsa tana dannawa.

Shi muma ya bita da ido, kamar mai kallon abun al'ajabi.

Ta gama danne-danne wayarta, ya ajiye masa ta tafi nata shagali.

Sai dai da ta sauka ƙasa, ta tarar baba uwani bata nan, ta tambayi su Asiya, suka ce mata tun safe ta fita ba ta dawo ba.

Ta tafi backyard, ta samu ball ta yi tayi, kamar ba matar ba sarake ba, ta window takawa yake hangota, yadda take sarrafa ball ɗin a ƙafarta ka san ƙanwar maza ce.

Da la'asar bisa kasada, takawa ya ɗau ruma suka tafi gida, suna tafe yana sake tambayar ta, me za ta cewa Mummy, ita kuma taƙi faɗa masa.

Ko da suka je, ya ce sai dai su shiga tare, ita kuma ta ce idan tare suka shiga, abun ba zai yiwu ba.

A falo ta tarar da ruƙayya tana danna remote.

Rumaisa cikin fara'a ta ce "Mummy tana nan ne?".

Ruƙayya tayi tsaki ta ce "Wace Mummy?".

"Jamila babarku"

"Sunan Mummyn ki ke faɗa haka?"

"Kin ji abun da na ji, ranar da ki ka faɗi sunan Ammi gatsal".

Mummyn ce ta fito tana waya, tana ganin rumaisa ta yi turus.

Ruma ta gaisheta, cike da duniyanci, ta yi murmushi ta ce "Amarya ba kya laifi, yau ke ce a sashina?"

Ruma ta ce "Eh Mummy wurinki na zo".

"To gani"

Ruma ta ce "Sirri zamu yi"

"Ba damuwa Bismillah" suka shiga wani ɗakin na daban.

Ruma ta ce "Mummy, na ji kin kai ƙarar papa ne, shi ne na zo na baki haƙuri, dan Allah ki janye, kar ki saka ayi taron nan, ni nayi laifin ba shi ba".

Mummy ta yi murmushi ta ce "Turo ki aka yi kenan? Gara na kai ƙararku ai, dan ban san laifin da na yi muku ba, kuma taro babu fashi, dole ku je ku wanke ni".

"Mummy, tayaya zan san kina yi wa papa asiri, sharri aka yi mini, baba uwani ce fa ta gaya mini, kina yi wa papa asiri"

A firgice ta ce "Baba uwani kuma?".

"Ita, kuma ba ƙarya take yi ba, tun da na kamata da wannan ɗazu da safe" rumaisa ta yi maganar tana ɗagawa Mummy, wasu layoyi, da wasu irin abu a cikin leda.

"Yanzu ko dai ki janye maganganun ki, ko kuma idan aka je gaban mai martabar, zan gaya masa komai, kuma mu ma muna da CID a sashinki, wadda take kawo mana rahoto. Abun da baku sani ba shi ne, na sanku tun kan na shigo cikinku, ina kuma sake maimaita muku, tunanin maza bakwai ne a cikin kaina, da kuma nawa na takwas.
Mummy ina roƙonki, da ki jingine makaman nan, ki sassautawa mijina haka, wallahi a dalilinsa nima bani da kwanciyar hankali, muraran nake ganin abun da mutane ba sa gani a kansa, dan Allah ki bari ya huta haka.

Ayshercool.

Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏





Mummy ji tayi, tamkar an sanya mata dabaibayin ƙarfe an ɗaure mata ƙafafuwanta, ta kasa motsi, jikinta kuma yayi wani irin mugun sanyi, ta kasa motsa ko ina. Har rumaisa ta gama yi mata maganar, ba ta iya cewa uffan ba, mussaman ganin wannan layoyin a hannun rumaisa, kuma rumaisan ta ɓare fatar tsaf.

A tsakiyar garden ɗin gidan, ta bawa baba uwani ta binne mata, shi ne cigaban aikin da ake yi mata a kan Adam, akwai irin layoyin a gidansu, akwai a gidan da ya zauna da aisha, wannan karon ma an yi ta saka a gidansa, saboda ana son ya din ga shige da fice a kai a kai, a in da layoyin suke.
Kuma wannan laya ta bawa baba uwani jinin mage, da za ta din ga zubawa a ƙasar wurin sa'ai da lokaci.

Da safe rumaisa na ta sauri, ta kammala abun da za ta yi kar ta makara, dan haka ana idar da sallar asuba ta hau ayyukanta, sai dai kanta ya din ga sara mata, ta din ga kamar wani sauti, daga bayan ɗakinta, kawai ta sauka ta zagaya, wanda a nan ta iske baba uwani, ta gama binnewa, ta jira ta bar wurin, ita kuma ta tone ba ta sani ba.

"Ina sake roƙonki Mummy, mu rabu cikin mutunci da kwanciyar hankali, abun da aka yi a baya, Ubangiji Allah ya yafe, amma idan aka cigaba a haka zaku ji babu daɗi, na san ni yarinya ce a kan ku, da ku ke yi mini kallon mara hankali, amma zan iya abun da tunaninku bai taɓa kaiwa kai ba, kamar. Na kama baba uwani, kuma ta yi mini bayanin komai, wanda kafin in dawo daga makaranta ta bar gidanmu, amma kar ki damu, ban gayawa kowa ba, daga ni sai ita muka sani, idan kin so, sirrin zai zauna daga ni sai ke, idan kuma aka matsa mini, ki tambayi takawa yadda nake" ta mayar da ledar cikin hijjabinta, ta fita.

Sai da ta fita sannan Mummy ta ji ta dawo hayyacinta.

Jikin Mummy ya fara tsuma, tana zazzare ido, gaba ɗaya ta kasa tunani ma, neman wuri ta yi ta zauna daɓas a kan gado, wani irin gumi ya din ga tsatstsafo mata, har ta tsakanin cinyoyinta.
"Lallai wannan uwani an yi ƴar........, ni zata tonawa asiri, mutuniyar banza da ta wofi?"

Jiki na rawa ta janyo wayarta, ta kira baba uwani.

Baba uwani ta fara koɗata, ta ce "Ke dalla saurara mini, ashe baki da hankali? Shi ne ki ka bari yarinyar nan ta kama ki, kina binne-binne a gidan?".

"Ni kuma? Ai ba ta kamani ba, wallahi ba ta gani ba"

"Ƙarya ki ke uwani, yanzu ta bar shashina, da ƙullin layoyin a hannunta, ni zaki munafunta? Ashe baki da mutunci? Tun yaushe na baki aikin, ki ka ajiye baki yi ba, har ta gani, kenan ma ke ki ka gaya mata ina yi wa Adam asiri".

Kamar baba uwani ta saka kuka, ya ce "Wallahi, wallahi hajiya ba haka aka yi ba, ina iya ƙoƙarina dan Allah kiyi haƙuri".

Kashe wayar mummy ta yi, tana fifita da hannunta, gaba ɗaya ta gigice.

Ruƙayya ta shigo ɗakin, tana duban Mummy ta ce "Mummy ya aka yi ne, wai me ta ce miki?"

"Bakomai, jeki hutawa zan yi" Ruƙayya ta ɗage kafaɗa ta fice.

Rumaisa ba ta tarar da takawa a in da ta bar shi ba, dan haka ta wuce sashin Ammi.

Ta tarar da shi a zaune a gaban ammi suna hira, sabir sai hawa yake wuyan takawa yana saukowa.

"Ammi sannu da gida"
Ammi ta ce "Yauwwa ƴar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login