Showing 129001 words to 132000 words out of 199108 words
maganar cikin rauni.
Kuka Mummy take tamkar ta aminta da abun da ya faɗa, sa dai ƙasan zuciyarta cike yake da baƙin ciki da takaici, tare da aniyar sake ɗaura ɗambar, kawo ƙarshen giwa, da adam har da wannan annamimiyar ƴar tayin da ke barazana ga harƙalarta.
***
Wajen ƙarfe biyar na yamma, rumaisa na zaune zuruuu kamar mara lafiya, shi kansa sabir ba shi da karsashi, ya zo Jikinta ya kwanta, yayi shiru shi ma ko wasa baya yi.
Iman ta ce "Haba Anty rumaisa, takawa zai dawo, tafiya ba mutuwa ba ce, wannan damuwar ta yi yawa ai"
Iman ta ce "Hmm ba zaki gane ba, ni fa ban taɓa zaton zan damu ba, nayi-nayi kar ka damu na manta, amma na kasa".
"To ba ga waya ba, idan ya kira sai ku din ga video call".
Rumaisa ta ce "Ni duk ba wannan ne ya dameni ba" Iman za ta sake magana, Nusaiba ta yi sallama.
Suka amsa mata, ta dubi iman ta ce "Amaryar uncle, his royal highness jabir, is waiting for you".
Iman kamar ta saka kuka ta ce "In yi masa me?"
"Iman me yake damunki ne? Ban gane ki yi masa me ba? Ki je ki ji mana"
A daƙile ta ce "To, zan je" Nusaiba ta juya ta fita.
Rumaisa ta ce "Kar ki damu, in sha Allah babu abun da zai faru sai ikon Allah, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, na san ba zata bari ba".
Rumaisa na cikin maganar, laila ta shigo, ta kalli iman ta ce "Iman, jabir fa yana jira" ta ƙarasa maganar tare da zama a kusa da rumaisa, ruma tana satar kallon fatar laila, kamar jikin tarwaɗa, gashi ko kunya ba ta ji, take tsukewa a cikin ƙananan kaya.
Iman kamar ta zubar da hawaye, haka ta tashi ta bar ɗakin.
Laila ta kalli ruma ta ce "Kina ji na ko?" Rumaisa ta ji kamar ta ce mata 'Da ni kurma ce?"
Amma a zahiri ta ce "Eh"
"Tun da yau mijinki ya tafi, dama ya bar sallahun kai ki makarantar matan aure, gobe in Allah ya kaimu za a fara kai ki, daga nan zaki kwaso kayanki na gidanki ki dawo nan. Ni na karɓi ragamar kula masa da ke kafin ya dawo, dan haka dole zaki din ga bin duk abun da na saka ki, bana son gardama ko rashin kunya, dan idan rashin kunya ce, sai dai ki koya a wurina. Idan kin dawo daga makaranta, zan din ga yi lesson da kaina, da kuma dabarun zaman aure.
Abu na gaba, zamu din ga gyaran jiki, naga kina da tsabta, kuma kin iya girki ma, amma dole zamu din ga shiga kitchen tare ki koyi wasu abubuwan.
Wannan fatar taki, so nake ta murje ta fi haka haske da kyau".
"Taɓ wallahi ba zan bleaching ba".
"Ni ma ba bleaching na ce ki yi ba, gyara za ayi, wannan gashin ma, ya ce ba kya son kitso, dole ya din ga shan gyara, ga iman nan, ita zata ja ragamar koya miki makeup"
"Ni gaskiya idan na yi wannan damɓare-damɓaren, fuskata ƙaiƙayi take yi, duk in ji ta ɗaure kamar ta tsohuwa".
Laila ta ce "To kar ki yi mana, kanki zaki yi wa, iyaka ya kawo wata matar mu shige masa gaba yayi wani auren, kuma dole ki koyi magana, ki daina yaɓawa mutane magana son ranki"
"Na iya magana, kawai sai an yi mini ba dai-dai ba, nake yaɓa maganar".
"Ke! Baki san komai ba game da rayuwa, shi kansa mijin naki, yadda ki ke yi masa magana, tun da ba sa'anki ba ne, ba haka ya dace ki din ga magana da shi ba, idan kin shirya zaman auren, sai ki bi instructions ɗin da zan din ga baki.
Abu na gaba dole ki ga maman Khadija".
Ruma ta yi ƙuri da ido tana kallon laila, wacecec kuma maman Khadija.
Kamar laila ta shiga ran rumaisa ta ce "Na san baki santa ba, amma zaki santa yanzu. Wannan ƙwailar da yake ce miki, a kankaro ki, kema ki shiga cikin sahun manyan mata".
Cikin zaƙuwa ruma ta ce "To ita maman khadijan me zata yi mini?" Dan a yanzu tana fatan su fito, a baya ne take zaton nono bashi da wani amfani a gareta, sai idan ta haihu za ta shayar, amma yadda ake gaya mata kalmar ƙwaila, yana ƙona mata rai.
Laila ta ɗora da cewa "Garin kunun sabayarta zan yi miki order, ki din ga amfani da shi kafin ya dawo, dan ni idan na saya, Canada ake tura mini shi, yana da daɗi, zai gyara miki fata da jikinki baki ɗaya, kuma ki ciko ki murmure sosai, idan kuma kin shirya cigaba da zama ana yi miki gori shikenan".
Ruma ta tuna iskancin da su Fauziyya suka din ga yi mata, wai a kalli ƙirjinta kamar plate, ga samha cikakkiyar mace, amma takawa ya aureta, ta gyara zama ta ce "To ita maman khadijan a ina take? Kuma yaushe zaki sai mini kokon nata".
Laila ta ce "Ni ban ce miki koko take sayarwa ba, garin kunun sabaya take sayarwa, amma ba a kano take ba, a zariya take, bayan federal palladan. Na daɗe ina harka da ita, kuma na haɗa mutane da ita sosai, na san ingancin kayanta. Zan yi waya da ita, a sayo, tunda tana tura kayanta ko ina, amma ba zan baki ba, sai na ga gwargwadon biyayyarki"
Rumaisa ta yi shiru tana kallonta, laila ta gama bayananta, rumaisa ba wani fahimta tayi ba, ita dai babban fatanta, a samo abun da laila ta faɗa na yin kunu, saboda ta sha ko ya fito ta huta gori.
(*INA UWAR GIDA DA AMARE, INA WANDA SUKA HAIHU, KO SUKA YI YAYE, INA MASU RAMA DA SU KE SON JIKINSU YA MURMURE SU YI ƘIBA, INA MASU YARA WANDA SUKE FAMA DA MATSALAR RASHIN GIRMA? SHIN KEMA MIJI NA YI MIKI GORI, KAMAR YADDA TAKAWA YAKE YI WA RUMAISA? SHIN KINA KUNYAR SHIGA CIKIN ƳAN UWANKI MATA, SABODA RASHIN NONO, KO KUWA ƊINKI NE BA YA ZANA A JIKINKI, SAI KIN HAƊA DA CIKO? RAMA CE TAYI MIKI YAWA, KO KUWA YAYE YA SANYA NONONKI YA ZUBE KAMAR BANA MACE BA. TO ALBISHIRINKU! KUKANKU YA ƘARE, HAKA ZALIKA KAKARKU TA YANKE SAƘA. MAMAN KHADIJAH TA SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYE, DA INGANTACCEN GARIN KUNUN SABAYARTA. BAYA CUTAR DA LAFIYA KO KAƊAN, ZAI GYARA MUKU JIKI, YA CIKO DA NONO, INA WANDA SUKA YI YAYE, KO SUKE SHIRIN YI, KU JARRABA WANNAN GARIN KUNU, ZAKU BAYAR DA LABARI, MAMAN KHADIJAH NA NAN A GARIN ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN, KO KU TUNTUƁETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA 08033411249*
Iman kuwa a sitting room ta iske jabir, ya wani hakimce yana danna wayarsa, tun da ta shigo ya kafeta da ido, kamar yadda ya saba. Ta nemi wuri ta zauna, tayi masa sbiru.
"Wai dan Allah iman me na yi miki ne? Meyasa ki ka tsane ni haka?"
Cikin mamaki ta ɗaga kai tana kallonsa, ganin yadda yake neman ya raina mata wayo, ya fi kowa sanin abun da ya sanya, ba ta yin sa, amma yake ta wani basarwa.
"Ke shikenan abu ba ya wucewa a wurinki ne?. Son ki nake yi da gaske, aurenki zan yi, magana ta riga ta yi nisa, na samu amincewar ammi, takawa kuma kan ya dawo ma wataƙila an riga an yi".
"Amincewata da ta mahaifiyarka ba ta da muhimmanci kenan?".
Yayi murmushi ya ce "Amincewar hajiya wani abu ne daban, ke kuma a kowane lokaci idan mun yi aure komai zai wuce, dan Allah ki daina taurin kai, ke kanki kin san ba ki da wani rufin asiri, da ya wuce amincewa aurena, idan ba haka ba, duk wanda suka zo a baya sun tafi, sun kasa ɗaukar kasada. Ni a nawa ganin zaɓe-zaɓe ba naki bane ba iman, kamata yayi ki gode mini, da na ce ni na ji na gani"
"Ko ba ka yi ɓoye-ɓoye ba, na san ni ba kowa bace ba, abun da ka ke son gaya mini kenan, amma kasancewata ba kowa ba, ba shi yake nufin zuciyata ba ta da ƴancin ta so ko ta ƙi wani abun ba, ina girmamaka a matsayin yayana, idan farincikin ammi in aureka shikenan, amma ni babu soyayya a raina".
Jabir ya ce "Haka ne, ammi ta yi iya ƙoƙarin ta a kanki, har keta billenta ta yi, ta nemi alfarmar ɗan ta ya aureki, amma ya ƙi hakan, dan yana ƙyamarki, na cancanci ki gode mini ne iman, ba ki ƙi ni ba a halin yanzu ba ki da zaɓi, aure shi ne mafitarki, idan ba haka ba kuwa wannan kyawun barazana ne a gareki"
Sannu a hankali jabir yake gasa mata munanan maganganu, amma ta yi iya ƙoƙarin ta, ta din ga haɗiyarsu, duk da yadda take ji, suna barazana ga zuciyarta.
Jin bugun zuciyarta ya fara ƙaruwa, kuma numfashinta ya fara sama-sama, ya sanya ta tashi ta koma ɗakinta.
Rumaisa na ta jin daɗi, tare da fatan, Allah ya sa laila da gaske take, za ta sai mata abun nan, Iman ta shigo, sai dai ba sai an gaya mata ba, ta san iman ɗin a cikin damuwa take.
Rumaisa ta yi shiru ba ta ce mata komai ba, ita ma ba ta ce mata ba, ta je kawai ta kwanta a kan gadonta.
Mintuna talatin ammi ta shigo, tana faɗin "Iman, ya ku ka yi da jabir ne, ba kya bani update?" Ta tarar da iman a kwance, kamar mai bacci.
Ammi ta ce "Iman ƴan kwanankin nan baccin nan ya fara yawa, duk in da ki ka samu sai bacci? Rumaisa ko ta gaya miki wani abu ne?".
Ruma ta ce "A'a ba ta ce mini komai ba".
Ammi ta ce "To shikenan"
Da daddare rumaisa ta ce A ɗakin iman za ta kwana, duk da ammi ta bata ɗaki, amma ta ce a wurin iman za ta kwana.
Cikin dare iman ta tashi ta yi salloli, sannan ta zauna ta ɗauki wayarta tana dubawa, rumaisa na kallonta, a haka bacci ya kwasheta.
Da safe rumaisa na baccin safe, laila ta shigo da system a hannunta, ta tashi rumaisa.
Ruma ta buɗe ido ta kalleta, "Kin manta hau zaki fara zuwa islamiyya ne? Tashi mijinki zai yi magana da ke"
Rumaisa ta kalleta ta ce "Da computer zan yi wayar?"
Laila ta dungurarwa da ruma computer a gabanta, tana kalla ta ga fuskar takawa.
Ta ce "Laaa video call a computer"
Yayi murmushi ya ce "Hi little mimi".
"Iyee daga zuwa turai har ka koma bature, irin...." Sai kuma ta kalli laila ta yi shiru.
Yayi murmushi ya ce "Ba ki tashi ba ne? Yau zaki fara zuwa islamiyya fa, ki tashi kiyi breakfast, ki shirya a kai ki"
Ruma ta yi miƙa ta ce "Shikenan weekends ma ba zan huta ba".
"Ki yi haƙuri, ina boy, bai tashi ba ko?"
"Eh, bacci yake shi da anty iman, kai har ka karya? Waye ya dafa muku abinci?"
"Har ɗaki aka kawo mana, na karya"
"To yaushe zaku fara taron?"
"Sai Allah ya kaimu anjima" ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mimi meyasa ki ka bani abun da zai sakani kuka?"
Jiki a sanyaye ta ce "Ba dan kayi kuka na baka ba, ni ba dare ba rana, abun ci mini rai yake, amma ba na ce maka kar ka tambayeni komai a kai ba, sai anjima, bari na ɗan ƙara rage bacci".
"Mimi tsaya ki ji".
"A'a gaskiya sai anjima" ta ture system ɗin ta kwanta.
Laila ta daki ƙafar ruma ta ce "Ke wace irin mashirirciya ce ne?" Ruma ta yamutsa fuska ta kalli ruman.
"Ya tafi wata ƙasar, kuna waya ki kashe? Babu wani abu mai jan hankali, ba rausaya murya ba karairaya, wai ce miki aka yi dan kika ƙanwar maza, ki din ga abu kamar namiji, you are not romantic at all, mijinki matashi ne, kuma kema kin san yana da masu son sa, ko dai ki gyara ko ki ga abun da ba kya so. Ki tashi ki yi wanka ki zo ki karya"
Ta ɗau system ɗin ta, ta bar ɗakin, rumaisa ta zumɓura baki sannan ta tashi.
Laila kuwa komawa tayi, tana jinjinawa takawa. "Takawa i salute your effort, Wannan matar taka, zan iya saka bulala in zaneta wataran, she's very stubborn, beside she's much more than how i expect, ba ta ji ga taurin kan tsiya".
Adam ya ce "Haba madam, duk ita kaɗai, ki yi ta haƙuri kema, halinku ne ya zo ɗaya shiyasa ba kwa jituwa, da ɗaya daga cikin ku na da haƙuri, zaku zauna lafiya, idan ku ka saba shikenan".
"Anya zan iya jurewa? Ba ta ji fa"
"Tuba muke, ayi haƙuri dai".
Rumaisa ta shirya cikin dogon hijjabi, hatta jakar islamiyya da litattafai adam ya sai mata komai, sidi ya ɗauke ta suka tafi makarantar.
Ya je ya gabatar da ita, mai makarantar ta ce ta san da zuwan rumaisa, aka kai ruma aji.
Mamki ne ya cika su kansu ƴan ajin, ganinta sanye da hijjabi irin na islamiyyar, suna mamakin kar dai matar aure ce.
Mai makarantar ta gabatar da rumaisa a wurin malamar da take ajin, zungu-zungui ta wuce ta je ta zauna, tana jin haushin kallon da suke yi mata.
Ajin duk manyan mata ne, dan da yawa sun haifeta, wasu kuma sun yi ƙanwa da ita sosai da sosai.
Aka yi lesson ɗin da za ayi a ka gama, har lokacin tashi ba ta kula kowa ba, sai da aka tashi suka din ga tambayarta ko matar aure ce ita, sai dai ta din ga bin su da ido, taƙi magana.
Sidi ya zo ya ɗauketa, amma ta ce masa ita ɗorayi zai kai ta wurin mama, ya ce ai ammi ba ta sani ba, ruma ta ce ba ruwansa, idan ba zai kaita ba, ya ajiyeta ta je ta hau napep.
Haka ya juya kan motar suka tafi ɗorayi.
A ƙofar gidan yara suka tsatstsaya suna kallon uwar motar da aka kawota a ciki, har da maƙwabciyarsu shamsiyya a leƙowa, tana ɗagowa ruma hannu.
Ruma ta ce 'Lallai matar nan, saboda ta ganni a mota, har da ɗago mini hannu, nan gaba a daidaita sahu zan din ga zuwa, in ga ko za samu masu kulani'.
Ta kalli sidi ta ce "Ba sai ka dawo ɗaukata ba, zamu yi waya da uncle Mahmud" ta shige cikin gida, bakinta ɗauke da sallama.
Gidan shiru, sai Aliyu da yake girki a kitchen.
Ya amsa mata ya ce "Koma bamu san da zuwanki ba, daga tafiyar mijinki jiya, yau kin fara yawo".
Ta ce "Ai da yake ba wurinka na zo ba ehe" ta shiga ɗakin mama, mai sunan baba yana kwance a kusa da mama, yana kallon tv.
Mama ta ce "Ke daga ina?".
"Makarantar matan aure wai ya saka aka kai ni, mai sunan baba ina kwana"
"Lafiya ƙalau"
Ba ta tsammaci wata magana sama da haka ba daga gare shi ba dama, dan haka ta zauna ta ce "Mama jiya ya tafi fa".
"Haka Aliyu ya ce mini, ina mai gidan nawa, ina ƴa ta iman, ki ka zo mini ke kaɗai?"
Mai sunan baba ɗan gyarawa yayi, yana jiran jin amsar da rumaisa zata bayar, a kan iman.
"Mama, ni in koma kenan?"
"Gaskiya dai, ba iman ba mai gidana, sai ke fitinanniya"
"Ai shikenan, gara na koma wurin ammi. Sabir yana nan ƙalau, iman kuma gari ba daɗi, tsoro nake ji kar ciwonta ma ya tashi"
A fuskar mai sunan baba ta ga razana, amma saboda azabar miskilanci yayi kamar bai san me suke faɗa ba.
Mama ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka, yara ƙanana da ku, har kusa abu ya dameku a rai".
"To ammi kin san familyn na su sai a hankali, sun takura mata da yawa, kin san ba ammi ce ta haifeta ba, sau kusan huɗu ana yinƙurin aurenta, wannan muguwar Mummyn tana hanawa, tana cewa mutane ba ta da uba, wai ammi ce garin tsince-tsincenta ta tsinto ta"
Cikin rashin fahimta mama ta ce "Ke kin sani a duhu, kina nufin ba ita ta haifi iman ba?"
"Hmm mama baki san badaƙalar da ke cikin gidan nan ba" nan ruma ta warware mata komai, sannan ta ce "Yanzu kuma wannan jabir ɗin ya ce son ta yake zai aureta, ammi tana ta murna, tun da shi ya san halin da ake ciki, ita kuma iman ba ta son shi sam, akwai wani wanda take so daban, amma ba za ta iya gayawa ammi ba, saboda ammi ta amince jabir ya nemi auren ta, ba wanda ta gayawa sai ni abun tausayi, kuma tsoro take ji kar wanda take so ɗin, ya ji labarin ga a halin da take ciki ya ce baya son ta".
Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, lafiyayyiyar yarinya mai mutunci kamar wannan, babu wanda zai ce ba ita ta haifeta ba, ni cikin yaran nan, da da wanda yake da ƙwari sosai, ai da an auro mini ita, to sai dai ba matar talaka ba ce, ni dai ina ƙaunar yarinyar nan fisabilillahi".
Cikin son sai ta yi pressing ɗin mai sunan baba rumanta sake cewa "Bari kawai ammi, kuma fa baki ga uban samarinta da suke sonta a haka ba, masu kuɗi ta ce ta daina soyayya, kawai ta zo ta fara son wani, amma taƙi gaya mini waye, ba ƙaramin son sa take yi ba. Amma wannan jabir ɗin, ya biyo kai tsaye ta wurin ammi, kuma yana daf da zuwa wurin mai girma wambai, shi kuma wannan wamban ba ɗaga ƙafa, dama yana ta yi wa ammi kashedi, ta aurar da ita ko ta mayar da ita in da ta ɗaukkota, cikin dare ina jin tana ta kuka".
Tsaki mai sunan baba ya yi ya tashi ya bar ɗakin, rumaisa kuwa ta yi wani guntun murmushi, ta tura saƙon yadda yakamata.
Aliyu ya shigo da plate ɗin indomie, ya ce "Me aka yi masa na ga ya fita yana tsaki?"
Mama ta ce "Shi wannan sai an yi masa wani abu ma?".
Ruma ta ce "Za mu ci indomie"
"Ai ko mayya ce ke, sai dai ki ci kan ki"
Tashi ta yi ta koma kusa da Aliyu, ta ce "Dan Allah zan ci".
"Wai ke da mijinki yake ajiye miki komai, ki zo ki saka mini rani".
Ruma ta ce "Allah sarki mijina, ya tafi ya barni, papa saurayina"
Aliyu ya ce "Ke fa baki da kunya ko?"
Flashing aka yi wa Aliyu, ta leƙa wayar ta ga an rubuta "Baby Hibba".
"Ohhh ni ƴa su, yaya Aliyu soyayya?"
Ya harareta, ya kira wayar "Hello my haidar".
"Kuɗin wayar sun ƙare ne ake