Showing 126001 words to 129000 words out of 199108 words

Chapter 43 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

834

wata ƴar ajinmu ta ce wai saɓo yayi Allah ya mayar da shi biri, da ya tuba, sai ya koma haka"

Takawa zai iya cewa rabonsa da dariya irin ta yau, tun kan aisha ta tafi Saudiyya, dan ruma labarai ta din ga bashi irin na ta'asar da ta din ga tafkawa.

A haka ya gama haɗa kayan, kusan tun da ya aureta bai taɓa bata cikakken lokaci kamar wannan ba. Ita abun da yayi mata daɗi a ranta kawai shi take aiwatarwa a rayuwarta.

Ya kammala haɗa akwatinsa, ya ajiyeta.

Ya ce "To budurwata, na gode da gudunmawa, sai Allah ya kaimu da safe, zamu je na yi wa ammi sallama, daga nan mu je gidan mai girma turaki sai mu tafi".

Ta ɗan yi shiru jiki babu ƙwari ta ce "Papa nan da wata shida, har ayi azumi da salla, kana can ko?"

Ya ce "In sha Allah".

"To wa zai din ga baka abinci, da shayin dare?".

"Saya zan din ga yi".

Ta gyaɗa kai ta ce "To shikenan, sai da safe".

"Allah ya tashe mu lafiya, ki kashe mini fitila" har ta kashe fitilar, ya ji kamar tana kuka.

"Mimi" ya kirata.

"Na'am" "Zo nan".

Ta koma gaban gadon ta ce "Gani".

Ya tashi zaune, ya zaunar da ita a kan cinyarsa ya taɓa fuskarta ya ji hawaye.

"Meyasa ki ke kuka?".

Cike da rashin wayo ta ce "Dan Allah idan ka je, kar ka yi aure, bana son kishiya, kuma bana son ka tafi".

Kawai ya kwashe da dariya ya ce "Ai fa dole nayi aure, tun da ni dai ba saƙago ne kamar ke ba. Ga rashin kunya da ki ke yi mini, daga taɓaki sai ihu da kururwa, ina sai dai ki yi haƙuri ".

"Amma dai ka san abun da ka yi mini bai dace ba ko? Ba kyau fa"

"To ai ba wanda zai gane, idan ba wannan maganannen bakin naki ne, zaki je ki faɗa ba"

Cikin damuwa ta ce "To idan ina yadda, ba zaka auri kowa ba, har da wannan samhar?".

Ya ce "Eh mana".

Ta ce "Taɓ! Wallahi na san Allah ya na kallona, kuma zai ƙonani, mama ta ce in din ga jin tsoron Allah a duk in da nake, idan ba ta ganina Allah yana kallona, kuma idan na lalace ban yi mata adalci ba. Ka yi auren ni dai ba zan iya ba, amma ban da samhar nan, dan na tsaneta" sosai hawaye yake kwarara a fuskar rumaisa, zai iya cewa tun da suka yi aure, duk bala'in da zai faru, sai dai tayi ta wulƙita ido, tana harare-harare, amma ƙarara weakness ɗim ta ya bayyana yau.

Kwantar da ita yayi a gefensa, sannan ya kwanta yana shafa kan ta ya ce "Let's make a memorable day, mu kwana tare. Amma dai zan yi shawara tun da kin ce ba kya son kishiya, idan kin canza halinki kin daina rashin ji, sai a fasa idan baki canza ba, samha zan auro. Ita ba zata din ga yi mini ihu ba, tun da tana so na".

Shiru ta yi masa, tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, to ta din ga yadda saboda ba ta san ya ƙara aure. Amma da ta tuna, idan yayi aure haka zai din ga wasa da samha, ita ma ya din ga kaita makaranta, su din ga zuwa cin abinci tare, ita ma ya din ga rungumeta kamar haka yana yi mata dariya, su din ga ball tare wataran kamar yadda suke yi.
A ranta ta ce bana son kishiya, amma ba zan ci amanar mama ba.

Bacci ne yayi awon gaba da ita, ba tare da ta gama tunanin ba. Adam kuwa ya rungumeta sosai yana shafa gashin ta.

"Am going to miss you mimi, am feeling like am leaving my priceless asset in Nigeria. A lokacin da mutane suke yi miki kallon mara kunya, wadda ba ta ji. Ni a lokacin nake hangowa amfanin ki, a cikin al'umma, kin zo da babbar fitila mai haska hanya a cikin rayuwata, duk da kina bani wahala, am still owing you a debt" ya ƙarasa maganar a hankali tamkar tana jin sa, ya sumbaci goshin ta.

Addu'a ya cigaba da yi, na Allah ya bashi lafiya, kafin ya dawo, dan wannan wani babban sirri ne mai nauyin da yake jin, ba zai iya sanarwa da wani shi ba.

Ya sake ƙanƙameta, yana tuna farkon haɗuwarsu, da abubuwan da ta yi masa zuwa yanzu.

Da safe tare suka karya, sai dai ta ƙi sakin jiki ta ci, sai kallonsa da take yi, tayi masa zuruuu da ido.
"Kalli gabanki, zan ƙware".

"Ni ba kallonka nake yi ba, gara ka tafi in huta, a daina takura mini"

"To mutumin da zai je yayi sabon aure fill, cikakkiyar mace ya rabu da ƙwaila, sai me dan ƙwaila ta ce ba ruwanta da shi?"

Ta haɗe rai ta ce "Ba ruwanka da ƙirjina, ka daina ce mini ƙwaila, kuma in sha Allah sai sun fito mini"

Ya sakata a gaba ya din ga dariya, ita kuma ta haɗe rai tana tura baki.

Bayan sun gama, da ita ta fito masa da akwatinsa, daga baya ta ce ba za ta ɗauka ba, tun da yake ce mata ƙwaila.

A ƙasa ya ce wa su baba uwani, idan ya tafi, zasu tattara su koma can gida gaba ɗaya, ba zai bar rumaisa a gida ita kaɗai ba.

Ƙarfe tara na safe, suka isa gidan ammi, ana ta yi wa takawa fatan alkhairi, abun mamaki sai ga Mummy ma a sashin Ammi, wai ta zo yi wa takawa Allah ya tsare, tun da bai je yi mata sallama ba.

Tana yi tana satar kallon ruma, ita kuwa ruma ba ta tata take yi ba, abun da ya dameta daban.

A gidan adam ya sauya kayansa zuwa shigar sarauta, ba kunya rumaisa ta ce "Masha Allah, saurayina ka yi kyau"

Yayi murmushi ya miƙa mata hannu ya ce "Ban mu kashe" ta bashi nata suka tafa.

Su Fauziyya da basu saba ganin taɓarar da rumaisa take yi, ko a gaban waye ba in dai suna tare da takawa, suka din ga ƙananan maganganu.
Laila kuwa kallon su kawai take yi, tana observing ɗin rumaisa.

Harabar gidan suka fito, hannunta na cikin na takawa, in da wasu za su raka adam gidan turaki.

Sai dai ya ga Mahmud riƙe da mukulli a tsaye a jikin motar da za a ja shi a ciki, nan aka tsaya kallon kallo.

Rumaisa a hankali ta ce "Papa" ya kalleta.

Tayi ƙasa da murya ta ce "Dan Allah kar ka watsa mini ƙasa a ido, na yi iya ƙoƙari, kan a kawo wannan mataki, dan Allah kar ka watsa mini ƙasa a ido, ko dan ammi ta ji daɗi, sau ɗaya ta ganku tare, shi ya yarda ya ja ka a mota, dan Allah papa Please, kar ka yi wani abu da zaka sa maƙiya su ji daɗi"

Kallonta yake yadda take yi masa magiya, Mummy kuwa kanta yayi bala'in ɗaurewa, ta tsaya ta ga ikon Allah, kawai ta ga takawa ya ja rumaisa sun shiga motar, Mahmud ya karɓi sabir, ya saka shi a gaban motar, ya shiga ya kunna.

Motar da ammi suka hau ita da laila, kuka ammi take, tana "Laila, kin ga Mahmud da Adam tare a wuri ɗaya, Allah na gode maka, Allah ka ƙara haɗa mini kan iyalina".

Laila ta ce "Is ok my dear ma, ai dama na sha gaya miki, addu'a da ki ke yi, Allah yana karɓa, lokaci ne kawai".

Rumaisa a mota kuwa, sai aikin rarrashi takawa yake yi, ta kalleshi ta ce "Papa, na gode da baka watsa mini ƙasa a ido ba, daddy na gode sosai da sosai, da ka kasance cikin masu yi wa papa rakiya, ammi za ta ji daɗi sosai "

Mahmud ya ce "Daughter, ba abun da ba zan iya yi miki ba, ba sai kin gode ba".

Ruma ta ce "To ba zaku yi magana ba? Ku gaisa"

Fuskar Adam ta kalla, yadda ya haɗe rai, ta ɗan girgiza kai ta ce "Papa, na ajiye maka saƙo a akwatinka, duk abun da ka gani, idan ka je, kar sake ka tambayeni komai a kai, kuma kar ka saka wani ya tambaye ni, har sai Allah ya dawo da kai lafiya".

Ya ce "Menene abun?"

"Idan ka je zaka gani"

Shiru ya ɗan yi yana tunani, a dai-dai lokacin da suka shiga gidan turaki, ana ta bushe-bushe, turaki yana daf da fitowa.

Takawa ya saukko daga motar, bai iya tsayawa gaisawa da kowa ba, duk da ga su jabir da Jamil, da sauran manyan mutane, sai ƙoƙarin rarrashin rumaisa da yake yi a gaban mutane.

Kuka take yi sosai, yayi ƙasa da murya ya ce "Ki na so ni ma na yi kuka ne?"

Ta girgiza masa kai. "Haba budurwata, a haka zamu rabu? Saurayi da budurwa fa ba haka suke yi ba, ki daina kuka, zamu din ga waya, Allah ya tsare mini ku, ya kula da ku".

Su Fauziyya tuni suka dira a gidan, suka wuce wurin Samha, suna bata labarin, abubuwan da suka faru a tsakanin ruma da takawa yau, wanda hakan ba ƙaramin jefata ya yi cikin matsanancin tashin hankali yayi ba, baba uwani ta yaudareta, da ba ta sanar da ita alaƙar da ke tsakanin takawa da ruma tayi ƙarfi haka ba.

Ta window ta hango takawa yana sharewa rumaisa hawaye, ya danƙa hannunta cikin na laila, ya nufi Mahmud da yake tsaye da Sabir a hannunsa, ya shafa kan sabir yayi masa kiss a goshi, ya nufi wata motar.

Da sauri Samha ta koma ɗakinta, ƙafarta har rawa take saboda tashin hankali, ta kira baba uwani a waya, ta rufe ta da bala'i.

Baaba uwani da ta rasa in da zata saka kanta, saboda ta ko ina, matsi da kyara take fuskanta ta ce "Ba laifina bane ba fa, Hajiya Jamila ce ta ce kar na sake sanar da ke komai, sai abun da ta yi mini izini".

"What? Mummyn? Ni za ta ci amana!? Kuma ta rufe ni ba ta gaya mini ba?" Sakin wayar ta yi tare da yin ashar.

"Lallai matar nan baki san wuta ba, kuma kin takata a yanzu, zan yi maganinki, da ni ki ke zancen".

Mummy ma na can ƙarshen kiɗima ta shigeta, ganin Mahmud da kansa, ya ja adam a mota, lallai tsuguno ba ta ƙare ba.

Ayshercool.
08081012143f
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Rumaisa na nan tsaye tana kuka, tawagar ta tashi, suka yi gaba.

Ammi sai rarrashin rumaisa take yi, laila ta ce "Wai ke ba kya jin kunya ne, wa ki ka fi iya soyayya, soyayyar da ko iya ta baki yi ba, ko Kunyar ammi ba kya ji".

Ammi ta ce "Babu ruwanki, mu ba ma wata kunyar sirikai".

Su Jamil suka ƙaraso, suka gaida Ammi, sai dai ammi ba ta san, meke faruwa ta takawa da su Jamil ba, dan haka normally ta amsa musu, kamar yadda suka saba.

Jabir ya dubi iman ya ce "Iman ko zaki zo in mayar da ke a mota ta?"

Ammi ta ce "Kar ka damu, kwa haɗu a gida, laila mu shiga ciki mu gaisa da mutanen gidan, tun da matafiya sun tafi"

Suka shiga wurin mama, sai wani cika take tana batsewa, sai dai duk da haka, ta shiga taitayinta ganin ammi tare da laila, dan kar ta san kar.

Ta dubi laila ta ce "Ashe kin zo garin?"

Cikin taƙama laila ta ce "Yeah, almost 2days"

"Yayi sannu da zuwa, wannan kamar matar takawa ko? Meya sameta take kuka?".

Laila ta ce "Abun mata da miji sai Allah, ga yarinta a kan ta, dole tayi kuka".

Mama ta ce "Mhmmm Allah sarki Aisha, har ta kai adam ya manta da ita, ya cigaba da rayuwarsa?"

Laila sarai ta gane magana matar turaki take nema, dan haka ta ce "Aka rasa iyaye ma a dangana, a cigaba da rayuwa ayi musu addu'a, rasuwar fulani ai mu aka yi wa, kuma babu yadda za ayi mu manta da ita, kuma takawa yana nan yana aiki tuƙuru a kan neman hakkinta. Kuma dan ya rasata baya nufin ba zai sake farinciki a rayuwarsa, da ya rasa soyayyar mahaifi ma bai mutu ba, dan haka dan Allah a daina kawo wannan maganar"

Laila ta miƙe ta ce "Ammi mu tafi"

Babu wanda ya kuma magana har suka fice.

Zee da tana falon aka yi komai a gabanta, shiru ta yi, dan kaɗan da aikin laila ka yi mata rashin kunya, ta kwaɗeka, saboda masifarta.

Takawa suna airport, ya kira iman, ya ce ta haɗa shi da rumaisa, ta miƙawa ruma wayar, sai dai ta yi shiru.

"Hello, mimi"

"Na'am"

"Ki yi mini Addu'a, nan da mintuna talatin jirginmu zai tashi"

"To Allah ya kai ku lafiya"

"Amma dai kin daina kukan ko?"

Murya can ƙasa ta ce "Na daina"

"Yauwwa buruwar mijinta, da kun koma gida, ki samu ki ɗan yi bacci, jiya bamu samu isasshen bacci ba. Sannan a gida akwai key ɗin wardrobe ɗina, na bar miki kuɗi a ciki, sannan zan din ga turawa laila kuɗi ko zaki buƙaci wani abun".

Ruma ta ce "To" daga haka ta bawa iman wayarta.

Su Fauziyya kuwa bayan sun gama kai wa samha rahoto, silalewa suka yi, suka bar gidan, suka bar ta da tension.

Zee ta tarar da Samha a zaune, abun duniya ya isheta, tamkar ta ɗora hannu a ka, ta fasa ihu saboda baƙin ciki, dan me Mummy za ta ce kar baba uwani ta din ga gaya mata abubuwa da suke faruwa a gidan Adam, sai wanda ta bayar da umarni?.

"Samha!" Zainab ta kira sunanta a karo na uku.

Samha ta ɗaga kai ta kalleta, "Sai magana nake kin yi shiru".

Ɗan guntun tsaki ta ja ta ce "Menene?"

"Labari ne mara daɗi bayan wanda su Fauziyya suka gaya miki. Laila ta dawo, sannan alamu sun nuna cewa yarinyar nan zaman lafiya suke yi da mijinta, kin ga zancen su Fauziyya ya tabatta".

Samha ta ce "Babar su Fauziyya ce banbar munafuka, wato hajiya jamila"

Cikin mamaki ta ce "Uwar ɗakin naki?"

"Zainab saboda tsabar matar nan ta mayar da ni ƴar iska, mun bawa wannan uwanin aikin, kawo rahoto a kan abubuwan da suke faruwa a gidan adam, ni burina auren adam, ita kuma hana shi sarauta. Ni yayi sarauta ko kar ya yi bai dameni ba, ni shi nake so. Meye haɗin aikinta da nawa, da za ta ce wa baba uwan wai kar ta din ga kawo mini bayanin abin da yake faruwa sai wanda ta yi mata umarni, ni zata mayar shashasha, na shanya baki na san na yi aiki tuƙuru a kansu, amma na yi sakacin da har shaƙuwa ta shiga tsakaninsu. To bari a gama watsewa, na je har gida na sameta".

"Ki sameta ki yi mata me ne? Ke kin san idan ki ka ce zaki yi fito na fito da ita, tafi ƙarfinki. Babarki ce a hatsabibanci, ki cigaba da abubuwan ki ba tare da ta sani ba, ki bita a haka, kar kuma sauya mata fuska".

"Ba zan iya jurewa bane zee, kawai ji nake idan ban zageta ba zan huce ba".

"Aikuwa ya zama dole ki danne, ko ta yi miki wani mummunan sharrin".

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Zainab na wuce yadda ki ke tunani, tun da ta ɓata nawa aikin, sai dai mu yi biyu babu, kuma son Adam yanzu na fara, sai na ga ƙwal uwar daka".

Rumaisa kuwa wuni tayi baccin dole, saboda koke-koken da tayi, kanta ya fara ciwo, dan haka tayi ta kwanciya tana bacci, surutun ma ya gagareta, ba ta taɓa zaton akwai wani abu da zai tsaya mata ya hanata walwala ba.

***

Mummy kuwa ta titsiye Mahmud a ɗaki, ta na tayi masa bala'i a ka, kamar ta ari baki, saboda tsan-tsar ɓacin rai da damuwa.

"Kai yanzu Mahmud dan Allah ba ka ji kunyar abun da ka aikata ba, matar da ba ƙaunarka take yi ba, ta fifita ƴaƴanta a kan ka, kai ka san ba ƙaunarmu suke yi ba, daga ita har ɗanta, amma dan abun kunya, kana jiran sarauta yana jira, dan me zaka tuƙa shi a mota, direbansa ne kai, ko saboda rashin sanin ciwon kan ka ne? Ko kuma dan ka nuna mini iyakata, ka nuna mini bani na haifeka ba?"

Yayi mata shiru yaƙi magana, hakan ya ƙara tunzurata, ta dungure masa kai da ƙarfi, amma cikin baƙin taurin kai, ko gezau bai yi ba.

Sai da ta zuciya ta yi hanyar fita, sannan ta tsinkayo muryarsa ya ce "Tambayar da rumaisa ta yi mini, ta jefa ni cikin damuwa, da taradaddin neman amsar, sai dai ban sani ba ko zaki tayani samo amsar?" Cak ta tsaya, ta waiwayo tana kallonsa.

Bai ɗago ba ya cigaba da cewa, bayan buɗar idona a hannunki, kin ginani a kan cewa, a duniya bani da babban maƙiyin da ya wuce giwa da kuma ɗan uwana Adam.

Na ginu a kan haka, a lokacin da na san gaskiyar wacece mahaifiyata kuma, sai ki ka nuna mini bata sona ne, ta zaɓi waɗancan ƴaƴan nata a kaina, shiyasa ke ki ka karɓeni ki ka riƙeni, kuma kin ce baki da wani buri da ya wuce na gaji kujerar babanmu, marigayi galadima. Na hau kan tarbiyarki da hanyar da ki ka ɗorani a kai, na sawa zuciyata tabbas mahaifiyata ba ta ƙaunata. Sai dai ko da rumaisa ta tambaye ni sau ɗaya me giwa ta taɓa yi mini, a zahiri da ya nuna bata ƙaunata? Sai kunya ta rufeni, a lokacin da na tuna kin yi mini shamaki da zuwa in da take, kuma kin koyar da ni ƙiyayyar ɗan uwana, ƙiyayyar da ta yi tasiri a tsakanin mu. A lokacin da rumaisa ta tunatar da ni, na sanya mahaifiyata kuka a lokacin da ta nemi alfarmata, ƙarƙashin umarninki, na ƙi yi mata, sai na ji a duniya bani da wani amfani.

Mummy ba ina nufin juya miki baya ba, bani da wata a duniya bayan ke, amma giwa na da hakkin haihuwata da ta yi, ba zan taɓa bari ki muzanta ba, sai dai ina fatan ganin tabattacen haɗin kai a cikin gidanmu, auro rumaisa cikin iyalinmu alkhairi ne mummy. Ban aikata hakan dan muzanta miki ba". Ya ƙarasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login