Showing 12001 words to 15000 words out of 199108 words

Chapter 5 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

784

komai".

"Ko kin ga na ƙara girma ne?"

Mama ta ce "Girman ne dai yake tinkaro ki".

"A ina?"

"Ba ko ina, yi kwanciyarki".

Rumaisa ta yi miƙa, ta shige cikin net ɗin ta.

Cikin hanzari mama ta ce "Ke meye haka?"

Rumaisa ta yi zumbur ta tashi ta ce "Mama a ina?"

"Meye haka, daga ke sai wando da vest, ba zaki ɗaura zani ko ki saka underwear ba?"

"Kaii mama, kin tsorata ni wallahi, zafi fa nake ji"

"To kuma sai ki kwana tsirara dan shirme, tashi ki saka zani ko kunya ba kya ji sai yayyenki sun shigo sun ganki a haka, ba kya jin kunya ma"

"To mama ba yayyena bane ba"

Haushi ne ya kama mama ta ce "Ke ubanki, kin tashi ko sai na zo?" Ba dan ta so ba, ta tashi ta ɗaura zani ta nemi wuri ta kwanta.

Washegari da safe bayan tafiyar runaisa makaranta, suka yi waya da Abubakar, ya tabattarwa da mama cewa da azahar zai zo gida.

Mama ta ji daɗin zuwan Abubakar sosai da sosai, saboda ya fi mai sunan baba sauƙin kai, da sauƙin fahimta. Bayan ya ci abinci ya huta, mama ta gabatar wa da Abubakar halin da ake ciki na batun son auran rumaisa.

Abubakar ya nisa ya ce "To mama ai babu wani laifi a ciki, wataƙila a dalilin auren ki ga ta nutsu, ni kaina ba wai ina son a aurar da ita ba ne, amma bamu san mai Allah ya ɓoye a lamarin ba.
Dan haka mama ki yi ta Addu'a tare da istikhara, sannan kuma a nemi amincewar ta, idan ta yarda shikenan"

"Nima abun da nake tunani kenan, bana son takurawa a lamarin nan, mussaman yadda ake surutu a kan ta, kuma ina jin nauyin matar sosai. Amma dan Allah ka shawo kan ɗan uwanka, dan shi ba ya son sabgar".

Abubakar ya ce "Karki damu mama, ki rabu da shi ki yi ta addu'a, idan da alkhairi Allah ya tabbatar mana"

Mama ta amsa da Amin.

Ammi ta cigaba da addu'a, tare da tsumayin jiran amsar da mama za ta bata.

***
Hajiya Lubabatu ce ta kawo wa mummy ziyara har gida, in da suka ƙule a ɗaki suna tattaunawa tare da shirya mugunta kamar yadda suka saba.

Hajiya Lubabatu ta ce "Wai dan Allah jamila zuwa yaushe zaki samo maganin nan mu koma wurin malamin nan?"

Mummy ta ce "Rabu da ni kawai, na saka wannan shashashar matar, ta kasa samo mini ranar a gabana aka fito da maganin aka yi masa amfani da shi, amma na kasa ɗaukowa saboda suna wurin".

"To yanzu shikenan kin fasa cimma ƙudurin birkita shin? Tun da dai malam ya ce aikin da kika buƙata ba zai yiwu ba sai an samu maganin da ake yi masa amfani da shi"

"Ba fasawa na yi ba, yanzu dai kan wani abun na mayar da hankalina"

"Wane abu kenan?"

"Yarinyar da ta zo da ɗansa ce, Mahmud ya ce mini ya ganta a gidan nan, tana zuwa yarinyar ce da bakinta ta gaya masa, kuma har shi adam ɗin ya ce kar a bari ta sake zuwa, idan da gaskiya mai zai saka ya ce kar a bari ta sake shigowa gidan nan? Kuma ba wannan ba kin san meya fi bani mamaki?"

"Sai kin faɗa"

Mummy ta gyara zama ta ce "Wai yarinyar yarinya ce ƙarama, ba babba ba ce ba, tayaya ƙaramar yarinya za ta kuɓuto da jariri, kuma ace an hanata zuwa gidan nan, ni fa ina tantama idan ɗan nan ma da gaske ɗan sa ne, da ƙyar idan ba wata ƙulalliyar suka shirya ba, na ji haushin rashin sanin yarinyar tana zuwa gidan nan tun a baya, da na san yadda zan na haɗu da yarinyar nan"

Hajiya Lubabatu ta ce "Kaii jamila, to ki yi mata me? Me za ta yi miki?"

"Ahh in samu bayanai mana, yadda zan kar giwa, in tona mata asiri".

"Ke ai ni lamarin giwar nan yana bani tsoro, hatsabibiya ce ta gaske"

Mummy ta ce "Ni zan gaya miki hatsabibiya ce ta gaske, shiyasa na yi alwashin kawo ƙarshenta"

Hajiya Lubabatu ta ce "Aikuwa sai mun cigaba da zagewa dan da alama ita ma a tsaye take, bari na tashi na tafi".

Suka yi sallama ta tafi.

Mama gaba ɗaya ta rasa ta ina za ta ɓullowa rumaisa balle ta yi mata bayani, ta san halin kayarta, idan ba ta so ba ana gabas tana yamma.

Abubakar ya samu suna tsaka da hira da shi da mai sunan baba, ya yi gyaran murya ya ce "Ni kuwa mama ce ta zo mini da wani zance"

Mai sunan baba ya ƙura masa ido, alamar yana sauraron sa.

"Mutanen da ta zo da yaronsu, suna son a basu aurenta"

"Kana goyon bayan hakan kenan?" Mai sunan baba ya katse shi.

Abubakar ya ce "Ba maganar ina goyon bayan hakan bane, makomar jaririn nan za a duba"

"Ita kuma ta ta makomar fa, karatunta da sauransu, kawai sai a aureta dan ta je ta yi raino, ita ba ta da ƴanci kenan? Ni dama tun da naga ana ta yi mata ɗawainiya na san akwai wata buƙatar da za su zo da ita, kuma guda nawa rumaisan take da za ayi mata aure yanzu?"

"Sunna ne a addinance ko ka manta Sheikh? Early marriage is better than early fornication, ko an gaya maka wannan tsalle-tsallem da take yana nufin jikinta ba ya jin komai na girma? Bai kamata mu yi saurin yin adawa da lamarin mu yanke hukunci ba, Addu'a yakamata mu yi.
Na san ka na sane da yadda ake yi da ita a gari, da mu baki ɗaya, wanda bamu da damar hana mutane cigaba da yaɗa jita-jita wanda dole ya shafi rayuwarta.
Kuma batun karatunta bana tunanin wani abu ne da zai gagara, yanzu sai ka gama zaƙewar ita kuma ta ce tana so, mu yi mata fatan alkhairi, atleast za ta shiga gida mai daraja da muke sanya ran ya zame mata alkairi a rayuwa, kar mu rarrabawa mama hankali"

Har Abubakar ya yi ya gama, mai sunan baba bai kuma kulashi ba, dan shi sam baya goyon bayan lamarin.

Rumaisa tana shimfiɗa tana waƙe-waƙenta, mama ta kalleta ta ce "Idan kin gama shimfiɗar zan yi magana da ke"

"Innalillahi, Allah ya sa ba wani abun na yi ba"

"Ni dai na ce zan yi magana da ke"

Rumaisa ta ajiye abun shimfiɗar, ta tafi gaban mama ta zauna ta ce "Gaya mini kawai hankalina ya kwanta"

Mama ta ɗan yi shiru tana nazarin rumaisa, sannan ta numfasa ta ce "Ki na ji na ko?" Ta jinjina kai alamar eh.

"Waya muka yi da hajiya, kakar sabir"

Rumaisa ta yi murmushi ta ce "Hajiya ammi".

"Eh, ta zo mini da wata magana ne, da dole sai da yardarki abun zai yiwu".

"Ni kuma, menene to?".

"Rumaisa, ta ce tana son ki auri baban sabir, ɗanta adam"

"Eyeee wai wa? Ni ko wa?"

Mama ta ce "Da wa nake magana?"

Rumaisa ta ce "Taɓ Ubangiji Allah ya kiyaye, haka kurum duk ƙawayena ba ayi musu aure ba sai ni, sai ka ce a ƙauye, ba sai na yi tsawo na girma za ayi mini aure ba, sai ayi mini aure ina ƴar haka, to wallahi bana son shi, ba zan aure shi ba taɓ baki san wannan mutumin ba ne".

Mama ta ce "Wai meye haɗinki da shi ne me yayi miki?"

"Ni bana son shi ne, haka kurum idan aka yi mini aure na daina yawo yadda nake so, kuma wai fa komai ya ce sai na yi, to wallahi ni ba zai saka ni abu na yi ba, sai dai ya kasheni"

Mama ta ce "Yanzu dai a cewa hajiyarsa ba kya so kenan?"

Kai tsaye rumaisa ta ce "Eh"

"To shikenan, je ki kwanta sai da safe" rumaisa ta tafi wurin kwanciyarta, tana ta yatsine baki kamar takawan ne a gabanta.

Ita rumaisa jin abun ma ta yi kamar almara, ita banda a ƙauye ba ta taɓa ganin amarya yarinya ba, ko ta ƙauyen ma tafi ta girma, sai ita a wani ce za ayi mata aure, auren ma da maƙoyanta a fili ta ce "Taɓ Allah ya kiyaye, wallahi ba na son shi".

Mama ta ce "Ai kin gaya mini na ji ko"

"Au, na zata a zuciyata na yi maganar" har ta yi bacci tsaki take yi, da ganin an raina mata hankali.

Da safe ta gama shirin tafiya makaranta, ta saɓa jakarta ta fito tsakar gida, ta tarar da mai sunan baba a tsaye, ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata ya ce wuce mu je. Ba ta ce komai ba ta yi gaba ya bi bayanta.

Suna tafe a hanya ya ce mata "Mama ta yi miki wata magana ne?"

Rumaisa ta ce "Eh mana, wai aure za ta yi mini"

"Ke me ki ka ce mata?".

"Ni dai na ce mata bana son shi, ai ba a yi wa yara aure"

Mai sunan baba ya jinjina kai ya ce "Good, zan tsaya miki duk yadda za ayi kar ki yadda da batun auren nan, ki ce ba kya so kin ji abun da na gaya miki ko?" Ta gyaɗa kai alamar eh ya ce "Good, idan kuma ki ka amsa zaki ga yadda zan yi da ke" suka cigaba da tafiya.

Ammi ta ɗan fara tsorata da shirun da ta ji, dan har ga Allah tun da ta yanke shawarar ta ji abun ya shiga ranta sosai da sosai, gashi haryanzu mama ba ta ce komai ba, gashi ba ta son yawan takura musu da ta sake kiran waya.
Ko da ta yi wa adam zancen haryanzu gidansu rumaisa ba su ce mata komai ba ya ce "Ina ga basu amince ba, kawai ki ƙyalesu"

"A'a idan ka ga na ƙyale, to na ga ba yadda zan yi ne, ni lamarin ya shiga raina sosai, ina saka ran da alkhairi a ciki".

Adam a ransa ya ce Allah ya sa su ce a'a, dan shi har wata kunya yake ji idan ya tuna wai rumaisa za a aura masa.

Gidan mama kai ya rabu biyu, Aliyu yana cikin waɗanda suke murna da abun, dan dama shi yana shiri da takawa, yayin da mai sunan baba Abdalla da usman suma suka ce ba su yadda ba. Yasir da Huzaifa kuwa, ba su ce eh ba ba su ce a'a ba, yasir ya ce gara ta tattara a aurar da ita mu huta.
Huzaifa ya ce "Ni babban jin daɗina, gidan masu kuɗi ne, da wani ƙojalallen wahalallen ne wallahi ba zamu yadda ba, amma nan mu je mu ci kayan daɗi, wallahi dan ubanta sai ta yadda ba zata yi mini baƙin ciki ba"

Rumaisa ta ce "Oho muku, ni dai bana son shi, kome za ayi".

Yasir ya ce "Ba ke ki ke son mai kuɗi mai kyau ba, gashi ya zo ki ce ba kya so, ke kin san menene son ma?"

Ta yi farat ta ce "Na sani mana, yanzu ba na ji ina son ku ba, ina son zama a gidan nan ba, ai shine son"

Huzaifa ya ce "Ji shashasha mara kan gado"

Abubakar ya ce "Ƙanwata, zo nan ki ji wata magana"

Rumaisa ta koma wurin yaya Abubakar ta zauna. Ya dubeta ya ce "Dan rumana ki girma mana, ki daina biyewa su Yasir, shi lamarin rayuwa Addu'a ake yi, Allah ya zaɓa mafi alkhairi"

Mai sunan baba ya fito ya ce "Ke tashi ki bar nan wurin, ta ce ba ta so, dole sai ka tursasata ta amsa ne?"

Abu ya nemi ya zama faɗa, sai da mama ta shiga tsakani.

Kasa jurewa Ammi ta yi, ta kira mama a waya take tambayarta yaya.

Mama ta ce "To, ni dan ta ni babu matsala, tun da kullum Addu'a da fatan alkhairi ka ke yi wa yaro, sai dai yayyenta wasu sun ƙi yadda, ita kanta ƴar ta ki ta ce ba ta so, mai sunan baba kuma ya goya mata baya".

Mama ta ce "Subhanallah, lamari bai yi daɗi ba, to shikenan ba damuwa"
Ammi har ta kashe wayar ta ji ta kasa jurewa.

Ta cewa Iman "Idan an idar da sallar magariba, ki shirya zaki rakani unguwa"

Iman ta amsa da to, ammi ta kira takawa a waya, ta ce masa idan an idar da sallar magariba ya zo zai kaita unguwa, ya amsa mata da to.

Mamaki ne ya kama takawa, da Ammi ta sanar masa da cewa gidansu rumaisa zasu je, ya fara tunanin mai zai saka ta ce su je gidan ba tsammani haka?
Ya din ga addu'a Allah ya sa ammi ba yarfa shi za ta yi ba saboda yarinyar nan.

Rumaisa kuwa ta fita sayen maganin sauro, daga zuwa soro ta ɗau keken Huzaifa ta tafi da shi sayen maganin sauron, shagon da za ta sayo ɗin a farkon layinsu yake, amma saboda tsabar neman magana ta ɗau keke.

Ta shiga gida ba ko sallama ta fara da "Waye ya ajiye mini mota a wurin da zan yi parking ɗin kekena, saboda an rainani".

Huzaifa ya ce "Uban wa ya saka ki ɗaukar mini keke, ban hanaki ɗaukar mini keken nan ba?"

"Huzaifa kana da damuwa, wannan kwaraɓaɓɓen keken kamar wani mota, ka kwantar da hankalinka, zan saya maka mota wataran".

Dalla wuce ki bani wuri, daga tsakar gida ta zauna ta ce "Mama ga maganin sauronki, canjin kuma na sayo coc zan sha, idan yaya usy ya dawo sai ya baki"

Ta ji shiru mama ba ta amsa mata ba, ta ware murya ta sake cewa "Mama ga aiken, canjin na sai coc".

"Ni zan biyoki tsakar gidan na karɓi aiken kenan?"

"A'a, zan ajiye miki a kan window, idan kin huce zan shigo ɗakin, na san sai kin yi mini faɗa na kashe miki canji, kuma ba laifina bane raina ne ya biya ta ɗau sanyi"

Mama ta ce "Zan kama ki ne"

Rumaisa ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Mama da wasa nake miki, kwata na faɗa da keken, bari na ɗauraye ƙafata na shigo".

Sai kuma ta ɗaga hanci sama ta ce "Hmmm warin turaren baban sabir nake ji".

Huzaifa ya ce "Malama ki nutsu, wane irin turarene mai wari kuma?"

"Kai yasin turarensa ba daɗi, tayar mini da zuciya yake"

Daga ɗaki mama ta ce "Idan kin gama tsokanar tawa ki zo kin yi baƙi".

"Baƙi da daddaren nan kuma wurina suka zo? Anya wannan baƙin alkhairi ne da daddare? Ai sai ace bani da gaskiya" ta je ƙofar ɗakin mama tana leƙewa, ta ga Adam da ammi sai iman.

"Kaii ammi ke ce da daddare, Innalillahi amma baku ji me nake cewa ba ko?"

Ammi ta ce "Bamu ji komai ba, ance ba a sonmu ban ga ta zama ba, na ce bari na zo ƙafa da ƙafa".

Rumaisa ta shigo ta zauna daga wajen bakin ƙofa ta ce "Ammi ina wuni?"

"Lafiya ƙalau maman sabir, kina lafiya?"

"Lafiya ƙalau ammi, iman ya kike ina sabir?"

Iman ta yi murmushi ta ce "Yana gida, yana gaisheki".

Ammi ta ce "Rumaisa, yau gani ga ki ga baban sabir, ki gaya mini meyasa ba kya son sa? Gaya mini abun da ya yi miki?"

Ruma ta kalleshi ta ce "hmm mama ki rabu da shi kawai, ni dai kawai bana son sa"

"Ai ba a ƙiyayya babu dalili rumaisa, gaya mini meya haɗaku?"

Rumaisa ta ce "Ammi kina ganin hantarata yake yi, yayi ta hararata"

Adam kuwa takaici ne ya ishe shi, kamar shi, wai ake lallaɓa wannan ƙwailar yarinya wai ta aure shi, wanda da shi mai kule-kulen ƴan mata ne, da bai san iya adadin ƴan matansa ba.

Ammi ta ce "Rumaisa, bani da nufin cutar da ke, har ga Allah ina matuƙar ƙaunarki, ba zan so abun da zai cutar da ke ba. Daga yanzu zuwa kowane lokaci magabata zasu fara yi wa adam maganar aure, bana son a bashi matar da zata wahalar da sabir kamar yadda mahaifiyar sa ta fuskanta.
Kin ga aisha ina da alaƙa da ita, itakaɗai mahaifiyarta ta haifa ta rasu, ta sha wahala sosai a wurin matar uba, mahaifinta yana basarake amma ta kwana ba ta ci abinci ba. A kulle ƙofa ta wuni a haraba, banda duka da cin mutumci, ta sha wahala a rayuwa sosai da sosai, zaki so sabir ya fuskanci irin haka?"

"To Ammi ba sai ki riƙe shi ba"

"Rumaisa dole wataran zan bar duniya, ko bana so dole sabir ya koma hannun mahaifinsa, ba ni zaki duba ba, ba baban sabir ba ɗan ki. Zaki samu cikakkiyar damar kula da shi sosai ya zama naki"

Wayar iman ta fara ringing, dan haka ta tashi ta fita waje amsawa.

Rumaisa ta yi shiru tana tunani, ammi ta ce "Ba zan takura miki ba rumaisa, ba zan so ayi miki auren dole ba, idan baki amince ba shikenan, ba zan takura miki ba, na so dai ki zama ɗaya daga cikin iyalaina ne, ba takuraki zan yi ba rumaisa".

Shiru ruma ta yi, ba ta ce komai ba.

Har ammi ta fidda ran rumaisa za ta yi magana, dan takawa ya fara ƙulewa.

Mama ta ce "Rumaisa ke fa ake jira ki yi magana".

"Mama tsoro nake ji, ƴan ajinmu sun ce maza mugwaye ne, wai ba ƴan goyo bane, tsoro nake ji ni yarinya ce".

Ammi ta yi murmushi ta ce "Ya danganta, kuma ba haka abun yake ba, ke kin yadda ba ƴan goyon bane? Ke yanzu ba ƙanwar maza ba ce, kalli yadda suke kula da ke fa, komai yi miki suke, da kin motsa damuwarsu a kanki take, da ba ƴan goyo bane, ai ba za su yi miki haka ba, ki yanke hukunci da abun da yake ranki, ba surutun mutane ba".

"Ammi na amince!"

Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login