Showing 9001 words to 12000 words out of 199108 words

Chapter 4 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

786

ce maganin damuwowinka, ko ba ka aureta ba kar ka rabata da ɗanta" a razane ya sake farkawa yana wani irin gumi, ƙirjinsa na bugawa da sauri.

Da sauri ya saukko daga kan gadon, ya buɗe tagar ɗakinsa, ya zubawa harabar gidan ido, ya tuna abubuwa da dama da suka wakana, shekarun da suka gabata.
Ganin bashi da wata mafita, ya sanya ya shiga banɗaki yayi alwala ya fito ya ɗau alƙur'ani.

Ɓangaren ammi ma tsayuwar dare take yi, tana kaiwa Allah kukanta a kan iyalanta, dan addu'arta bayan nemawa kanta gafarar ubangiji, ƴaƴanta kawai take yi addu'a.
Ta haɗa da roƙon Allah ya ɗorata a kan iyayen rumaisa su yarda da auren nan da take son haɗawa, dan a jikinta take jin rumaisa alkairi ce ga ɗan ta.

Yau jikin mama da ɗan sauƙi, ruma sai shirin tafiya tahfiz take yi, su Huzaifa sun goge mata uniform ɗin, ta cika tsakar gida da waƙe-waƙe kamar an yi mata bushara da wani abu mai muhimmanci.

"Ruma ki rufe mini baki da waƙe-waƙen nan, ki yawaita tasbihi, wannan surutan da waƙe-waƙen ba in da za su kai ki"

"Mama ina tasbihin nan fa".

"A'a, ni wasu lokutan ina raina ibadar da ki ke yi, ki na da ƙarancin ibada rumaisa, idan kina cikin farinciki ki yawaita ambaton Allah, dan wasu lokutan idan kana cikin matsala ko damuwa sai addu'a ma ta gagareka, ki din ga yawaita ambaton Allah ba waƙa ba"

Cikin mamaki rumaisa ta ce "Mama yanzu sai damuwa ta yi wa mutum yawa ya kasa ambaton Allah, to ko a hannun 'yan bindiga, addu'a na yi ta yi musu, Allah ya ƙwatoni, amma ni mai zai dami mutum ya kasa addu'a "

Mama ta yi murmushi ta ce "Rumaisa kenan, lokaci yana nan zaki gane abun da nake nufi".

"Au fata ki ke yi mini" tayi maganar cikin tura baki.

"Ya za ayi in yi miki fata, faɗa nake yi miki, ki ƙara nutsuwa".

"To hajiya mama, yanzu dai ki bani kuɗin makaranta zan tafi"

"Ke idan babu kuɗin makarantar ba zaki ba kenan?" Huzaifa ya tambayeta yana ƙoƙarin ɗaukar agogonsa.

"Ni fa ba na son katsalandan ina ruwanka"

"Ni kar ku yi mini faɗa, ki ɗauka ki tafi".

Rumaisa ta ɗau kuɗin, ta fice tana hararar Huzaifa.

Ammi ta din ga lissafin ta ina za ta ɓullowa wannan al'amari, turaki zata fara gayawa, ko kuwa ta fara nemo iznin majaifiyar rumaisa tukuna?
Daga bisani ta yanke za ta fara tuntubar ɓangaren rumaisa, idan sun amince shikenan, sai dai tana fatan su amince ɗin ma.

Takawa har garin Allah ya waye bai samu ya rintsa ba, abubuwa da yawa sun dame shi, kasancewar yau weekends ne, ya sanya karyawa ma a ɗakinsa yayi bai fita ko ina ba. Dama shi ba wasu abokai ne da shi ba, daga abokan aikinsa sai su jabir.

Wayarsa ta cika masa kunne, duk da gandar da yake ji, da ya gaji da jin rurin wayar, sai da ya tashi ya ɗauko wayar ya duba.
Kakin rundur ƴan sanda ne cp baba habu yake kiransa, adam ya ɗaga wayar tare da yin sallama.
Cp ya amsa masa suka gaisa sannan ya ɗora da cewa "Adam kana garin nan kuwa? Wai ba zaka fito ka yi magana a kan abun da yake faruwa ba, sai sharri ake yi maka kala-kala kai kuma ka ƙi magana"

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Me zan ce? Ko na faɗa ba za a yarda da ni ba, ƙanin mahaifina ya fito ya wanke ni, amma ba a fasa surutu ba, me zan ce? Su yi ta yi idan sun gaji za su daina ne"

"Kana nufin ba zaka ce komai ba?"

"Ko na ce ba za a daina ba, ka ga maganar ba ta da amfani"

Cp ya ce "Ai shikenan, ɗazu mun yi magana da commissioner, saboda sabon posting ɗin da gidan jaridar nan ke cigaba da fitarwa, na yi magana da manema labarai, na sanar musu hukumar ƴan sanda mun san da case ɗin, sai dai abu ne na sirri da ba ya buƙatar a fito ayi ta yayatawa, shi ya sanya muka yi shiru muka yi ta bincike, kuma haryanzu muna kan yi ma."

Adam ya nemi wuri ya zauna a gefen gadonsa ya ce "To shikenan yallaɓai, na gode sosai da sosai"

"Kar ka damu, ai hakkinmu ne baka kariya, kuma abun da muka faɗa hakan yake ai, Allah ya tsare, wannan ba wani abu bane ba duk aikin maƙiya ne, kuma ba za su yi nasara ba"

Adam ya ce "Haka ne, na gode sosai"

"Masha Allah, Allah Ya ƙara tsarewa"

"Amin ya rabb sir, na gode" daga haka ya kashe wayar. Yana gama wayar ya ji zaman ɗakin ya ishe shi, dan haka ya fita domin ya gaida ammi ya ɗan fita.

Duk a falon sashen ammi ya tarar da su, har ammin, ana koyawa Sabir zama an shiryashi cikin wasu kaya masu kyau, an zaunar da shi a gefen kujera, cikin dabara iman tana taje masa sumar kansa, sai kai hannu yake yana turewa alamar ba ya so.

Adam ya fara gaida ammi, sannan ya ɗau sabir ya zauna da shi a jikinsa.

Adam ya karɓi brush ɗin hannun iman, ya cigaba da taje masa kai, amma ya cigaba da kai hannu yana turewa yana son yin kuka.

"Kai rigimamme, baka son gayu?" Adam yayi maganar yana murmushi tare da kallon ɗan nasa cike da ƙauna.

Sabir yayi shiru yana kallonsa.

"Yi mini dariya mana, an ce kana dariya amma ba ka taɓa yi mini ba"

Ammi ta ce "Kai ai wannan ɗan naka kai ya yo, babarsa kawai yake washewa baki gaba ɗaya yayi mata dariya, har mamakin irin soyayyar da ke tsakaninsa da ita nake yi, da ya ganta har wani ƙara nutsuwa yake yi".

A ransa ya ce 'Aikuwa ba zan ba ta riƙonsa ba, ya tashi a sangarce da rashin kunya kamarta ba' ya ɗaga kai yana kallon ƙwayar idon sabir, take aisha ta sake faɗo masa a rai, dan suna ɗinar kama da sabir, duk da ya fi kama da shi.

Ammi ta ce "Ina ta magana ka yi shiru, tunanin me ka ke yi ne?" Yana ɗago ido Ammi ta ga hawaye kwance a idonsa.

Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?"

Yayi murmushi ya ce "Lafiya lau ammi"

Ammi za ta yi magana, hadimarta ta shigo, ta durƙusa ta ce su Samha ne suke neman iso.

Ammi ta ce, ace su shigo.

Samha ce da ruƙayya, suka shigo tare tana ganin adam sai da ta yi hamdala a zuciyarta, ta wani lumshe ido, wata irin ƙaunarsa da soyayyarsa na sake ratsata.

Suka ƙarasa, suka gaida ammi ta amsa musu cikin fuska, samha ta kalli adam ta ce "Yaya ina kwana?" Ta yi maganar cikin rausaya.

"Lafiya ƙalau, kuna lafiya?"

"Lafiya ƙalau, sabir na zo gani, ammi yaushe za'a kai mana shi ne? Na gaji da jiran na kasa jurewa".

Ammi ta ce "Banda abunki samha, yaron ai haryanzu jariri ne, ba a haɗaku da jego ba".

"Haba ammi, tun da muka rasa fulani ai shi ne madadinta"

Ta matsa kusa da adam, za ta ɗau sabir a hannunsa, sai da ta taɓa shi, wani irin kallo take masa ji take kamar ta rungume shi, ko ta samu sassauci a kan abun da take ji game da shi.

Ta ɗauki sabir tana yi masa murmushi, wanda a ƙasan zuciyarta ji take kamar ta buga shi da ƙasa, dan yadda ba ta ƙaunar uwarsa shi ma ba son sa take yi ba.
Miƙa sabir yayi ya hau kuka, duk yadda ta so ta rarrashe shi yaƙi yin shiru, ya cigaba da kuka ba shiri adam ya karɓe ɗan sa, ta ji tamkar ta dunƙule hannu ta daki kan yaron ko ta huce.

Cikin iya siyasa ta ce "Ammi wai har ya iya ƙyuya ne?"

"To gashi dai ya yi miki, ɗan na ku ne ɗan ganin dama, ko dariyarsa babarsa kawai yake yi wa"

Da sauri samha ta ce "Wace babar ta sa?"

"Rumaisa, yarinyar da ta zo da shi"

Jin an ambaci labarin da Mummy ke son ji ya sanya ruƙayya cewa "Ai ammi haryanzu tana nan?"

"Tana nan mana, ina za ta je?"

"To ammi zuwa take ta ganshi?"

Kan ammin ta bata amsa samha ta ce "Ai an ce mini an kai ta wurin turaki rannan ko?"

Ammi ta ce "Eh"

Ruƙayya ta sake cewa "To ammi gidan nan take zuwa?"

Maimakon ammi ta ba ta amsa sai ta ce "Ruƙayya an ce mini Mahmud ya zo gari ko?"

"Eh ya dawo"

Ammi ta ce "To masha Allah"

Iman ta ɗauko baby carrier ta ce "Yaya kawo na saka shi a Carrier ko zai koma barci, na ga yana ta rigima dama yau da wuri ya tashi"

Adam ya ce "Zo ki ɗau abunki iman, na fuskanci duk abin da na yi iman sai kin nuna mini ban iya ba, ni ban san a ina ki ka koyi raino ba, tun da mu dai ba jariri ne da mu ba"

Iman ta yi dariya ta ce "Ni na isa?"

"Gashi nan kuwa" yayi maganar cikin sigar wasa. Ya bawa iman sabir ya tashi ya bar falon, a rayuwar duniya samha ba ta kishi da aisha kamar yadda take yi da iman, saboda akwai alaƙa mai kyau a tsakanin takawa da iman, ga iman da kyau tamkar ita ta yi kanta.

Suka gama zamansu, daga bisani suka tashi za su tafi, Samha ta ajiye wata leda cike da kayan sawa da na wasa, wai sabir ta kawowa, ammi ta yi mata godiya sannan suka tafi.

***
Ba kowa a gidansu rumaisa, kowa ya fita da masu makaranta da sauransu, sai mama itakaɗai, kasancewar ta ji sauƙi, ya sanya ta ɗora abincin rana, dan ba ta son su dawo ba ta kammala abinci ba, yanzu ƙaramarsu babbarsu za ta zo ta fara kwanciya da tura baki ita yunwa.
Sai dai babu tsammani ta ga kiran ammi a waya.

Ta ɗaga wayar suka gaisa, ammi ta kuna yi wa mama ya jiki.
Sun ɗan taɓa hira sannan ammi ta ce "Yauwwa maman rumaisa wata magana nake son mu tattauna da ke, duk da kamata ya yi na zo ƙafa da ƙafa, ina da wasu baƙi ne da zan yi yau, kuma maganar yakamata mu yi ta"

Mama ta nutsu ta ce "To ina jin ki, Allah ya sa lafiya".

"Yauwwa, zuwa wannan lokaci tun da Allah ya riga ya haɗamu, mun riga mun zama ɗaya, tun bayan da na baro ku, nake ta tunani a kan maganar da ki ka yi mini a kan rumaisa, da kuma wasu dalilai na makomar jaririn nan, shine na yanke shawarar mai zai hana adam ya auri rumaisa, kin ga maganar wata gulma da ɓacin suna ya ƙare, kuma kin ga za ta samu cikakkiyar damar kula da sabir kamar yadda take buƙata, amma me ki ka ce?"

Jiki a sanyaye mama ta ce "Aure kuma rumaisan? Shekararta goma sha uku fa, kina ganin yadda ake fama da ita, ga kuma karatunta".

Ammi ta ce "Maman rumaisa ba zai gagara ba, mu ma duk da ƙuruciyar aka yi mana aure, kuma ba abun da zai samu karatunta, za ta cigaba idan aka yi auren nan ni da adam za a yi wa alfarma kuma ina tabattar miki in Allah ya yarda zai zama alkhairi, yanzu amsarki nake jira, zan kai maganar ga magabatansa, tun kan ace za a bashi wata matar, ban san wa za a bashi ba, ko dan makomar rayuwar marayan nan".

Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, amma gani nake rumaisa ba za ta iya raino ba, ita ma ba hankali ta cika ba"

Ammi ta yi murmushi ta ce "Babu damuwa, ai ba sakar mata rainon za a yi ba, ya zamana dai ta samu kusanci da shi sosai yadda take so".

"To, bari yayyenta su zo mu tattauna, abun da suka yanke shikenan"

Ammi ta ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi, ina saurarenku dan da wuri nake son ayi komai a gama"

"To shikenan, duk yadda muka yi zaki ji ni" tun da suka yi sallama mama ta kashe wayar take zullumi. Ayi wa rumaisa aure ta je ta yi me a gidan auren? Yarinyar da ban da zunzurutun ƙuruciya da wauta ba abun da yake damunta.

A haka mama ta ɗora girkin nan, take aikin jikinta duk a sanyaye.

Rumaisa ce ta yi sallama, ta shigo da jakar makarantarta a ka, tana yamutsa fuska.

Mama ta kalleta ta amsa mata, rumaisa ta jefa jakarta ɗaƙi, ta cire hijjabinta ta kalli mama ta ce "Mama ki aika aje a yi wa mai ice warning ba ruwansa da ni, me na yi masa da idan na zo wucewa zai din ga cewa gata can, sau biyu yana yi mini, kar na yi abun da ba shikenan ba a zo ace na yi tom" tana gama maganar ta ɗau buta ya wuce banɗaki.

Bayan ta fito ta kalli mama a taɓare ta ce "Mama wai ba a gama abincin ba, ni fa yunwa nake ji" mama ta bi ta da kallo tana hango rumaisa da aure.

Ta gama taɓararta mama ta kammala girki, ta ci ta tafi makaranta, sai da yamma da mai sunan baba ya dawo, mama ta yi masa zancen.

Aikuwa ya haɗe rai ya ce "Dama na san ɗawainiyar da suke yi da ita, dole a ƙarshe su nemi wani abu, wane irin aure yaushe aka haifi rumaisan da har za a wani ce a aureta, mutumin da faɗa suke yi ba sa shiri, kawai ki ce musu ba zai yiwu ba su yi haƙuri".

Kasancewar usman yana nan ya ce "A'a fa ayi tunani, yarinyar nan kuna ganin abun da take yi a kan yaron nan, me ake nema a aure ne ba mutum na gari ba, kuma in da za a iya riƙeta ba, idan ta amince kawai ayi musu fatan alkhairi a nawa ganin, mussaman yanzu da ƴan unguwa suke ta ƙananan maganganu a kanta, wataƙila ana yi mata auren ta nutsu"

Wani mugun kallo mai sunan baba yayi masa, dan haka yayi shiru, kuma tun da ya kafe a kan ba ya so, ba zai canza magana ba.

Gaba ɗaya hankalin mama ya rabu biyu, kowannensu yana da gaskiya, ita kanta ba ta shirya rabuwa da rumaisa yanzu ba, dan Allah ya sani rumaisa ba za ta iya ɗaukar ɗawainiyar aure a yanzu ba, dan a sangarce take, sai dai kuma tana matuƙar jin nauyin ammi ta ce mata ba zata basu auren rumaisa ba.

Ayshercool.

08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Maganar ta yi ta damun mama, ta fara tunanin ko Abubakar za ta kira a waya, dan neman shawarar sa, dan ya fi sauƙin kai da fahimta.

Har zuwa dare mama kallon rumaisa kawai take yi, gashi yau ɗin kamar rumaisan ta san abun da ake ciki, sai taɓara take kala-kala da ƙuruciya.

Da daddare ta gama shimfiɗarta za ta kwanta, ta ɗaga ido suka yi ido huɗu da mama.

"Mama wai na ga kina ta kallona?"

Mama ta ce "Mhmm, babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login