Showing 18001 words to 21000 words out of 199108 words

Chapter 7 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

790

wanda ya ga ba zai iya haƙura ba ya nemi hujja ya kai ƙarata shikenan"

Jamil ya ce "Lamarin ƙasar nan ai sai Addu'a, Allah ya kyauta ya bada nasara, nima akwai special assignment da zan tafi jigawa, na ji kana cikin wanda za su je Lagos ko?"

Adam ya ce "Eh, aikin ma nake dubawa yanzu"

Jamil ya ce "Allah ya sanya mu gama da aikin nan lafiya, kalli yadda muke wahala a kan ƙasar nan amma ba a gani, kalli aikin da muka yi a kan tsohon ministan harkokin waje, amma dan wulaƙanci wai kotu ta bayar da belinsa, amma daina maganar ni gaba ɗaya sai in ji aikin ma ya fita daga kaina" Jamil yayi maganar cikin damuwa.
Adam ya ce "Haba Jamil, bai kamata mu karaya ba, ko da muna yi ba a ɗaukar mataki, wataran za a ɗauka, haƙuri zamu yi mu cigaba da yi, idan ba haka ba haka ƴaƴanmu da jikoki zasu taso su ɗaora da bauta babu ranar da talaka zai yi ƴanci"

"Kana da gaskiya, amma ni fa na tsorata da batun garkuwa da aisha, anya baka tunanin shiri ne, saboda abun da muke yi?"

"To ba na ce ba, zancenka zai iya zama gaskiya, kuma zai iya zama akasin hakan, duba da yadda dama ƙasarmu babu tsaro, kuma kai tsaye garin da babu tsaron ta tafi, dan haka bana zargin kowa"

"To, Allah ya yi mana jagora, ya bayyana gaskiya a duk in da take".

Adam ya amsa masa da Amin.

Rumaisa ba ta yi burki a ko ina ba, sai a ƙofar gidan maƙwabciyarsu, tana tafe tana kuka har ta je ƙofar gidan, ta sauke kayan dutsenta, ta shirya tsaf, ta tattare hijjabinta, ta fara auna manyan duwatsu zuwa cikin gidan nan.

A rikice matar gidan ta fito, a matuƙar tsorace, jikinta ko mayafi babu, domin ganin meke faruwa.
Amma tana buɗe ƙofar gida, rumaisa ta sauke mata wata ƙatuwar marmara a bakinta, take bakin ya fashe, kan ta yi wani abu wani dutsen ya sauka a goshinta.
Rumaisa ta cigaba da aika duwatsun nan babu ƙaƙƙautawa tana kuka, tana faɗin "Munafuka, wallahi ba zan yafe miki ba, ni ba ƴar iska ba ce".

Kururwa matar ta din ga yi, tana neman agaji, mutane suka fara taruwa, aka rirriƙe rumaisa, amma ta din ga kuka tana ƙoƙarin cigaba da jifan.

Gidansu rumaisa aka je aka faɗa, Allah ya sa usman yana nan, ya je ya danƙota, tana kuka.

"Meye haka rumaisa, baki da kai ne? Dan me zaki din ga yi wa mutane jifa a gida?"

"Ba ita ta je take gayawa mutane wai na yi cikin shege ba, tana nufin ni ƴar iska ce ina wasan banza da maza" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfinta.

Usman ya ja hannun rumaisa, ba tare da ya ce wa kowa komai ba, ya ja ta zuwa gida.

Hankali a tashe mama ta ce "Rumaisa, kanki ɗaya ki ka je ki na yi wa mace jifa a cikin gida, tana ta kurma ihu wai a taimaketa zaki kasheta?"

"Cikin kuka ta ce "Wallahi da zan iya sai na kashetan, dan me za ta ce mini ƴar iska? Cikin shege fa yana nufin mai wasan banza da maza".

Mama jiki a sanyaye ta ce "Rumaisa rayuwar duniya haƙuri ake yi, sai ki zo ki gaya mini, ni na ɗau mataki"

"Wallahi idan na gaya miki ba zaki ɗau mataki ba, cewa zaki yi na yi haƙuri, kuma wallahi ban haƙura ba, sai ta ga abun da zan yi mata"
Rumaisa ta shige ɗaki tana kuka, Usman ya ce "Ai wallahi mama ban da kin hana da da kaina zan ci uban matar nan, duk yadda ki ka ɗauketa ƴa ki ke mutunta mata, amma ta yi mana wannan wulaƙancin".

Mama ta ce "Dan Allah usman a rayuwarku ku koyi haƙuri, da ƙyale mutane da halinsu, wasu lokutan da kai da rumaisan duk halinku ɗaya ai".


Ammi kuwa sake kiran mama ta yi, domin ta sake tabattar da rumaisa ta amince, dan ta fuskanci rumaisa ƴar buyagi ce, kar sai ta je ta kaiwa turaki maganar rumaisa ta mayar da hannun agogo baya.

Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga suka gaisa.

Ammi ta ce "Ina maman sabir ne, a bani ita mu yi magana"

Mama ta miƙawa rumaisa waya, ta ci kuka ta ƙoshi.

Muryarta a dashe ta amsa sallamar ammi.

Ammi ta ce "Rumaisa lafiya kuwa, na ji muryarki a dashe?".

"Ba maƙwabciyarmu ce ta ke cewa mutane na yi cikin shege ba, ƴan unguwarmu suna yi mini kallon ƴar iska mai wasan banza da maza"

Ammi ta ce "Subhanallah, ki kwantar da hankalinki, kin ga yana daga dalilin da ya sanya nake son ayi auren nan, ki yi haƙuri ki manta da su, yau zan je gidan turaki mu yi magana, dama kiranki na yi na sake tabattarwa idan kin amince, nan da watanni uku kacal za ayi in sha Allah".

Ayshercool.
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Rumaisa ta yi ajiyar zuciya ta kasa cewa komai, ammi ta sake cewa "Kin dai amince ko? Idan aka yi aurenku shikenan babu wanda zai sake yi miki kallon mutuniyar banza, ni na san ke ba mutuniyar banza bace ba, kuma mijinki ma ya sani, dan haka ki rabu da su, kar ki sake kula kowa a cikin su kin ji maman sabir?"

Rumaisa ta ce "To, ina sabir yake?"

"Yana nan ƙalau, yanzun nan iman ta ɗauke shi ta fita da shi".

"To a gaishe su" ba ta sake magana ba daga haka, ta miƙawa mama wayarta ta kwanta, zuciyarta na cigaba da ƙuna, da ta tuna kallon da ake yi mata sai ta ji ranta ya sake ɓaci fiye da da.

Ammi ta kammala shirinta tsaf, ta fito falo, ta yi wa ma'aikatanta sallama, ta fita haraba, tana fita ta hangi Mahmud yana nufar in da motoci suke, ya ƙara ƙiba abun sa, kai da ka ganshi ka san hankalinsa a kwance yake ba shi da wata damuwa.
Ammi ta tsaya tana hangensa, ya ɗan daɗe yana duba abu a wayarsa, daga bisani ya nufi motar da zai hau, ƙarasawa ammi ta yi, zuwa in da direba yake jiranta a tata motar, suka yi ido huɗu da Mahmud, amma sam bai kulata ba, sai ta tsinci kanta da kasa shiga motar.

Mummy ta ƙaraso cikin shiri, da alama fita zasu yi ita da Mahmud, tun kan ta ƙaraso ta ga abun da ya faru, dan haka ta ƙaraso da fara'arta ta kalli ammi ta ce "Ran giwar galadima ya daɗe, fita zaki yi ne?"

Jiki a sanyaye ammi ta ce "Eh".

"Ok, ya Mahmud ƙarami, yakamata ko sau ɗaya a kawo mini shi sashina, ba dan halina ba".

Ammi ta jinjina kai kawai ta buɗe motar da zata fita. Mummy ta ce "Mahmud ka shiga ka ga ɗan wurin Adam kuwa? Ka san sunanka ma aka saka masa"
Mahmud ya haɗe rai ya ce "Me ganin nasa zai ƙara mini?" Ya buɗe motar ya shige.

Wani abu ne mai ɗaci ya tsayewa ammi a ƙirjinta, ta san da gayya mummy take wasu abubuwan.

Kasa sake kallon in da su Mahmud suke tayi, har motar ta fice daga gidan.

Suna tafe a hanya Mummy ta ce "Mahmud, yakamata ka je ka ga yaron nan, sannan ka yi wa ɗan uwanka barka tare da gaisuwar rasuwar matarsa, kar ace ni nake zigaka"

Mahmud da yake murza sitiyari ya ce "Dan Allah mummy ki ƙyaleni da sabgar mutanen nan, ina wuri ɗaya hankalina a tashe ni bana son tashin hankali da ɓacin rai, ni a kan haka sai na bar ƙasar na koma in da na fito, ba dai A'isha ce ba? Na ce Allah ya jiƙanta ya sa ta huta, shi kuma jariri Allah ya raya why sai na ta bin su ina wani gaisuwa abun da ba addini ba".

Mummy ta ce "To shikenan, sarkin faɗa, ni zan saka a ɗauko yaron ka ganshi, duk da nima ɗin sai na roƙa za a kawo mini shi, sau ɗaya na taɓa ganin yaron, shi ma sai da na taka da ƙafata na je".

Mahmud ya ce "Kin gani ko, Mummy meya kai ki? A wulaƙantaki a banza, dan Allah tun da ba sa sonki a sabgarsu, ki ƙyalesu su je sun cinye yaron, ina jin Samha ma na surutun wai ta je an yi mata wulaƙanci a kan yaron, sai ka ce dole ni fa bana zuwa in da ba a buƙatata"

Mummy ta yi dariya ta ce "Sarkin tsari, mu bama son zumunci ya samu matsala ne" ya ɗan ɗage kafaɗa alamar ko a jikinsa.

Ammi kuwa har suka je gidan turaki, ba ta hayyacinta, ta yi zurfi a tunani, sai da direban ya ce mata sun zo, sannan ta dawo hayyacinta ta sauka, ta shiga gidan.

Tun da mama ta ganta take ta wani cin magani, tana hura hanci, samha ce dai ta din ga rawar jiki da ta ga ammin, tana tambayarta ya sabir.

Ammi ta amsa mata cikin sakin fuska ta ce "Dan Allah samha ki aika ayi mini iso wurin mai girma turaki"

Samha ta ce "To ammi" gaba ɗaya samha ta din ga tsuma, har a ranta take jin, anya ba a kan batun aurenta da takawa ammi ta zo ba, amma ai idan haka ne, da mai girma turaki ne zai yi mata zancen. Da haka ta je ta nemawa ammi iso wurin turaki, ammi ta shiga wurinsa.

Cikin sakin fuska da girmamawa, suka gaisa da turaki, ya ce "Tun ɗazu muke tsumayinki da ki ka ce mana zaki zo"

Ta risuna ta ce "Tuba nake, ayyukan iyali ne suka sha kaina, tuba nake Allah ya baka nasara"

Turaki ya ce "To Madalla, Allah ya yi mana jagora ina abokin nawa, baki zo mini da shi ba?"

Ammi ta yi murmushi ta ce "Yana gida, ka san baya son mutane, yana ƙyuya, kar mu zo ya cika maka kunne da kuka, ko yayi ta zare maka ido" tayi maganar cikin murmushi.

Turaki ya ɗan yi dariya ya ce "Ai barewa ba ta gudu ɗanta yayi rarrafe, haka zalika kalar kumbo kalar ƴaƴanta, haka shi takawan yake ai ko da yana ƙarami, da aisha ya ɗauko da an ga haƙuri da fara'a, amma takawa dai kam hmmm"

Ammi ta yi dariya ta ce "Kun fi kusa ranka ya daɗe, ba ruwana" suka yi dariya gaba ɗaya.

Ya ce "To giwa meke tafe da ke ki ke son ganinmu da gaggawa haka? Allah ya yi zaki samemu, dan gobe in Allah ya kaimu muke sa ran tafiya umara"

"Allah sarki, Ubangiji Allah ya sa ayi ibada karɓaɓɓiya"

Ya amsa da amin, tare da sake tattara hankalinsa a kan ammi.

"Allah ya taimake ka, dama wata muhimmiyar magana ce ke tafe da ni, wani hukunci na yanke da zartar da shi dole sai da izininka, kuma kai zaka yi mini jagora zuwa ga tabattauwar abun cikin hukuncin Allah"

Ya jinjina mata kai cikin nutsuwa alamar yana sauraren ta.

Ta ɗora da cewa "To bisa ga al'ada ta masauratar nan, duk cikakken ɗa a gidan nan, a kan yi masa zaɓi na matar da zai aura, ko ya kawo wadda yake so ƴar mutunci idan ta yi a aura masa. wani abu ne ya taso a kan yarinyar nan rumaisa, ƴan unguwar su suna ta yaɗa jita-jitar wai ciki ta yi aka kaita aka ɓoye ta haihu, sunanta dai ya ɓaci a unguwar su, na ga babu wata hanya da zamu bi domin wanketa face Adam ya aureta, duba da irin matsanancin son da take yi wa yaron nan da ta zo da shi, har ina ganin kamar rabata da yaron na shiga hakkinta, saboda na san ciwon abun, ga wannan abu da ya kunno kai game da rayuwarta, na ga abu ɗaya zan iya yi shi ne in sanya adam ya aureta, amma ya ka gani ranka ya daɗe?".

Turaki ya ce "Ikon Allah, kin ga nan Jamil ya zo mini da zancen, akwai buƙatar Samha ta maye gurbin Fulani, duba da yadda ta daɗe tana son adam, dan har na yi na'am na so na tuntuɓeki, to sai gashi kuma kin zo da wani zance da yakamata a tsaya a duba. Tabbas! Idan har da yadda zamu yi yarinyar nan bai kamata mu bari ta wulaƙanta ba, dan haka a wannan karon ma samha sai dai ta yi haƙuri, ko kuma idan yana da ra'ayi ya haɗasu biyu, amma rumaisa ita tafi cancanta ya aura, duk da ƙanƙantarta".

Ammi ta ɗan ji rasss, ba za ta yi fatan adam ya haɗa rumaisa da samha ba, duk da rumaisa yarinya ce amma ba za ta yi fatan ta zama bora ba, tun da dai haryanzu ba ta isa rayuwar aure ba, tana son ya aureta ne dan ya inganta rayuwarta, a haka idan ta ce za su cigaba da ɗawainiya da rumaisa, ƴan uwanta ba zasu harda ba, dan ta lura suna da gudun abun hannun wani.

Turaki ne ya katse mata tunanin ta hanyar cewa "Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san akwai ƙalubale, a ƙa'idar masarauta, ƴaƴan sarakuna ƴaƴanmu suke aure, ko ƴaƴan wasu manya, akwai gwagwarmaya idan aka kai maganar nan gaban su wambai"

"Allah ya taimakeka shi ya sanya na zo wurinka, na san kai kaɗai ne zaka iya shiga lamarin nan ka tsayawa adam, jikina yana bani akwai alkhairi a game da lamarin nan, rumais alkhairi ce ga adam"

Ya ɗan yi shiru ya ce "To babu laifi, in Allah ya yarda idan na dawo, zamu yi magana da su, na sanya zancen cikin addu'a idan alkhairi ne Allah ya tabattar ya kawo komai da sauƙi"

"Amin ya rabb, idan komai ya daidaita bana son abun ya wuce watanni uku, kar wani abun ya kutso"

Turaki ya ce "Babu damuwa, babu abun da zai gagara da ikon Allah"

Ammi ta risuna, ta sake yi wa turaki godiya, sannan ta tashi ta fita.

Samha ce ta raka ammi har mota, tana yi mata ta gaida gida.

Ammi na tafiya samha ta koma ɗakin ta, ta ɗau wayarta ta kira jamil.

Yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Yaya jamil, yau ma ammi ta zo wurin mai girma turaki, dan Allah idan ka zo yau ka tuntuɓe shi da maganar, ka ji ko ita suka yi?"

Jamila yayi tsaki ya ce "Ke kin fiye abun haushi wallahi"

"Dan Allah yaya ka taimaka".

Ya ce "Gaskiya bana nan, bana gari sai dai ki jirana dawo, idan na dawo kuma yana umara, na san duk abun da ake ciki dai, in dai a kan maganar ne zasu tattauna da mama"

Samha ta ɗan yi shiru sannan ta ce "To shikenan, na gode " ta kashe wayar cike da fatan Allah ya sa tattaunawa suke a kan ta maye gurbin Fulani.

***
Ana idar da sallar magariba, Huzaifa ya saka rumaisa a gaba yana ta mata faɗa, ta ƙi cin abinci sai mita take a kan abun da aka yi mata a unguwa.
Aikowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login