Showing 165001 words to 168000 words out of 199108 words

Chapter 56 - Kanwar maza 3&4 Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

828

ita zata kawo mata ziyara.

Rumaisa ta din ga murna kusan shekara da aurenta, sau ɗaya mama ta taɓa zuwa gidanta.

Ta cewa takawa, ya ɗaukko mata sabir, dama anty laila ta ce yana ta rigima, Adam ya ce sai dai su je ta ganshi su dawo gida.

Ta ce "Amma saboda me?"

"Ya fara wayo, ba zai kwana a tsakaninmu ba".

Cikin damuwa ta ce "Amma papa saboda me? A ɗakina zamu din ga kwana da shi".

"Saboda mun daina raba ɗaki daga yanzu, sai ya shekara biyu ko uku, ya isa shiga makaranta, kan lokacin kema kin kammala makaranta, zan ɗaukko shi gaba ɗaya ya dawo gidan nan, a gyara masa ɗakin sa"

Kai tsaye ta gane nufinsa, a tata wautar, da suka dawo gida, shikenan ta huta, amma taji ya kawo wata maganar daban.

Kamar da wasa, taga da gaske takawa yake yi, ba zasu sake raba wurin kwana ba, babban abun da ya ƙara sa shi farinciki da bashi mamaki, bai wuce jin ya koma normal ba har a gidan.

Sai washegari suka tafi gidan ammi, ana ta shirin bikin iman da mai sunan baba.

Suna mota kan su sauka takawa ya cewa ruma "Kalli can" ta ɗaga kai, ta hango mai sunan baba tare da iman, tana magana yana murmushi.

Ruma ta yi dariya ta ce "Manya gatan wasa, su mai sunan baba an tafi duniyar love".

"Ina tausayawa iman zama da wannan yayan naki, dan dai ta nace ne kawai, amma gani nake kamar za ta sha wahala, mutum sai izza da jin kai".

Ta haɗe rai ta ce "Papa abun ma ba kara, yayana ne fa"

"Shi ɗin fa, kema ai kin san gaskiya, gashi dai ƙanwata yake so, amma ko zan wuce sau goma ko kallona ba zai yi ba".

"To ai kaima baka kula shi"

Ya ce "Oho muku dai, ki taho mini da key ɗina, kya je ku gaisa, ni ta baya zan shiga"

Ya buɗe motar ya fice, duk da murmushi yake yi, iman na masa zancen su saka kaya iri ɗaya ranar dinner, yana ce mata shi kunya yake ji, ba ya son taron mutane.
Tana yi masa magiya, tana ganin rumaisa ta nufeta tana murmushi suka rungume juna, ta ce "Mimi sannu da zuwa ya Abuja?"

Ruma ta ce "Abuja ba daɗi".

Iman ta ce "Haba dai? Baki ji daɗin garin ba ne ko yaya?"

"Ke dai a bar zancen kawai" ta risuna ta gaida mai sunan baba, tamkar ba shi ne yake murmushi ba, ya amsa cikin basarwa.

Sai da ya lura da yadda tayi ƙiba, ta ƙara kyau da haske, kuma daga yadda take yawan faɗan Adam, ko waya ake yi da ita, ya sake tabattar masa da tana cikin kwanciyar hankali.

Sabir har da wata ƴar ƙara, saboda murnar ya ga miminsa, Ammi ta ce "Allah ya shiryeka sabir, wani ma sai ya ce ba a kula da kai, kullum sai yayi kuka mimi"

Ruma ta yi dariya, tana kuma rungume shi, soyayyarta da Sabir, haɗin Allah ce kawai.

Rumaisa suka koma hutun makaranta, sai dai duk ranar da takawa ya addaba mata, da safe sai ta lafke ta ce ba zata je makaranta ba.
Haka zai yi ta fama da ita, sai dai ta je a makare, har makarantar suka fara complain da yawan fashinta da makara.

Gefe guda kuma, yana ta fama a kan son gano, suwaye SMOKE, saboda ya san mutanen da ya addabawa da yawa, in dai aiki ya biyo ta kanka, babu ruwansa, kawai zai yi aikinsa ne, dan haka takamaimai ya kasa gano suwaye.

Ranar da mama ta zo, kamar rumaisa ta shige cikin mama, ta sauketa da kayan ciye-ciye kala-kala, sai dai mama ba ta fi awa biyu ba, ta ce Aliyu ya tashi su tafi, dama shi ya kawota, rumaisa har da kuka, mama ta ce babu amfani zarya a gidan siriki, haka suka tafi.

***

Magiyar da Mahmud yayi ta yi wa mai sunan baba ce, ta sanya ya bashi damar saka masa hannu a harkar gininsa, ƙofofi na alfarma, da glasses na window, haka ya saka a gidan da Iman za ta zauna, aka yi tiles mai kyau, gida yayi kyau sosai dai-dai zaman amarya.
Kuma ya yiwa mai sunan baba alƙawarin cewa; ta ɓangaren sa babu wanda zai sanarwa da cewa ya taimaka masa a harkar ginin.

Lokaci yana ta ƙaratowa, aka kai kayan lefen iman, Akwatuna shida da kit, dai-dai gwargwado yayi ƙoƙari iya ƙarfinsa.
Sai dai da yake maƙiyi, ko ruwa ka shiga sai ya ce; ka tayar da ƙura, haka aka din ga kushe lefen nan, wai kamar iman, a rasa abun da z aa kawo mata, sai wannan kayan, babu wadda aka taɓa aurarwa a gidan, aka yi mata ƴan wannan kayan tsiyar, sai ita.

Laila ta saka aka kwashe kayan lefen aka mayar gidanta, ta ce ba shegen da zai sake zuwa ya ga lefen, su sun karɓa kuma sun yaba, dan haka duk wani munafuki, ya je yayi yadda zai yi.

Iman kuwa da rawar jiki ta kira mai sunan baba, tana yi masa godiya.

Rumaisa sai murna take tana cewa "Amarya tawa ango nawa, wai ni ranar bikin nan ina zan je ne ma?"

Takawa ya ce "Sai ki rabu biyu kawai, rabi a nan rabi a can". Shi kansa takawa, ya yaba abun da umar ɗin ya kawo, a zuciyarsa dan bai furta ba.

Ammi kanta bakinta yaƙi rufuwa, dan ta yaba nesa ba kusa ba.

Turaki da kansa ya yi wa iman kayan ɗaki, kamar yadda yake yi wa ƴaƴan Galadima idan za su yi aure.
Wani kayan kitchen da sauransu kuwa, laila ce tayi wa iman, takawa ya sai mata kayan electronics, kuma a hakan gudunmawa ko ta ko ina kawota ake yi.

Mahmud yayi sallama a falon, suka amsa masa, sabir da gudu ya nufe shi, yana kiran daddy, har yana neman ya faɗi, yayi carf ya ɗauke shi yana murmushi.

Ya risuna ya gaida ammi, ta amsa masa cikin sakin fuska.

Ya kalli laila da a sanadin rumaisa, suke gaisawa, saɓanin da da har ta ƙaraci zamanta a gidansu faɗa suke yi.

Ya ce "Hajjaju barka da wannan lokaci?".

Laila ta ce "Mamuda kana lafiya?"

"Ki daina ɓata mini suna mana, daughter ashe tafiya ku ka yi?"

Ruma ta ce "Wallahi kuwa daddy, ya garin, ka karɓo offer taka kuwa? Wane aikin ne kuma"

"Na karɓo, an bamu ni da yayana?"

Rumaisa ta ce "Papa, to ai papa yana da aiki".

Ya harareta ya ce "Ba shi ba. Aikin coustom ne"

Ruma jikinta ya ɗan yi sanyi sannan ta ce "Allah ya sanya albarka ya tsare muku, a kula da aiki daddy, dama na san kai me gaskiya ne, ka bawa ammi ta gani".

Ya ƙarasa ya ajiyewa ammi envelope, ammi cikin jin daɗi ta karɓa ta buɗe tana dubawa ta ce "Alhamdilillah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi, ya sa rai da lafiya su mora, Allah ya tsare maka"

Ya ce "Amin na gode"

Laila ma sanya albarka suka din ga yi, goga Adamu kuwa kamar bai san me suke yi ba.

Iman ma ta ce "Allah ya sanya alkhairi yaya".

Ya amsa da "Amin amarya. And mutum nawa zaku gayyata na wurin dinner? Zan ɗau nauyin abinci".

Ammi za ta yi magana, laila ta ce "Godiya muke, Allah dai ya saka da alkhairi malam mamuda"

Yayi murmushi ya miƙe ya ce "Iman, bayan biki, mijinki zai je Abuja interview, offer ni da shi ne. Kar ki gaya masa yanzu, kin san halinsa zai ce saboda zai aureki ne, an raina abun da yake da shi. Interview ɗin ma kawai zai je ne, dan kar ya gane daga nan a ka samo mana aikin, saboda link ne kawai na tura masa na ce ya cike CV ɗin sa"

Rumaisa ta ce "Mai sunan baba, ya samu aiki daddy? Allah sarki baban marayu. Daddy Allah ya saka maka da alkhairi, ya biya maka buƙatunka na alkhairi, Allah ya nuna mini lokacin da zaku kalli juna kai da papa a matsayin ƴan uwa ba maƙiya ba, ku zauna a gaban ammi ta ji daɗi".

Rumaisa har da kuka, dan abun ya zo mata a mugun bazata, bata taɓa tsammani ba.

Laila ma kanta godiya take masa, iman kuwa kasa magana tayi, ammi na kuka rumaisa na kuka.

Adam kuwa jikinsa ne yayi sanyi gaba ɗaya.

Mahmud bai ce komai ba, ya rungumi sabir ya fita.

Laila ta ce "Ke kuma mimi maimakon kiyi murna, sai ki hau kuka, daga ke har ammin?"

Rumaisa ta ce "Anty laila ba zaki gane bane, baban marayu ne mai sunan baba, tun tasowarsa, bashi da burin da ya wuce rayuwarmu tayi kyau ta inganta, bai ajiye komai ba saboda mu, su kuma gaba ɗayansu basu da burin da ya wuce inganta rayuwata, ban taɓa kukan rasa abu na dai-dai talaka ba, komai suka samu ni.
Albarkacin anty iman ya samu aikin yi, lallai sirikarmu mai albarka ce, ki sa a ranki You will marry the best husband ever in this world" tayi maganar tana murmushi.

Papa ya ce "Wai best husband ever saboda son kai"

Laila ta ce "Ba son kai ta faɗa ba, nima naga alamar hakan"

Ruma ta ce "Ammi yi haƙuri, garin shirme na na saka ki kuka"

"Bari rumaisa, da ke da familynku babu abun da zan ce muku sai godiya, Allah ya ƙara mana zumunci"

Suka amsa da amin.

Ammi ta ce "Rumaisa, yaushe su uwani zasu koma bakin aikinsu ne, baki ce komai ba haryanzu, aikin gidan nan yayi miki yawa fa"

Ruma ta ce "Ammi Asiya ce kawai zata dawo, ta isa zamu din ga aikin tare"

Ammi ta ce "Amma meyasa?"

"Kawai Ammi"

Adam ya ce "Ammi, nima ina goyon bayan hakan, mutum ɗaya ya isa"

Ammii ta ce "To shikenan"

***

Mummy kuwa abubuwa gaba ɗaya sun kwance mata, asirin ya daina ci gaba ɗaya, bata taɓa zaton akwai ranar da za ta zo, ace asirin da take yi ya daina ci ba.
Gashi yanzu sosai suke rigima da Hajiya Lubabatu, wanda ta kai har hajiya Lubabatu ta ce kowa ta je ta ji da matsalarta itakaɗai.

Ɓangaren Mahmud ma yanzu gaba ɗaya ta fara kasa gane kansa, gaba ɗaya yanzu ya watsar da shiga sabgoginta, sama sama suke yanzu.

Abun da ya sake tayar mata da hankali, bai wuce yanzu Fauziyya da duk masu neman aurenta sun gudu, ruƙayya ma sai tarkace, dan yanzu gaba ɗaya ma ta fara kasa gane kan ruƙayyan, domin kuwa wasu abubuwa take, da ta kasa gane kanta, kamar ba ta cikin nutsuwarta.

Babban abun da ya sake jefata cikin damuwa, bai wuce yadda samha ta daina zuwa ba, Fauziyya ta je har gidan turaki, sai dai fa ba a wanyeta lafiya ba, saboda yadda samha take ta cika tana batsewa.
Fauziyya ta ce "Wai Samha lafiya kuwa?"

Samha ta ce "Kin ga Fauziyya, ni fa ban san dalilinki na zuwa ma gidan nan ba, saboda na riga na raba gari da ku, na zaci Mummy ƴa ta ɗauke ni tsawon wannan lokaci da nake tayi mata biyayya, ashe raina mini hankali kawai take yi, amfani take da ni, ta caimma muradinta, dan haka ku je kuyi rayuwarku nayi tawa".

Fauziyya ta ce "Mummyn ki ke gayawa haka, duk abubuwan da tayi miki a rayuwa".

"Tayi mini uwar me? Na sakankance ta din ga cutata, muka yi da ita duk yadda za ayi, za tayi na auri adam, idan na bata haɗin kai, ƙarshe ta cewa baba uwani duk abun da ya faru kar ta din ga gaya mini, sai wanda tayi mata umarni, sa'a ta ci da ban zo har gida na zazzageta ba, na bar maganar".

Cikin fusata Fauziyya ta ce "Do you really know what you are saying samha? Mummy ki ke gayawa haka?".

"An gaya mata ɗin, ke sau nawa muke zama da ku aci mutuncin wasu, na faɗa ɗin, kuma ki fice ki bar mana gida, kuma wallahi tayi mini wani gangancin sai na tona mata asiri, fice ki bar mana gida". Haka suka rubu tsiya-tsiya dutse a hannun riga.

***
"Khadija" mai sunan baba ya kira sunan iman da ke gabansa.

"Yaya umar"

"Ki yi haƙuri da abun da zan baki, na ga ana bayar da kuɗin gyaran jiki da sauransu, ina yawan gaya miki ni ba mai ƙarfi bane ba, dubu saba'in ce a hannuna, za ta ishe ki? Ina ƙoƙarin kama miki wurin da zaki yi hidimar biki ma"

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce "Yaya Umar, albarkar auren muke buƙata, anty laila na da event, a nan zamu yi taron biki, ka barsu ka yi wata hidimar da su kawai"

"Kin raina ko?"

Ta ce "A'a, ban raina ba wallahi, ka kashe kuɗi da yawa sosai ne"

"Ko nawa zan kashe ai ba zan biya ba, mutum sukutum fa za a bani, ban faɗi ba ki karɓa da haƙuri"

Kallonsa take tana jin tamkar ta gaya masa batun samun aikin nan, amma ta fasa, saboda gargaɗin da Mahmud yayi mata.

***
Jabir da Jamil har mamaki suke yi, yadda adam ya tattarasu yayi watsi da su kamar basu taɓa rayuwa tare ba, ya cigaba da harkokinsa shikaɗai.
Duk da takawa bai fiye samun shiga wurin aiki ba, saboda yawan tura shi assignments da ake yi, ko haɗuwa suka yi da jamil, Adam ba kula shi yake yi ba, kamar bai san shi ba.

Faɗan da Mummy suka yi da Hajiya Lubabatu, ya sanya jabir daina zuwa gidan gaba ɗaya, dama ɓangaren Mummy ne ko na ammi, ammi yayi mata rashin mutunci, Mummy kuma sun samu saɓani da mahaifiyarsa, dan haka ya daina zuwa gidan gabaki ɗaya.

Iman ta sha gyara yadda yakamata, kamar wata balarabiya, fatar nan tayi kyau. Nusaiba ma joining ɗin su tayi a shan sabayar maman Khadija, da maganin maman ilham mai tula-tula, ammi dai tana shan kunun sabayar, kasancewar baya cutar da lafiya, suka yi kyau abun su.
Mussman Iman da ya ƙara fito da kyawun fatarta, gashi ta ƙara cika gwanin sha'awa.
Abu kamar wasa Nusaiba har tallatawa ƙawayenta maganin maman ilham take yi, da maman Khadija mussman ƙwailayen nan, tare da basu cikakken adreshin su.
Maman Ilham na zaune a no. A1 kawo road Kaduna state 0813 561 3021.
Maman Khadija kuma, na zaune a garin zariya Bayan federal palladan08033411249 , haka zalika tana tura kayanta ko ina a faɗin Nigeria, masu shirin yaye da basa son nono yayi musu ciwo ya zube, wanda basa son bayan yaye yaransu jikinsu ya lalace, ga maman Khadija da maman ilham sun shirya tsaf domin tabattar sun gyara ku.

Rumaisa tamkar amarya, takawa ya gwangwajeta da kayan fitar biki, na gani na faɗa, har da zobe da abun hannu na gwal.

Yanzu baya ƙaunar dalilin da zai sanya ace masa ga tafiyar da zai bar gari, saboda rumaisa.

Yau saura kwanaki huɗu a fara bikin mai sunan baba, ruma tana can tare da iman da anty laila wurin gyaran jiki.

Takawa ya dawo gida, sai shikaɗai a gidan yana falo yana duba wata magazine, kawai ya ga Samha a tsakiyar falon.
Mamaki ne ya kama shi, ya tashi zaune saboda ya baje sosai yana hutawa, kuma baƙi ba sa hawowa saman sai dai su tsaya a ƙasan bene, sai in ruma ce ta kawo su saman benen.

"Samha lafiya ki ka shigo babu ko sallama?"

"Adam zuwa nayi na ji matsayina a wurinka"

"Matsayin me fa?"

"Adam baka san me nake faɗa ba, ko raina mini hankali kawai ka ke yi? Ka daina ɗaga wayata kayi blocking numbers ɗina, Adam zuwa yaushe zan cigaba da jiranka?".

"Samha dama ni na ce zan aureki ne? Samha meyasa ba zaki ɗauki ƙaddara ba?"

Cikin fusata ta ce "Amma kai ka ce zaka aureni bayan ka auri wannan yarinyar"

Adam ya ce "A'a, ni ban ce ba Samha, cewa na yi idan Allah ya ƙaddara, bana sha'awar tara mata a gida, iyalina su tashi kamar yadda tsarin rayuwar gidanmu take, dan Allah Samha ki yi haƙuri, na san kin so ni, amma Allah bai ƙaddara zan aureki ba, dan Allah kar ki haddasa mini matsala a rayuwar aurena".

"Matsala Adam, shikenan bani da makoma kenan?"

"Kina da makoma mana, matsayinki ba zai taɓa canzawa na ƴar uwata ba, kuma na san a manemanki ba zaki rasa mai sonki da zai aureki ba, kiyi haƙuri"

Samha ta ajiye jakarta, ta saka hannu ta ɓalle botiran abayarta, matsatsiyar t-shirt ɗin jikinta ta bayyana, ƙirjinta tamkar zai yi magana.

Ta ce "Adam kalleni da kyau? Me na rasa? Meye ban fi wannan ƙwailar yarinyar ba? Da me ta fi ni ne adam, shikenan wahalar banza nayi a rayuwata".

"A'uzubillah" ya faɗa da sauri sannan ya ce "Samha ba iya sura ce dubawa a mace ba, qualities sannan sannu-sannu ba ta hana zuwa, ita ma ɗin za ta zo in da ki ka je. Abunda rumaisa tayi mini a rayuwa, ko meye ba ta da shi, zan iya haƙuri na jure, saboda martabarta da mutuncinta a idona, idan har kina son na aureki, sai dai ki nemi iznin rumaisa, idan har ta amince ba wani abu".

Ta nuna kanta da yatsa ta ce "Adam, ni ce zan nemi iznin wannan ƴar talakawan wai ta bari ka aureni?"

"Babu wata mafita idan ba hakan ba, ba abun da na nema na rasa a wurinta, dan haka dan Allah Samha ki tafi kawai, bana son yi miki wulaƙanci, amma dan Allah ki tafi".

"Papa, yau ko nemana ba ka yi ko, ka sallama ni in gama gararambata, sai yanzu aka gama gyaran gas.... Sai dai rumaisa ba ta ƙarasa ba, idonta yayi mata mummunan gani, Samha a tsaye a gaban mijinta ta turo ƙirji, kamar ta rungume shi, shi kuma daga shi sai dogon wando, da riga armless.

Zagaye su tayi ta wuce, yayin da ya ji wani irin abu mai kama da tsoro da rikicewa ya kama shi.

"Kin ga Samha, dan Allah ki kama hanya ki fita, kar ki haddasa mini matsala a gidana tsakanina da matata muna zaman lafiya"

Samha ta yi murmushi ta ce"Kamar gaske, wai matarka, ayi dai mu gani" ta figi jakarta tayi waje, tare da mamakin girman da rumaisa ta yi, ga abun arziki duk ya fito dai-dai da jikinta.

Rumaisa kuwa kai tsaye ta shige ɗakinta, ta jefar da jakarta da mayafinta, kawai ta faɗa toilet ta shiga ta rufe ƙofa, tana jin yadda zuciyarta take yi mata zugi da raɗaɗi, ta dinga kokowa da wani abu mai zafi da ɗaci, da yake mata kai komo, yaƙi wucewa.

A rikice Adam ya shiga ɗakin yana kiranta, amma tayi masa banza a banɗaki, yafi ƙarfin mintuna ashirin, yana yi mata magiyar ta fito, amma tayi burus da shi.

Sai haƙura yayi ya tafi, tana jin fitarsa ta fashe da kuka, saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login