Showing 135001 words to 138000 words out of 199108 words
gabanta na faɗuwa, ko wani abun hajiya Lubabatu ta je ta kitsa masa, sai dai ta ji ya ce mata "Mun yi magana da jabir galadima, idan turaki ya dawo, zuwa ranar lahadi idan Allah ya kai rai, zamu kai kuɗin auren yarinyar wurinki iman wurinsa, ya ce mini kun gama magana, zamu sanya watanni biyu ne kawai auren"
Gaba ɗaya sai ta ji ya ɗaureta ta da jijiyoyin jikinta, ammi ta ce "To ranka ya daɗe, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Laila ta ce "Lallai ma jabir munafuki ne, yana sane da uwarsa ba ta so, amma yake maganar kai kuɗi? Kodayake hakan shine dai-dai, ta auri jabir ɗin, mu ga ta tsiya, Allah ya tabbatar da alkhairi, ai Allah ya fi su"
Ammi ta ce "Subhanallah, Allah ya kawo mini ƙarshen wannan fitintinu, ni abubuwan ma sun isheni, Addu'a dai nake tayi, Allah ya shiga lamarin nan, bai kamata a hukunta jabir, da laifin mahaifiyarsa ba, tun da shi mutumin kirki ne".
Ruma ko sunan jabir ba ta son ji, dan haka ta bar falon gaba ɗaya, ita zaman gidan duk ya isheta, gida kullum cikin tashin hankali da bala'i, an saka mutum ɗaya a gaba da masifa.
Harabar gidan ta fita shan iska, tana ta zazzagawa, tana kallon fulawoyi, ga sanyin la'asar, yanayin yayi mata daɗi sosai.
Daga sashin Mummy ta hango jamil, ta tsaya tana kallon sa, su kullum suna gidan nan, kodayake ba abun mamaki bane ba, tun da ƴan uwa ne, amma ita a wurinta duk wanda ya fiye zuwa wurin Mummy ba shi da gaskiya.
Ga mamakinta taga yana tunkarota, dan haka ta haɗe rai zata juya ta tafi, ya cimmata da sauri ya ce "Ɗan tsaya mana, yau Allah ya sa mun haɗu, magana zamu yi"
Ta ƙare masa kallo ta ce "Maganar me?"
"Magana a kan abun da ki ka cewa mjinki na kina zargina da kisan Aisha"
Ruma ta ce "Ba rami meya kawo rami,? Ni ban ce ka kashe anty aisha ba, kuma da mijina ku ke magana ba ni ba, dan haka babu ruwanka da ni"
"Amma ko menene ke ki ka kitsa misa, daga auroki ƴar mitsitsiya da ke, kin rikita mana zaman lafiya family"
"Dama can ba zaman Allah da annabi ku ke yi ba, kuma na faɗa ɗin, idan kana da gaskiya, maiyasa a da baku damu da anty aisha ba, sai yanzu kake damun baban sabir, wataƙila ma da kai ake haɗa baki ake ɓata masa suna"
Jamil ya ce "Kin san me ki ke faɗa kuwa?"
"Malam danginmu babu mahaukaci, ban yi gadonsa ba, kuma babu ƴan shaye-shaye"
Jamil ya ce "Ni fa jami'in tsaro ne, zan iya amfani da kakina wurin ladabtar da ke, da tursasaki a kan kiyi bayanin abun da ki ke ɓoyewa".
"To meya hanaka yin hakan tuntuni? Ka yi mana, amma ka sani na san da batun saka sunan anty aisha, a matsayin magajiya da mai girma turaki ya yi, a kan filin sa, da wani kamfani da haɗin gwamnatin tarayya suka karɓa jingina, ake amfani da shi, ana bashi wani kaso, na kuɗi, wanda kai tsaye yake shiga asusun anty aisha. Ka ga idan baka kiyayeni ba, zaka tsinci talatarka a laraba"
"Wa..ww..waye ya gaya miki wannan maganar? Kenan adam saboda wannan maganar, ya fara tunanin ɗora zargin sace matarsa a kaina?"
Rumaisa ta ce "Kai ma kenan saboda ka wanke kanka daga zargi, ya sanya ka ƙirƙiri cewa ya kashe matarsa yayi tsafi da gangar jikinta?"
Mamakin rumaisa ne ya mamaye shi, ya ce "Kuma aka ce miki ni ne na yaɗa wannan maganar? Me ki ke nufi ne?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "Ba ina nufin kai ne ba, kawai na yi tunanin, kowaye ya saka aka sace anty aisha, shi ne ya yi wa mijina sharri, ni ba ƴar sanda ba ce ba, amma ƴar baiwa ce, garkuwa da aka yi da anty aisha shiri ne, kuma idan ba ka da hannu, kar ka damu kanka, sai dai ita rayuwa, iyawa ce, abu ƙailalan zaka yi, ya jefeka cikin masifa a gaba, har ƙarshen rayuwarka, ka sani iya wuya ina bayan mijina, kuma kar ka sake tunkarata da wannan maganar"
Dafe kai Jamil yayi, ya ja da baya,gaba ɗaya ya ma rasa ta ina zai fassara maganganun rumaisa ne? Ta hargitsa masa zance cikin zance wace irin yarinya ce ne haka? Kamar ana controlling ɗin ƙwaƙwalwarta da remote?.
Lokacin da rumaisa ke daf da shiga sashin ammi, taga laila ta fito da sauri, ta yi wa sidi magana, akan ya kawo mota, zasu tafi asibiti iman ta suma.
Da gudu ruma ta shiga sashin ammin, iman na kwance a in da ta barta ɗazu tana bacci, ashe daga haka ta suma, ammi na ta magana amma shiru.
A gaggauce suka ɗauketa, tuni ammi zuciyarta ta karaya, saboda yadda jikin iman ya saki, kuma Ammi ta ɗora alhakin hakan a kan hajiya Lubabatu, da ta zo ta yi mata wannan cin mutuncin.
Ammi ta ce Rumaisa da Nusaiba su zauna a gida, ita da laila suka tafi kai iman asibiti.
Rumaisa ta kasa zaune ta kasa tsaye, lokaci lokaci ta din ga jan uban tsaki ta ce "Allah ya tsinewa babar jabir ɗin nan, da bata san darajar ɗan Adam ba, daga ita har shi wawan jabir ɗin, mara zuciya"
Nusaiba ta ce "Ya zaki din ga zaginsa, shikuma me yayi miki?"
"Ba ruwanki da ni, ai naga take-takenki, ke kike goya masa baya, ke ki aure shi mana" duk da Nusaiba ta girmi rumaisa sosai, dan ta girmi iman ma, amma haka tayi shiru ta kasa magana.
Sai dare laila ta dawo, suka tashi gaba ɗaya suna tambayar laila ya jikin iman ɗin.
Laila jiki a sanyaye ta ce "Da sauƙi, sai dai jini ya hau, zuciyar ta kumbura, amma ta farfaɗo ta samu bacci."
Ruma ta ce "Anty laila dan Allah a fasa auren nan mana, ko dan ceto rayuwarta"
"Ai ni zan fi so yi auren nan, dan nuna mata iyakarta, kuma magana tun da ta riga ta je gaban wambai, rusata ba abu ne mai sauƙi ba, mutumin nan ba ayi masa wasa".
Rumaisa ta rasa abun sa yake yi mata daɗi, ji take kamar ita ce a halin da iman take ciki.
Nusaiba ce ta shirya, ta tafi asibitin, dan taya Ammi kwana da iman.
Yau sai ga rumaisa da tashi cikin dare tana sallar dare, tana yi wa iman da yayanta addu'a, idan da alkhairi Allah ya sa mai sunan baba ya auri Iman. Dan ta san mai sunan baba, akwai zafi, amma mutum ne mai kyautatawa da tausayi, kuma ba ta taɓa ganin abun da ya damu da shi sosai bayan ita da mama ba sai iman.
Da gari ya waye, laila da rumaisa suka je duba iman, suka kai musu abinci.
Iman ta farfaɗo, amma ta yi pretending, bacci take yi, saboda ba ta son magana, dan numfashinta sama-sama take yin sa.
Ammi da Nusaiba suka koma gida, an yi sa'a ruma da anty laila an ɗan fara shiri, sannan laila ta sarawa tsagerancin rumaisa, mussaman jiya, da ga tsigalewa hajiya Lubabatu.
Wayar iman na hannun rumaisa, dan yanzu wayar kamar ta su ce su biyu.
Rumaisa ta kira mama ta ce "Mama dan Allah ki zo ki duba iman, ba ta da lafiya muna asibiti"
Mama a duk lokacin da ta ji an ce iman ba ta da lafiya, hankalinta yana tashi, mussaman da ciwonta yake mai hatsari.
Bayan ta gama wayar ta dubi laila ta ce "Anty laila".
"Na'am".
"Wai yaushe zan yi video call da papa ne?".
Laila ta ce "Sai lokacin da ki ka fara bin umarnina"
"Anty laila dan Allah, so nake na ganshi"
"Kin fiye taurin kai ne, sai lokacin da ki ka fara yarda zaki yi abun da nace miki ba gardama"
"To me ki ke so na yi?"
Ta ce "Ba wannan ba ma, so nake mu bashi mamaki, sai kin fi haka kyau da cika, ke baki ga yadda jikinki ya fara yi ba ne"
Ruma ta ce "Na gani, kullum idan na je wanka ina dubawa, idan sun fara girma".
Laila ta yi dariya ta ce "Ashe dai kina son su fito".
"Wallahi ina so"
"To ki mayar da hankali da cigaba da shan kununki, bayan sabayar maman Khadija ma, akwai maganin maman ilham, shi kuma a iya fito da nono yake aiki, baya sanya ƙiba, haɗinta haɗi ne mai kyau ɗan mambila ita ma.
Rumaisa daga lokacin da mace tayi aure, zama bai ganta ba, shekaruna a ƙalla talatin da huɗu, amma kalleni kamar ƴar ashirin da biyar.
Bana zama, abu ba sai ya lalace ake gyara shi ba, garkuwa ake yi kafin ya faru, nan gaba kina haihuwa kina shayarwa, dole zasu ranƙwafa ko su zube, amma idan ki ka tattala su, ki ka kula da su, tsaf zaki yi ta haife-haifenki, ba tare da kin sirewa miji ba.
Kuma ba ina nufin ki je ki sai abun da baki san menene ba ki sha, ba haka nake nufi ba, duk abun da na baki kiyi amfani da shi, na san kyansa da ingancinsa, kuma na san da me aka yi shi.
Kin ga maman Khadija na ta haɗin kunu ne na sabaya, da yake gyara jiki, ya sanya ƙiba da gyara fata, kuma kowa na iya sha.
Ita kuma maganin maman ilham, akwai matan da suna da ƙiba, basa buƙatar yin ƙibar, gyaran nonon kawai suke so, ita maganinta haɗe-haɗe ne, na natural abubuwa, ba shi da side effect kayanmu ne na islamic da saiwoyi masu kyau, ake kawo mata daga mambila ta haɗa.
Ya ki ke gani, idan mutum ya haɗa garin kunun sabayar maman Khadija, da kuma maganin gyaran nono na maman ilham?
Rumaisa ita mace ba ta zama ba gyara, dan haka so nake ki cika kiyi kyau, kan dawowar takawa".
Ruma ta yi shiru sannan ta ce "Ni fa na zata kawai amfaninsu a shayar da ɗa, ashe mutum gori ake yi masa idan bashi da su"
Laila ta ce "Sosai makuwa, shiyasa ake son gyarawar ai, kuma gori ba iya na mata ba, har na miji, wanda ya fi kowanne takaici ba, miji yayi miki gori dan baki da su, ko kin bari sun lalace"
Ruma ta sake gyara zama ta ce "To ita ma na maman ilham ɗin zaki sai mini?"
"Eh mana, mai ze hana? Ki din ga biyayya kawai, mun gama magana da ita ma".
Cikin farinciki ta ce "Allah ya sa su fito kan papa ya dawo, kin san me? ce mini fa yake, wai nasa yafi nawa girma, wai nawa kamar girman wake, daga baya kuma wai kamar murfin jarkar faro".
Ƙyalƙyalewa da dariya laila ta yi ta ce "Rabu da shi, kan ya dawo zai sha mamaki, sai ki rama. Ai tun da akwai kunun maman Khadija, da kuma haɗin maman ilham, an wuce wurin, kin wuce gori mutuniyar".
"Allah ya sa anty laila, to zasu kai kamar na samha? Su Fauziyar nan, wai a dubi samha ta fini komai amma ya aureni, idan nawa suka fi nata, ai ba zai aureta ba ko?"
Laila ta ce "Wannan kuma effort ɗinki ne zai sanya, ya aureta ko ya fasa"
*INA MASU SON WUCE GORIN KISHIYA, DA NA MIJI, KAI HAR MA DA NA ƳAN UWANKI MATA, TO KU GARZAYA KU GWADA KUNUN SABAYAR MAMAN KHADIJAH DA KE ZAUNE A ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN ZARIYA 08033411249, KU TUNTUƁETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA*
*HAKA ZALIKA KU HAƊA DA MAGANIN MAMAN ILHAM MAI TULA-TULA, MAGANINTA INGANTACCE NE, WURIN BIYAN BUƘATUNKU, BA TARE DA CUTAR DA LAFIYARKU BA, KU TUNTUƁETA TA LAMBAR WAYARTA 0813 561 3021 TANA NAN A KAWO ROAD KADUNA*
*HAJIYATA KAR KI BARI MATA SU SHA GABANKI, SU RIGAKI MALLAKAR MAGANIN MAMAN ILHAM, DA NA MAMAN KHADIJAH, MACE SAI DA GYARA, SUNA TURA KAYANSU KO INA A FAƊIN A NIGERIA, HAR MA DA ƘASASHEN DA MUKE MAƘWABTAKA DA SU*
Bayan sallar azahar, mama ta je ta duba iman, jikin da sauƙi, amma dai tana jin jiki sosai.
Laila kuwa mama ce ta burgeta, saboda yadda take komai nata a nutse, gashi tun da tazo, rumaisa ke tsokanarta take son sakata magana, saboda kamar kakarta ta mayar da ita.
Mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ya tarar mama bata nan, abun da yafi komai ɓata masa rai kenan, dan haka ko abinci yaƙi ci, ya koma ƙofar gida ya zauna.
Ya kai awa guda da rabi sannan mama ta dawo.
Mama kamar ƴa da uba, a wajen ta fara yi masa bayani, dan ta san ba shi ba, hatta sauran ƴaƴanta, ba sa son su dawo su ga bata nan, amma na sa yafi yawa.
"Ƙanwar mijin rumaisa aka kwantar a asibiti na je dubata, daga nan na wuce mandawari na sada zumunci da ƴan uwana"
"Wacce daga ciki?"
Mama ta ce "Wadda ka ke tsoratawa mana, iman, ciwonta ne ya tashi, ban ma tarar da hajiyar ba, sai wannan yarinyar, da wata yayar mijin rumaisan".
"To ya jikin nata?"
"Jiki Alhamdilillah, amma dai har na taho bata buɗe ido ba"
Mama ta ɗan yi shiru tana nazarin mai sunan baba, sannan ta shiga gida.
Mama na shiga gida, umar ya ciro wayarsa ba tunanin komai ya kira wayar Iman.
Sai dai rumaisa ta ɗauki wayar.
"Ina me wayar?".
"Mai sunan baba muna asibiti fa, ba ta da lafiya, ba ta tashi ba haryanzu"
Ya katse wayar ya tashi, duk da yunwar da yake ji, ya shiga gida yayi alwalar magariba ya fito.
Ya gama yanke koma menene, yau sai ya je ya ga jikinta, dan gaba ɗaya hankalinsa ya tashi.
Bayan kowa ya tafi, ya rage daga iman sai nusaiba, laila ta ce za ta je gida tayi wanka ta dawo, ba sai ammi ta kwana a asibitin ba, su kwana ita da iman da Nusaiba.
Tun kan ya shigo, gabanta ya tsananta faɗuwa, ba tare da ta san dalilin hakan ba, sai dai ba tare da tayi tsammani ba, ta ji an murɗa ƙofar yayi sallama.
Da sauri iman ta fara kiciniyar neman hularta, dan kanta ko ɗan kwali babu, ba ta taɓa zaton mai sunan baba, ko da wasa.
Nusaiba ta ce masa "Ina wuni"
Ya amsa mata a taƙaice kamar yadda ya saba.
Ba tare da fargabar komai ba, ya je gaban gadon, ya zauna a kan kujerar da ke gaban gadon.
Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Yaya umar ina wuni"
"Ban ganshi ba" ya bata amsa. Kamar yadda yayi tsammanni, ta ɗago ta kalleshi, ta mayar da kai ta sunkuyar.
Ya waiwaya ya kalli nusaiba ya ce "Can you excuse us?" Ba musu Nusaiba ta tashi ta fita.
Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Meya sameki?" Yayi maganar kamar ɗan sanda na tuhumar mai laifi.
"Bani da lafiya"
Jin shiru bai ce komai ba, ya sanya ta sake ɗagowa, ya zuba mata ido, yana jiran ta bashi amsa, dan wadda ta bashi ba ta gamshe shi ba.
"Zuciyata ce take kumbura"
"Meyasa?"
"Nima ban sani ba"
Ya ce "Kin sani"
Shiru ta yi tana wasa da yatsunta.
Ya ce "Well, Allah ya sauwwaƙe, kin san condition ɗinki, bai kamata ki din ga wasa da lafiyarki ba, and na ji rumaisa ta ce You are getting engaged very soon, Allah ya sanya alkhairi"
Kawai ta fashe da kuka, yayi ƙuri da ido yana kallon ta, dan bai san me zai ce mata ba.
Tayi me isarta, sannan ya ce "Auren ne ba kya so?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Meyasa ki kai shi gidanku, idan ba kya son shi?"
Iman ba ta san ya aka yi ta tsinci kanta da yi wa mai sunan baba bayani ba "Bana son shi, mamansa ta ce ba zai auri wadda ba ta da asali ba, gashi ya riga ya kai maganar wurin wambai"
"Idan ba kya son shi, wa ki ke so?"
Ɗagowa ta yi a hankali, suka haɗa ido, jikinta yayi sanyi yayin da mai sunan baba yaji tsigar jikinsa tana tashi.
"Kuka ba ya maganin matsala, Addu'a ce magani, Allah na iya canza komai within seconds"
A sanyaye ta ce "Labarina ba zai canza ba yaya umar, yarinya ƴar tsintuwa"
Ya miƙe tsaye ya ce "Zai canza, put your trust on Allah, Allah Ya ƙara lafiya" tabi bayansa da kallo, wata irin ƙaunarsa na ratsa zuciyarta.
Yayin da shi ma yake jin matsananciyar soyayyarta da tausayinta a nasa ran, ji yake tamkar kar ya tafi, sai ta samu cikakkiyar nutsuwa ta kwantar da hankalinta.
Yana daf da kaiwa ƙofa, Jabir ya buɗe ya shigo.
Ayshercool
08081012143
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Kallon-kallo suka shiga yi, tsakanin shi da umar, sai dai babu alamar mai sunan baba zai bashi hanya, sai jabir ne ya kauce masa ya bashi hanya.
Mai sunan baba na fita, ya jiyo muryar jabir yana yi wa Iman tsawa "Wai iman waye wannan, meye alƙarki da shi, uban me ya zo yi wurinki?"
Cikin wata irin azababbiyar zuciya mai sunan baba ya koma ɗakin, motsin shigowarsa ya sanya jabir haɗiye sauran maganar sa.
Mai sunan baba ya taka, ya je gaban jabir ya tsaya, ya ce "Ni zaka tambaya waye ni, da dalilin da ya sanya na zo wurinta"
Jabir ya haɗiyi yawu cike da kishi ya ce "Na san kai yayan matar Adam ne amm....
Umar ya kaste shi ta hanyar cewa "Bani da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ku, ƙanwata ake aure a familynku, sai dai akwai mutunci da karrama juna, albarkacin ana auren ƙanwata a familynku, ni yakamata ka yi wa duk wannan tambayoyin ba mara lafiyar da ke kwance a gadon asibiti ba, ko ba ka san abun da yakamata ba".
Da ƙyar jabir ya aro jarumta, dan gani yake, da yayi kyakykyawan motsi, mai sunan baba zai iya kai masa naushi, ya ce "Amma ka san babu wata alaƙa tsakaninmu meyasa za ka zo in da take, aurenmu fa za ayi"
Mai sunan baba ya ce "Amma ba ayi ba ko?" Jabir yayi shiru.
Mai sunan baba yayi tsaki, ya nufi hanyar fita, a daidai lokacin laila suka shigo ita da Nusaiba, bai kula su ba ya fice.
Laila ta ce "Waye wannan?"
Nusaiba ta ce "Yayan rumaisa ne ya zo duba iman, shi ya korani waje ma".
"Au ya koraki waje ma, wane irin abu ne zaku din ga barin ƙarti suna kaiwa suna komowa a