Showing 1 words to 3000 words out of 190952 words
Chapter 1 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
๏ปฟ๐ซ *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*๐ซ
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always๐
_โ๐ฟM Shakur_
_Bismillahil Rahmanir Raheem, da Sunan Allah Mai Rahama, Mai Jinkai_
_This Novel is solely work of fiction, banyi dacin zarafin wani ko wataba, dafatan zan nishadantar daku_
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
_What is drugs?_
_What are illicit drugs?_
_mesa people do drugs?_
_What do they feel when they do it?_
_why why why shaye shaye?_
_Oh Hey VIPs dina๐๐ผ ever been curious about this questions? Well this novel will walk you through everything dangane da shaye shaye, overcoming it and many many more ku gyara zama a kakkabe zani_
1๏ธโฃ
Horn da akayi yasa mai gadi yafito da saurinshi daga dakinshi that is just beside the gate ya zare sakatan gate din ya wangale gate din sabida motar ta shigo, wangale gate din da akayi yasa wata yar budurwa da bazata wuce 25-26yrs ba da wani matashi ke zaune gefenta kan plastic chair yana sanye da bugaggiyar shadda milk duk suka dago kansu suna kallon Gate din ganin wanda zai shigo ciki da alamun tadi sukeyi abunsu dan kowannen su na dauke da murmushi kan fuskarshi, motar gidansune ta shigo har zuwa inda ake parking motar yay parking, bude bayan motar akayi wata yarinya fara dake sanye da jean da t-shirt ne tafito ta tsaya tana turo baki tai kini kini da rai, white flat shoe ne na vine a yar karaman kafarta da dududu size dinta bazai wuce 37 ba yar kafar, sai pencil jean din jikinta daya tsaya mata a daidai idon sahu, kafarta na haggu sanye dawani hadadden leg chain daya kama yar faran wrist din kafan nata, yama kafan nata kyau sosai bana wasaba dan silver color ne, ba karamin kamata sky blue Jean din chinos din yayiba batada wani girman ass but is a lil bit bumpy saidai tanada wani mahaukacin hips curve, irin matan da ake cema cylinder shape kenan, wani white non logo t-shirt ne ajikinta yadin so soft fari kal babu ko single stain ajikin rigan, tasaka wani simple necklace mai hawa uku masu dauke da pendent din moon shape wanda the last one ya sauko har kasan wajen gab da cikinta suna walkiya, babu komi kan fuskarta batasa makeup ba, dan ficicin pink lips dinta sun bushe sosai sai manyan idanunta da kwayan idanun kenan mai ruwan toka ko kadan ba bakake bane, tanada cikan gira baki, sai dan karamin sky blue dan gyalen data yane kanta dashi da ana ganin almost rabin kitson ta yan fici fici kalaba masu kyau sosa, wrist dinta na haggu sanye da digital watch sai dayan wrist din tadaura wani fine simple bracelet daya karama little tiny hand din nata kyau, ko kadan bata da girman jiki, batada wani tsayin kirki badai gajera bace, sanan batada kiba kawai she is super portable, bata da girma kuma baxaka kirata karama ba. Kallon direban daya bude kofa yafito tayi bayan ya kashe motar, turo baki tayi tareda hararanshi cikeda tsiwa tace "kai Isa bazaka bani jakana ba ninagaji da tsayuwa" da sauri Isa direba yazo wurin cikeda girmamawa yace "sorry Autan Mummy, dan gyara na dauko miki to" matsawa gefe tayi tana kwafa tareda kama waist dinta da hannu daya tana jiranshi yadauko mata jakan ya bata, wani bagpack yadauko mata irin na yan matan nan da yan makaranta ke amfani dashi da ake goyawa abaya fari ya mikamata yana murmushi yace "yauwa to ungo gashinan nadauko miki Auta" hannu tasa ta fizge jakan kaman ana fada sanan tajuya ta tafara tafiya tana fita daga parking tent din tai cikin yard dinsu, das das take tafiya kaman bataso tayi hips dinta na juyawa gashi jean ne ajikinta abin looks so alluring to the eyes, tundaga nesa take ballama Ya Siddiqa dake kallonta cikeda takaicin ta harara, saida takaraso wajen taja wani mugun tsaki tace "bashi ko tara eh? Anwani kafe mutun da idanu kaman za'a tsotsemai jinin jiki, sa'ido dai sana'ar banza ne" tai wani fari da ido tai gaba abinta batare data gaida koda mutumin dake gefen Siddiqa ba, azuciye Siddiqa ta tashi daga kan kujeran zata bita da sauri Sadiq yarike mata hannu yace "me haka ina zaki? Ki barta yarinya ce bakigani ba" cikin fushi Siddiqa ta fizge hannunta tace "Baby wlh duk rashin kunyan ta tai dani ni kadai bazan ma tanka taba, amma tsabagen rashin kunya ta kallemu taja tsaki sanan tacemana sa'idawa, that's an insult wlh saina fasa mata baki yau agidan nan" kafin yamayi magana ta fizge hannunta tai ciki tsabagen yanda kirjinta ke zafi yana tafarfasa sabida yanda Auta tamasu itada Sadiq rashin kunya haba mana, agaban wanda zata aura zata disgata.
Bude kofar falon nasu tayi ta shiga daidai Auta dake shirin shiga corridor ta waigo jin anbude kofan, harara ta balla mata cikin murya kasa kasa tace "mayyar tabiyoni" dawani irin gudu Siddiqa tanufota dan taji metace wato itace mayya, ganin Siddiqa tabiyota da gudu yasa ta yunkura zata gudu amma ina Siddiqa tariga ta chapke bayan riganta ta fizgota azuciye ta bugata da bangon corridor cikin fushi tace "uban waye sa'idawa? Su waye zasu shanye miki jini sanan wakike cema mayya?" zaro idanu tayi cikeda rashin kunya tana kokarin ture hannun Siddiqa data chakumo gaban white t-shirt dinta tace "me haka? Kika batamin white rigana wlh saikin wanke shi, ki sakeni nace ko" bude kofar wani daki dake corridor akayi wasu yan mata guda biyu suka fito duk sunfi Autan girma alamun yayyunta ne suma dake kama da Siddiqa sosai, black beauty dasu, daya daga cikinsu wacce daga gani ita kebin Siddiqa tace "yauwa Ya Siddiqa cimana uban mara kunyan shegiya mai idanun mazuru" cikeda tsiwa tana kokarin ture hannun Siddiqa ta kwace kanta tace "eh kekuma mai idanun gapiya, gapiyan ma maicin kashi" dariya tayi sosai tace "eh gwaradai gapiya maicin kashi da mazuru mai satan kaji, kinji Ya Siddiqa lallasata dama atike nake da ita" bude wani kofa akayi dake facing corridor alamun dakin shine kodai master bedroom kokuma dakin wani babba agidan ne, wata matace baka itama Siddiqa na kama da ita sosai ta fito da akalla zatai shekara hamsin da hudu 54, dattijuwa ce amman jikinta nada kyau sosai tana sanye da doguwan rigan atampa da aka mata stone work hayaniyan dataji yasa tafito agurguje daga bayi dan tun dazu tana bayi ganin yanda Siddiqa ta chakume Auta yasa da sauri tajawo kofar dakin tanama Siddiqa wani irin mugun kallo tace "me haka kika chakume auta kasheta zakiyi?" cikeda fada dajin haushi Siddiqa tace "Mummy wai yarinyar nan nida Ya Sadiq zata kalla tacema sa'idawa, sanan wai zamu shanye mata jini, kuma wai ni take cema mayy......" da sauri Auta ta chabe maganar cikin muryanta mai zaki da dadi kaman zatai kuka tace "Mummy karya take mini, aini bance hakaba, sune keta kallona kuma sai hararana Ya Siddiqa takeyi fa, ni banmata komiba daga dawowa na" kafin Mummy tai magana Siddiqa ta bugata da bango tana jijjigata tace "dan ubanki nike miki karya, bakida kunya ko sabida kinga kinyi girma kema kin fara nono" cikeda jin dadi Lubabatu Mai bin Siddiqa tace "yauwa Ya Siddiqa ki gurje shegen bakin datake mana rashin kunya dashi abango, shegen bakin kaman tsuliyan kaza" harara Auta data fara kuka ta watsama Lubabatun tafashe da kuka tace "muguwa kawai, agulmawiya, ai nadai fiki nonon kumadai, da fuska ki kaman burnt abinci" yowa wajen Lubabatu tayi cikin son ta jibgeta tace "dani kike?" Lubabatu tai wajen ta daga hannu zata sharara mata mari Mummy ta daka musu tsawa. "Siddiqa! Luba!" duk dagokai sukayi suka kalleta, harara Mummy ta zuba musu tama Siddiqa dahar lokacin ke chakume da Auta tace "cikamini yarinya kafin na mugun sabamiki" sakinta ahankali Siddiqa tayi da sauri Auta tai wajen Mummy tafada jikinta tasaki kuka, cikin kuka tace "Mummy kinga Ya Siddiqa ta shakemin wuya kasheni takeso tayi, Mummy kice mata karta karacemin nafara nono banso" tafashe da kuka sosai, ta tsani insuna fada suce mata sabida tafara nono ne kaman su take musu ranshin kunya ta tsani maganan, shafa bayanta Mummy tayi cikeda lallashi tace "zan musu magana, ta Allah batasu ba kinji, je wuce dakinki kiyi wanka zan kawomiki abincin ki yanzun nan" gyadama Mummy kai tayi tasa hannu tana share hawaye tawuce sumi sumi sanan ta juyo ta kalli yanda suka tsaya charko charko suna kallonta wani matsiyacin murmushi tayi irin na neman tsokanan nan sanan tama Siddiqa da Luba gwalo, da sauri Luba tace "Mummy kinga tana mana gwalo ko" da sauri Auta tabude kofar dakinta ta shiga, kwafa Luba tayi cikin konkoni tace "wlh gamuwata dake bazatai kyauba, nakama yarinya wlh sainai mata jina jina saidai duk abinda za'amin amin" cikeda fushi Mummy tace "mafashi, inbaki daketa ba kin raina Allahan daya hallice ki, shegiyar yarinya yar bala'i kawai, da katon kanta kaman na giginya" bude kofa Luba tayi ta shiga tana magana ciki ciki tana kunkuni tace "badai kaina ba kan autanki dai" daga murya Mummy tayi tace "me kikace dan ubanki?" turo baki tayi da kyar tace "aini badake nike ba" "kimayi kiga in ban zubar miki da hakora ba da ranan nan" Mummy tafada tana huci, tabe baki Zeenatu da tuntuni tana tsaye tana kallon draman batare datace musu komi ba tayi tajuya zata shiga dakin da sauri Mummy tace "zonan Zeenah" juyowa tayi tama Maman tasu kallon haushi tace "gani Mummy" binta Mummy tayi da kallo daga sama har kasa tace "nasan duk yayana kece slow poison, wanan dabakice uppan ba Allah kadai yasan me kike hadawa aranki, wlh ko kurjewa naga Auta tayi, kurjewa nace to wlh sainaci ubanki, wuce kije kitchen kihado mata abincinta kikaimata taci" hararan kofar dakin da Autan ke ciki tayi tajuya tai hanyar fita daga Corridor, kallon Siddiqa dahar lokacin ke tsaye idanunta sun cika da kwalla tap tsabagen yanda abinda Mummy tayi ya bakanta mata rai tayi, yarinya tazo tamata rashin kunya sanan tama wanda zata aura Ya Sadiq rashin kunya dudda haka Mummy batace komiba, murmushi Mummy tayi ta taho wajen kama hannun Siddiqa tayi suka fita daga corridor sukai falo cikeda lallashi tace "ya isa to kekuma, bakomi Auta zatayi kudingajin haushinta ba, yarinya ce, dududu guda nawa take aduniya eh? Daga ke har Sadiq din ai duk yayyinta ne? Yakuri kinji zan mata magana zata dena, wuce ki koma wajen Sadiq kinbarshi shi kadai, kuma ki saki ranki karya ganki duk wani iri yagane akwai matsala, nunama saurayi ake kana tsananin son dan uwanka, tashi kitafi" tashi Siddiqa tayi tawuce tafita daga dakin deep down bata hakura ba tai alkawarin saitaci uban Auta wlh.
Fitowa da Zeenatu tai daga kitchen rikeda plate da jellof rice kekai dayaji fried plantain akai yasa Mummy tace "ahaka zaki kaimata abincin kaman zaki kaima awaki? My friend go back to that kitchen ki daura abincin nan kan tray, ki dauko mango juice din dana hadamata kidaura akai da glass cup, ki kuma samata salad ki sako mata nama guda biyar kinsan tanason nama" juyawa Zeenatu tayi tana kunkuni tace "saikace president zan kaima abinci" kasan cewan Mummy bataji taba yasa ta gyara zama tacigaba da kallon datake yi, jin Zeenatu tasake fitowa yasa tadago kai ganin tayi yanda tace yasa tace "kuma wlh ko kallon banza kika mata sainaci ubanki, kina bata abincin kifito kinajina ko banso adameta bacci zatayi" gyadamata kai tayi tai corridor.
Bude kofar dakin Zeenatu tayi babu kowa adakin saidai karan saukan ruwa dataji alamun tana wanka, dakin fess fess sai kamshi yake, fentin dakin off white ne sai dan gadonta dakeda girma normal normal an shimfida bargo mustard, curtains dinta kuma combination of white and Mustard kana shiga dakin zaka gane mai dakin nason this two colors white da mustard, karasawa ciki Zeenatu tayi tana kallon cookie jar dake kan bedside drawer ta dako rabi basuyiba, suma sunada cookie din dan Mummy ke ijiye musu adaki yara sudan sami kayan kwalama but su harsun cinye nasu dayake su ukune da ita sai Ya Luba, da Ya Siddiqa, itako Auta dakinta ita kadai dudda ma tsabagen rigima da fadan dasuke yi ne yasa Mummy taraba musu daki but dudda haka shegiyar bata iya kwana ita kadai dakin kawai zamanta ciki da ranane kawai dare nayi takeyin dakin Mummy, Mummy ma saitai bacci take iya sneaking out ta tafi dakin babansu in yana garin in kuma bayanan to tare suke kwana, ajiye mata abincin tayi akan gado daidai lokacin tabudo kofan bayin tafito daure da mustard towel dinta akirji daya saukan mata iya cinya tana kallon Zeenah data ijiye mata abinci tana turo baki takaraso ciki tana hararan ta tace "me kikemin adakina dakin kine eh, kifita kona hadaki da Mummy wlh" hararanta Zeenah tayi saikuma tai murmushi cikin lallabawa ta kalli jar din cookies din tace "auta indan dibi cookies dinki?" wani kallo auta tamata saikuma ta balla mata harara ta zauna kan gado abinta tareda daukan tray din tadaura kan cinya zata faraci, ahankali Zeenatu ta zauna kusada ita murya chan kasa irin muryan begi begi dinan tace "haba yar kanwata Rahima naaa, indan dauka, 2 kadai zan dauka namufa yakare ne please" turo baki tayi ta make mata kafada ashgawbe tace "ba bakusona ba Mummy kadaine ke sona agidan nan, kuyita sa Dady namin fada, jiya saida kikaja Dady yasani nai wanke wanke bansan wani gulma kikamai ba, bazan bayarba" da sauri Zeenatu tadaura hannunta kan kafadarta aranta cewa take "shegiya mai shegen kafiya wacce bata mantuwa kawai, zaki gane kurinki ne yau" cikin sigan lallashi tawani jawota jikinta tace "kai, Allahu Rahima, to kiyakuri bazan karafadamai ba kinji Autan mu, yakuri, in dauka eh Autan Mummy da Daddy mu" wani irin murmushi tayi cikedajin dadi ta gyadamata kai tana gyara zama tace "dauki 10 nabaki duka" tashi Zeenatu tayi da sauri cikeda jin dadi tai wurin jar din tace "thank you Rims Auta" tadebi cookies din tai hanyar fita daga dakin sanan ta juyo ta kalleta ganin bata faracin abincin ba tana kallon abincin tace "kici abincin mana" yatsine fuska tayi ta dago kanta ta kalli Zeenatu tace "Ya Zeenah the food smell peprish wlh" aran Zeenah tace "mayya, ba Ya Zeenah ba ko Anty Zeenah zakice min bazanji tausayin ki ba, kinsaba kirana ai gasai, hancinta kaman na aljanna hartaji kamshin yajin" murmushi tayi tace "common ai Mummy bata bari asa yaji tasan bakison yaji, ci babu yaji ko kadan, natafi" gyadamata kai tayi tadebo rice din takai baki, maida kofar Zeenah tayi tarufe bayan tafito takafa kunnenta jikin kofar tana murmushi kaman an mata kyautan makka ba'a banza Mummy ke cemata kunama slow poison ba saitayi baxaka taba cewa ita bace ko zata iyaba, su Siddiqa da Luba biyemata suke suyita hauka tana haukata su, itako cin ubanta take ta karkashi.
Ahankali take tauna shinkafan dan bata iyacin abinci da sauri sauri ba, wani irin masifan yaji dataji waaaa abakinta kaman an nika attarugu buhu daya a abinci yasa tafeso abincin waje furururr da gudu, da sauri tadau mango juice din dake kan tray din ta kwankwade tana nishi da sauri da sauri, ajiye cup din tayi ganin batadena jin yajin ba yasa ta shiga hurama bakinta iska tawani irin zabura ta mike tray da abincin duka suka kifo kasa tana nishi fast fast, idan akwai one thing da her whole body baya iya tolerating in this life is pepper, wani irin ihu takurma tareda fashewa da kuka tana kiran Mummy hakan yasa Zeenah ta kwasa da gudu tana dariya tai dakinsu ranta fess, tai maganin mara kunyan.
๐ซ *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*๐ซ
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always ๐
_โ๐ฟM Shakur_
2๏ธโฃ
Bude kofan dakinsu da gudu tayi ta shiga tasaka sakata da sauri Lubabatu dake kwance tana danne dannen awaya tace "kekuma dawa zaki shigowa mutane daki da gudu haka?" hannu Zeenah tasa abaki alamun tai shiru kar Mummy tajisu hakan yasa Lubabatu tai shiru tana kallonta, ihun auta dukansu sukaji ta kwalama Mummy su kira tana kuka sosai atare dukansu suka fashe da dariya Lubabatu ta taso daga kan gadon da sauri tazo wajen da Zeenah ke tsaye tana dariya tace "me kika mata makira eh?" wani irin murmushi Zeenah tayi kafin tace "wanan Black Cameroon pepper dinan na container na juyemata duka a abincin aiko taci shine take kukan nan gobema takara zama bayan tasan hanyan kitchen asa nakai mata abinci saina samata wanda yafi wanan" takara kwashewa dawani dariyan, shiru Lubabatu tayi tana kallonta cikin jin haushi tace "haba Zeenah ai duka kuma yay yawa kema kinsan koni bana iyacin Black pepper nan fadanshi yay yawa balle ita dabama tason yaji ko kadan inda tata ta za'abi da karma ai girki da attarugu just tomato and onion, inama laifin 1 spoon koshi ya isa yakoya mata lesson kika juye duka kinsan awa nawa zatayi tanajin yajin kuwa?" maganan Luba yasa Zeenah itama duk taji wani irin badadi zatayi magana sukaji muryan Mummy tana ihu tace "wlh, wlh kashekine kawai bazanyi ba yau Zeenatu inna kama ki, muje Auta" takama hannun Autan dake kuka sosai tabude dakinta suka shiga ciki dakine hadadden gaske komi tsaf yana kamshin turaren wuta, zaunar da ita tayi akan gado tace "zauna ina zuwa bari na kawo miki gishiri da ruwa yajin zai tafi stop crying" gyadama Mummy kai tayi tana hura baki tana kuka Mummy tajuya tafita da sauri daga dakin tai kitchen dinsu taje ta dauko salt da ruwa a fridge tahado mata da yogurt tadawo, gishiri da ruwa tabata da sauri ta karba tasha sosai tana kuka