Showing 66001 words to 69000 words out of 190952 words

Chapter 23 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

411

da rana jikin ya rikice haka yake lallabawa, tuni yakarbi sick leave awajen aiki, dan yanzu mataimakin shi shiyahau kan kujeran chief judge din high court, yaranshi kullum suna tareda shi adaki, ko Mummy tasan yaran sunason mahaifinsu to the extreme saisa suke bata tausayi yanda duk sukai zuru zurun sabida rashin lpy shi, another thing data kara lura dashi shine duka yaran basu damu da itaba ayanda suka shaku suka kuma damu da baban su basu shaku da ita hakaba, karfa abun yazamto tana kokarin bata yar wata agarin haka tarasa soyayyan nata lura da hakan yasa duk in suna zaune su kadai ko tare da baban su zata shiga cikinsu taita jansu jiki tana musu hira nai dadi, tsawon one week dinan Sadiq din Siddiqa yazo yagaida Abba yafi sau uku, while Sameer bai samu yazoba dan washe garin ranan dayakai Rahima Rehabilitation Centre yana zuwa office aka turashi wani assignment maiduguri dazai daukeshi 1 week.



Yau lahadi, tun safe as usual akai mata detox dinta taci kuka takoshi idanun nan sunyi suntum suntum akasa taci breakfast dinta dan dole, saida taci dan dolenta kullum wasu irin abinci ake bata da bata sansu ba kuma kullum sai sun tasata agaba tai wanka ga shan magani safe, rana dare, saida tai almost 30min a dinning sanan aka maida ta daki akace taje tai bacci, bacci tayi sai wuraren 1 ta tashi, tana kalle kalle.



Shigowa Sameer yayi rehab Centre da motarshi, parking motar yayi a parking space yana kallon premises din da kaman bakowa komi kal kal kafin yabude motar yafito yana sanye dawata blue shadda dayasha aikin hannu yana baza uban kamshi kanshi ba hula danshi gaskiya ba ma'abocin son hula bane, wayarshi yadauka yamaida kofar motar yarufe sanan yawuce reception yana takun nan daidai, yana shiga kafin ma yakarasa receptionist din ta gaida shi. "welcome Sir. What can we do for you sir?" ahankali yace "I came for a visit, want to see a patient" da sauri tace "your name sir" ahankali yace "Lieutenant Sameer Simran Sameer" da sauri ta shiga database dinsu nan tagani sanan ta kalli security that is at the door tace "Bala take him to visit room" sanan ta kallai tace "you will see her in a bit sir" gyadamata kai yayi yawuce Bala yakaishi har wani daki dakenan hadadde harda TV ga kujeru biyu ga table a tsakiyan su, ga water dispenser wayarshi yaciro yana dubawa.


Landlines din ward receptionist din takira wata nurse tadauka tace "Nurse patient number 16 have a visitor, take her to visit room" gyadamata kai Nurse din tayi tace "OK" tajuya tana kallon Rahima data tashi daga bacci tun dazu ta tashi zaune ta kifa kanta jikin window tana kallon waje yanda bishiyoyi da flawan backyard din keta kadawa sabida iskan da akeyi kaman za'ai ruwan sama, karasawa wajen gadon tayi ta tsaya akanta tace "number 16" ko kallonta Rahima batayiba dama tasan bazata kalleta ba dan gabaki dayansu yanzu tadena musu magana cikin patients dinsu kuwa har yau magana baitaba hadata da wataba dudda tana ganin wata datake yawan kallonta intaje wanka ko dinning amma ko kallon kirki basu isheta ba, ahankali tace "kizo ana kiranki come with me" ko kallonta Rahima batayi ba bakumata da alamun tashi hakan yasa nurse din ta kwalama Asabe kira. "Asabe, Binta" tanajin haka ta sauko daga gadon tana balla mata harara da kumburarrun idanunta, ta mugun rame sai fari data kara kaman mara jini kitson ta ya tsufa sosai dan gashin gaban kanta yasoma zarewa yana warware kanshi yana kwanciya dan tanada coily hair daman sosai kaman gashin jaririya, hulan kanta ta gyara batare data kalletaba hakan yasa Nurse din takama hannunta, ahankali take tafiya dan batada karfi ko kadan cikinta daman tunda aka fara mata detox dinan ya hargitse kaman ba nataba, agaban wani daki taga sun tsaya da aka rubuta visit a sama sanan nurse din tasa hannunta tabude kofan, karan bude kofa da Sameer yaji yasa yadago kanshi yana rike da waya ahannu, tundaga kan crock shoe kafarta yake kallo har zuwa wandon da rigan dayamata yakuma dan mata yawa wani irin kyau tarame bana wasaba kafin ahankali yasauke idanunshi kan fuskarta dayay ja tsabagen kuka kaman jini zaifito, idanunta sun kumbura sunyi suntum suntum sunyi jaajir gashin idanun duksun tattare looking so moist, idanunta sun kode, shigo da ita ciki Nurse din tayi ta kawota har wurin kujeran sanan ta kalli Sameer cikeda girmamawa tace "welcome Sir," gyadamata kai Sameer yayi tajuya tafita tarufo musu kofa, tsayawa tayi awajen atsaye batare data dagokai ta kallai ba sai kallon takalman kafafun ta takeyi takasa hada ido dashi, kallonta yayi from head to toe sanan ya mayarda kanshi kan wayanshi yacigaba da danne dannen wayanshi, takai almost 20min atsaye bata zauna ba, batace uppan ba, ga kanta akasa kafin taja wani uban ajiyan zuciya tafashe da kuka sosai tasa hannunta akan idanunta tanayi kaman zata shide, dago kanshi yayi ya kalleta yanda take kukan kaman wacce aka zane sanan yadan tabe baki yatashi tareda daukan wayanshi da carkey daya ijiye kan table yajefasu cikin aljihu gaban riganshi yayi hanyar kofa yabude kofan yafita batare daya sake koda kallonta ba, da sauri tajuya tabishi tabude kofan tafito yana cikin tafiya adan corridor taji takama hannunshi gam hakan yasa ya tsaya chak tareda juyowa yazuba mata idanunshi dababu alamun wasa cikinsu, fashewa tayi da kuka sosai gabaki dayan wurin ya dau karan kukan ta tace "ka maidani gidanmu, ka kaini wurin Mummy na" yanda take kukan yasa Nurse data shiga wani office awurin tafito tazo wajen da saurita, jin sahun tafiya yasa Rahima tajuyo tana ganin Nurse takara damke hannunshi gam gam tana kallon fuskan shi tace "dan Allah ka kaini wurin Mummy na kaji, please ka kaini dan Allah karka bari su tafi dani please, wlh banson wurin nan dan Allah kaji" ganin Nurse ta iso wajen yasa takoma dayan gefenshi talabe tana kuka sosai tana ihu kallon nurse din yayi yace "don't you have any female security here?" da sauri tace "we have sir" "call them suzo su tafi da ita ciki" yafada sounding a lil bit bitter, wani irin dan banzan ihu tasaki. "noooo, dan Allah in kanama Allah ka kaini gidanmu, wlh bansan wajen nan" wani mugun kallo yamata da idanunshi yanuna mata hannunshi, ahankali tasake shi cike da tsoron shi tana kuka sosai tana tsaye gab dashi jikinta narawa ko minti biyu ba'a yiba saiga Binta da Asabe tana ganin tasake damke hannunshi tana neman shigewa jikinshi da hannu daya Asabe ta dagata sama sukai ciki da ita tana kwala ihu tana juyowa tana mikama Sameer hannu, mugun kallo ya watsa mata yajuya yafice daga wurin, saida yaga Dr sanan yabar Centre.



Aranan da daddare yaje yagaida Abba dayasoma jin sauki sosai, Mummy kaman zata hadiyeshi da kallo amman tunda ya kalleta sau daya ya gaidata bai sake bata second look ba haryay briefing Abban kan Rahima tasoma samun lafiya and she is responding to treatment, Abba yaji dadi ranan, yaji dadi wani sabon karfi yaji ya shigeshi har saida yafita sallan isha'i tareda da Sameer shida rabon shi daya fita masallaci harya manta amma news din Rahima yabashi karfi.






Wasa wasa Kwanaki nata tafiya, yau satin Rahima uku a Rehabilitation Centre, tun ranan da Sameer yazo yadubata babu wanda yakara zuwa yaduba ta daga gida, babu ranan duniyan dabazatai kuka ba, and Alhamdulillah ana bata kulawa sosai ita kanta tanajin chaji ajikinta amma tsabagen yanda ta tsani wurin da abubuwan da ake mata aciki yasa taji babu abinda takeso kaman ta ganta a gidansu.



Yauma kaman kullum da sassafe aka tadasu suje wanka, tana cikin bayi tana wanka taga anbude labule an shigo, baki tabude zatai ihu tana jan towel dinta danta rufe jikinta matar datashigo tasa hannu ta rufe mata baki tareda rage murya tace "listen to me, kina ihu Asabe zasuzo nan, so kiyi shiru ba jikinki na shigo nagani ba ko wani abu magana nazo namiki" da sauri ta gyadamata kai tana kokarin daure towel dinta, janye hannun matan tayi daga kan bakinta tabi boobs dinta da kallo takai hannunta zata taba da sauri Rahima ta koma gefe hartana neman fadi matan ta riketa tana washe mata baki, tana sosa kai, idanunta bakin kirin hakama lebenta, tureta Rahima tayi tana turo baki tace "niki saken" sakinta matan tayi tana soshe soshe tace "dalla sabida ina sonki ne dan kinada kyau saisa ma nace bari nazo nataimake ki nidama last 2weeks duka duka shegen mijina bayan ya dannamin saki yakawo ni nan, tunda nazo kullum nake ganinki kina kuka bakima kowa magana, kullum ke kadai" tai shiru tareda daga hammatan ta tana sosawa kaman mahaukaciya, yatsine fuska Rahima tayi cikeda kyaman ta takoma baya dan ganinta take kaman mahaukaciya, dariya tayi ta sauke hannunta tace "kinga nan wurin kashemu sukeyi, inba hakaba antaba raba nawa da abinda kesashi jin dadi, shaye shaye fa, inhar zasuce zasu rabamu da shaye shaye to su rabamu da shan ruwa ko cin abinci man, ruwa baya kore damuwa ko bakin ciki amma shaye shaye kina sha wayyooo matsala da bakin ciki bye bye, bana wanan soshe soshen da amman sabida ban samu Cociene dina na shaka ba na 2weeks anan wurin shine nafara haka kaman mahaukaciya, kullum suyita kada kuka da maburgi acikina dan bantan uba" tai shiru tana kwakulo hancita tana lumshe ido tsabagen yanda abin kdmata dadi, tace "yau zamu gudu mubar gidan nan da daddare, akwai wani supplier na saurayina kuma da zaizo ya kwashemu da daddare amota anan baya, haurawa zamuyi kin gane, electric fence ne but zamu baza bargunan mu akai, in kinaso zanje dake kema ki gudu amma zaki biyani dubu goma inkin yarda" da sauri Rahima tazo kusada ita tace "eh zan biyaki Allah, Mummy na zamu kira muna fita zata turomiki kudin, da gaske dan Allah zaki fitar dani ko karya kikemin?" murmushi matar tamata tasa hannuwanta duka biyun tana sosa kai tace "eh kibarmin komi a hannuna nasan wurin nan lungu da sako, nine number 00, amma sunana Shagali" da sauri Rahima tace "Shagali?" gyadamata kai matar tayi tana sosa kunne tace "eh Shagali sunana, yanzu wuce kifita, karfe takwas nadare nurses ke fita shift dazaran ta dakin ku tafita kifito kawai zaki ganni kibar komi a hannuna" da sauri Rahima ta gyadamata kai tana murmushi tace "nagode" wuyan ta ta shafa tace "kinada kyau ga kira saisa zan taimaka miki, u look so innocent, wuce kifita kar Binta ko Asabe sukamamu" ko damuwa ma batayi da batagama wankan da kyau ba tafito tana murmushi ta ijiye sabulu da soap a box dinta tawuce ward dinsu.


Inkika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa, zaki biyani ranan da bakida shi.
How to subscribe
Pay 300 to 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din BIN ABINDA ZUCIYA KESO.
Ranan har Nurses saida suka dinga mamakin ta ganin ranan ne rana ta farko da batai kukaba, batai gardaman shan magungunan taba har akai magrib, dama ba ruwanta da Salla dan tunda aka kawota ko hanyar masallaci bata taba biba sai agogon bango ward din take kallo, agogon nabugawa karfe 8 dot taga nurse din dakin ta tashi daga kan kujera, ta dau wayarta da wani littafi tawuce tafita da sauri ta diro daga gadon sauran yan dakin suka bitada kallo hararan su tayi tace "sa'idawa mutum bazaije yay fitsari lafiya bakuma yanzu adai rage" tabude kofa tafita tana fita tahango Shagali awurin kofar wajen da hannu tamata alama tazo da gudu tai wajen hannunta Shagali takama sukai wata hanya da batasan da ita ba tunda aka kawota Rahab centre, hanyar lungu ne haka suketa gudu itada Shagali har suka bullo backyard wajen masallaci wasu mata guda uku tagani awurin suna fitowa tace kowaya tsugunna Rahima tahau kansu ta dane kan fence, tsugunawa sukayi Shagali tasaki hannun Rahima data rike tace "hau bayansu ki dirka kijiramu" hawa bayansu tayi amma dudda haka batakai tsawon ginin ba dan bata da wani tsawo hakan yasa Shagali tahau ta cincidata sama ta taka bargon dasuka shimfida kan electric fence din ta mike tsaye gabanta na faduwa hango uban tsawon ginin dasuke cewa ta dirka ga wajen daji duk ciyayi, da sauri murya kasa kasa gudun kar ajisu Shagali tace "wai bazaki dirka ba sai an kamamu wai babygirl?" fashewa Rahima tayi da kuka tana neman tsugunnawa dan tanada fear of height tace "am scared bazan iyaba" wani irin tunkudata shagali tayi aiko ta kwala uban ihu tafadi tipp akasa tasaki kuka sosai, hawa fence din Shagali tayi ta dirko sauran ukun ma suka diddirko kasa kana ganinsu kaga kwararrun yan duniya, sanan Shagali ta tashi ta daga Rahima dake kuka sosai ta kakkabe mata jiki tace "sannu kinji oya mu gudu mota na chan gaba" gudu sukahau yi Shagali na rikeda hannun Rahima dake shirin suma tana kuka kaman yarinya karama, sundan yi nisa Rahima ta zube akasa dan karfin ta yakare hakan yasa sauran suka tsaya suna tsaki sukace ce "wai mesa kika dauko wanan yar yarinyar shagali? Sai bata mata lokaci take" cikin jin haushi shagali tace "sonta nake baruwan ku, kuma dai naga taimaka muku nayi tomena cewa me yasa na daukota" ganin kaman suma tayi yasa Shagali ta dagata tagoyata abaya sukahau gudu kusan na na 45min sanan suka kai titi aiko saiga wata yar akwalan mota datai parking ita kadai akan hanyan da motoci basawani guduwa, da sauri wani mutumin yafito daga motar yabude musu baya suka shiga daya cikinsu ta shiga gaba, Shagali ta zauna kusada Rahima tace "bani ruwa in kanada shi" ruwa yamiki mata yace "Shagali ta Shagulgula dama ashe zan kara ganinki yau akwai holewa kenan" dariya shagali tayi tace "jamuje Bala" kunna motar mutumin yayi yaja itakuma ta debo ruwan ta watsama Rahima kan fuska hakan yasa tabude idanunta ganinta amota yasa tace "mun gudun?" fuskarta shagali ta shafa tace "eh mungudo yanzu zamuje musha dadi abinmu da sassafe saimu kaiki har gidanku ki kwaso mana kudade ko" turo baki Rahima tayi tace "yanzu zaku kaini" ahankali Shagali tace "a'a sai safiya zamuje yanzu sun riga sun kira yan gidanku kina zuwa za'a maidake gwara kibari gobe kinji" ahankali ta gyadamata kai tai shuru ko kadan she is not comfortable dasu haka taga sunkai wani uncompleted building a cikin wani anguwa da duk gine gine ne da ba'a gamaba, ya kashe motan suka fiffito Shagali tafito da ita tana tafiya ahankali suka shiga gidan rawa suka hauyi suna ihu mutumin ya shiga shigo musu da gorunan coke yana basu daidai biyu Shagali ta karba tazo inda Rahima ke zaune ta mika mata tareda kashe mata ido daya tace "ga coke, amma coke dinan yaji hadi nake gaya miki, so kisha kadan dan harkan manya ne you are too small for this, yanzu ma nabaki ne dan nasan kinyi kewan abin" karba tayi tarike tana kallonsu suna rawa sosai kaman ansaka musu waka suna rawa suna shan coke din harda mutumin daketa shafe shafe da Shagali, dauke kai tayi ta makure a bango ta kunshe ido har saida taji shiru sanan tabude idanun ahankali, ganinsu tayi duk sun baje akasa suna bacci suna munshari, kasa koda runtse ido tayi sabida sauro awurin ga kukan dasuke yi na bala'i, haka tazauna idanunta biyu ita kadai har asuba, sai wuraren asuba sanan tabude coke din dataji already marfin abude ne takafa abaki dan kishi takeji, wani shegen daci da dadi taji hakan yasa ta yatsine fuska tacireshi daga bakinta, sai bayan ta hadiye sanan taji wani dadi a bakinta kaman tasha bitter chocolate hakan yasa tadauka takafa abaki tanasha tana wani irin sauke ajiyan zuciya saida ta tada goran sanan ta yar tana yatsine fuska sai chan kuma tafara jin dadi, murmushi tayi kafin taji wani mahaukacin bacci na dibanta daganan kuma ba tasake sanin inda kanta yakeba.
39.






Wuraren 8 na safiya namijin yafara tashi ya bubbuga Shagali dake kusada shi yace "Shagali kutashi mutafi kafin masu gini suzo su ganmu anan" da sauri ta mike ta bubbuga sauran kawayen nata dake kwance gefenta kafin tai wurin Rahima dake bacci ta akasa ta bubbugata da hannu tana kiran sunanta. "Baby, Babygirl" bude idanu Rahima tayi kadan takara maidawa tarufe su tace "niki barni bacci" da sauri Shagali tace "baidai yar yarinyar nan ta shanye duka wanan mix dinba? Na shiga uku na lalace" kwashewa da dariya sauran matan sukayi daya daga cikinsu tace "da ke zata jira saikin cemata ta shanye sanan zata shanye, angayamiki sabon shigace, tunda kikaga yar yarinyar nan a gidan nan aito kinsan ta kware kan harkan, nidai tattara ta mutafi mota mubata ruwa kota iya bude ido tanuna mana gidansu mukaita tabamu kudi" dagata Shagali tayi suka jata har mota suka sata cikin mota duk suka shiga Shagali tadau ruwa ta zubamata a fuska sanan takafa mata goran ruwan a baki tana watsa mata a fuska, dan kurba tayi, bude ido tayi kadan, Shagali ta jijjigata da sauri ganin tabude ido tace "ke inane gidanku zamu maidake gida mu karbi kudi mu wucene" cikin maye tace "uhmmmm gidanmu, wurin Mummy na?" da sauri Shagali tace "eh inane gidan?" washe baki tayi tace "gidan Alhaji Sambo, number 1 Sambo Street GRA nanne gidan muuuuuu" tai wani uban ihu, da sauri direban yadauki hanyan itakuma tacigaba da bacci tana surutai har saida sukakai layin data fadi, baki Shagali tabude tace "ashe yar gidan masu kudi ce" a daidai address din data fadamasu yay parking, ruwa Shagali takara kwara mata a fuska tace "bude ido ke mun kawoki gida, ga gidanku nan" ahankali tabude idanunta dudda dishi dishi take gani bai hanata gane Gate din gidansu ba da sauri takara bude ido ta tashi tana tangadi tace "Mummy na, laaaa gidanmu" ta shiga neman abin bude kofar mota, budemata Shagali tayi tace "kiyi sauri ki kawomana kudin muna jiranki anan" gyadamata kai tayi tafita tana washe baki hartana fadi kasa ta tashi tsaye tana kakkabe jikinta tana kallon Gate dinsu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login