Showing 21001 words to 24000 words out of 190952 words

Chapter 8 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

397

ganinan zuwa" katse wayan yayi yatashi ya kalli agogon bango this is 8, akwai meeting dayake dashi by 5 Allah yasa bazaiyi missing meeting dinba, key motarshi yadauka yafito daga office din yasauka kasa, motarshi yabshiga yatada yaja motar da mahaukacin gudu yadau hanyar zaria.




Sha biyu saura minti uku ya shigo Ahmadu Bello University tsabagen mahaukacin gudun dayayi, cikin sickbay ya shiga yay parking yafito sai wani irin kallonshi both yan mata da samari dake shige da fice ake ganin soja real soja ba security ABU ba, wayarshi yadauka yay dialing number Mu'az din ringing daya Salisu yay dauka. "am outside d sick Bay come out" yay maganan authoritatively as usual, ko one minute ba'ayiba wasu samari biyu suka fito kana ganinsu kasan bazasu wuce sa'onin Mu'az dinba, suna hango Sameer da kayan sojoji suka ganeshi, gabansu sai faduwa yake ganin babba ne sosai ashe yayan nasu, ga tsawo ga cika ga kyau dan yamafi Mu'az kyau, yana tsaye inda yake dudda shima kallo daya yamusu yagane sune har suka karaso gabanshi, cikeda girmamawa Salisu yace "Sannu da zuwa Yaya Sameer nine Salisu damukai waya, wanan kuma" yanuna nakusa dashi yace "shine Abdul shima abokin Mu'az ne duk ajinmu daya, muje kaganshi" yay maganan tareda dan satan kallon fuskarshi dan all this while dayake magana yakasa hada ido dashi sabida yanda yake da mugun kwarjini, gaba sukayi yana biyeda su abaya har wani daki dakenan emargency, bude kofa sukayi suka shiga gadaje uku ne adakin amma Mu'az ne kadai on admission ana karamai ruwa sai wani irin juyi yake idanunshi a rufe gam hawayen azaba nafita ta gefe baimasan inda kanshi yakeba, karasawa sukayi ciki ahankali yaja kujeran gaban gadon ya zauna tareda folding hannunshi akirji yana kallon Mu'az din kaman mai shirin gano wani abu yakai almost 3min ahaka sanan yajuyo ya kalli su Salisu dake tsaye agefe yace "bayan ya iso school jiya medame dame kukayi?" Abdul ne yace "bayan ya iso bamuyi komiba munje munyi sallan magrib saina dafa mana abinci zamu faraci kenan wata yar ajinmu takirashi" yanuna Mu'az tace "wai yabata ganmu ba, Mu'az was like bataganmu a inaba? Wai birthday party wata friend dinmu Zee Zainab, wai ancika Zainab nema tace mata takira mu taji, nan tabamu address din inda ake party mukai wanka muka shirya muka tafi......" yay shiru, wani mugun kallo yamusu da saida cikinsu both ya kulle yace "continue, what happen bayan kunje party?" sunnar dakansu sukayi atare Abdul yace "it was a very naughty party, Zainab din dama tadade tanason Mu'az shine shine....." yakasa magana hakan yasa Salisu yay jarumta yace "shine tazo tazauna kan laps din Mu'az , she kissed kumatun shi agaban mu, yana tureta taki sakinshi she hugged him ta zauna duka kan laps dinshi tafara rawa tana twerking ana ihu anamata manni tana gogamai kirjinta akan nashi, mudai muna gefe babu halin muyi magana but naga yanda yake ta keto zufa harta gamamai idanunshi yacika da kwalla sanan ta tashi tatafi shikuma yamike tsaye da sauri yana kokarin samo natsuwarshi yafice muka bishi abaya, sosai yake tafiya da sauri muna kiranshi yaki amsasu the next thing dat we know was ya yanke jiki yafadi ahanya rike da cikinshi and we ended up here" yadade yana kallonsu har suka gama labarin sanan yajuya ahankali batare dayace musu komiba yajuya yay facing Mu'az din dahar lokacin yake nonnokewa idanunshi a kulle hawaye nafita, ahankali yakai both hands dinshi yadaura kan saman goshin shi dayay zufa ya shafa goshi, Murya chan kasa yakira sunanshi. "Mu'az" wani irin motsi yayi kafin ahankali yabude yan fici ficin idanunshi dasukai mugun ja yadaura su akan Ya Sameer dake sanye da kayan sojoji, ganin Ya Sameer ne da gaske Yas yawani irin tashi ya rungume shi ya fashe da kuka kaman irin yaron dayaga maman shi after a very long time, juyawa su Salisu sukayi suka fita daga dakin dan basu space, sunkai wajen minti biyar kuka yake a jikin Ya Sameer yana pating bayanshi kafin ahankali yadago kai cikin ciwo sosai yace "yaushe kazo Ya Sameer?" tashi Sameer yayi yakarasa wajen new bottle water dayagani yabude batare daya kalleshi ba yace "not quite long" wani katin magani yaciro daga aljihun wandonshi sanan ya ballo guda daya tak dan karami yadawo gaban gadon ya mikamai, karba Mu'az yayi yasha sanan ya karbi ruwan ya ijiye, yasake zama akan kujera yana kallon agogon bango it takes less than 5min ciwon ciki zai sakeshi, ware ido Mu'azu yayi yana shafa cikinshi jin yarage ciwo sosai yace "laaaa Yayan mu ciwon yadena" cikeda surutu irin nashi yace "Ya Sameer wlh nazaci mutuwa zanyi kaji yanda cikina da marana keyi kuwa kaman ana yaki awurin, kaima yana maka haka?" ya tambayi Sameer daya tsareshi da ido yana share fuskan shi dan har yanzu akwai ruwan hawaye kan fuskan dama dama.
"Mu'az" Sameer yakirashi da dan kakkausan murya hakan yasa yadan kalleshi a diddire, "aure kakeso? Tell me the truth, idan aure kakeso zan maka aure after all one semester yarage maka a school kagama, aure kakeso?" da sauri ya girgiza mai kai yadan sunnar dakai dan maganan ta mugun bashi kunya yace "a'a'' "then what happen last night?" ahankali yace "Ya Sameer nima bansani ba" cikin yanayin jin haushi yace "don't lie to me Mu'az, I hate lies, kasan I already know everything, so just tell me the truth" murya chan kasa yace "Yaya Sameer Zainab ce, she...she..." yakasa magana yadanyi shiru kafin yace "rawa tayi ajikina, ayanda tayi yasa naji wani mugun sha'awa yakamani kaman zan mutu, saikuma tasakeni shine cikina yafara ciwo daganan kuma sai yanzu dana ganka anan" shiru Sameer yayi yarasa maisa yan gidansu keda wanan masifar ciwon cikin part of abinda yasa Muhammad da Nuru sukai aure kenan, kallon Mu'az yayi yace "you have problem Mu'az, banson kabata rayuwanka, inhar bakada dauriya is better you get married kasami wacce zaka dinga saukar da bukatunka akanta, hakkina ne nakula daku kuma am just like you guys father, that Zainab avoid her any day data kara zuwa inda kake let me know, no more partying you take care of yourself understood?" gyadamai kai yayi ahankali tareda yin murmushi hawaye nataruwa akan idanunshi, ganin haka yasa ahankali Sameer yadaura hannunshi kan goshin shi ya shafa yana kallon fuskarshi, ahankali yace "Ya Sameer kaima haka cikin ka kema ciwo?" dan daure fuska Sameer yayi kafin yatashi daga kan kujeran yace "lemme call your friends u need to see your Doctor kafin natafi" wucewa yayi yabude kofa yafita hakan yasa Mu'az yahau dariya yace "laaa Ya Sameer kunyana yaji wai hahahaha" yahau dariya kaman wani mara lpy, yana cikin dariya aka bude kofa aka shigo hakan yasa ya tsayar da dariyanshi su Salisu ne suka shigo da Ya Sameer dakuma Dr dake magana daya Sameer, musabaha sukai da Dr sanan yabashi prescription sanan yakalli Mu'az yace "atashi atafi gida patient" murmushi Mu'az yayi yadauko daga gadon ahankali da taimakon su Salisu binshi da kallo Sameer yayi ganin yanda yay wani wawan rama this ciwon da baima kai 24hrs ba, fitar da shi waje su Salisu sukayi hakan yasa shida Dr sukai waje suma, sallama sukai da Dr sanan yabude motar ya kalli su Mu'az yace "get in" shi shiga sukayi sai kallonsu ake yakoma gaba ya shiga yatada yaja motar suka fita daga ABU chan wani gida a off kay aka kamamai kasancewa hardly dan 400 level ke samin accommodation a school parking yayi a kofar gidan duk suka fito kudi mai yawa yaciro ya mikama Salisu yace "thank you, mun gode" sanan ya kalli Mu'az yace "do you need anything Kiddo" turo baki Mu'az yayi ya kalli su Salisu dasukai murmushi jin an kirashi da kiddo da sauri suka juya suka shiga gidan hakan yasa ahankali yazo yay hugging Ya Sameer din yace "I love you Ya Sameer" kanshi ya shafa yace "love you too Kiddo, stop crying whenever you are sick, crying is for the weak and my brother is not week or are you?" dagokai yayi ahankali ya kalli Sameer kafin yya dariya yace "No am not weak" "guud boy, if you need anything always call me okay" gyadamai kai yayi ahankali ko kadan baiso yatafi, hannunshi yakama yarike yace "Ya Sameer kazo muje ciki nadafa ma Indomie" da sauri Sameer yadan yatsine fuska yace "Indomie? Indomie is for children, kune Indomie generation daman" da sauri Mu'az yace "to zan dafama rice and stew" ganin yanda yadamu yasa yace "don't worry next time okay, yanzu I have a meeting to attend by 4, bye" hannu yadagamai hakan yasa ya shiga mota yatada Mu'az namai bye haryabar anguwan, awani masallaci ya tsaya yay azahar a masallacin sanan yafito ya cigaba da journey.





*******
Wasu kyawawan dankunne Mummy ta dauko ta makala mata akunne tace "wow Masha Allah, Autana kinga yanda kikai kyau kuwa yau kowa awurin birthday dinan keza'a dinga kallo" kallon kanta tayi a madubi yanda tai wani mahaukacin kyau dan zama tayi ta chanchara ma kanta makeup dan ta iya yima kanta makeup sosai, tama saman idanunta wasu black smoke eyeshadow daya karama fuskarta kyau abunka da fara, lips dinta tasaka musu wani pink lipstick daya karamusu karanta sukai kyau, tayi eyebrows masu kyau idanunta dudda batasan lashes ba zaka zaci lashes tasa sabida yanda ta taje gashin idon da massacre hakan yasa sukai tsayi sosai, hannu Mummy ta nuna mata alamun komi yayi 👍 sanan tace "to tashi kisa kaya nasan yakusan isowa" tashi tayi da sauri takarasa gaban gadonta inda taciro kayan dazata saka, wani blue jean tadauka tasaka.💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫



_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔





✍️ M Shakur


1️⃣5️⃣



Kunna motar yayi yaja yana tafiya ahankali yazo yawuce su ko lura basuyi dashi ba yay gaba da gidan yana hango asalin mutanen cikin gidan dake main rawan dan anbude Gate, rawa kawai suke na hauka definition of real clubbing suke yi abunsu, ga drinks tako ina sunasha, wata mace dan wandon datasaka mai kama da pant ne ta zameshi kasa zuwa wurin gwuiwa ta shiga rawa da bare duwaiwai ta hakan yasa mazan sukayi ihu suka taru akanta suna zuba mata kudi suna shasshafa ass din suna ihu suna DJ DJ give us shake up your bombom, duksun rude, ganin haka wata tafito itama da nonuwanta waje ta hanyar tuge bra ta yar akasa dan attention din yakoma kanta da mugun sauri Sameer ya dauke kai yace "subhanallah!" txt message daya shigo wayanshi ne ya kalla _we are close Lieutenant at kaduna kano express road already_
dan gaba yayi sanan yay reverse yasake wucewa ta kofar gidan yafita daga layin yafito hanya ta yanda dazaran sunzo zasu ganshi ya kashe motar ya saukar da tinted glass din motarshi kasa yana kallon hanya, ko minti biyu baiyiba ya hangosu sun taho motoci biyune na gaban golf ne da maza kusan takwas ke ciki mutum uku a gaba hudu a baya suna fanfala uban gudu kaman motar ambulance, sai dayan vehicle dinkuma nakama mutane ne, horn ya danna musu sau daya hakan yasa suka gane suka karyo kwana suka shiga layin da gudu shima ya kunna motar ya shiga, ta baki bakin layin sukai parking dan basuso su gudu, kashe motar yayi yabude yafito kaman yanda suma suka fito suna sanye da normal kayan gida sai bullet proof jacket maroon color da aka rubuta NDLEA ajiki, musabaha sukai da Sameer kafin yace "musu let's go, no shooting no maltreatment, just catching them dat is all what we are up for" atare dukansu sukace "yes Lieutenant" wani mugun respect suke bashi dan Sameer yayine kawai arayuwa, sukai wajen da gudun su, wata yarinya dake kiss da saurayin ta agaban gate dinne idanunta a lumshe kaman ance ta bude ido tabude ta hango maza da soja na dumfaro su da sauri, fizge bakinta tayi tawani irin kurma uban ihu. "policeeee, everybody runnn!" dudda dukansu are drunk kalmar police kalma ce da duk wani dan shaye shaye is so caution of, sunan kaman kararrawa yake in the mind so it always ring and alarm to their ears, kaman an zubamusu wani irin dawowa hankalin su, firgigit idanunsu ya washe diddirkowa sukai daga motan sukahau gudu wasu suka yanka dajin wajen yayinda yan NDLEA din suka chapke na chapkewa suna dannesu suna kulle musu hannu da disposable plastic handcuff, some na dagasu suna kaisu mota suna rufe su aciki su dawo su kwashi wasu, all this while masu rayen cikin gidan bamasu saniba, cikin gidan Sameer yashiga wasu yan NDLEA guda hudu biye dashi, ihu gidan ya dauka kowa gudu yake, Djs dinma sukabar kayan kidan sukai tatayi, wasu sun rasa inda zamasuyi hakan yabasu ikon kamasu, wasu are running to the fence jumping suna shiga dajin baya suna guduwa, karasawa Sameer yayi yasa hannu ya cisge wayoyin kidan hakan yasa gidan yay tsit.....





Ihun da Chris yaji tako ina da kuka wanda matayen da aka kama keyi yasa yasaki Rahima daya danne ta suna kaukawa dadan ragowan karfin daya rage mata yatashi da sauri dagakan jikinta jin ihu da sahun gudu ga music da kida dake tashi tun dazu shima yay shiru kaman an kashe, labulen window yadan kama ya yaye kadan ya leka wani irin dallo idanu waje yayi hango abokanenshi maza da mata su kusan 15 da aka kamasu an daure musu hannu da disposable plastic handcuff ansasu kneeling down agaban gate ana fitar dasu daga gidan one by one, wasu yan NDLEA guda biyu kuma tsare dasu gudun karsu gudu, dawani irin mugun sauri yasaki labule window jikinshi har rawa yake ya kalli Rahima dake kwance yanda ya barta duk riganta ya chukwuikuye idanunta a lumshe tasaki baki abude tana bacci, hannunta yakama yadaga ta zaune yace "Beautiful stand up let's run" wani irin luuu Rahima tayi takoma kwance tana buge hannunshi cikeda masifa, tsaki yaja da sauri yadauki key motarshi daga kan table yabude kofan ahankali gudun karyay kara asirinshi ya tonu sanan ya leko da kanshi kadan dan duba ko akwai mutane a falon, ganin babu kowa a falon yasa da gudu yafito yay hanyar kitchen sabida yabita backyard fence ya dirka ta baya ya arce daidai lokacin Sameer ya shigo flat din, ganin Chris yafito daga wani daki da gudu yayi ta kitchen yasa yabishi da gudu, daidai ya shiga kitchen wani officer NDLEA dayaji fitowanshi ya labe abayan kofan gudun karya ganshi yafito ya tadiyeshi yafadi timm akasa, ihu Chris yayi dan yaji zafin faduwan yace "officer I didn't do anything naaa, we are just having birthday party fa, why u wan arrest me en? Wetin I do naaa?" dagashi officer yayi bayan ya kulle hannayen nashi cikin tsawa yace "my friend shut up, we we are busy having sleepless night to make sure youth like you stop all this kind of life and be serious with your education so that u guys will have a bright future but you guys are here busy taking what is killing you and killing your future as well, let's go my friend" ya fincikeshi sukabi ta gefen Sameer dayay irin tsayuwan sojojin nan yana kallonsu suka fita sanan yadaura idanunshi akan dakin dayaga Chris yafito daga ciki kafin ahankali yadaga kafa yafara tafiya daidai boot dinshi na making sound yakarasa wurin dakin da Chris yafito daga ciki, yadade yana kallon kofan yanabin rubuce rubuce da Zane zanen dake jikin kofan da kallo zanen shisha pot dasu cigarette ne a jikin kofan katakon da akai da biro, ahankali yazare hannunshi daga bayanshi yakama handle din kofan yabude kofan wani irin warin wiwi da sauransu ne suka dakanmai hanci hakan yasa ya yatsine fuska kafin idanunshi su sauka kan Rahima dake kwance tana dirkan baccinta hankalinta kwance, kallo daya yamata yagane musulma ce ita, ita kadaice musulman dayagani tunda aka fara fito da matayen dake wurin, wani officer ne ya shigo dakin yana tahowa wajen Sameer yace "da saura ne Lieutenant?" gyadamai kai Sameer yayi kafin ya nunamai cikin dakin dayake tsaye a gabanshi da sauri officer ya shiga cikin dakin yay inda Rahima ke kwance, hannu daya yasa ya fincikota hakan yasa ta tashi tsaye luu kaman zata fadi, turo baki tayi sosai idanunta arufe cikin fushi da shagwaba in a very slow way tace "leave me aloneeeeeeee Chris" tai baya luuu takoma zata fada kan kujeran a mugun buge, sake fincikota officer yayi yana kokarin kama hannun ta tabaya ta fizge kaman zatai fada dashi tana layi, cikin slow tsiwa irin na wanda ya bugun nan tace "leave me kona dalla maka mari, I want to shower, uhmmmm wanka nake kadena damuna, kawomin ruwa in sirka ruwan zafin Ya Siddiqa" tawani irin zube akasa wurin kafin ta daura kanta kan table din dasu shisha pot kekai tacigaba da bacci, officer zai kara kamota akaro na Uku Sameer yace "wait!" tsayawa chak officer yayi ya kalli Sameer din dahar lokacin bai shigo dakinba, takowa yayi ya shigo cikin dakin, babban bottle water Swan daya gani kan side drawer gadon dakin yadauka ya shiga budewa yana tahowa inda take kwance gaban kujera ta daura kanta kan table tana bacci tana surutai kasa kasa, matsamai Officer yayi yakoma baya, tsayawa Sameer yay akanta ya cillar da marfin goran gefe, daga goran sama yay da hannu daya ya shiga kwararo mata ruwa kaman ana mata fitsari akai yana sauka saman dankwalinta, dudda she was damn high amma saukan ruwa dataji akanta yana sauka kan fuskarta wasu na shiga kunnuwanta, wasu na gangarawa wuyan ta zuwa cikin riganta yasa ta mugun zabura kaman wacce ta zare ta mike tsaye tana shashare fuska tana wanan nishin da mutum keyi in ruwan sanyi na tabashi tana sauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login