Showing 138001 words to 141000 words out of 190952 words

Chapter 47 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

420

kituro_


_duk wacce ta karanta min littafi batare data biyaba Allah ya isa ban yafeba, in bakida kudin biya karki karanta, inkika karanta keba yar halak bace😙_







Wajen gadon Rahima tayi gabanta nafaduwa sosai albasan data yanka takai jikin hancinta ta shafe ajikin hancin nata kafin ta danne albasan daidai wajen, almost 2min Rahima ta shiga wani irin tari na wanda baida karfi ko kadan ajikinshi, da sauri Ummi ta dagota ta zauna kan gadon tasa kanta akan cinyarta jikinta mugun zafi tana kiran sunanta. "Rahima, Jewel, Jewel" Ummi takira sunanta adan dimauce ganin yanda takeyi kaman zata mutu, da kyar ta iya bude idanunta dasukai jajir tadaura su kan Ummi, ajiye ta kawai Ummi tayi tacire mayafinta ta ijiye nan kan madubi tabude bayin ta shiga ruwan zafi tahada mata sosai sanan tafito tazo gaban gadon Rahima na kwance yanda ta barta ko motsin kirki bata iyawa sai nishi take kaman zata mutu bama ta iya kuka, wani mugun tausayi Ummi taji tabata da sauri takama hannuwanta tace "sannu, sannu Jewel, sorry, zomuje na kaiki bayi" ahankali Ummi ta dagata tai kasa tsayuwa Rahima tayi kaman Ummi ta daga paper haka takeji tabi gadon da kallo tana buga salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un Sameer zai kashe yar mutane" jinin data gani ya bala'in bata tsoro, tsayar da Rahima tayi da kyar sanan takama hannunta tadaura a bayan wuyanta sanan takai hannunta gefen cikinta tarike ta gam tajata, kasa daga kafa Rahima tayi sai jini daya shiga bin kafafunta yana gangarowa kasa da yawa salati Ummi tayi dan ta tsorata tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, you are bleeding kar jininki ya kare, zauna" mayarda ita kan gado Ummi tayi gabanta nafaduwa da sauri tajuya tai wajen kayan Rahima data gani a akwati anan kasan dakin ta shiga dubawa pant taciro da pad da Allah yataimaketa tagani sanan tadauko wata yar doguwan riga tadawo wajen gadon, hannunta narawa sosai tahada mata pad guda biyu jikin pant din sanan takama kafafunta tasaka mata tawuce bayi da sauri towel tadauka ta tsoma a ruwan zafin data hada tafito dashi tazo kafafuwa ta dasuka baci da jini ta shiga sharewa jin muryan Noor yana kwala mata kira yasa tace "help Sameer to his room ya shirya we are going to the clinic now ina zuwa ganinan fitowa" tai maganan tana share mata jinin saida tagama tass sanan takoma bayi ta wanke towel din tass ta ijiye tafito, doguwan rigan tadauka ta zura mata sanan tasake komawa akwatin ta nemo wani karamin hijab tazo ta saka mata sanan tadan dagata ta janye zanin gadon daya mugun baci ta shiga bayin Rahima ta saka a washing machine tafito tana kallon yanda katifar itama tai stain but batada lokacin gogewa, juyawa tayi tafice, ganin Sameer da Noor basa falon yasa tai dakin Sameer tun kafin tabude kofa takejin kakarin aman Sameer alluran was way to much for him, over dose Mummy tamai sosai hakan yasa wanan mugun ciwo yakamashi yahade mai da zazzabin dayake yi da safe.

Da sauri tabude kofa ta shiga hango Sameer da Noor dake rikeda shi tayi abayinshi yana kwara amai kaman zai sume Noor namai sannu, da sauri tai bayin cikeda mugun damuwa tace "har yanzu bai dena aman ba Noor" hannunshi Noor yamika mata yace "Ummi rikeshi dan zai iya fadi ina zuwa" rikeshi Ummi tayi gabanta nafaduwa sosai idan akwai abinda ta tsana shine taga yaranta na rashin lpy, wardrobe dinshi Noor yaje yadauko mai wata simple t-shirt dinshi Black mai v- neck sai wando da belt yadawo bayin lokacin aman ya tsaya towel yadauka yajika ya share mai baki da wuya da kirji daya bata sanan ya rikeshi da taimakon Ammi suka iya sakamai rigan, sanan yasaka mai wandon suka fito daga bayin Noor suka fita dashi waje bai gani wlh sai magana dayakeji sama sama his eyes are blur amota sojoji sai yimai sannu suke ganin ogansu ba lpy, a motan shi Noor yasashi zai shiga Ammi tace "muje ka dauko matar, saura ita, itama ba lpy" da sauri Noor yace "subhallahi" ya kalli sojojin dasuka zagaye gaban motan yace "stay here dashi" sanan yabi Ummi sukai cikin gidan suka hau stairs sukai small palor abu yataka dayaji yay kara hakan yasa yadaga kafafunshi tareda kallon kasa ganin syringe yasa ya tsugunna ahankali yadauka yana kallo ganin dan ragowan ruwan allura mai kala baki baki, da sauri Ummi tace "alluran miye wanan kuma?" tashi Noor yayi saikawai yajefa syringe din cikin aljihun shi yace "I don't know" dakin Rahima Ummi tabude suka ta shiga yana biyeda kallo daya yama katifar yadauke kai da sauri, karasawa wajen Rahima dake wani irin nishi Ummi tayi tace "innalillahi this girl is in pain, zoka dauketa Noor mutafi" ahankali Noor yataho yanda yaga tanayi yaji wani irin mugun tausayinta aranshi dan shi mutum ne yabada bala'in tausayi yafi all the four of them tausayi, Ya Sameer kuma yafi dukansu jarumta da courage dan baya mantawa da Baban su yarasu shi kadai ne baiyi kukaba ya daure sanan ya jagoranci komi dashi da Baffa sukama Abban su wanka, shi Muhammad kuma is very simple, Allah ya yishi da bala'in saukin kai sai Mu'az, Mu'az very innocent ga shegen surutu akun gidansu kenan, daukan Rahima yayi ahankali yaji jikinta kaman wuta yawuce yafita daga dakin Ummi biyeda su harsuka sauka kasa, kofar falon Ummi tarufe tazaro key daga bayan kofan ta kulle kofar da key tasa key acikin purse dinta sanan suka tafi, abaya ya kwantar da Rahima Sameer kuma ya zauna agaba amma ya kwantarmai da kujeran ya rurrufe kofa itakuma Ummi takoma motarta direba yajasu sojojin na dagamusu hannu suka tafi.




Babban clinic dinsu, wani private asibiti da family su duka ke amfani dashi Noor yatafi, dayake an sansu da mai asibitin abokin Abban su Sameer ne kafin yarasu aka karbe su akai emergency room da Sameer, Rahima kuna aka shiga da ita wani daki Ummi tabisu shikuma Noor yabi Sameer.

Yanda Rahima ke nishi yasa da sauri aka shiga mata fixing drip aka samata oxygen sanan babban likitan dake dubata ta kalli Ummi tace "meya sameta haka Madam?" tana maganan idanunta suka sauka kan riganta daya jikeda da jini da sauri Dr ta yaye rigan tace "My God she is bleeding, wat happen to her" batare da Ummi tabari sun hada ido ba tace "I think she had a tea" da sauri Dr dayake musulma ce tace "subhallahi, take her to tea theater girls" tama nurse din magana tana kwance agogon hannunta tana zare zobunan ganin Yanda Ummi tayi yasa takamota suka fito daga dakin kujera ta nuna mata tace "just sit here your daughter will be fine okay am coming" tai maganan tana wucewa theater, Noor ne yadawo wurin yazauna kusada Ummi data mugun damu yace "ina suka kaita Ummi?" ahankali Ummi tace "theatre" dan jim yayi baice komiba, chan Ummi tamika mai wayanta tace "nemomin number Baffan ku?" karban wayan Noor yayi ya shiga binciko number yace "Ummi da ba'a kirasu ba banso kowa yasani" girgiza kai Ummi tayi ahankali tace "Baffan ku mahaifin kune idanda mahaifinku nada rai adole yazonan ko Sameer danshi ne kuma shi mahaifinku yaba amanar ku" dialing number Baffan Noor yayi yamika mata takarba takara akunne ta sanar da shi yanama kan hanya ne yace mata bari yay kwana yazo.

Wani likita ne yafito yana share zufa da towel da sauri Noor yatashi Ummi zata tashi Noor yace "Ummi please ki zauna kinsan yawan tafiye tafiyen nan might result to a problem" ahankali Ummi tace "to amma ya Sameer din?" murmushi Dr yamata yace "sweet mother kenan bamu da kaman ku your son is fine" sanan ya kalli Noor yace "you are his brother right?" gyadamai kai Noor yayi hakan yasa Dr yace "come with me" binshi Noor yayi har zuwa office dinshi yanunama Noor wajen zama sanan yakarasa ya zauna yana cire lab coat din jikinshi, yace "we were lucky to stabilise his condition wlh inda ace kunbar shi baku kawoshi hospital ba daya rasa ranshi dan he took overdose na sex arousal inducement injection, and daban daban aka hada masu karfin bala'i dasukafi karfin jininshi, maza sun kasa gane cewa amfani da wanan abin baida kyau kaga kaman su Viagra da sauransu dasuke karama mutum karfin sha'awa kaji kana bukatar mace duk sunada illa, zakai having sex dinfa kagama but zai sakin maka mugun zazzabi da ciwon kai wasu har rayukansu magungunan nan ke costing nasu, barinma shi daya hada kala kala daban daban Allah he is lucky Allah yace yanada sauran kwana aduniya saisa kuka kawoshi on time, yanzu mun tsotse all maganin daga jikinshi sanan munyi stabilising nashi, sai magungunan dazan rubuta maka da you will have to get them for him" gyadamai kai Noor yayi ahankali dudda kam yaga alluran a kasan dakinsu but yakasa gasgata Ya Sameer can do something like that, mezaiyi da sexual inducement drugs, gaskiya ba Ya Sameer akwai dai wani abun akasa.



Karban prescription sheet din yayi yafita daga office din yay pharmacy yasayo magungunan yakaima Dr, Dr ya karba sanan yafito yadawo wajen Ummi ya zauna, ganin anyi la'asar yasa yawuce yafita la'asar yayo a masallaci sanan yafito yadawo cikin asibitin yazauna kusada Ummi.



Dr data duba Rahima ne tadawo daga theater ganin Ummi da Noor yasa tace "please kubiyo ni zuwa office dina" tashi Noor yayi da taimakon shi yadaga Ummi ta tashi tana takawa da kyar sukai office din Dr, kujera ta nuna musu, zaunar da Ummi yayi sanan ya zauna dayake ta sansu sosai dan she is use to the family tace "Mummy who rape that girl? Innalillahi wa innailaihi raji'un baida zuciya ne eh, baida imani ne ina imanin shi yaje, me yarinyar nan tamai yay raping dinta harda tear........" da sauri Noor yatashi yafita dan bazai iyajin sirrin yayan shiba ko kadan he finds it disrespectful yafita tareda rufo musu kofa yay hanyar dakin da aka kai Sameer din.

Cikeda tsantsan damuwa Ummi tace "yanzu yatake?" ahankali Dr tace "I've stitch her yanzu, yanzu zan baki magungunan da za'a sayo mata dan ta warke da wuri sanan tahade, tear datasamu ne yasa she was seriously bleeding but yanzu mun tsayar da bleeding din, and tanada maleria 2+ shima we are treating her on it bayau zatabar hospital dinan ba sai munga tasami sauki sanan zata dinga sit Bath konan da anjima ne idan ta farka sai anmata, Mummy zaki iya kina mata ko nasama miki nurse dazata dinga mata" ahankali Ummi tace "zandinga mata" rubuce rubuce Dr tayi tamikama Ummi tace "ga magungunan da za'a sayamata yanzun nan" karba Ummi tayi ta tashi tafito ahankali Noor tagani zaune inda suke yana ganinta yatashi yarikota yazo ya zaunar da ita sanan ya karbi takardan yaje phamarcy magungunan ta dayawa harda drip daban daban da allurai yadawo yakaima Dr sanan takoma wajen Ummi ya zauna saiga Baffa yashigo reception din da sauri Noor yatashi karasowa Baffa yayi wajen yana gyara zaman babban rigan jikinshi yazo wajensu cikeda girmamawa Noor yagaidashi amsashi yayi yace "ina Sameer din? Meke damunshi? Me ake bukata kayi komi?" gyadamai kai Noor yayi yace "nayi" da sauri Baffa yace "muje na ganshi" yin dakin sukayi dudda ba'a barsu sun shiga ba but suna hangoshi yana kwance karin ruwa akemai a duka hannayenshi, haka suka juya suka koma wajen Ummi.






Suna asibitin har isha'i, sallan isha'i sukayo suka shigo ciki har lokacin Ummi na zaune a reception dudda tai salla suka karaso wurin Baffa yace "Noor dau mahaifiyar ku ka kai gida bazata iya zaman jinya ba, Mu'az yazo yazauna da Sameer din kai kawuce gida wajen iyalinka" da sauri Noor yace "Baffa zan zauna dashi please karka hanani" dan jim Baffa yayi saikuma yace "tom, shikenan ka zauna bari naje na ijiye mahaifiyar taku agida" da sauri Ummi tace "natafi Rahima fa" cikeda tausayinta Baffa yace "akwai nurses around sanan ga Noor, kinsan ke bakida lafiya Dr yace miki kidinga hutawa, gobe za'a iya kiran mahaifiyar yarinyar tazo ta kulada ita" da sauri Noor yace "bama sai ankirasu ba Nabila tazo gobe" yay maganan dan Sameer already told them about Mummy su Rahima wani kallo Baffa yamai yace "Nabila mai karaman yarinya ne zatazo jinya baridai Allah yakaimu gobe zamuga me ai faru, tashi muje" daga Ummi Noor yayi yafito da ita har wajen motar Baffa yasata abaya zama tayi ahankali sanan ta kalli Noor cikeda damuwa tace "dan Allah Noor ka kula dasu da kyau kaji, in Yayanku yatashi ka kirani nai magana dashi" gyadamata kai yayi cikeda tausayinta yace "to Ummi karki damu he will be fine" maida kofar yayi yarufe Baffa yashiga yaja motar suka fita daidai lokacin wayan Sameer dake aljihunshi yadauki ruri, kallon wayan yayi ganin Abba ajiki yasa yadanyi mamaki waye kuma Abba, har wayan takatse bai dauka ba sai akira nabiyu yadauka yakara akunne kafin yay magana Abba yakira sunanshi. "Sameer" ahankali Noor yace "baida lpy kaninshi ne Noor" da sauri Abba yace "subhallahi meke damunshi?" "zazzabi ne kawai munama hospital yanzu" salati Abba yayi cikeda damuwa ya tambayi Noor address din asibitin tareda fadamai zaizo gobe in sha Allah, komawa ciki Noor yayi yana waya da Nabila, dakin Rahima yafara zuwa ganin Nurse aciki datace mai ita zata kula da ita yasa yafita daga dakin yayi dakin Sameer zama yayi yana kallon fuskan Sameer din yana waya da Nabila ahankali kafin suyi sallama.






**
Kiran sallan assalatu yasa Sameer yabude idanunshi dasuka mai mugun nauyi ahankali, sosai yaji ciwon kan dayakeji yaragu sosai sai dan tashi zuciya, hannunshi ya kalla dayaga ana karamai ruwa on both hands sanan yaga Noor zaune kan plastic chair yadaura kanshi jikin gadon yana bacci dan lumshe idanu yayi yana kokarin tuna abinda yafaru dashi kafin yabude idanun da kyar, hannunshi yadaga yadaura kan Noor ahankali sanan yadaga, ahankali yatashi da kyar ko'ina ajikinshi namai wani irin ciwo yadanja jikinshi ya jingina da gado, motsin da Noor yaji yasa yabude idanunshi ganin Sameer ne yatashi yazauna yana cije lips tareda dafe kanshi dayadan saramai yasa yace "Ya Sameer katashi, sannu meke maka ciwo, bari nakira Dr" yajuya zai fita hannunshi Sameer yarike da sauri yajuyo yace "menene meke maka ciwo Ya Sameer?" yatsine fuska yayi cikeda dauriya da jarumta irin tashi yace "am fine, I want to shower jikina ba dadi" ahankali Noor dayaji kaman zaimai kuka dan yasan dauriyace kawai yace "sannu bari nakira Dr acire maka drip din" yajuya yafita ko minti biyu ba'a yiba yadawo tareda Dr Sameer, kasancewan Dr yasan Sameer sosai yace "Soja antashi wai sannu an jijjiga file din sojoji, meke maka ciwo yanzu?" dan murmushi Sameer yayi yace "nothing just wanna shower" da sauri Dr yace "yes zakafijin dadin jikin ka, sannu" yay maganan yana ciremai, ahankali ya sauko da kafafunshi kasa duk suna kallonshi sanan yasauka daga kan gadon ahankali dan lumshe ido yayi da sauri tareda dafa goshin shi dan jiri yakeji da sauri Dr yarikeshi Noor ma haka, Dr yace "I think kabar wankan nan sai anjima jiri baigama sakinka ba" dan yatsine fuska yayi ya cije lips cikin muryanshi dake tattare da ciwo yace "I can manage, Noor help me to the toilet ka kawomin kaya?" rikeshi Noor yayi yace "yes akwai some of new kayanka dana karbo daga wajen tela amota na dakuma few English wears" bayin yabude suka shiga yamai setting hot water sanan yajuya yafita tareda rufomai kofa.



Kaya Sameer ya shiga cirewa bayin very clean dan asibitin masu kudine sosai, rataye kayanshi yayi a hanger sanan yabi gabanshi da kallo ganin alamu alamun jini, runtse idanu yayi yana tunanin abinda yafaru, ahankali yasa hannu ya kunna hot shower ya shiga wanka komi nadawo mai fresh a brain dinshi, saida yagama wankan tass sanan yay wankan tsarki yay brush da sabon brush da asibitin suka ijiye musu abayi da sabon toothpaste sanan yadau sabon towel yadaura yakira sunan Noor da muryanshi da bata fita da kyau. "Noor" da sauri Noor yay gaban bayin yace "ganinan Yayan mu, na shigo bayin?" ahankali yace "give me soft cloth marasa nauyi" wata faran polo shirt Noor yadaukan mai da dogon trouser sanan yaje gaban bayin yace "gasunan Ya Sameer" murya chan kasa yace "come inside" bude kofan ahankali Noor yayi ya shiga yabashi kayan ya kwashi wayanda yacire daga kan hanger yafita dasu ya linke ya ijiye cikin jakan kayan, almost 5min yadauka sanan yafito daga bayin yana tafiya ahankali yay wani irin mugun kyau yadan fada, tashi Noor yayi da sauri yariko shi ya zaunar dashi gaban gado yana kallon fuskanshi yace "sannu Ya Sameer, are you hungry maizanje nasayo ma?" girgiza ma Noor kai yayi yace "am not hungry I want to observe salat" da sauri Noor yace "OK" dadduma dayake tareda kayan daya dauko daga mota yaciro ya shimfida mai zama yayi ahankali dan jiri shiyafi damunshi yay sallolin azaune sanan yahada dana asuba da aka tada a mosque din hospital, saida yay azkar yatashi daga kan dadduman yahau kan gado, fitowa daga bayin Noor yayi yazo yay salla akan nashi dadduman yana idarwa ya tashi yajuyo yana linke dadduman yana kallon Ya Sameer din dayaga ya lumshe ido kaman wanda yay zurfi a tunani yay shiru, ijiye dadduman yayi yazauna akan kujera hannun Sameer yakama yarike ahankali yace "Ya Sameer menene, tunanin me kake?" bude idanunshi dasuka danyi ja yayi yadaura kan Noor, murya chan kasa kaman wanda baiso yace wani abu yace "where is my......wife?" maida kanshi kasa Noor yayi yace "tana hospital dinan itama" bude idanu da kyau Sameer yayi _HOW TO SUBSCRIBE_
_Zaki turo 300 to account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting BIN ABINDA ZUCIYA KESO, marasa banki can buy MTN card 300 kituro_


_duk wacce ta karanta min littafi batare data biyaba Allah ya isa ban yafeba, in bakida kudin biya karki karanta, inkika karanta keba yar halak bace😙_
ya kalli Noor dayadan dagokai yana kallon Sameer din, kallon da Sameer yakemai yasa yace "batada lpy ita.....ma".





Slm uwar gida. Shin kina fama da matsalan mijinki baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login