Showing 39001 words to 42000 words out of 190952 words
Chapter 14 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
a nice family you have Masha Allah, Allah ya rayamana" ahankali Abba yace "Ameen Ameen" Chairman yace "yaranka nakama dakai sosai wlh, Rahima ce kadai batai kama dakaiba" yanuna Rahima dake gefen dadi dan itakadai ce fara a yaran as auran duk black beauties ne, murmushi Abba yayi ya kalli fuskan Rahima yace "Rahima auta" dan dariya sukayi Mummy tace "Alhaji food fa is ready akawo ne?" da sauri Chairman yace "No no madam abarshi bayan isha'i lokacin Sameer ya iso, sai ayi komi by then in sha Allah" hira suka cigaba dayi kafin akira isha'i suka tashi sukai masallaci su Siddiqa kuma sukai dakin dan zuwa yin salla, wayan Chairman dana dasuka bari akan kujera dan zuwa salla ne ya shiga ringing, ahankali Rahima tace "Mummy ana kiran wayan abokin Abba" gyadamata kai Mummy tayi tace "eh" ganin wayartai shiru na Abba yadau ruri yasa Mummy tace "bani wayan nan Rahima ingani" tashi Rahima tayi tadau wayan takawoma Mummy karba tayi ta kalli wayan Lieutenant, da sauri tace "ina ganin abokin Baban ku dazaizo ne yakira wayan Chairman yaji shiru yakira na baban ku, tashi kije kidubo waje Rahima inkinga bako ki shigo dashi kar abarshi a tsaye" gyadama Mummy kai tayi ta tashi daga kan kujeran tawuce tafita, slippers dinta dake bakin kofa tasaka tai hanyar Gate tana turo baki yau ko kadan bata hutaba, ahankali tabude Gate dinsu ta leko wani black mota Bentley tagani pake akofar gidansu gawani mutun tsaye jikin motar da bata ganin fuskarshi dan yabata baya fuskarshi na kallon hanya rikeda waya a hannunshi yana dannawa yana sanye da skyblue shadda bugaggiyar gaske tundaga Gate din takejin kamshin dayake yi, fitowa tayi daga Gate din gabaki daya ta tsaya daidai Gate dinsu tadan daga zazzakar muryan ta tace "kaine ke neman Abban mu?" wani irin juyowa Sameer yayi hannunshi daya sanye cikin aljihun wandonshi daya kuma yana rike da waya faduwa gabanta yayi sosai dan taga fuskarshi sabida hasken wuta dayazagaye kofar gidansu, kaman yanda ta zuba mai ido haka ya zuba mata ido, daure fuska tayi ta dauke kai daga kallonshi sabida yanda yawani cikamata ido tace "me kazo gidanmu?" daure fuska yayi yace "are you talking to me?" juyawa tayi batare data kalleshi ba tace "ance kashigo" tabude Gate dinsu ta shiga, ahankali yabiyo bayanta ya shigo gidan yana kallon yanda take tafiya kaman zata tashi sama har zuwa gaban flat dinsu ta tsaya ta juyo tareda kallonshi dan tasan inta shiga batare dashiba Mummy zatace mata ina bakon, kallonshi tayi yanda yake tafiya daidai hannunshi har lokacin a cikin aljihu dayan kuma yana daddanna waya yana tafiya ahankali, ashagwabe kaman zatai kuka dan ta gaji bacci kawai takeso tayi tace "ni kayi sauri kona tafiyata wlh na barka anan" dagokai yayi ya kalleta jin anbude Gate yasa ta kalli Gate da sauri ganin Abba ta ne yasa da sauri ta taho inda yake jikinta har rawa yake ta kallai tana satan kallon Abba tace "uhmm sannu dazuwa, ance ka shigo ciki" "Lieutenant" yaji Abba ya kirashi hakan yasa yajuya da sauri ganin Abba ne da Chairma yasa yakarasa suka hade ya mikamusu hannu cikeda girmamawa yace "welcome sir" cikeda farin ciki Abba yace "yaushe kazo Lieutenant?" ahankali yace "just now sir" kallon Rahima dake tsaye Abba yayi yace "what are you doing outside Rahima?" ahankali tace "Mummy tace naje na shigo dashi taga yakira wayar ka ne" cikeda fara'a Abba yace "Allah sarki sorry masallaci mukaje munbar wayan mu aciki, kumuje ciki" da sauri Rahima tai gaba suka biyota abaya suna hira.
Sallama Abba yayi suka shigo falon tashi Mummy tayi cikin fara'a tace "sannu ku da zuw......" kasa karasa maganan tayi sabida sauka da idanunta sukayi akan Sameer dayake shine ya shigo na karshe, cikin fara'a Abba yace "kinga shine Lieutenant din, Lieutenant meet my wife the mother of my children" cikeda girmama wa Sameer yace "barka da dare Mama da fatan na sameku lpy" wani irin murmushi Mummy tayi tace "lpy kalau Sameer, aiko suna mai dadi shigo shigo mun barka tsaye, zoga wuri ka zauna" tanunamai kujera zama yayi anatse looking compose fitowa su Siddiqa sukayi harda Rahima cikeda girmamawa suka gaida Sameer. "sannu da zuwa ina yini" kallonsu yayi fuskanshi cikeda murmushi yace "sannunku ya school" ahankali sukace Alhamdulillah, murmushi Abba yayi yace "to Masha Allah sannunku da zuwa Chairman and Lieutenant Sameer, this is my Family, Allah has blessed me with four daughters, ga Siddiqa nan" ya nuna Siddiqa yace "itace babban y'ata ta farko, mai sunan Mamana, ansamata rana in sha Allah June-July zata rubuta final exams dinta accounting taje karantawa August ne bikinta nan da four month" cikin jin dadi chairman yace "masha Allah, Allah ya sanya alheri" atare Abba da Mummy sukace Ameen, Abba yace "sai Zeenatu" yanuna Zeenatu dake kusada Siddiqa yace "she is my second daughter Zeenatu, tana 300 level a makaranta tana karanta mass communication tace ita yar jarida takeso tazama" duk dariya akai afalon Zeenatu ta boye fuskarta cikeda kunya, Abba yace "sai Lubabatu" yanuna Luba dake zaune kusada Zeena yay murmushi yana kallon Zeenah yace "itace tace tanason ta gaji mahaifin ta saidai ba Civic law ba shari'a law takeyi tana 300 level itama" kabbara chairman yayi Sameer yay dan murmushi, Abba yace "sai autan gidan Rahima" yanuna Rahima yace "kwanan nan ta shiga University, medicine tai applying bata samu ba sai suka bata veterinary medicine, nace tafara shi ahaka mugani next year saitai applying change of course hopefully zasu bata medicine din" ahankali Chairman yace "Allah ya yarda".
Wani irin kallo Mummy kema Sameer harsaida yaji ajikinshi yadago kai hada ido sukayi wani irin murmushi tayi tace "atashi aci abinci bayan angama sai kumana introducing kanku ko Lieutenant" gyadamata kai Sameer yayi batare daya kalleta ba, Mummy ta kalli yaran tace "alright girls to the kitchen time for dinner" tashi dukansu sukayi sukai kitchen, warmers da suka shiga fitowa dashi Rahima kuma ta kwaso broken plates tana tafiya ahankali takawo tsakiyan falon dayake fankacecen falone suka ajiye Mummy kuma tafito daga kitchen din tai corridor ta shiga ciki, dakinta tayi tabude wardrobe dinta, wani hadadden lace dinta ta ciro na 98k da aka mata dinkin riga da skirt blue black ne kalan lace din, agurguje ta shiga shiryawa cikin kayan aiko sun kamata chip chip kaman wata yar matashiya ta zauna gaban madubi hoda ta shafa tasaka wani jan jambaki sanan ta daura kallabi tafito tai dakinsu Siddiqa, drawer su dasuke saka gyaluluwan su tajawo tabude wani hadadden dan karamin gyalen Lubabatu blue taciro tana murmushi, yafawa tayi akafada tana kallon kanta a dogon babban madubin su, koyan murya tafarayi agaban madubin cikin wani murya irin na yan gayun nan tace "Lieutenant Sameer sauko kaci abinci please, ko kanaso adafama wani special ne?" wani irin murmushi tayi tace "yes yes yayi" da sauri tafito ta maida kofan tarufe hartakai hanyar fita ta juyo da sauri tace "turare" dakinta takoma ta feshe kanta da turarurruka sama da shida sanan tafito tana taku daidai kaman jimina, ahankali ta yaye labule tafito tana kallonsu ganin duk basu sauko kasa an faracin abincin ba, dan ware ido tayi ta juyasu cikeda yanga takaraso cikin falon tana kallon Sameer da hankalin shi kekan maganan da Abba keyi dan zancen politics sukeyi, cikin wani irin strange new voice tace "Sameer, I mean lieut" tawani kaurara Lieut din, tace "sauko kaci abincin ka karka biyema wayan nan indai Abban sune zai iya kai gobe yana maganan siyasa bai gajiba" dagokai Abba yayi ya kalleta, murmushi tayi tace "Alhaji cemai ya sauko please" kallon Sameer Abba yayi da Chairman yace "let's all have dinner, bismillan ku" saukowa kasa Abba da Chairman yayi hakan yasa ahankali Sameer ya sauko kasa shima tareda tankwashe kafa, cinyoyin shi Mummy tabi dawani irin kallo kafin ta juyo ta kalli su Siddiqa tace "oya ku matso za'ai having dinner" sanan ta kalli Rahima datai shiru ita kadai kan kujera duktai wani kalan tausayi she is not just comfortable dandai Abba nanan ne da wlh tuntuni tagudu dakinta, murmushi Mummy tayi tace "sorry Autana oya come have your dinner sai kije ki kwanta bacci kikeji ko?" gyadama Mummy kai ashgawbe tayi ta sauko kusada Mummy tazo ta zauna ta dafata murya chan kasa tace "Mummy tare zamu kwanta ko?" girgixa mata kai Mummy tayi tace "no Autana sai bakin mahaifin ki sun tafi, idan kin kasa baccin kije dakin yayinki ki kwanta kinji" gyadamata kai tayi Mummy tai murmushi tace "gud now let's eat" dan satan kallon Sameer Mummy tayi ganin hankalin shi bamaya kansu yasa cikin wata yar murya tace "me zakaci Lieuttt?".
💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
2️⃣3️⃣
Dan juyowa yayi ya kalleta cikeda natsuwa yace "anything local meal Mama" wani irin murmushi tayi tace "shikenan Lieut" ta kalli Rahima tace "bani plates let's serve ko" gyadama Mummy kai tayi ta tashi, Mummy kuma ta kalli Abba tace "Abban su meza'a zuba muku?" kallon chairman Abba yayi yace "mezaka ci Chairman" dan dariya yayi yace "fried rice is okay" jin haka yasa Mummy tace "angama" plate din Da Rahima tabata ta karba ta dau wani ta zuba white rice da beans agefe, sea food stew ta zubamai dayaji sea food tasa spoon tadaura kan tray, sanan ta dau wani portable bowl tazuba pepper soup tadaura kan mini tray din tace "Rahima dauka ki kaima Lieut" dudda tsakanin su baifi 2 zuwa 4 feet ba saida ran Rahima yabaci ganin Abba na wurin yasa ta dauka ahankali ta mike tana tafiya kaman batason yi tana kallon Sameer din da bamaya kallon inda suke hankalin shi hakan zancen dasu Abba keyi, karasawa tayi kusada shi tadan duka zata ijiyemai abincin agabanshi daidai shima ya juyo suka hada ido, gyalen data yafane akafada ya sauko hakan yasa idanunshi suka sauka kan wuyanta da jelan kitson kanta suka sauka awurin, turo baki tayi ta ijiye agabanshi ta tashi tsaye, cikin wani irin murya na wanda ya cika fam kaman zai fashe da kuka tace "akwai wani abu dakake bukata?" dan haka Abba yakoyamusu tun suna yara inhar yay baki sukai serving na bakin su tambaye su if they need any other thing that is how to make your guest comfortable, tsayawa yayi chak yana kallon fuskanta, this is the first time daya bama fuskarta 1min attention, a kumbure ganin iskanci dayake mata yasa tace "eh?" cikin wani irin yanayi nako ajikinshi yace "me kika ce? Can't hear you?" kafin tai magana Mummy tace "kiyi magana da kyau mana Auta bakowa kejin yar muryarki ba" turo baki tayi idanunta suka cika da hawaye ta kallai kaman yanda yake kallonta da kyar tace "nace dawani abu dakake so namaka?" ba yabo ba fallasa yace "get me a fork" juyawa tayi fuuu tai kitchen dinsu, Mummy ta shiga zuzzubawa kowa na dakin abinci, dawowa tayi rikeda fork shi kadai a hannu tuk kafin ta iso Mummy tadan Harare ta tace "haka akemaba bako abu? Jeki daura fork din on a very nice plate ki kawo" sjarr hawaye ya zubo mata ta mugun gaji juyawa tayi takoma kitchen din ta dauro fork din kan plate tadawo tazo har gabanshi ta ijiye mai, sanan tajuyo Mummy tanuna mata kusada ita tace "zoki zauna kici abincin ki kowa nacin abinci banda ke" zama tayi kusada Mummy, Mummy ta shafa kanta tace "me zaki ci eh?" makema Mummy kafada tayi kaman a idanun Abba yace "zuba mata abinci taci, so kike ciwo ya kamaki" zuba mata fridge rice Mummy tayi dan kadan sanin bazata ci, karba tayi tadan saci kallon Abba ganin hankalinshi nakan Abincin dayake ci yasa ta kalli Mummy dake kallonta girgiza mata kai tayi, hakan yasa Mummy ta shafa kanta tace "please eat Rahima ko kadan ne" tai maganan tadan saci kallon Sameer dayakai tamarin juice bakinshi yana sha anatse. Ahankali ta shiga cin abinci kadan kadan shiru akayi dakin tsit anacin abincin, Mummy gabaki daya tarasa sukuni bata sakan talatin cikakke bata saci yanda Sameer kecin abinci ba baimasan tanayi ba, almost 30min suka dauka sunacin abincin sanan aka gama su Siddiqa sukai clearing falon tass, Chairman ya kalli Mummy yace "I really enjoy your food Madam, I must say Chief judge is lucky to have you wlh, saisa kullum he is looking fresh" dan dariya Mummy tayi cikeda jin dadi Chairman ya yabeta Abba yay murmushi, ahankali Sameer yace "thank you so much for having us Sir" yadan kalli Mummy yace "it was such a nice meal Mama, I really enjoyed it" tashi tsigan jikin Mummy yayi sabida yanda yay maganan cikin wani irin yanayi tana kallon fuskarshi tace "Allah Sameer" gyadamata kai yayi yanadan gyara zama, ahankali tace "to ko nagode muku naji dadi yanda kukaji dadin abincina" ajiye toothpick Abba yayi ya kalli Chairman yace "sai asan juna ko yanzu Chairman, gani ga Family na nan duk kun gani" dan dariya Chairman yace "ahhh what can I say, as you all know nine chairman din NDLEA, ni family man ne, matana yarana 6, 5 boys 1 girl, my eldest son yana University yana karantan computer engineering, sauran yara mazan duk secondary school suke, macen kuma bata fara school ba har yanzu breastfeeding nata akeyi" Abba ne yace "masha Allah Allah ya raya mana, in sha Allah one day I will bring all my family over mu kulla zumunci" da sauri chairman yace "da izinin Allah kuwan" shiru akayi Mummy takosa Abba ya tambayi Sameer nashi, kaman Abba ya shiga zuciyan ta yace "Lieutenant kaifa" dan murmushi Sameer yayi yace "actually ahhh, well I don't have much to say" wani irin ajiyan zuciya Mummy tasauke tana kara gyara zama tana kallonshi tsigan jikinta har wani irin tashi yake in yana magana. cikin calmness dinshi yacigaba yace "nine first born din gidanmu, the eldest, I have 3 brothers, mu hudu maman mu ta haifa, my Dad is late" ahankali kowa na dakin yace "Allah ya jikanshi" dan murmushi yayi yace "Ameen, so that's all akaina" da sauri Mummy tace "are you single Sameer, bakai aure ba?" gyadama Mummy kai yayi batare daya kalleta ba yace "not yet Mama" da sauri Mummy tace "how old are you? I mean shekarun ka nawane?" wani irin kallo Abba yama Mummy dan he felt somehow datai tambayan dan tana shiga privacy nashi ne a yanzu, he already told us abinda yakeso musani game da shi why asking him wasu questions kuma. Dan juyowa Sameer yayi ya kalli Mummy ido cikin ido yace "39 Mama" Mummy wani ruwa yafara dan tsiyayo mata the way he looked at her right in the eyes and say to her face he is 39 was damn sexy, goosh Sameer is hot wlh, dan murmushi tayi tabude baki zatai magana Abba yace "yaudai kin dawo yar jarida wifey" dan dariya Mummy tayi tace "Alhaji just wanted to know Lieutenant better ne kasan kona nema mai mata tunda yadawo tuzuru" tai maganan tana kallon Sameer dan dagokai yayi ya kalleta kafin yasake dauke kai, ahankali Abba yace "to Alhamdulillah, Siddiqa kutashi kutafi dakinku ku kwanta" tashi duk sukayi Rahima ma ta tashi zata bisu Abba yakirata. "Rahima" da sauri tajuyo ta kalli Abban, da hannu yamata alamun tazo yace "come back here" dawowa tayi ahankali tazauna a inda Abba ya nuna mata akan kafet a tsakar dakin duk sukai shiru a falon, tashi Abba yayi yahau kan kujera yace "kutashi kuhau kujera please" tashi duk sukayi sukahau kan kujera harda Mummy duk aka natsu, gyaran murya Abba yayi yace "to Alhamdulillah ina farin ciki da irin wanan rana" ya dubi Chairman da Sameer yace "a yanzu na daukeku Family na najini, aduniyan nan banda kowa ni kadai mahaifiyata ta haifa kafin daga baya ta rasu, gona biyu data barimini dasu na shiga dakaina makaranta harna dawo mutumin nan da kuka gani yau zaune agaban su, saisa dudda kudina I try as much as possible naga ina rayuwan rufin asiri sabida nasan duk wani wahalhalu na rayuwa, banda haka kuma randa komi zai kare wanda ba'a fata my family will be able to survive, bakomi nasa Rahima should stay back ba inaso ka dauketa amatsayin yarka ne" yadafa Chairman sanan ya kalli Sameer yace "Lieutenant inaso kadau Rahima amatsayin kanwarka kuhadu kumata fada, d'a na kowa ne, mutum shi kadai baya ya kula da danshi sabida idanu biyu kacal Allah yamai, but by the time aka hadu ana kula da yaron idanu dayawa akanshi yaron yasan da haka saikaga ya natsu, baran muku karya ba duk cikin yaran nan nawa dakuka gani banda fitinanniyar yarinyar, yar bala'i, da tonan fada, rashin kunya da rashin ji kaman Rahima ba, nasan Rahima bataji wanan bazan taba musawa ba amma bansan rashin jin yakaiga harta Tara abokanai na banza kuma maza harsu dorata kan shaye shaye ba, bansa abin yakai hakaba, sonake kumata fada sosai da sosai" Abba yay shiru yana kallon Rahima da kanta akasa, Chairman ne ya nisa yace "Rahima ki daure ki rabu da iyayen ki lpy, nasan kowa baya tsallake kaddaran shi but abokanen banza kaika suke baro su halaka maka rayuwa, ki rabu dasu baki babu su daga yanzu kinji" gyadamai kai tayi ahankali Sameer na kallonta.
Ahankali Chairman yace "saura kai Lieutenant, mezaka fadama kanwar naka" dan nisawa Sameer yayi ya gyara zama yace "In Islam Shaye Shaye is forbidden, na farko akwai manufofin shari’ar musulunci guda biyar akwai ;
1- حفظ النفس kiyaye rai
Duk wanda yasha taba, yasha su shisha, codeine, tramadol da sauran su dakeda illa akan lafiyan shi domin kwayoyine masu kashe rayuwan dan Adam, duk sun shige anan da duk wani abu da mutum zai sha ya cutar da kansa.