Showing 27001 words to 30000 words out of 190952 words

Chapter 10 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

399

akofar gidan yabude mota yafito sanan ya zagayo ta side dinta yabude mata kofan, fitowa tayi ta tsaya tana kallon ko ina, hannunshi yamika zai rike nata da sauri ta janye tace "ni karka rikeni" dan juya ido yayi sanan ya rufe motar yakarasa gaban Gate din bude Gate din yay ya shiga ciki tana biye dashi, babban tsakar gida ne da aka gyara ga kayan dj duk anyi setting up ga balloons ga kujerun da aka jera dayawa na baki, turo baki tayi dan yasoma dama zama jikinta yin hakan tace "ina mutanen to?" murmushi yayi yace "just few of my friends are inside with their babes chilling you know, the dj sun tafi cikin gari dauko some stuff, the main party zai fara dan anjima insun dawo let's go" binshi tayi ciki tana kallon ko ina har zuwa dan flat daya kachal dayake big compound din tun kafin su shiga sukejin warin wiwi, bude kofan yayi ya shiga yana mata alamun ta shigo itama shiga tayi wasu mazane guda uku tareda yan matan su dasukaci uban attachment suna smoking weed ga shisha pot agabansu dawasu kwalaban abubuwa, yatsine fuska Rahima tayi ta juya zata fita da sauri yakamo hannunta yace "No beautiful don't go, I promise you will have fun today, beside we we are not sitting here am taking u inside" yay maganan yana janta ahankali zuwa ciki batare daya kalli abokan ba suma suka share shi basu cemai komi ba, wani daki yabude dakin gado ne da kujera a gyare tsaf ga TV dake aiki, zaunar da ita yayi kan kujera yace "sit here, bari naje na kawo mana abubuwan mu let's have fun, don't worry I will take care of you kinji beautiful, now smile for you" dan murmushi tayi ganin duk yanda yabi yadamu sabida yaga ta daure fuska, tashi yayi yafita zuwa mota, wani babban basket yadauko dake dauke da shisha pot guda uku dawasu kwalabai ya shigo gidan, yay dakin datake, aijiyewa yayi a gabanta sanan ya maida kofan yarufe yadawo kusada ita ya zauna ya fito da shisha pot daya ya daura akan table din dake gaban kujeran dasuke kai yace "do you do shisha Beautiful" girgixa mai kai tayi hakan yasa yay dan dariya yace "what! kinyi missing, Shisha tsabagen dadinshi jizakiyi kaman kimutu barinma yanda na zuba harizona aciki hulala baby, yay maganan yana ciro wasu kwalabe guda biyu suma yadaura agabansu yace "this are mixture of codeine and a lil bit of crack, crack din just half teaspoon da kyar my guy yabarmin shi 50k" kallonshi tayi tace "menene crack din?" cikin gurbataccen hausan shi yace "Yayan Cocaine ne Crack, Cocaine elder brother kenan Beautiful in kinsha crack inspiration ne kawai zaita zuwan miki baby, wani irin dadi da murna zakiji, feeling kaman ke kadaine aduniyan nan, bakida matsala ko daya, have a sip a feel it" yamika mata kwalban daya bude karba tayi tana kallon bakinshi kafin ahankali ta kurba, lashe baki tayi tadanyi murmushi tace "laaaa dadi kuwan" murmushi yayi yace "yes da madara madara acrack din sanan ga codeine saisa kikaji yay dadi but don't take much this is your first time" sake kurba tayi, zata sake maidawa baki yace "wowowo is okay, gwara kima shisha wanan shan, this is big for you dan crack can kill you wlh, oya let's see how many kalan buso hayaki kika iya let's play a game" yay magana yana bata mouthpiece din shishan, shima ya rike nashi mouthpiece din, yace "let's do it in one, two, annndddd three" atare suka zuko shishan kafin su janye daga baki, shiya fara mata alamu ta kalleshi hakan yasa ta kallai yawani irin huro hayakin daga hancin shi in style din circle circle, ware ido tayi kafin ta huro nata hayakin ta baki yay wani irin saman dakin kaman an bude teargas tafi ya shiga mata yace "yayyy beautiful u are really smart, ya kikaji shishan strawberry flavour ne yahadu ko" murmushi tayi bamata kulashi ba tsabagen yanda shishan yamata dadi takara kaiwa bakinta, murmushi yayi ya dauko kara daya na weed yaciro lighter daga aljihun shi ya kyasta sanan ya maida lighter yakai weed din bakinshi ya zuka hakan yasa ta kallai tana huro hayakin shishan, karan weed din yamika mata yace "zaki sha?" hararan shi tayi tace "give me a new one" dauko wani yayi ya kunna mata yabata karba tayi tashaka ta fuzar sanan tasha shishan tana murmushi today is just the best day of her life, inda ace su Ya Siddiqa sundan dadin abin nan da saisun saye duka weed da codeine din duniya gaba daya, lumshe ido tayi ta wani irin jingina da bango bacci nawani neman kwasheta dan abubuwan sun soma bugar da ita tun tana bashi amsar maganan shi harta zo bamataji da kyau, zata karakai dan gutsuren weed din bakinta Chris ya karba da sauri da mouthpiece din shishan ya ijiye su kan table yace "hey beautiful, you have had enough, don't want you to pass out is okay" dan turo baki tayi cikeda rashin jin dadi murya chan kasa da bata fita sosai, very slow tace "give me the shisha" hannunshi yasa ya shafa soft kumatunta yana kallon yanda take lumlumshe ido murya chan kasa cikeda sonta yace "you are the first Muslim girl I've ever loved in my life my god u are so beautiful, so pretty" dan bude ido tayi kadan ta hararai kafin tasa hannu ta kabar da hannunshi dake kan kumatun ta, cikin magagin bacci da maye tace "stop touching me" dan kara matsowa kusada ita sosai yayi yanajin tashin kida alamun mutane sun fara zuwa kenan dayake ansan yana tareda babe saisa ba'a zo an tadashi ba, matsowa kusada ita sosai yayi ya manna ma kumatun ta kiss ahankali yace "baby stand up mu kwanta akan gado, your Mum said we should have fun so let's have fun" yay maganan yana kokarin daga ta tureshi tayi batare data bude idoba tace "leave me alone" ganin tanada gardama and she is a lil bit stubborn yasa yawani irin fizgota jikinshi, da sauri ta bude idanunta dasukai jajir tana kokarin tureshi amma yaki barinta wani irin ihu ta kurma amma ko kadan ba'a jinta sabida karan kidan dake tashi agidan, kama fuskarta yayi tana kokarin kwancewa ya manna mata kiss abaki ya shiga laluban boobs dinta da tuntuni suke idanunshi baida burin dayawuce yaga yataba........






Wuraren four ya shigo Abuja hakan yasa yakara gudu sabida yakamata yay attending meeting dinan is his first meeting as lieutenant, kuma meeting ne da harda Chief of staff din Nigeria akan how to ensure security a Nigeria, yakai ta wuraren express road din Abuja wayarshi ya shiga kara, kallon wayan yayi while driving ganin Marshal barobaro kan screen yasa yarage gudun motarshi yagangara gefen hanya yay parking tareda daukar wayar yay answering call din tareda kamewa yace "Sir!" daga tachan bangaren Marshal yace "Lieutenant that meeting is not going to hold, am in the airport going out of country right now, until I get back" anatse yace "I wish you journey mercy sir" "thank you Lieutenant" ya katse wayan, ajiyan zuciya ya sauke tareda sauke ajiyan zuciya Allah nasonshi sosai dudda ya iso Abuja inda ace akwai meeting din babu yanda zaiyi yakai Barrack batare dayay latti ba, yin latti kuma is considered as unethical aspect of his profession, wani mahaukacin sauti daya daki dodon kunnenshi yasa yabude ido da sauri motace dake dauke da saurayi guda daya sai yan mata biyu akai dasuka sha attachment suna cikin wanan motar mara marfin sama, saurayin na driving da hannu daya yana shan shisha da hannu daya, bin motar yay da kallo hartai dan gaba kadan sanan tawani sha kwana, shi mutum ne dazaran mind dinshi yabashi yay abu yake, hakanan suna wucewa yaji kawai yanaso yabisu, tada motar yayi yakarasa har daidai inda yaga sunyi kwana ya kalli layin motoci yagani pake a wurin daban daban hakan yasa yay kwana ya shiga layin tayoyin motarashi sai taka kwalban su tutolyin yake, kashe motar yayi bayan yay parking abayan wata mota camry dayagani awurin yanajin tashin kida ga samari cike a awajen wasu kan saman mota suna zukan taba, wasu kuma na shan shisha ga mata gefensu, wasu rike da kwallaben giyoyi, ga ihu dayaji yana tashi tako ina, kashe motar yayi yana kallon yaran yace "why are all this Indomie generation so stubborn? Me sukeji a shaye shaye bayan clearly yana rubuce ajikin taba and other stuff cewa shaye shaye na kisa da wuri? Why are children taking what is harmful to their health" dan tsaki yaja yadau wayarshi ya shiga turama number dayay saving da NDLEA sako.
_"am at kaduna-kano express road, some bunch of gang are partying with loud music on and using hard substances and other illicit drugs which according to constitutional law of Nigeria clearly state that they're illegal and as such anyone caught on such act must go for six month rehab, you need to invade into this premises and investigate properly with immediate effect, let's all come together and make Nigeria great again"_.
*Lieutenant Sameer Simran Sameer*

Ko minti daya baiyi da tura sakon ba sukayo reply "stay there lieutenant, we are on our way", gyara zama yayi yana kallonsu dudda su hankalin su bayama kanshi shaye shayensu kawai suke suna rawa suna wasa da yan matansu dabasu da banbanci da karuwai suna turenci.💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫



_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔



✍️ M Shakur





1️⃣7️⃣



Tashi yayi yawuce bedroom dinshi ranshi abace wasu kananun kaya ya dauko, Black jean yasaka sai wata Ash color riga short sleeve mai gajeren hannu yasaka, rigan nada V neck daya bayyanar da kwantaccen gashin kirjinshi, rigan ta kamashi sosai, kaman rigan zata barke ajikinshi sabida yanda ta bayyanar da kiranshi na full packs man, Black jacket yadauka yadaura kan rigan yasaka wani boot baki yadau car key dinshi, kana ganinshi kaga soja yafito daga flat dinshi yaso ya shiga wajen Ummi but no Inya dawo yaje, he don't want to waste anytime, motarshi ya shige yaja tareda danna horn mai gadi ya budemai gate yabar gidan.




Tashi Ummi tayi daga jikin window bayan taga taga fitanshi jikinta ya mugun yin sanyi takoma kan gado ta zauna ta buga uban tagumi cikeda damuwa ta daga hannayenta sama tace "wanan wani irin jarabawa ne Ya Allah meke damun Sameer ne dako kadan mace bata gabanshi?" tai dan shiru tasa hannu tai maza ta goge hawayen dake shirin zubomata, tasowa Nuru yayi yazo kusada ita yabata side hug cikeda damuwa yace "Ummi kidena damuwa okay, kidinga mai addu'a in sha Allahu har jikokin shi zaki gani nan bada jimawa ba kuwan" fuskar Nuru ta kalla tace "anya? Kaduba pa am sure sabida maganin dana gayamishi Baffa shi yakawomai ne yau da safe yasa yaki shigowa dan baisoma yasha, Noor ya zanyi da raina eh? Yayanku fa Noor duk ya girmeku nesa ba kusa ba, yabaka almost 8yrs but look at you now da Nabila batai having miscarriage ba da kanada yara biyu aduniya, I tot yanda na kawo maganan Asiya he will accept da gudu sabida cousin dinshi ce kuma naga suna shiri yarinyar na sonshi sosai, bazai wani sha wuyan neman aure ba dan da gudu Baffa zai bashi ita amma kalli abinda yama" ahankali Nuru yace "Ummi kibar maganan Asiyan nan, it won't work, ai dama tun kafin kiturani na gayamiki kice Yaya Sameer ya auri Asiya ai kaman kin kara koranshi daga zancen auren ne, Yaya Sameer dason girma tsiya inya auri Asiya ai kaman ya yankin ma kanshi ticket din raini ne, ni nasan dama bazai taba koda da wasa he will not accept maganan nan, kawai kiyitamai addu'a Ummi what goes around comes around, Yaya Sameer zaiyi aure one day one day" cikeda damuwa sosai Ummi tace "Ya Allah, Ya Allah kadubi lamarin nan nawa, Ya Allah ka karkata zuciyan Sameer zuwaga wata mace, Ya Allah kahadashi da wacce zaiso sosai, Allah ka aurarmin da yaron nan badanni ba badan halina ba" tasake share hawaye daya zubo mata rungumeta Nuru yayi yace "is okay Ummi ya isa hakanan" haka yacigaba da lallashinta har Muhammad shima yadawo duk suka taru suna bama maman nasu baki harsuka samu ta dawo normal tadan wartsake tabiye musu sunata hira.




Tunda aka shigo dasu headquarter anan reception aka zubesu duk wanda zai wuce saiya kallesu, gabaki dayansu akasa suka zauna bama abasu kujera ba, Rahima tai kuka har idanunta sun kumbura kaman zaka taba jini yafito, daukan sunayen su akayi gabaki dayan su saiga wata mata ta taho da kayan first aid box a hannunta tareda daya daga cikin officers din dasuka kawo su suka taho gaban Rahima. Rahima yanuna mata yace "ga wacce batason ta mutun nan amma take shaye shaye, duba kafan Dr, tai targade Lieutenant ya gyara mata dazu" murmushi Dr tayi ta tsugunna a gabanta tana tattaba kafan ahankali kafin ta bude first aid kit din tadauko wani man zafi ta shafa mata sama sama tace "ya gyaru kamai muscles pain take having, wanan balm din kuma will kill it nan bada jimawa ba" sakin kafan tayi auduga ta dauka ta daura kan goshin nata tana share mata jinin wajen tace "what is your name yanmata?" shiru Rahima tayi batare databata amsaba tai banza da ita hakan yasa Dr din ta kalli fuskarta tacigaba da aikinta tace "young girls kaman ke always think shaye shaye is a gateway to having fun, inspiration, zero worries da sauran, aganinku shaye shaye wayewa ne irin kema kin isan na, but my dear is a lie bahaka abin yakeba, yes nasan shaye shaye nasa ka manta da matsalolinka, ka manta da bakin ciki da duk wata damuwa data addabi zuciyarka, kaji kaman kai kadai Allah ya hallita a duniyan nan, kaji yes a yanzu u can stand up to anybody kodakam babanka ne, inkayi you can stand up against anyone and anything in fact u can even stand against the world, shaye shaye nabaka wanan karfin da boldness din da jarumtar aganin ku but my dear is not true, duk ba hakabane, shaye shaye is mess with the heart and mess with your brain the IQ dinki, baya komi illa destroying dan Adam, tundaga na lafiyan shi harda sauran su and kill u wulakantaccen killing ma, but you know you still have time, u are young, you are too beautiful karki bata rayuwanki akan wanan shaye shayen da kikejin dadinshi nayan mintoci, see duk abinda dadinshi ba dawwamamme bane den babu amfani yi, dadin da last for few hours ko for a day dadi ne? Ki natsu kituba Allah zai yafemiki kisan me kikeyi kokya samu rabauta" tana maganan tana shafa gyaramata injury din goshin nata sanan ta shiga hada kayanta, ahankali Rahima tasa hannu ta share hawayen dasuka cika idanunta suka sake zubowa sharr, ganin Dr looks friendly yasa murya chan kasa tace "I want to use the restroom" dagokai Dr tayi ta kalleta jin tamata magana for the first time, murmushi ta sakin mata tace "stand up muje na kaiki" ahankali ta tashi tana dafa bangon wurin tanadan dingishi suka wuce itada Dr din, officer yace "kuma two minutes nabaki" da Dr suka tafi daidai sunkai wajen bayin wani yafito daga wani office ya kwalama kira yace "Dr you are needed here" da sauri ta kalli Rahima tace "shiga this is the rest room, zakiga ladies side inkin shiga" tai magana tana tafiya, bude kofan Rahima tayi ta shiga rest room din, dan passage ne awajen dakeda two pathways dama da haggu da akwai kofofi, ko kadan bata lura da sign din ladies da gentlemen ba take nuna Wannene bayin maza dana mata ba tabude kofar dama ahankali tanadan dingishi ta shiga, maida kofar tayi tarufe tai ciki, saida tai dan tafiya sanan ta iso main falon bayin wasu jerin bayi guda shida ne sai wash hand basin da manya manyan mirror a bangon, da sauri takarasa tabude bayin farko ta shiga ta mayar ta rufe, bayin so clean babu datti kodaya kodan bayin maza ne saisa oho, but bayin mata dai always yacika datti, mayar da kofan tayi tarufe tasa sakata sanan ta daga riganta sama tasa hannu a aljihun bayan wandon ta taciro wayarta da tuntuni take wurin Allah yaso ta babu wanda ya kirata da asiri ta yatonu sun kwace dan duk an karbe wayan sauran, maida wayan silent tayi da sauri sanan taciro number Mummy tana goge kwallan datake yi tai dialing number har wayan ya katse ba'a daukaba, haka tasake kira shima ba'a daukaba fashewa tayi da kuka tayi mara kara tana taushe bakinta, ba karamin tashi hankalinta yayiba takira mummy sau 17 times bata dauka ba bakaramin tashi hankalinta yayi ba yanzu kwana zatayi a wurin nan, gashi an fara kiraye kirayen sallan magrib, share hawaye tasakeyi, ahankali tasa hannu ta sauke cover bayin, zama tai kan sitter ta rufe fuskarta da duka hannayenta tana kuka tajima ahaka sanan tai shiru ta share idanunta tana kallon wayan sanan ta shiga saka wasu nambobi tadanyi jimm tana kallon number kaman mai tunanin wani abu kafin ahankali tai dialing number tasa hannu ta share hawayen daya zubomata takara wayan a kunenta, har wayan tagama ringing ba'a dagaba hakan yasa tasake dialing number akaro nabiyu, wayan na gab da tsinkewa aka dauka batare da ance komiba, ajiyan zuciya ta sauke mai kara kafin cikin muryan ta dake rawa sosai tace "h......he.....hello" hannu tasa tasake share hawayen daya zubomata tareda jan majina irin na wanda yaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login