Showing 96001 words to 99000 words out of 190952 words

Chapter 33 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

431

ta shareshi tacigaba dajan charbinta, jitayi zuciyarshi na kumfa Ummi maisonshi dake kula dashi kullum hakane yauke fushi dashi tamaki amsa gaisuwan ta, ahankali yasa hannunshi dakedan rawa yakama hannunta data rike charbi dashi, wani mugun kallo tamai batare data cemai uppan ba bakinshi narawa sosai yace "ki...yafemin....Ummi" dan gyaran murya yayi danji yayi muryanshi na dishashewa yace "I'm sorry Ummi, please ki yafemin" fizge hannunta tayi daga nashi tacigaba dajan charbinshi ahankali ya kwantar da kanshi kan kafafunta wasu irin hawaye masu bala'in dumine suka shigo zubomai, yakai almost 5min ahaka sanan yadago kanshi ya kawad da fuskanshi gefe yasa hannu ya goge hawayen tass, sanan ya kalleta da idanunshi dasukai ja sosai yace "kiyakuri Ummi dan Allah, zan tafi aiki karnai latti, mezan taho miki dashi inzan dawo? Akwai fruits?" ganin ko kallonshi batayiba yasa yatashi kaman wanda jinin jikinshi yakare yajuya yay hanyar kofa, hannu yasa zai bude kofa Ummi tadanyi gyaran murya da sauri yajuyo, babu alamun rahama kan fuskarta tace "in kaje dakinka ka tabbatar ka tattaro kayanka tatas ka jera a akwati kabarmin gida danyau bazaka kwanan mini agidaba, kariga kayi aure kabarmin gida kenan, and the so call yar shaye shayen matan taka koma ina kace take better go and bring her dan in mutane sunzo zasuje su ganta ba rehab zan dinga turasu ba gidanka zan turasu" tai maganan tana watsamai harara, juyawa yayi da sauri yafita daga dakin, ko kallon Mu'az dake zaune afalon baiyiba yawuce yafita Mu'az yabishi da kallo ya mugun bashi tausayi dan yaji me Ummi tacemai.

Fkat dinshi yaje ya shiga sauko da akwatinan shi dan baya iya ja da maganan Ummi jiyama he regard it as kaddara ce kawai, ahankali yashiga hada kayan shi na amfani barin ma takardun shi yana tunani yagama gidan tass amma dayake aiki yatasashi agaba baibi takan zubama gidan furnitures ba, message ne ya shigo wayanshi, ajiye kaya a akwatin yayi yadau wayar, ganin message daga Abba ne yasa yabude.
_"Assalamu Alaykum Son, I will really like to see you in person inkasamu chance maybe koda anjima ne I ka dawo daga aiki, sai secondary, akwai interior company danai contacting dan kayan dakin Rahima, they called sunaso suzo suyi taking measurement din dakunan dan yau zasu fara kawo kaya, I don't know how you will go about it thanks_
Dan jim yayi dan baiwani so Abba ya wahalar da kanshi shizaisa komi besides bawai auren dindindin bane yarinyar dazai rabuda ita, reply kawai yama Abba da address din gidan dan baisan mezaiyiba, hada kayanshi yayi daga bayama Mu'az ya shigo yatasashi suka hada tsaf a akwatuna guda hudu tsaf sanan ya shiga wanka agurguje yazo ya shirya cikin uniform Mu'az sai kallonshi yake, yana gamawa yatasashi suka gunguro kayan yasaka a Boot sanan ya shiga mota yatafi, hawaye Mu'az ya share na bakin ciki.




Wuraren karfe goma Mummy ta shigo gidan, parking tayi tafito taci gayu sosai har wata yar kiba yakara tasa wata dog uwar atampa dayasha stone work, jakanta tadauka sanan ta kwalama gateman kira tace "ya shigo da sauran kayan inya fito daga bayi" dan cewa yayi yana bayi tai ciki, sallama tayi ta shiga falonsu babu kowa sai su Siddiqa dake kallo suna ganinta duk suka tashi da gudu. "oyoyo Mummy, Mummy ya sunan ina tsaraba?" dariya tayi ganinsu tace "yanzu mai gadi zai shigo muku da tsaraba....." kasa karasa maganan tayi sabida jakunkunan goro da sweet data gani ta kalli yaran tace "wayan chan goron da sweet na miye?" Luba tace "na Abba ne jiya da daddare yabama mai gadi yakawo ciki, yacewai saikin dawo zai fadi mana goodnews din" da sauri Mummy tace "good news, what could possibly be this goodnews" ta kallesu tace "ina baban naku yake" "yana study room" jakanta tabawa Zeena tace "kaimin daki bari naje wajenshi naji wani news ne" juyawa tayi tai kofa zata fita kenan saiga Abba zai shigo murmushi tayi tadawo baya tace "Abban su ai wajenka zani, naga goro yara suncemin goodnews ne wai kace saina dawo zaka fada" shigowa dakin Abba yayi tareda kana hannun Mummy ya zaunar da ita kan kujera yace "ku zazzauna kuji" washe baki Abba yayi farin ciki kaman zai zuba ruwa akasa yasha, ya kalli goron sanan ya kalli Mummy yace "kinsan goron waye?" da sauri Mummy itama ta washe baki ganin yanda Abba ke murmushi tace "saika fadi" cikeda murna Abba yace "goron daurin auren yarki ce" cikin rashin ganekan zancen Mummy tace "daurin auren y'ata, wace y'ata?" da sauri yace "Rahima" dawani irin sauri Mummy tace "Rahima! Rahima Auta na, ita kama aure?" washe baki Baffa yayi yace "jiya tadawo ai itada Sameer yamaida ta rehab, so around 9 nadare aka daura auren" yay maganan yana chusa hannu acikin aljihu yaciro wasu kudade sababbi ya ijiye kan jikinta yace "ga sadakin ta nan dubu dari da hamsin" faduwa gaban Mummy yashigayi sosai da sosai jin ya ambato Sameer, ahankali bakinta har rawa yake tace "Abban su wa.....w....waka aurama Auta?" wani hadadden smile Abba yasaki mai sauti yace "you will not believe it, this calm, natsastsen yaron mai hankali Sameer dakika sani shiya aureta" wani dry saliva Mummy tahadiye tana kallon fuskan Abba da babu komi aciki sai farin ciki bakinta narawa sosai tace "wa......wani.....Sameer Alhaji?" da sauri Abba yace "sai ance kinfara tsufa kidinga fadama mutane me yarinya ce, lieutenant Sameer Simran Sameer dinne baki sani ba, Sameer na aurama Rahima" wani irin faduwa gaban Mummy yayi wani irin abu taji suna tasomata hakan yasa ta lumshe ido tareda sa hannu tadafe kanta tana kokarin dannewa, ganin yanda tayi yasa Abba yace "wat is it Wifey?" kaman jira take tawani ma Abba ihun da batasan ta iya irinnshi ba tace "for God sake don't call me Wifey Abban su because is being long you stop treating me as such, ka tashi kadaumin yarinya dasai ranan nan nasamu da kyar kafadi mini cewa kauye ka kaita inda bazata iya dawowa ba, sai yanzu kuma kana gayamin ka aurar min dda iya, Alhaji are you trying to show me niba mahaifiyar Rahima bane saisa kake yanke decision akanta without letting me know eh? Because I think I left this house yesterday in the morning amma har akai komi bakasan yakamata ka kira ka sanar dani ba, Alhaji karasa wabda zaka aurama Auta sai Sameer wanan tuzurun duka duka shekarun Rahima nawa? Ina zata iya zama dashi ko kake yakashe ta?" hannu Abba yasa zai jawota yace "calmdowm wife" da sauri su Siddiqa suka tashi suka fita daga dakin sukai dakinsu.
Abba yace "don't be paranoid, this is such a good news da yakamata ma we should throw a party, Sameer is a good man you know, mu godewa Allah tasami miji haka kinga yanzu hankalinmu zai kwanta munsan zai natsar da ita and discipline her above all we know she's in a safer hands koba hakaba" sharr hawaye suka zubo daga idanun Mummy tace "celebrate, Alhaji kaci we should celebrate? Kadau yar jinjirar yarmu kabama tsoho ne I will celebrate, yaushe Auta zata iya daukanshi, ka aurama yarinya tosho abokin babanta sa'an kane fa" murmushi Abba yayi yace "Sameer dan 39 ne sa'a na? Kinfara tsufa wifey, banda hakama yau kananun yara suka fara auran tsofaffi su zauna lpy kijisu shiru, I think all this maganganun dakike yi aren't necessary" cikin fushi Mummy tace "Alhaji Rahima fa a cikinshi take iya tsayinta, mesa ba zaka aura mata wani ba ko cikin yayan abokanen kane sai Sameer eh, wanan katoton tuzurun yaro jiki kaman basamude....." ganin tanata surutai yasa Abba kawai ya karkada kai yace "I need to run some errand anjima nadawo zan baki wasu kudi dazakiyi ma Rahiman hidima, aure anriga an daura ki dauka haka Allah ya kaddara, saina dawo" yadau car key shi dake kan center table yafita binshi da kallo Mummy tayi kafin tafashe dawani irin kuka, bata taba sanin zata dawo gida ta tarar da wanan bakin news dinba kaman zata mutu takeji, zuciyanta yay mata daci da zafi, Rahima ta auri wanda takeso wlh bazata yardaba, ita Rahima harta isa tai kishi da ita inaaa!
57....











Fashewa da kuka Mummy tayi taci kuka harta godema Allah, ranan haka tawuni cikin kunci da bakin ciki, gawani kishin jaraba dake cinta kaman zata hadiyi zuciya tamutu, hatta y'ay'anta kasa gane kanta sukayi. Wanan kenan.


Yana zaune a office dinshi har yamma baimasan a ina zai kwana yauba dan yan interior company nan nagidanshi a auna nan a auna chan anata kawo kaya, he is so worried akan Ummi dake fushi dashi, knocking kofarshi akayi hakan yasa ya kalli kofan tareda rufe system dinshi yace "common in" bude kofan akayi Noor ne da Muhammad suka shigo duk sunamai murmushi saikuma yaga matayen su rikeda yaransu a hannu sunci gayu hakan yasa yatashi kafin yaga Mu'az ya shigo rikeda wani cake da aka rubuta happy birthday ajiki da happy married life ga uban balloons, dan zaro ido yayi like wats all this, maida kofan Nabila tayi tarufe Mu'az yakaraso ya ijiye fine cake din kan table dinshi tareda kunna fireworks din hakan yasa dukansu sukahau mai waka. "happy birthday to you, happy birthday to you, Happy birthday to Yayan mu, happy birthday to youuuu, hip hip hurray" sukahau tafi, murmushi yayi yazagayo hannu yasa yakarbi Princess daketamai dariya Nabila tace "ina yini Ya Sameer" ahankali yace "lpy lau" sanan ya kalli jaririyan Fadila ya shafa kumatun ta yace "babygirl you came to my office today" duk dariya akayi Fadila tace "happy birthday yayan mu, ina yini" ahankali yace "Alhamdulillah" sanan yanuna musu dogon kujeran office din yace "ku zauna" sanan ya kalli Noor da Muhammad dake tsaye yace "ku zauna" zama sukayi kan kujeran dake gaban table yanunama Mu'az stool yazauna shima kafin ya koma kan kujera ya zauna rikeda princess yay murmushi tareda kallon cake din yace "I've forgotten yau birthday dina ma" yasake murmushi sanan ya kalli Noor yace "thank you guys" akadanyi shiru, ahankali Noor yace "Yaya Sameer, I came here we all came here not just for this" ya nuna cake, yace "Ya Sameer tun ina dan karami I watch how you live your life akan gaskiya dayin abubuwan gaskiya, one thing dana sani kanka haryau har gobe shine you don't just do things anyhow kome kayi I know akwai reason behind it, Ya Sameer ko prostitute today kace zaka aura I will support you dan nasan kasan me kakeyi, I trust my brother and I stand with you in every step you take, worry not okay, Ummi zata sauko itama I assure you this" ajiyan zuciya yasauke yana kallon cake din kafin ahankali yace "there's more to wat am doing ku kannai nane dole ma sanar daku, banso iyaye susan maganan dan ba hurumin mu bane mutona mata asiriba is left for Abban su should find out dakanshi" labarin Rahima yashiga basu tatas, duk dakin dama Fadila da Mu'az sune masu saurin kuka saida sukayi, Sameer yace "I just see Rahima kaman kanwar mu su Asiya and Yusra, I look at the whole case like look at Princess, ga babygirl all of them are children nobody knows tommorow, lemme save this girl dan nima inada kannai da y'ay'a mata, and if by saving her from that wicked is by marrying her am ready to do it, shikenan" tasowa Mu'az yayi da sauri yafada jikin Sameer yahau kuka, ahankali Sameer yay patting bayanshi yace "kaga nahanaka kuka u see princess namaka dariya" dagokai yayi ahankali ya kalli yayan nashi yace "Ya Sameer I want to be like you when I grow up, u truly have a heart of gold" kanshi Sameer ya shafa yace "stand up jeka zauna awurinka" tashi yayi yakoma yazauna, Muhammad ne yace "to yaushe zakaje ka daukota daga rehab? Inyazo ta dinga zuwa as an outpatient saisu dinga bata appointment" ajiyan zuciya Sameer yasauke yace "Ummi tace nadaukota but yau ana zuba funitures, am planning gobe zan daukota" gyadakai Muhammad yayi da sauri Nabila tace "Ya Sameer ni banma gantaba but Allah yadauramin sonta already and I promise you zamu riketa as a sister kuma amana batare any stigmatisation or abu makamantan hakaba ko Fadila" gyadamata kai Fadila tayi tana share hawaye, Nabila tace "but inaso ka daukota da safe, ka kawota gidana ko Fadila, we call mai lalle da saloon agayara mata kai, da daddare saimu kaita dakinta, we have to make it special I think we should throw a party ko baby" ta tambayi Noor, kafin yabata amsa Sameer yadan yatsine fuska yace "No banson party, banson anything noise" tasowa Fadila tayi tazo wajen Yaya Sameer din tace "bamu kudi, we need to get kayan dazata sa ready gobe" Nabila najin haka ta taso itama tazo tace "yauwa kin tunamin yarinya ranan bikin ta bazata saka tsofaffin kayaba, Ya Sameer akwatinta fa" dariya Noor yayi yace "yauwa ku damai dan yayanmu zai iya ya share komi babu ruwanshi" yanda sukamai chaa aka yasa yadau wallet dinshi yabude yaciro Atm card yamika musu yace "gashi, pin 5474" ihu duk akayi cikeda murna Noor yace "ehen let's cut cake and feed yayan mu is his birthday" yanda sukamai hayaniya a office yasa yace "wai ya akayi aka barku kuka shigo Barrack dinan?" da sauri Mu'az yace "cha musu mukayi we are lieutenant Sameer Simran Sameer family and today is your birthday we are giving you a small surprise" girgixa kai yayi suka shigo gutsuro cake suna bashi har yasamu da magrib ya tarkatasu suka tafi.








Washe gari!
Daren jiya bakaramin fada Mummy da Abba sukayi ba, tun yana ganin abin nata shirme harsaida yace mata waito me danna auramata Sameer me eh, shima yamata kacha kacha ganin ya shareta hakan kuma zaifi jawo mata olla dan tanason jin information daga gareshi yasa tasameshi safiyar yau tabashi hakuri sanan ta tambayeshi ya ake ciki yanzu, yace mata kampanin interior sungama saka mata kaya duk wani kayan bukata data sani tundaga kan kitchen dining labulalye da sauran su sun saka, dama quotation din dasuka min nakomi was 11.9m, nabasu 8m, to inaso anjima zan basu sauran kudin, Sameer yacemin zaije Rehab Centre yadauko ta da daddare zanje gidan nafadi mata dakaina na aurar da ita" da sauri Mummy tace "zamuje tare nai kewan yarinya na" dan shiru yayi kafin yace "no tafiyan namiji daban naku na mata daban, idan uba yatashi zaije gidan yarshi shi kadai yake zuwa" shiru Mummy tayi kafin ta gyadamai kai tace "shikenan gobe ni naje naduba gida idan da gyare gyare nayi" kudi Abba yaciro dayawa yabama Mummy gashi kimata siyayya sanan yafito tareda kwallama Siddiqa kira tafito yace "yauwa kije dakin Rahima ki tattara yan kayanta zan kawo miki babban trolley na, da school books dinta kihada komi kikai motana, make sure u pack anything dakikasan tanaso fa" da sauri Siddiqa tace "to Abba" ta shiga dakin shikuma Abba yashiga dakinshi yafito dawani babban jakan Lv yashiga dakin yabama Siddiqa tahau aiki, ganin batasauri yasa yashiga tayani gwanin ban sha'awa Abba is just so happy, jiya harda sallan dare dan gani yake Allah gata yamai daya bama yarshi dake shaye shaye kamilin namiji irin Sameer.
***






Wuraren 11 na safe yay parking motarshi agaban rehab din batare da security sun bari yay parking acikiba ya leko yace "Sir sorry, we are celebrating 20yrs anniversary yau saisa kowa anan yake parking you can come in sir" kashe motar yayi yafito Mu'az dake taredashi shima yafito yana sanye da kananun kaya, shikuma Sameer na sanye da uniform yay wani irin asirtaccen kyau ko mesa oho, sai kamshi yakeyi, rufe motar yayi suka shiga ciki shida Mu'az dake biyada shi, compound din yagani an gyara anyi decorating da balloons black and golden, ga tables da chairs da aka zuba awajen all patient dinsu maza da mata zazzaune suna shan drinks wasu nacin abinci wasu kuma nacin snacks gawani soft music natashi, all the patients looks very happy sai hira ake, dan the only thing dake joining maza da matansu is sport randa za'ai sport other than that kuma babu saiyau da aka fitoda kowa sabida 20yrs anniversary da Hope Rehabilitation centre ke celebrating, ahankali yake tafiya yana kallon koina kaman eyes dinshi is searching for someone, chak ya tsayar da tafiyan dayakeyi hango Rahima dayayi dake zaune itada wani fair guy da naman idanunshi kenan so black tsabagen shaye shaye, tana sanye da uniform dinta na rehab saidai kanta babu kodan hulan nan data saba sawa kuma anbata taki sawane sabida an mata tsifa an wanke mata kan dama ance mata yau za'a kawo mai kitso tamata, an mata parking gashin aka bata wani pink ribbon takama gashin dashi tasaki jelan gashin dayakai har tsakiyan bayanta bakin dukya kanannade abinku da coily hair, bakaramin kyau tayiba sabida gashin mutane dayawa maza da mata anata mata magana sabida yanda tai kyau tai kaman wata little angel irin yaran yan gayun nan, tai mugun kyau, damasu biyune kadai a table dinsu tana rikeda cocktails a cup da straw keciki tana zuka shikuma yagama cin rice yana goge baki yana kallonta dan yarinyar ta masifan burgeshi kaman yasace ta yakeji yasakin mata murmushi yace "finally yau munsami normal food munci, amma kullum aita bama mutum abincin magani ewwww" yatabe baki, kyalkyacewa da dariya tayi ya mugun bata dariya dudda batasan guy dinba ita kadai ke zaune yazo yasame ta yazauna ya ijiye abincin shi yana shi yahau mata surutu.






Wani irin abu Sameer yaji yadaki kirjinshi ganin yanda take hirada wani daketa kallonta kaman zai hadiye ta kanta ba hula iska na kada gashinta, ahankali yashiga dunkule hannu kirjinshi namai wani irin zafi.
58.


Agurguje

Da sauri Mu'az yakama hannunshi yarike gam yana kallon inda Sameer din ke kallo yace "Yayan mu itace Rahiman?" gyadamai kai Sameer yayi ahankali batare dayabar kallonsu ba, baki Mu'az yasaki yana kallonta baisan lokacin dayace "wow! My Godddd! She is so beautiful wlh" wani haushine Sameer yaji yatasomai da sauri yajuya yay cikin office din Dr dan inyaje wajen zai iya abinda he might regret yashiga yamai bayani zaidau Rahima zasu dinga dawowa as an out patient, gyadamai kai Dr yayi sanan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login