Showing 30001 words to 33000 words out of 190952 words
Chapter 11 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
mugun kukan nan, ahankali cikin kuka tone tace "In..i.....ina police station ankamani dazu, please come and get me Mama, am so scared, please come and get me kinji" tafashe dawani irin kuka mai tsuma zuciya, katse wayar akayi batare da ance komiba hakan yasa ta kifa kanta abangon bayin tafashe da kuka sosai, tai kuka na kusan minti biyar sanan tadago kanta tasake dialing number, ringing daya wayar tayi akai picking call din kafin ma tai magana muryan wata mata tarigata tace "I told you time without numbers karki kara kirana in your life, I don't have anything to do with you, an kamaki a police station what is my business with that? Mahaifinki judge ne so call him up not me, banda alaka dake or anything yarinya, stop calling me Mama mamaki kin barota achan gidan ubanki, in danta ninema rot a police station din ko agefen yatsana stupid girl, mtsww" ta katse wayan tareda jamata dogon tsaki, wani irin kuka tafashe dashi she is feeling kaman ta shake kanta ta mutu why did she even call this woman? takai almost 10min tana kuka kafin tadago kanta ranta yay mugun baci, cikin fushi tasake dailing number matar ringing daya aka dauka kafin matar tai magana tarigata tace "you know what calling you was the biggest mistake danayi sama da mistake din dayasa aka kamani aka kawoni nanma, how can I think a wicked woman like you can help me? Your heart is so black and dark da baisan menene help ba in this life, I hate you nima, I hate you with every single heart beat dina, My Mummy is better than you sau miliyan she can't never ever stand and watch me in pain, she is the best Mummy in the world, best Mummy, the absolute best, and I love her, I love her with all my heart, I can ever rot here saidai in Mummy na bata duniya, inhar nakara sa wanan hannun nawa nakiraki ba sunana Rahima ba, trust me inda ace Allah na laifi dazan iya cewa laifin dayayi shine yabama a wicked woman like you ciki harta haihu you deserve to be a barren cus you don't have soul saidai Allah baya laifi, I hate u, I hate......." katse wayan da akayi dip yasa tazare wayan daga kunnenta ta wurgar da wayan a kasan bayin ta shiga rera kuka tana kiran Mummy, she is so sad, she is so so sad, how can she even think if calling this woman mema yakaita eh? Mema yakaita, buga kofan bayin datake ciki taji anyi. "open the door"
💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
1️⃣8️⃣
Muryan mace taji, azabure ta tashi tsaye ta shiga kalle kalle bayin tana neman inda zatabi ta gudu, dan karamin window dake wurin babub abinda zai mata dudda rashin kibanta bazata iya wucewa tawajen ba hakan yasa ta tsaya tana kallon kofan tana share hawaye batare data bude kofan ba, cikin tsawan matar tace "I said open the door Lady, da uban wa kike waya abayi haa, and maiya kawoki bangaren maza, open the door!" aka mugun daka mata tsawa da yasa ta matso kusada kofan tasa hannunta kan sakatan tabude, turo kofan officer tayi batai wata wataba ta dauke ta da mari tass! Rike kuncinta tayi tana dafa bango, tsugunnawa officer tayi tadau wayar data yar akasa tasa hannunta agaban riganta tawani irin finciketa tajata tareda bude bayi suka fita, suka fito main waje daidai lokacin Sameer ya shigo wajen shida wani dake rike da byro da wani paper dayake nunamai.
Ganin yanda ake kallonta yasa ta hadiye kukan datake yi ta dage ta ture hannun officer data kama mata gaban riga tace "dalla malama kidena jana tunda ni ba akuya bace muguwa kawai" da hannu officer ta nuna kanta tace "ni kike cema muguwa?" hararanta tayi da idanunta dasukai jajir suka kumbura tsabagen kuka tace "eh ance muguwa azzaluma m....." tass! Officer ta dauke ta da mari saida Sameer dake duba list yadago kanshi ya kallesu, fashewa da kuka sosai Rahima tayi tana shafa inda ta mareta tace "ance muguwa azzaluma, uban mena miki zakiyi ta marina kina jana, what have I done, banza kawai wacce tai kwantai ba miji" wani dan gajeren murmushi Sameer yasaki da gefen baki, ya maida kanshi kan list din da aka bashi yana dubawa zagin ya mugun bashi dariya ne tayaya akai tagane tai kwantai batai aureba, ohhh this Indomie generation children are damn hilarious.
Cikin fushi matar ta waiga ta kalli all the staff dake aikinsu abinsu dan irin wanan fadanne tsakanin yan shaye shaye dasu sun saba gani is not a new thing, hannu tasa tadau kulkin dake kan desk din Kusada su tace "zanci ubanki ne yau" cikin tsiwa tana kuka tace "ubana yafi karfin kicishi wlh, a inda ubana zai ubanki bai isa ya tsayaba saidai yazo bara" bugamata kulkin officer tayi a kafada hakan yasa tafasa wani wawan ihu da saida kunen kowa ya amsa, sake dago kai Sameer yayi ya kallesu ganin haka yasa officer dake nunamishi list din yajuyo yace "officer!" batare data kalleshi ba tace "officer I caught this gurl tana waya abayi shine on top of that takemin rashin kunya tana zagina, tana....." juyowa officer tayi zatai magana chairman yabude kofar office dinshi yafito yana kokarin sanya glasses dinshi a ido yace "Laraba enough! Lieutenant come with me please, officer give him the list" bama Sameer list din officer yayi yakarba yataho yawuce ta gabansu batare dayama kallesu ba yay upstairs, bude office din chairman yayi ya shiga, zama yayi akan kujeran da chairman ke nunamai yabashi hannu gaisawa sukayi, cikin harshen hausa Chairman yace "welldone Sameer am proud of you wlh, kasan mesa nakira ka, acikin yaran nan akwai mutum daya da I really don't know what to do about, am a leader you know Sameer and I don't want to be bias during the course of my work, bansan mezanyi ba I had to call you, kanada hankali sosai duk girman mutum sometimes idan zakadau hukunci dolene ka nemi shawara koda wajen dan cikin kane" yadanyi shiru kafin yamikama Sameer din hannu yace "kawo list dinan kaga" mikamai list din Sameer yayi ya karba yace "sunan yaran nan ne dakuka kamo, wanan yarinyar da officer ke bugunta yanzun nan she is the daughter of Chief judge of the federal High Court na nan Abuja, Rahima Sambo Rikadawa, da farko danaga sunan I was like maybe is just a random person dat happens tanada surname na judge din garin nan, saida na kira wani friend dina lawyer danasan yasan Chief Judge sosai and asked him about yaran Chief judge nawa yacemin four and call the names for me which wanan yarinyar dakake gani happens to be his last born, kana hango abinda nake hangowa Lieutenant?" ya tambayi Sameer daya natsu yana kallonshi gyadamai kai Sameer yace "a Chief Judge is someone that is very vulnerable, mutum ne da kusan idanun kowa na kanshi, aikinshi aikine dakesa kai makiya dayawa sanan kai masoya dayawa abin kanzama kaman 50-50, ko 60-80, cikin makiyan harda nakusa dashi wanda kawai neman abinda za'ai amfani dashine atunkudeshi wani ya gaje kujeran shi na Chief judge din babban birnin tarayya, inhar press zasu samu koda gutsuren information ne kan yarshi na shaye shayen illicit drugs abin can cost him alot to the extend da zai iya tarnishing image nashi and his reputation a society mu, bayan haka, yanadaga cikin mutane masu yankewa drug dealers hukunci yau ga yarinyar shi na drugs" dan ajiyan zuciya Sameer ya sauke ya gyara zama tareda ijiye hannayenshi akan table yace "me kakeso daga gareni Chairman?" ajiyan zuciya Chairman ya sauke yace "bakaga nasa akai yarinyar dinning ba, all the staff anan babu wanda yasan abinda nasani, I want to isolate the girl from the rest of the gang sainai contacting mahaifinta yazo dakanshi ya dauke ta kaita rehab yarage nashi, mun bashi itane yanzu dan kare shi dakuma aikinshi daga bakin Al umma amma in muka kara kama yarshi akaro nabiyu ni I will release d information nabar press suzo su gudanar musu da interview kafin atattarasu akaisu government rehabilitation centre koya kagani?" gyadamai kai Sameer yayi yace "sauran yaran fa?" cikin dan damuwa kadan Chairman yace "what do you think Lieutenant?" dan shiru yayi kaman mai tunani yace "they have to go for rehabilitation, rayuwan su zai taimaka, Nigeria muna so muyi eradicating shaye shaye idan aka samu yara kusan talatin suka dena shaye shaye cigaba da Nigeria ne sosai, yayinda idan ka barsu baka kaisu ba ka kaddara mutane talatin dinan zasuje su koyama wasu mutane talatin din shaye shayen ne, kaga rate of shaye shaye yasake increasing kenan" gyadamai kai Chairman yayi yana yaba fikran Sameer yace "hakane, za'a kaisu, bari na nemi mahaifin nata abokina yabani contact dinshi dazan iya samun shi" gyadamai kai Sameer yayi, dialing number Abba chairman yayi harta gama ringing ba'a dauka ba, hakan yasa yacigaba da kirashi har sau biyar ba'a dagaba, knocking kofar akayi hakan yasa ya ijiye wayan yabada izinin shigowa, wanan officer data daddaki Rahima ne ta shigo rike da wayan Rahima dake ringing tace "Sir wayan yarinyar chan ne her Mother has been calling, I want to ask for your permission idan na amsa na sanar da ita mun kama yarta kokuma na kashe wayan" hannu chairman ya mikamata alamun tabashi wayan hakan yasa ta mikamai ta juya tafita, sake daukan ruri wayan ta shiga yi ganin Best Mum akan screen yasa Chairman yay pikin tareda sawa a speaker kafin yay magana Mummy tariga shi. "Autana where are you, sorry dakika kira ina kitchen dasu Siddiqa, wai har yanzu baku gama birthday party bane da Chris I think I asked you to come back kafin 6 gashi yanzu ana kiran magrib......." dan gyaran murya Chairman yayi yace "this is Alhaji Muhammad Mustapha Abdullahi the Chairman of National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) in Nigeria, please madam is your husband there I will like to speak to him" sosai gaban Mummy yafadi hakan yasa tace "innalillahi Malam please ina y'ata take? Ina Rahima na? Ina Autana? Yarinyar dataje birthday maiya badaku da ita kuma?" yanda duk take maganan a hargitse yasa yace "calm down madam, I asked is your husband there I want to speak to him" arude tace "no, no, bayanan yay tafiya yace port Harcourt this morning, please ina y'ata? Me takeyi awurin ku?" shiru Chairman yayi yana sauraron yanda Mummy tarude ahankali yace "I am sorry to announce this sad incident like this Madam, but your daughter Miss Rahima Sambo Rikadawa has been caught taking Illicit drugs, Codeine, Crack, Tramadol, Weed, and shisha, she has been detained here according to the constitutional law, after some inevitable steps da we must carried out akanta, we are going to hand her over to rehabilitation centre inda zatai spending period of 6 months, thank you Madam for your time and do have a wonderful night rest" ya katse wayan tareda kashe wayan gabaki dai ya ajiye kan table Tareda danjan tsaki yace "mahaifinta yay tafiya Yaya kenan? Kaga tashi muje muyi salla" tashi sukayi suka fito daga office din suka sauka kasa inda suka tarar su Chris duk nacin abinci anbasu abinci a takeaway faran shinkafa da stew da dafaffen kwai, duk sunyi zuru zuru sunaci kaman ance in basuci ba za'a kashe sune.
Magrib sukayi suka fito daga masallaci suka shigo cikin premises dinsuna dan tattaunawa, reception suka shiga wata mata suka hango sanye dawani bakin dogon riga dayaji stones tayafa wani mayafi milk color na manyan mata akai tarike wani handbag na LV tana magana da receptionist din wurin tana fada tace "ina kuka kaimin y'ata where is Rahima? Kubani y'ata natafi da ita shairi ake mata Rahima batashan komi saidai in wanchan yaron Chris shine ya koyamata taga yanasha ta dandana dan dama shiyay inviting nata to birthday party shi" cikin masifa Chris yace "No dey lie Madam, your daughter sabi everything so tey she dey carry for bag go school, no dey lie for my head ha'a see me see gbese o" cikin fushi Mummy ta juya zatai magana taga wani magidancin mutum tareda wani cikakken dogon bakin yaro dake sanye da jacket baki dabai ja zip dinba, rigan dayasaka mai ruwan toka ya bayana da kirjinshi hartana hango kwantaccen gashin kirjinshi baki sidik, dan girgiza kanta tayi ta saita idanunta kan Chairman kafin ta kalli wasu manyan hotunan frame dake jikin bangon reception din na president, da vice president saikuma hoton shi da aka rubuta chairman NDLEA, cikeda masifa tace "good ka iso Chairman, I guess you are the one I spoke to a while ago, ina y'ata take? Kubani y'ata natafi gida, shairi kuke mata Rahima babu abinda tasani, she is my last born, yaushe na haifeta duka duka da zaku kamomini yarinya daga taje birthday coursemate dinta kucemin shaye shaye take? How on earth is this possible?" anatse Chairman yace "Madam until your daughter's father is back and come here dakanshi I'm not releasing Rahima nor giving her to you" yana maganan yay hanyar office dinshi binshi Mummy tazo zatayi security suka tareta hakan yasa ta tsaya daga wurin, ganin bala'inta bazai yi komiba burinta shine tasamu su saki Rahima su koma gida asirinsu arufe batare da Abban su yasani ba amma taga ina wayan nan basuda mutunci hakan yasa ta shiga rokon security su barta taje taga Chairman sukaki.
Shiga office din sukayi daidai wayar chairman yahau ruri karasawa table din yayi yadau wayan ganin Mahaifin Rahima ne yasa yay picking yasa a kunne ya nemi waje ya zauna yace "good evening to you Sir, this is Alhaji Muhammad Mustapha Abdullahi Chairman din NDLEA, I've been calling you na sanar dakai wani muhimmin abu, mun kama yarka awani gida nan hanyar Kaduna kano express road ita da wasu yara maza da mata su talatin da daya da sunan birthday party tana shaye shayen miyagun kwayoyi da gwamnati tabada umarni duk randa muka gani yanayi mu kamashi sanan mu aika dashi rehabilitation centre, ganowa damukayi Rahima yarka ce mukuma dan matsayin ka akasar nan munkuma san yanayin matsaloli da fitintinu dazaka fuskanta in duniya tasan me ake ciki yasa mukace bari mu maka alfarman kiranka mu sanar dakai shima badan komi ba saidan labari dakuma yanda ake yabata akan aiki bisa gaskiya dakake yi ne" shiru Abba yayi na kusan minti takwas tunani yake Rahima shaye shaye, party da maza ahanyar wajen gari, shaye shaye, innalillahi wa innailaihi raji'un, Chairman ne jin shiru yasa yace "kana jina" ahankali cikin murya datai rauni sosai Abba yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un" saida yafada sau uku yasake yin shiru yama rasa maizaice, Murya chan kasa data nuna karara alamun bacin rai da tsantsan damuwa yace "Chairman banda abinda zan cemaka sai Allah nasaka da alkhairi, wlh bazan maka karyaba wutan kaina ta dauke dib I don't know wat to think, alfarma daya zakamin kawai yanzu zan kira mahaifiyar ta tazo ta dauke ta sutafi gida, first flight zan biyo nadawo garin nan gobe dasafe zanzo har office dinka nasameka zamuyi magana da kyau, nakumayi alkawari binciken case dinan da kyau nagode" ahankali Chairman yace "mahaifiyar yarinyar is already here badai mubata yarinyar bane daman munce dole sai munyi magana dakaine, yanzu kuma tunda munyi zamu sa abata ita sutafi gida" ajiyan zuciya Abba yasauke yama kasa magana hakan yasa Chairman ya katse kiran yana girgiza kai yace "rayuwa kenan saikaga a good man ya haifi boka, jarabawan Allah kanzo tako ina, please Lieutenant help me tell them sukaima matar yarinyar nan sutafi gida" tashi Sameer yayi yafita daga dakin ganin babu kowa a upstairs din yasa yay dining din dayake anan sama dama dining din yake yasaba zuwa NDLEA din so ba bakonshi bane babu inda baya shiga saidai in baisoba, bude kofan dining dinyayi tana zaune kan kujera ta kifa kanta kan table tana kuka ga takeaway din rice da stew dinta agefe ko kallonshi batayi ba, hannayenshi yazuba a aljihun wandonshi yay wani irin tsayuwa irin na sojojin nan yace "Ke!" da kakkausar muryan shi da sauri ta dago kanta gabanta na faduwa sabida yanda ya kirata, dauke kai tayi daga kallonshi ganin wanan mugun bakin sojan nanne daya mata wankan ruwa dazu. "zoki fita ur Mum is waiting at the reception" dawani irin mugun sauri ta juyo tareda ware jajayen kumburarrun idanunta tace "Mummy na kace?" shiru yayi bai amsata ba sai zubamata manyan idanunshi masusa mutane shakkan shi dayayi yana kallonta, dawani irin sauri ta tashi gabanta nafaduwa ta taho tana dingishi tabi ta gefenshi tafita da sauri tai hanyar stairs, ahankali yajuya yafito shima ya tsaya a daidai bakin benen har lokacin hannayenshi na cikin aljihun wandonshi yana kallon yanda take tafiya tana dingishi da sauri tana sauka, saida tagama sauka daga benen sanan tafashe da kuka sosai tana yarfe hannu kafin ta kwalama Mummy data juyama stairs din baya tana waya kira. "Mummy!!!" da sauri Mummy dake waya tajuyo ganin Rahima ga bandeji a goshi tabi tai daka daka kaman ba yarinyar data bar gida fess fess ba yasa ta zare wayan daga kunnenta tana kallonta, dawani irin gudu Rahima ta taho tana dingishi takarasa tawani fada jikin Mummy tareda fashewa da kuka sosai mai tsuma zuciya, bayanta Mummy ta shiga shafawa tace "ya isa, ya isa, am here now stop crying" dagota tayi tasa hannu tana sharemata hawaye tareda shashafa goshinta inda taga bandeji tace "maiya sameki anan maisa kike dingishi" cikin kuka tanuna Chris ashagwabe tace "wanchan matsiyacin ne Mummy mai