Showing 18001 words to 21000 words out of 190952 words
Chapter 7 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
yay awon gaba da ita hakan yasa Mummy ta kwantar da ita tareda tashi ahankali tawuce bayi inda tabata ta gyara sanan tai wanka tafito tana kallon Rahima datai dai dai agado tana tikan baccin ta, shiryawa tayi cikin kayan bacci tawuce tafice daga dakin tai dakin Abban su dudda yana study but inya dawo zai samsta anan dan batason anything dazaisa yaje dakinta.
Around 5:02 ta tashi jin muryan Abba na kiranta, a firgice ta bude idanunta dasukai jajir dan kowani gaban jikinta najin kiran Abba ta kallai tanadan sassauke kai, babu alamun wasa kan fuskarshi yanuna mata kofa yace "wuce kije ki dauro alwala kiyi salla" gyadamai kai tayi ta tashi ahankali dan jiri take gani sosai bacci bai isheta ba, ganin tayi hanyar bayi yasa yajuya yafita dan sauri yake antada salla, bayin ta shiga ta wanko fuskarta tadauro alwala tafito tana kallon ko ina na dakin tadanji dama dama dan jirin yaragu sabida wanke fuskar datayi, wurin wardrobe din Mummy tayi tana kallon kofa da sauri tabude wardrobe din, hannunta tamika ganin hannunta baikai safe din dake chan sama ba yasa da tai wajen mirror, kujeran wajen ta dauko tahau kai ta tsaya hakan yasa takai safe din, password din da taga Mummy tasa jiya ta shiga sawa dan tana gani ta haddace shi tsaf akanta, bude safe din tayi jikinta har rawa yake, one bottle of codeine ta dauko gudun kar Mummy tagane sanan tasauko kara daya na wiwi tana waigen kofa, gyara zamansu tayi tsaf gudun kar mummy tagane sanan ta maida safe din tarufe tasauko tadau kujeran ta maida inda yake gaban madubi, sanan tadawo tarufe wardrobe din taboye abubuwan a jikin towel dinta sanan tabude kofa tafita tai dakinta, da sauri ta maida kofar tarufe jakar makarantan ta ta dauka ta zuba su aciki sanan ta rufe ta ijiye tana murmushi har wani murna takeyi kafin tai bayin ta, brush tayi sanan tai wanka tafito daure da towel, mai tadauka tafara shafawa saida tagama tsaf sanan tasake fadawa kan gado taja bargo ta lumshe ido ko minti biyu ba'ayiba bacci yasake awon gaba da ita.
Cikin bacci taji ana shafa mata fuska bude ido tayi da kyar tana turo baki ganin Mummy ne yasa ta mirgino ta daura kanta kan cinyar Mummy cikin muryan bacci tace "Mummmmm niban tashi ba" dagata Mummy tayi tace "tashi kafin Abban ki yakara tambayan ki, kinyi salla?" girgiza ma Mummy kai tayi ashagwabe, hakan yasa Mummy tace "toki barshi basai kinyiba, tashi ki shirya school, kinga yau zaku riga baban ku fita saisa naciro miki wanan abayan da gyalenshi ki saka banso kisa jean baban ku yahau miki fada" saukowa daga gadon tai da sauri tadau doguwan rigan da Mummy ke nunamata data ijiye kan kujeran mirror ta warware doguwan rigan tana daure fuska, hadadden doguwan rigane mai bala'in kyau na Dubai bakine complete babu kwalliya ajikinshi sai hannun doguwan rigan da aka bishi da wasu silver kullatai da akai musu design din flowers yay mugun kyau rigan. Cikeda rigima sosai ta kalli Mummy tace "Mummy nine zan sa kayan nan? Ni wlh bazan saba so ake zafi yakasheni eh" cikeda lallabawa Mummy tace "haba Auta na, Ke kinfiso ayita miki fada na yaune kawai gobe baban ki zaiyi tafiya yabar mana gida zakiyi yanda kikaga dama kinji" wurga rigan tayi chan wajen kofa tace "wlh ni banaso ni english wears zansa" dafakai Mummy tayi ta kalleta yanda ta zauna akan kujera ta juyamata baya tana kumbure kumbure, tasowa Mummy tayi takaraso har gaban madubin ta bayanta ta tsaya ta dafa kafadarta tana kallon fuskarta ta madubi tace "haba my fine princess, Princess Rahima na, yar lelen mamanta, duk gidan nan babu wanda zai nunamiki kyau wlh kai duk Abuja ma, beauty yar gidan Judge, yarinya inba dandan president ba sai rijiya adanmini murmushin nan mana" Mummy tadan chakuleta hakan yasa tafashe da dariya, ganin tafara dariya yasa Mummy tadauko rigan tace "imaza shiryo kici gayu kifito ina jiranki kizo kiyi breakfast kinji" gyadama Mummy kai tayi Mummy tawuce tafita.
Shiryawa tayi cikin dogon rigan tadau gyalen ta yane kanta dashi tadau wayarta tajefa cikin jakanta sanan ta giya jakan tabude kofa tafito tai falo, zaune taga duka yan gidan nasu a dinning, tunda tafito Abba ya tsareta da idanunshi dake cikin fararen glasses hakan yasa takaraso ahankali tayi kusada Mummy, da hannunta shiga wasa kafin murya chan kasa tace "ina kwana Abba" tea Abba yakai baki ba yabo ba fallasa yace "lpy" juyawa tayi ta kalli su Siddiqa da suma duk sun shirya zuwa makaranta dan hararan su tayi ta gefen ido sanan tace "ina kwanan ku" Siddiqa ce kadai ta amsa dan sauran basuda lokacin dan iskan gaisuwanta. "kin tashi lpy Rahima" ko amsawa batayiba tazauna kusada Mummy suka faracin abinci, tea kawai ta iya tasha dan ko kadan bata iyacin abinci inba Mummy ta samata abinda tasaba samata ba, batajin dadin cin normal abinci saida suka gama tsaf sanan suka tashi, 5k Abba yaciro daga pocket yamikama Siddiqa yace "gashi nan dukanku, adawo lpy" sanan ya kalli Rahima da nugayen ido yace "kibari akawomin karanki kiga abinda zai faru yau, kuwuce kutafi" wucewa sukayi suka fita, gaba Rahima tayi fuu tabarsu tana zuwa tabude gaba ta shige ta rufo kofar da karfi, da sauri Luba tace "iyye Ya Siddiqa bakene ke zama agaba ba, bari naje nafadama Abba" hannunta Siddiqa tarike da sauri tace "kubarta, muje inada hot presentation this morning, banda lokacin Rahima yanzu" duk shiga bayan motan sukayi direba ya shiga yajasu har zuwa University of Abuja, Siddiqa yafara saukewa agaban department dinta na Accounting tana 400 level, dubu dai dai tabama Zeena da Luba, duk suka mata godiya sanan tajuya tagaba tabama Rahima nata 1k din ta hanyar ajiye mata akan jiki, cikeda tsiwa Rahima tadau kudin ta jefar ta window tace "mezanyi da kazamin kudin ku? Mummy na tabani ☓2 of your chicken change, 10k dan haka banso" cikin tsananin fushi Siddiqa ta kalli kudin data jefo mata akasa tace "ni kika jefa da kudi Rahima?" "baki fasamata baki bane saisa har yanzu take mana iskanci" cewan Luba, ganin abin na neman zama rigima yasa Idris direba yace "dan Allah ayahakuri, bakuyi fada agida bane zakuzo kuyi a makaranta gashi anata kallonmu, kinga Siddiqa wuce ajinku kiyakuri yarinya ce" cikeda tsiwa Rahima tace "wlh ka kara cemin yarinya saina katsama mari hala nama kala da yarinya" bude marfin gaban motan Siddiqa tayi ta fincikota waje ta bala'in tsorata hannu tadaga zata wanketa da mari da sauri tarufe fuskarta tafashe da kuka jikinta na rawa tace "wlh kika dekeni saina gayaki da Mummy" sakinta Siddiqa tayi ta matsar da ita gefe ganin duk yanda ta tsorata sanan ta kalli direban tace "kaisu Lubabatu department katafi tajama kanta da kafarta zata taka tundaga nan har Vet wlh" tai maganan tana rufe marfin motan, direba yaja yay gaba, buga kafa ta shiga yi akasa tana kuka sosai Siddiqa tai tsaki tace "sai girma ba hankali, katuwa dake kina kuka cikin makaranta gashinan sai kallonki ake, ki kwana anan" juyawa tayi tai tafiyanta cikin department dinsu tabarta awajen sai kallonta ake.
Sauke jakanta tayi daga baya tana kuka tabude ta ciro wayarta ko tsayawa rufe jakarma batayiba tarike adayan hannun ta shiga neman layin Mummy, horn taji an danna mata da sauri ta daga kanta da idanunwanta dasuka rine da hawaye, kallo daya tamishi ta dauke kai wani shegen yaron ajinsune Chriss sunanshi Christian ne dayasamata ido, ajinsu daya shima Veterinary medicine yakeyi, duk inya ganta saiyace Hi beautiful amma ko kulashi batayi, fitowa yay daga motan da sauri hadadden guy ne yaci gayu sosai da wandonshi dayay ass down gawani hadadden sneakers akafarshi da katon sarkan cross yakaraso gabanta, cikeda damuwa yace "Hey Beautiful what happen? Why are you crying like this? Who was that Goddamn gurl that drag you out of the car?" yay maganan cikin fushi, daure fuska tayi tasa hannu tana share hawayen daya gama wanke mata fuska, cikin bala'i tace "is none of your business, leave me alone" "noo I can't, I can't leave you alone, u don't look good beautiful, let's go we have class by 9, and is to 9 now" kallonshi tayi da dara daran eyes dinshi, murmushi yamata yadan daga mata gira daya tareda cije lips dinshi yace "please beautiful let's go, I know u can't walk from here to our department, so let's go okay, plsss her majesty, plssss " yawani ja please din, dauke kai tace "okay" murmushi yayi cikeda jin dadi yana bala'in son Rahima tun rana na farko data fara attending lectures, batama uban kowa magana a ajin dudda yanda kowa yake shigemata gashi sai mahaukacin kokari da inba kaga tana amsa tambaya ba baxaka taba cewa tanada kokarin ba. Hannu yamika yace "lemme help you with the bag beautiful" murmushi tadanyi dan haka takeso ana treating dinta kaman sarauniya ta mikamai karba yayi da sauri yataho yabude mata shiga tayi sanan yarufe yazagaya ya shige shima yatada motar.
💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
1️⃣2️⃣ & 1️⃣3️⃣
Shiga cikin motar yayi ya rufo kofar sanan yadaura jakan nata akan jikinshi ya tada motar yaja ahankali, baya wani gudu dan baiso sukai department dinsu dawuri, soyake yadanyi hira da ita yanda yaci sa'a takula shi yau dinan, dan satan kallonta yayi sanan yace "who is she?" yadan kalleta itama kallanshi tayi wani iri yaji sabida yanda dara daran idanunta suka sauka akanshi da sauri ya kalli hanya yace "I mean who was that girl that made you cry?" daure fuska tayi cikin dan fushi tace "my sis, elder sis" dan yatsine fuska yayi cikin isa yace "tell her Chris yace today should be the last day dazata saki kuka haka inba hakaba saina rama miki" wani irin murmushi tasakinmai ta mugun ji dadin yanda yay maganan, kallonta yayi ganin tana murmushi yasa shima yay murmushi baisake cemata komi har sukakai department dinsu na Vet, tun kafin yayi parking suka hango lecturer ya shiga ajinsu kuma ka'ida ba'a barinsu shiga in lecturer ya shiga, dan ajiyan zuciya yasauke yace "wat a day! We are late" daure fuska tayi tamiko mai hannu tace "give me my bag I want to go, thanks for the ride" zare key yayi daga jikin motar ya kalleta yace "beautiful let's chat a bit now, lecturer yariga ya shiga please" harara ta watsamai cike da rashin kunya tasa hannu zatadau jakan da sauri ya fizge jakan hakan yasa bottle din codeine yafado kan kafarshi dan dama bata rufe jakarba bayan tadauko waya dazu, wani irin kwalalo ido tayi cikeda mugun tsoro ta kalli kafarshi kaman yanda shima yake kallon kafar kafin ahankali yamika hannu yadau kwalban dudda yasan codeine sosai danba bakonshi bane but yanaso yakara tantancewa shine yake gani bawai gizo idanuwanshi kemai ba, dago kai yayi zai mata magana takawo hannu zata fizge kwalban da sauri yadauka da hannunshi harda jakan yay sama hakan yasa karan wiwi shima ya fado kasa dagawa yayi tareda ajiye jakan agefe ya kalleta yanda yaga tai zuru zuru yasa yagane natane ita kesha bawani ba, ahankali yace "so you do drugs beautiful?" girgiza mai kai tayi ahankali muryan ta har rawa yake tace "n....no....banawa bane ba" fashewa yayi da dariya sosai harda rike ciki saikuma yadago kai yace "alright naji, lemme take them then" yashiga bude marfin zai kafa abaki kaman zatai kuka tace "karka shamin abuna wlh" sake kyalkyace wa da dariya yayi kafin yasauke ya kalleta yace "you don't have to lie to me am your friend and your secret is safe with me, besides codeine ai na yarane, will show you abubuwan dat will make you feel kaman kina heaven" dan kaiwa baki yayi yasha kadan sanan ya janye ya mika mata rufewa tayi ta fizge jakanta ta zuba ciki ta rufe, kallonta yake tayi shidai tana bala'in burgeshi ga shegen kyau kaman ita tai kanta, dago kai tayi ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta danyi murmushi tace "zantafi" murya chan kasa yace "before you go, how about I give you invite to my birthday is in two days Beautiful, you know I will feel honored if a beautiful girl like you will grace my occasion, please Beautiful" yay maganan yana ciro katin invite din daya hadu iya haduwa kallo daya zakama Chris din kagane shima iyayenshi nada dan kudi ba laifi, makemai kafada tayi tana kallon katin tace "once I live school bama fita again" da sauri yace "how about you attend the pre birthday party" da sauri tadan yatsine fuska tace "and when is that?" "tommorow 2pm, then ai muna school u can come and leave by 4 kitafi gida, and is just few people, please do dat for me My beautiful Friend kinji" shiru tayi tadan juya ido saikuma tace "okay I will think about it, to if I decide to go who is taking me to the place?" da sauri yace "give me your number Beautiful, I will enter school tomorrow just for you saimu tafi tare kinji her majesty" murmushi tayi yanda yake lallabata namata dadi tace "Tom" ta mikamai wayanta, karba yayi ya sassaka numbers dinshi yay saving da sunanshi sanan yabata, karba tayi tajuya tafita daga motan tanata waige waige harta sami kasan wani bishiya ta zauna, hango ta dayayi all alone yasa yafito yay wajen haka yadinga janta dahira harta saki jiki suka dinga hira yanata sata dariya cikinta har yana kullewa kaman dama chan sunsan juna daga wani wurin, kusan zaniya cewa Chris is the first friend datayi tunda ta shigo makarantar nan 100level 2months ago.
Karshe ma batai attending aji kodaya ba ranan motar Chris ta shiga yasauketa a unguwarsu tamai waving bye sai gobe sanan tawuce gida, sai murmushi take Chris is really funny and such a sweet guy yana treating dinta like a queen, duk duniyan nan banda Mummy that treat her like a queen shine second person that treat her like a queen tana zuwa xatabama Mummy labarin shi tayi friend a school yau.
***************
Washe gari.
Cikin full shiganshi na kayan sojojin shi ya shigo Barrack din da motarshi Bentley da plate number kana gani xakasan na sojane, parking yayi a inda aka tanada dan parking kafin yabude motar wasu sojoji da aikin su shine gadin wajen sukazo da sauri daya daga cikinsu yabude mai motar tareda saramai. "Sir!" ahankali yafito daga motar bakaramin kyau kakin sukamai ba, yafito cikin shi ganshi na sojoji, lips dinshi sunyi pink sosai kaman wanda ke mura, hannu yasa yazare bakin glasses din dake kan idanunshi sanan ya maida kofar yarufe yasa key a wando yajuya ya shiga building din, lift ya shiga dayakai shi 4th flour sanan ya shiga wani office da aka rubuta Lieutenant ajiki, shiga office din yayi yana kokarin zaro wayarshi dake aljihu data fara ringing, wayar yaciro ya kalla ganin Ummi ke kiranshi yasa yakarasa ya zauna kan hadadden kujeran shi sanan ya amsa wayan.
"Soja na ankai office lpy?" dan murmushi yayi da muryan shi mai natsuwa da dadi irin muryan full cikakken namijin nan yace "Ummi na, yes nakai inama cikin office yanzu haka, inaso nai some paper work ne yau, gobe ne zandanyi supervision na various post din mutane" cikeda jin dadi Ummi tace "Masha Allah karka manta katofa addu'a, Allah yakare ka daga shairin makiya, Baffan ku kana fita yana shigowa, yakawo ma rubutu wai kadinga sha" dan lumshe ido yayi irin na gajiya da zancen Baffan nan kafin yadan yatsine fuska yabude ido yace "okay" jin wani kira na shigowa wayanshi yasa yacire wayan daga kunnenshi ya kalli wayan ganin Mu'az ne yasa ya maida wayan kunnenshi yace "Ummi bye, Mu'az na kirana bari na amsa naji" "oh ba jiya jiyan nan yakoma school ba hope badai kudi yakeso ba, karka sake kabashi kudi Sameer kuna bata yaron nan da kudi dayawa jiya babu wanda bai bashi kudi agidan nanba harda Baffan ku" dan murmushi yayi yace "okay Ummi naji bye" "alright son bye" katse wayan yayi yana kokarin kiran Mu'az din kiranshi yakara shigowa hakan yasa ya amsa da wuri. "Mu'az" ya kirashi kai tsaye dan bai fiye wanan wasan ba, daga ta chan bangaren cikin dan dari dari wanda yadau wayan yace "Yaya Sameer Salisu ne, Uhnn Salisu abokin Mu'az na school ajinmu daya" dan shiru Sameer yayi dan Mu'az hardly bama wasu wayanshi meya faru yau abokinshi ya kirashi, kai tsaye yace "uhum Salisu" irin alamun yanajinshi, cikin tsoro tsoro da fargaba yace "Yaya Sameer Mu'az baida lpy, yanzu haka muna sick Bay tun jiya da daddare baisan inda kanshi yakeba, we tot he will feel better tun jiya saisa bamu kira kowaba but munga har yanzu ciwon kaman ma is getting worse ne" sosai yaji zuciyarshi tabuga dudda all his brothers he is not into them like that dan bayason raini ko kadan but yana sonsu sama da tunanin kowa barinma Mu'az da kusan shine ya raineshi dan lokacin Ummi was battling da rasuwan babansu which Mu'az was a year old daya rasu saisa yakeson yaron danshi yakemai komi a lokacin, natsuwa yayi dan part of training dinshi da akayi tun yana sabon soja shine dakewa and not to panic kodakan mutuwan iyayensu ne, su sojoji ne they're meant to protect lives not to sober, soja jarumi ne maikuma dakakkiyar zuciya, anatse yabashi tambaya kai tsaye. "meke damunshi?" cikin wani irin murya kaman Salisu zaiyi kuka yace "ciwon ciki ne, terribly ciwon ciki" shiru Sameer yayi yana sauraronshi. "juyi kawai yakeyi kaman ana zaremai rai yana kuka sosai shine naga yana yawan mana maganan ka kaine babban yayan su shine nafara kirana danna sanar dakai" ahankali yace "don't leave his side,