Showing 69001 words to 72000 words out of 190952 words
Chapter 24 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
wani irin tura Gate din tayi Gate din yay kara kaman za'a balla hakan yasa gateman yafito da sauri yace "waye anan?" ganin Rahima ne yasa yay gum dan yasan zata iyamai rashin mutunci, ahankali Rahima ke tafiya tana tangadi tana kallon ko ina kafin cikeda murna ta kwala wani uban ihu. "Mummmyyyyyyyyy naaaaaa!"
Gabaki dayansu suna zaune a dakin Abba suna hira dan yau Abba yaji sauki sosai, jin murya kaman na Rahima ta kwala ma Mummy kira yasa duk sukai shiru Abba yace "sainaji kaman an kirak....." "Mummmyyyyyyyyy naaaaaa" Rahima tasake kwalama Mummy kira tana juyawa da sauri Mummy da Abba suka tashi Mummy tace "kaman muryan Auta na, meya faru ba 6 month kacemin zatayi a rehab ba ko an sallamota ne?" tai maganan tana bude kofa Abba biye da ita da sauran yaran duk sun kosa suga Rahima ce da gaske, sake kwalama Mummy kira Rahima tayi tace "Mummmyyyyyyyyy" da sauri Mummy tabude kofan falo tafito tai turus ta tsaya ganin Rahima sanye da uniform din rehab dayay datti sosai barin ma kasan wandon dakejan kasa dukta tattake shi, babu hijabi ajikinta sai hula, Abba yabi ta gefen ta yafito tareda saukowa daga dakalin barandar yana kallon Rahima kaman amafarki, ganin Abba yasa Rahima tafashe da dariya cikeda maye tace "laaaaaaaa Abba kadawo kaman tsoho wlh" tai maganan tana karasawa gabanshi inda ya tsaya churr kirjinshi na bugawa hudu hudu, hannu tasa akan gemunshi da fura fura ya cika tace "tsoho ne kai, kudi, bani kudi Abba" tai maganan tana tura hannunta a aljihun gaban jallabiyarshi tana lumshe ido kaman wacce bacci ke shirin tafiya da ita, warin da Abba yaji kaman na giya kona menene daga bakinta da numfashinta yasa yadan kawad dakai saikuma yadago kai ya kalleta cikin wani irin yanayi kaman wanda zai fashe da kuka, cikin raunanniyar murya mai nuna tsantsan ciwo yace "Rahima ya akayi kika dawo gida?" kyalkyacewa da dariya tayi cikeda maye tace "uhmmmm gudowa mukayi dasu Shagali, nahau kan gini nai tsalle nafadi tippppp akasa hahahahahha" ta kwashe da dariya kafin ta kama hannun Abban tace "Abba fitsari nakeji wlh tiles din bayin nan yay kal kal yau ka wanke ne?" tai maganan tana sakin hannunshi tsugunnawa tayi agaban Abba batare data cire wando ba tasaki fitsari awurin tana wakan fitsari "siiiiiiiiiiiii, fitsari futu futu, Mama da Baba suna kallona yayyyy yafitooo, agayara agayara fitsari zai shiga gidan takalmin Abba" tai maganan tana bin fitsarin datasaki da kallo dake gangarawa zai shiga takalmin dake kafan Abban ta tana washe baki cikeda mugun murna, wani irin juyawa Abba yayi cikin tsan tsan fushin daya dade baiyi irinshi ba yay ciki da sauri Mummy tabishi abaya ganin a yanayin daya juya yashiga daki tace "Alhaji kaga mezakayi eh? Kaga bakada lpy bakadade da farfadowa ba, so calm down and relax nasan duk inda Sameer yake rehabilitation centre sun riga sun kirashi, kabari ya iso ya mayar da ita please mijina karkamata wani abu, dan Allah kaji Abban su" ko kallon Mummy baiyiba tsabagen bacin rai yafada dakin Rahima yay wurin wardrobe dinta yabude kaman zai karya kofofin, babban akwatinta nasama yaciro ya yar akasa tareda budewa Mummy tabude baki tana kallonshi tace "Alhaji me haka? Koranta zakayi daga gidanne? Ina zata? Watake dashi aduniyan nan banda mu?" wajen kayan sawanta Abba yabude yadinga jido uban kayan da baisan iya yawan su ba da kalansu ba ya watsa akan akwatin haka yadin ga kwasan kayanta duk wanda hannunshi yasauka kai saiya jawo ya wurga a akwatin har akwatin ya cika yamaida akwatin yarufe yaja trolley yafito ya shiga dakinshi, drawer shi yabude yaciro wrappers din yan dubu dubu guda biyar yadauko car key duk mummy nabiye dashi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Alhaji, Abban su Abban su please talk to me my hysband dan Allah kaji, koran Rahima zakayi ne?" fitowa falon yayi yanajan akwatin batare dayabi takan Mummy ba Mummy biye dashi sukayi hanyar fita daga falon inda su Siddiqa dake gaban daki suka tsaya suna kallon Rahima, Mummy ta kwalama Siddiqa arude tace "Siddiqa kuzo kuga abinda babbanku yayi, baban ku yahado kayan Rahima a akwatin koranta zaiyi? Ina yakeso taje? Hannunka baya rube ka yanke kayar, addu'a zamu mata, addu'a makamim mumina, ka dauka Rahima itace jarabtar wanan Family namu, and I assure you babu abinda ya gagari Allah, dan Allah mijina karka korata instead ka maidata gidan Rehabilitation din" wurin kofa Abba yayi batare da maganganun Mummy sun shiga kanshi ba, da sauri Siddiqa ta tare Abban su Zeenatu ma haka duk suna kuka dan basu taba ganin mahaifin su yay fushi hakaba, ahankali Siddiqa tace "Abba mekakeyi ne ina zaka kai Rahima? Eh talk to me Abba na" cikin wani irin Kunan rai ya kalli Siddiqa yace "tashi daga gabana" yanda yama Siddiqa maganan saida gabanta yafadi da sauri suka matsamai yay wurin motarshi yabude boot ya wurga jakan ciki sanan yarufe yakoma gaba yabude motar ya kunna dantai warming sanan yadawo inda Rahima take tsugunne tai fitsari tana wasa dashi yazo wajen hannunta yakama ya finciketa ta mike tsaye tace "leave me Abba, bacci nakeji" ko takanta baibiba yajata ya wurgata a bayan mota saida kanta yabuge yamaida kofan yarufe, yakoma gaba ya shiga yatada motar gateman yabude mai yafita batare daya lura da motan su Shagali dake gaban gidansu kadan ba, wani irin fanfala uban gudu yake akan titi, ikon Allah ne kawai ke tafiya dashi saida yawuce zuba tawajejen hanyar Suleja ya tsaya awani babban farm house dinshi ya kashe motar ya fito ya shiga Rahima na cikin motar tana yaren da baiji, shiga cikin gidan yayi babban gidan gona ne dake daukeda bishiyoyi kala kala, ana kewan kifi da kaji masu kyau ciki, daga Gate ya tsaya ya shiga kwalama wani mutumi dake cikin dakin kaji kira cikin fushi. "Habu, Habu, Habu" da sauri wani dan mutumin dake cikin dakin kaji yana dubasu yajuyo jin ana kirashi ganin Abba yasa yafito da sauri yakaraso gaban Abba ya tsugunna cikeda girmamawa cikin hausan shi da bata fita da kyau tafi kaman da fulatanci yace "barka da zuwa Alhaji" cikin kunan rai Abba yace "Habu kataba bani labarin garinku dakace mini kauyen kayayau ne ko gwamnati batasan da itaba hakane?" gyadama Abba kai Habu yayi yace "kauyenmu asalin kauye ne aradu, ba wuta ba ruwa, ba waya, arafi muke wanka muyi wanki, adaji muke zuwa muyi bahaya, yawancin yan garinmu bama susan da akwai wani abu wai binni ba, wayanda kuma sukasan da binnin tsoron zuwa sukeyi wai cinye mutane kukeyi anan binni, konima wanan kaddaran nanne yafito dani daga garin dahar yau bansan akwai binni ba, sanan mutanen binnin nada kirki" ahankali Abba yace "gud, matarka nachan ko da yaranka guda tara daka fadamin?" da sauri ya gyadamai kai yace "I, duk suna chan taki yarda tadawo binni wai tanaso ku mutuwa ya kamata ta mutu a inda aka yanke mata cibiya, kudi albashina nakan raba biyu nakai mata rabi, tana saida su gyada dafaffiya, mascara, sanan baban d'ana jauro mun sayamai shanu ahirin da biyar yana kiwansu muna sayar da hura da nono a kauyen mu" gyadakai Abba yayi cikeda gamsuwa da bayanin shi yace "Habu kasan mesa nakemaka tambaya kan garinku yau?" da sauri Habu ya girgiza kai, Abba yace "kasan shaye shaye?" da sauri Habu ya gyadakai yace "nasani ba giya ba ahai ai tatil aita hauka ana layi akan hanya" gyadakai Abba yayi cikin wani irin bakin ciki yace "to Habu y'ata na shaye shaye, an kaita wurin magani tagudu, sonake kazo kashiga motar nan ka kaini garinku inaso nabama matarka rikon y'ata, inaso nakaita kauye, inda bazata tataba samun access to shaye shaye bane, bazata ga inda zata sayo abubuwan shaye shaye ba, danko namaidata Rehabilitation centre sake gudowa zatayi dan tariga tasan hanyan guduwa, kauyenku kauyen kayayau ne kuma irin wajen nake son mata harsai tayi wata ni shiddan nan tabar shaye shayen, tahakura dan kanta sanan zan koma na dauko ta, Rahima needs iron hand tana bukatan abu haka, by the time tai rayuwa irin wacce bata saba da itaba hankali zai shigeta dan kanta, zata gane gata ake mata a rehab datake samun gado ta kwana, tasamu shawa tai wanka, lokacin dataga batada wani option dayarage ta shiga rapi tai wanka, kokuma tasha ruwan rapi, kokuma ta kwanta tai bacci akan gadon kara ko kasa, tasha nono tai hamdala ta goge baki, tai kwadayin shaye shaye ta nemi inda zata samu tarasa, tai kewanmu takasa ganinmu wlh zata natsu, I believe tahakane kadai Rahima zata natsu tabar wanan mugun dabi'an na tir" da sauri Habu ya kalli Abba gabanshi nafaduwa dim dim yace "tooofah, saidai wani hanzari ba gudu ba garinmu akwai wani......." da sauri Abba yatare shi yace "zaka rikemin y'a ko ba zakayi ba na nemi wani wajen Habu?" Abba yay maganan cikin bacin rai, da sauri cikin kuma damuwa sosai Habu yace "zanyi wlh Alhaji, kaida kamin komi karufamini asiri, kabani ci, sha, tufafi da abin kwashewa na gagara maka wanan, wlh zanyi wlh" "gud rufo gidan mutafi banson jin wata magana" komawa yayi ciki da sauri yadauko key yafito yarufe gidan sanan yazo gaban mota Abba yabudemai ya shiga yarufo kofa Abba yakoma ya shiga motan yana kallon Rahima dake hauka sosai har lokacin tana wakoki, girgiza kai yayi hawaye yataru a idanunshi da sauri ya hadiye su yatada motan yaja, koshi kanshi Habu saida yaji tsoron irin gudun da Abba keyi, tun Rahima na haukanta hartai bacci.
Awa takwas yadauke su suka shigo garin Gombe, Habu nata nunamai hanyar kauyensu, suka dau wani hanya wacce itace hanyar kauyen, kauye da yadauke su kusan awa biyar sanan sukakai wani daji, ahankali Habu yace "dole zamu ajiye motan anan Alhaji mu karasa da kafa dan babu hanyar motar kuma, kauyen mu chan bayan dajin nanne saisa bama asan damu ba a Nigeria nan" saukowa Abba yayi batare daya damuba Habu ma yafito boot Abba yabude yaciro akwatinta yabama Habu yace "rike wanan" akai Habu yadaura sanan Abba yabude baya yajawo kafafun Rahima dake narka uban bacci, kuka tahauyi cikin Bacci tace "sakeni" kota kanta Abba baiyiba ya kulle motar yarike hannunta gam yahau janta bacci take dan taki bude ido bin Abba kawai take luuu kaman zata fadi tsabagen karfin mix din data sha tafiya kawai suke, har dare tamusu ahanyan nan amma ko darr Abba baiji aranshi ba, sunyi tafiya kusan na awa daya akafa sanan Abba yafara hango haske hasken fitilu Habu yace "mun iso, ga kararkaran mu chan" karasawa sukayi dudda darene amma all abubuwan da Abba ke gani shine bukkoki kusan hamsin ko dari azagaye, baiga ginin gini ba saidai ginin kara dasu bukkoki, sai gaishe gaishe Habu yake dayan kwararrun mutanen dake waje kafin yakarasa chan gaba wurin wasu bukka guda biyu da bishiya ke tsakanin su, sallama ya kwada. "Assalamu Alaykum mutan gidan nanan" daga ciki aka amsa. "muryan wa nikaji kaman mai gidana" dan dariya Habu yayi saiga wata mata tafito da daurin zanu a kugu babu riga ajikinta sai wani yaro agwai data rike akan cikinta yanshan dogon nonon ta dayakai cikin ta tsabagen tsawo dayan kuma yaron na wasadshi da hannu yana surutu irin na dadin nonon nan da yara keyi, bata da kiba sosai sai tsayi da gashin kanta data tufke kaman na yar bararoji, an kitse na gefe da gefen gaban kanta guda biyu jelar gashin har wajen kirjinta, saiga wata yarinya dazata fi Rahima tsayi itama rikeda fitila tana dagawa tana haska fuskokin su ganin Habu yasa matar da saka uban tsalle nonon na lilo da sauri dan karamin yaron ya saki nono ya juyo jin maman shi ta daka uban tsalle yana kalle kalle, matar tace "wayyo Allah na mai gida kadawo, Mairo kufito ga babban ku yadawo" wasu yarane suka dinga fitowa daga bukkan Abba ya saukar da kanshi kasa ganin babu riga a jikin matar, dudda baya ganin fuskokin su da kyau sabida darene bai hanashi ganin yaron dake shan mama ba, tsalle sukahau yi har wasu mutane suna fitowa daga bukkoki su suna lekowa, ganin haka Habu yace "bamu asabari muzauna magana zamuyi ba dawowa nayiba" da sauri ta kalli yarta tace "Mairo dauko as abari babbanku yazauna" da sauri yarinyar ta shiga ciki ba'a jimaba tafito da asabari ta shimfida Abba na kokarin zaunar da Rahima ta kwanta tana bude idanunta tana kallon kowa, zama matar tayi takalli yaran dasuke tsaitsaya suna kallon baban nasu duk maza gabaki daya kansu daya kaman yan shidda ta haifa, sai wani babba da yake sanye da kayan fulani da tsayinshi daya da Mairo wacce take itakadai ne mace ayaran, sai wanda ake bama nono shima namiji yakama yara Tara cib cib, yaran kaman bakwaini, anatse Habu yace "kinga wanan shine Alhajin danake fadamiki daya bani aiki a binni" da sauri takama baki tace "laaaaa shine baka gayamin ba ke Mairo kawoma Alhaji fura dan Allah yasha" da sauri Abba batare daya dago kai ya kalleta ba yace "a'a kibarshi nagode, magana nazo nayi dake dan yanzun nan zamu koma" da sauri ta gyara zama tace "to to ina jinka" Ahankali Abba yanuna Rahima dake kwance kusadashi databude idanu tarr tana kallon kowa awurin yace "nakawo miki y'ata ki rikemin ita na tsawo wata shida ne, kisamata tsaro bana wasaba, banda haka zan biya ki kinji, sanan zan aiko muku da kayan abinci gobe, dan Allah zaki rikemin ita?" da sauri tace "Alhaji harda su biya? Nawa zaka biyani to dan kaga yar bukkan mu tamana kadan nida yara Tara gakuma ta goma ta kawomana, dole sai....." da sauri Habu yace "Ladi" hannu Abba yadaga mai yace "barta, nawa ake Gina bukka anan?" ahankali tace "sun karamai kudi da muttala hudu ne yanzu muttala goma ne wlh wasuma har muttala shadaya suke karba" bandir din yan dubu guda biyu Abba yaciro yamika mata yace "ga dubu dari biyu agida bukkan na block amuku ginin sanan sauran kudin ki rike, ki kulamin da ita, gatanan gakuma kayanta intai ba daidai ba ki gyara mata, amana nabaki ita dan Allah kar wanda yanuna mata hanyar barin garin nan nasan ko zata shekara bazata taba ganewa ba" rudewa kam Ladi tarude karshen rudewa ma ganin uban kudaden da Abba yabata kaman a mafarki, dama sune yan gayun kauyen nan sabida Baban su Safara dake aiki a binni yanzu kuma ga wayan nan kudin ga yarinyar binni ai bakanta, da sauri tace "wlh, wlh, wlh na dauka zan kula da yarka na rantse da Allah, amana na dauka halak" ta kalli Habu tace "kagayamai komi kan kauyen ko?" kafin Habu yay magana Abba yace "ya sanar dani kuma dama irin kauyen nan nakeso ta zauna aciki, kome yataso ayi badamuwa wlh nan da wata shidda zanzo na dauketa" murmushi tayi tace "masha Allah, Allah yakusan bamu jika kenan" murmushi Abba yayi dan baigane hausan nata sosai ba yace "to mun tafi, Habu tashi mutai" wani irin zabura Rahima tayi ta tashi tsaye tana kallon Abban daya tsaya yana kallonta tace "Abba ina zaka ka barni anan? Su waye wayan nan?" ko kallonta Abba baiyiba dan baimaso yay magana da ita tsabagen haushin ta dayakeji yace "Ladi ariketa karta biyomu muntafi" mikama Safara yaron hannunta matan tayi takama Rahima gam tarike hakan yasa Rahima ta shiga kokawa da ita amma takasa koda fizge hannunta dan kashin Ladi yafi na rodi karfi, ganin takasa kwatan kanta yasa ta fashe da kuka tana kwalama Abba kira. "Abba meyakawo ni nan? Su waye wayan nan? Abba ina zaka ka barni eh? Ina mummy na Abba? Abba kaima ka tsaneni kaman mamana ko? Ka kaini chan wani wuri da bansan su ba yauma kasake kawoni wani wuri daban San kowa ba? Abba waime namuku da babu wanda kesona? Abba katafi ka barni kuma? " Abba yanajin duka kalamanta dudda sun mugun tabashi amma yadaure ko juyowa baiyiba har suka bace mata daga gani yanaji tana kuka tana kwalamai kira har suka shiga daji yadena jin kukan ta.
40.
Saida sukaga sun bace bat sanan Ladi tasaketa ta kama hannunta gudun karta gudu tace "kinga muje daki dare yayi kiyi bacci yarnan" fashewa da kuka Rahima tayi tace "dalla chan kisaken ni" janta Ladi tayi tai cikin yar bukkan da ita yaran suka biyosu duk suka shigo ciki, dakin babu komi sai kwanuka da aka jera irin kwanukan da dinan masu kama da langa tuwo da miya, sai asabari da aka shimfida akasa, sai buhun simenti da taga lodi lodin kaya aciki kaman kayan sawan sune, dakin zarnin fitsari, washe baki Ladi tayi ta zaunar da ita kan as abari mai kyau tace "sannu da zuwa yar binni" ta kalli Mairo data zauna kusada ita tana kallon Rahima kaman zata hadiyeta tace "kawo ma yar binni fura da nono tasha" make musu kafada Rahima tayi tace "baza'a sha kazamin fura da nonon ba" da sauri Mairo ta kalleta tace "kika karama Maman mu rashin kunya saina fasa miki baki aradu" babban namijin ne daya shigo da akwatin Rahima yana wasa da tayoyin kafan trolley yadago kai ya kalli Mairo yace "dalla to dake tayi ki wuce kakawo mata furan akace" kwafa Mairo tayi tai wajen randa shikuma saurayin yataho kusada mamansu ya zauna yana washe mata hakora yace "mama dan ban wani abu man cikin kudin" hararan shi maman tayi tace "to sannu tunda ina tsoron kane Maccido, kaga gobe da safiyan Allah Mairo zataje saro mini gyada da masara, su Tasallah zataga nariga nafita ne wlh, na kece raini, sari zanyi na kece raini na azo agani, saina siye amfanin gonan tass saidai suzo suna siya awurina" furan Mairo takawo ta ijiye mata a gabanta Rahima tasa kafa ta shure furan yazube da sauri Ladi tace "ke yar binni zanci miki kaniya fa, huran kika zubar, yasin zan batamiki raifa, Ke kauyen nan ba'a haka mai wulakanta abinci kyalli madam na zuwan mai da daddare wlh barina kiga yanzun nan zaki gansu sunzo, munada dodanni kala kala, akwai abubuwa agarin nan da inhar zaki kwantar da kanki muyi