Showing 123001 words to 126000 words out of 190952 words
Chapter 42 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
ganin Sameer tareda wata yar yarinya da kanta ke kasa yasa tadauke kai kaman bata gansu ba, tsayawa yayi chak yana kallonta ganin haka yasa Baffa yace "ku shigo mana Sameer kabar yarinya atsaye angayama kowa sojane irinka?" shigowa yayi ahankali Rahima biyeda shi yasami waje yazauna aksa Rahima ma haka a gefenshi, ahankali kanshi akasa yace "ina yini Baffa, Ummi ina yini, ina yini Mum" tsaki Ummi tayi ta mike tsaye tareda kallon Baffa tace "Baffan su bari nadan kwanta" , ya kalli Mummy su Yusra tace "bari nadan kwanta Maman Asiya" bata tsaya jiran amsan suba tawuce tafice abinta daga dakin Sameer yabita da kallo ranshi duk adagule saikuma ya saukar da kanshi kasa, jin shiru yasa cikin siriruwan muryanta dake dan rawa Rahima tace "ina yini Abba, ina yini Mummy" daga Baffa har Mummy murmushi sukayi kafinma Baffa yay magana Mummy tace "ahh lallai su Soja yanzu nagane abinda yasa kaki aure dawuri ashe jira kake ka dallo mana balarabiya haka, yarinya murya kaman an busa algaita, Masha Allah, Allah yay albarka sanan Allah yabada zaman lpy yakawo zuri'a dayyaba" ahankali Sameer yace "Ameen, mun gode Mummy" sanan Baffa yay gyaran murya amatsayin shi na babba nakuma mahaifin Sameer yashiga musu waazi yana tunatar dasu hakkokin aure da yanda ake rayuwan aure, waazin yadan dau lokaci sanan yamusu addu'a shima yace "tashi Sameer ka dauki matarka ka kaita har dakin mahaifiyar ka ta gaidata" gyadamai kai Sameer yayi yamike tsaye itama Rahima ta tashi ahankali kanta akasa yana gaba tana biyeda shi har falo babu kowa a falon sai Asiya dake kallon wani Indian series ta kwanta kan dogon kujera da alamu sauran kodai suna flat din Noor kona Muhammad dayan biyune danya tabbatar Ummi ce ta kadasu data sauko maybe sun cika falon da hayaniya, baice ma Asiya komiba yay dakin Ummi Rahima biyeda shi, ahankali yabude kofar dakin Ummi tareda yin sallama Ummi na zaune kan kujeran dakin rikeda littafin zikiri tana karantawa, ga akwatuna guda 24 jere atsaye a tsakar dakin hadaddun gaske jin sallama yasa ta dago kanta Sameer tagani da matarshi da kanta ke kasa, hannu ta nunamai babu alamun wasa kan fuskarta tace "karka yarda kabar yarinyar nan ta shigo dakina mena fadamaka? Nacemaka babu ruwana da auren ka babu abinda yashafeni daku to me kake neman chusamin ita, take her out of this room Sameer!" Ummi tafada tana dakamai mummunan tsawa, fashewa da kukan da tuntuni Rahima ke rikewa tayi Sameer yakama hannunta ahankali suka juya zasu fita cikin fushi Mummy tace "and kadawo ka kwashi tarkacen nan" tanuna mai akwatunan tace "darajan Baffan ka yasa nabari ma aka shigomin dasu daki but Allah yakawo ka yanzu kaje kadawo kafita dasu"
Da sauri Sameer yajuya yafita da Rahima yazauna da ita kan kujera murya chan kasa yace "stop crying am coming" tashi yayi yakoma cikin dakin yabar Rahima da Asiya datai kaman kallo takeyi afalon, wani irin murmushi Asiya tayi ta tashi zaune saikuma tamike tsaye tazo daidai gaban Rahima dake goge hawayen da takeyi da bayan hannu tace "this is what you get for marrying wanda baison ki, Allah kara kuma in sha Allah kwanannan Ummi zata sa yasake ki yakadaki gidan ubanki" wani mugun kallo Rahima tamata kawai tsoron Sameer yasa tai shiru dan nan gidansu ne amma dasaita nunama yarinyar nan ainda take ita bama ta iya komiba dan tafi uwatta iya rashin kunya, gwalo Asiya tamata tajuya tafita daga falon tai waje.
Sallama Sameer yayi ya shiga dakin yana kallon fuskan Ummi data amsashi da kyar, kaman zaiyi kuka haka yakeji, karasawa gabanta yayi ya tsugunna ahankali yakama hannunta ahankali yace "Ummi am sorry dan Allah kidena fushin nan dani konazami kwanciyan hankali please Ummi na, Ummi" yakira sunanta dawata raunanniyar murya ita kanta Ummi tasan tai kewan danta but Sameer go against maganan ta tanunamai batason yarinyar nan amma ya aureta saisa ta sallama shi haka akema yara marasa jin magana da taurin kai.
Ganin taki kulashi yasa yadaura kanshi saman hannunta yay shiru itama kasa korashi tayi duk sukai shiru, lumshe ido Ummi tayi kafin tabude su ahankali jin saukan hawaye kan hannunta, cikin wani yanayin bakin ciki tace "Sameer kanuna min niba komi bace, ban isa dakai ba, Baffan ma da matarshi basu nunamin komiba amma kowa na family nan yasan yanda Asiya ke sonka dudda kuwa bata fadiba, dataji batun aurenka bakaga rashin lafiyan datayi ba kaman zata mutu, yau dataji za'azo nanne ma tasami kuzari haka, har kunyan kallon iyayenta nake sabida abinda kayi ka gwammace ka auro yar shaye shaye daka auri kanwar ka da aka haifa agaban ka kasan kalan tabiyan ta , yarinya natsassa mai hankali" ayanda ta karashe maganan zakasan abin yamata ciwo sosai, ahankali Sameer yadago kanshi bayan yagoge hawayen dasuka zubomai kanshi akasa yace "Ummi kiyakuri kiyafemin, wlh bazan iya auren kanwata bane saisa" "ai naga wanan yayarka ce" girgiza matakai yayi yace "am sorry Ummi, kinji please nasan namiki laifi banmasan mezance ba, please kiyakuri Ummi, am dying inside kidena fushi dani kinji"._BIN ABINDA ZUCIYA KESO_
_How to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din BIN ABINDA ZUCIYA KESO, Marasa bank can also send MTN card 300_
72.
"p....ls Ummi.....na" yay maganan muryan shi na breaking sosai, sosai Ummi taji she can not longer go on with this fight, tai missing Sameer dinta bana wasaba sauran yaran basa wani kula da ita kaman yanda Sameer ko tarinta yaji sai yace me kikeso Ummi, Sameer always put her first, dagokai tayi ta kallai ahankali irin kallon nan nayaya zanyi dakai hakan yasa Sameer yakama hannunta yakai kan fuskarshi ya lumshe ido, sharrr wani hawayen yazubo daga idanunshi, wani irin jawoshi Ummi tayi tasashi ajikinta ta rungume tana kokarin hana kanta kukan datakeji tace "sabida kaga ina sonka ina dagama kafa Sameer saisa kakemin duk iskanci da kaga dama, kanamin kashi da fitsari akai, for 39yrs kaki yarda kai aure sabida yanda nake sonka nakasa maka dole dan banson kayi rayuwa da abinda bakaso saisa koda kanunamin bakason Asiya ban zafafa abinba dan nasan ba'ama namiji dole, ya auri macen dabayaso wahala zatayi, shine zakaje ka auromin yar shaye shaye listen I might, might forgive you but I will never accept yar shaye shaye as my daughter in law nagayamaka, and stop crying, you are my Soja crying is for the weak men and my boy is not weak right?" gyadamata kai yayi ahankali yana dago kanshi daga jikinta, hannunta tasaka ta sharemai fuskan tass tai murmushi ganin kaman bashiba tace "is alright nahakura amman as far as am concern baruwana da yar shaye shayen daka auro" hannun Ummi yakama ahankali yana kallon fuskanta he don't know why but anytime aka kira Rahima da yar shaye shaye he feels bad, zuciyar shi batamai dadi, ahankali yace "tadena Ummi, am changing her bazata karaba, ko damaba badan kanta tayiba...." tabe baki kawai Ummi tayi tadan tureshi alamun batason maganan batare data cemai komiba, kwantar da kanshi kan cinyarta yana sauke ajiyan zuciya sosai taji yabata tausayi ahankali ta shiga bashi head massage tana tunane tunane ahaka bacci yay awon gaba da shi awurin.
Nabila data shigo daukan ma princess apple daga fridge din Ummi ne taga Rahima ita kadai afalon tana share hawaye da bayan hannu tausayi tabata sosai, Apple din tadauko tadawo inda take tace "Amaryan mu tashi muje shashin mu duk muna chan" ta dauketa ta tafi da ita chan flat din Noor dasuke ciki da ita, su Noor ne a falo da Muhammad da Mu'az sai Asiya duk suna buga game da sabuwar ps6 din da Sameer yasaima Mu'az, suna ganin Rahima duk suka natsu wani natsu suna wani murmushi adole ga matar yayansu ta shigo,
Daki Nabila tai da Rahima inda Fadila ke tare da yaransu tana musu wasa, zama duk sukayi sukahau hirada ita suna janta da magana amma takasa amsasu sai kallon kyawawan yaransu take dudda yaran duk Black beauty ne dan iyayensu bakake ne amma sunada wani irin kyau da kiba da kana ganinsu sai sun baka sha'awa, har azahar daga bayama bacci ne ya kwasheta ganin tana gyangyadi yasa Fadila tace "ki kwanta mana Rahima kin zauna kinata gyangyadi" gayamata kai tayi tacire katon gyalen daya isheta taijiye a gefe ta kwanta ahankali tareda daura kanta afilo sai bacci, dauke kai Fadila tayi daga kallonta ta kalli Nabila dake rikeda Princess datai bacci tace "wlh ina bala'in sonta, ni yarinyar burgeni take gashi batada magana shiru shiru, I trust Ya Sameer nasan komi yazo karshe tunda dai ta shigo hannunshi" Nabila tace "hakane, ga kyau kaman ita tai kanta kinmasan menene Fadila, anytime inna kalleta sai naji tana tunamin da Ummi, sai inga kaman tana yanayi da Ummi intai wasu abun saikuma inga kaman idanuna ne kemin gizo hala sabida ina tausayinta ne" dan dariya Fadila tayi tace "nikuma kinga bangani ba, bari kiga naje wajen Baby tun dazu bansashi a ido ba" hararanta Nabila tayi tace "wato yanzu kinsaba babu zancen kuka da tsoro kuma ko" kyalkyacewa da dariya Fadila tayi tace "wuce nan, ai tunda na haifo Amra nasan kar harkan shi kanshi Baby yanzu mamaki yake wai ashe zan taba dena kuka" dariya Nabila tayi tace "adaiyi ahankali Amra is just 2month plus kafin kije kiyo mata kani ko kanwa jarabatu" dariya Fadila tayi tafice daga dakin falonsu tayi daidai dukansu ukun na shigowa dan masallaci sukaje wajen Muhammad tayi ta mikamai Amra tareda kama hannunshi tarike tana kallonshi, murguda baki Mu'az yayi yana kunkuni yace "akama anata lalatamu ana soyayya agaban yara" da sauri Muhammad yace "mekace?" washe baki yayi yace "ni ba dakai nakeba" murmushi kawai yayi ya kalli Fadila yace "muje flat dinmu I want to sleep" ficewa sukayi, Noor ya kalli Asiya dake kallo abinta yace "Asiya je ciki kicema Nabila ta samen in my bedroom" tashi tayi da sauri cikeda girmamawa tace "to Yaya" dakin tabude ta shiga kallo daya tama Rahima dake bacci tadauke kai ta kalli Nabila tace "Anty Ya Noor yace kisamai in his bedroom" murmushi kawai Nabila tayi tace "ganinan" tashi tayi ahankali gudun kar Princess ta tashi ta kwantar da yarinyar kusada Rahima sosai sai sukai kwanciya kaman uwa da y'a na bacci sanan tai murmushi tajuya tafita daga dakin tareda maido musu da kofa tarufe.
Wuraren la'asar Rahima ta farka daga bacci tana dan mika ganin yarinya a kusada ita tana bacci hankali kwance yasa tasaki murmushi tana kallon yarinyar kafin tamika hannu ta taba kuttubeben kumatun yarinyan tana dan murmushi sanan ta janye hannunta ta tashi ahankali tazauna, idanunta ne suka sauka kan wayan Nabila dake ijiye kan side drawer, wani irin faduwa gabanta tayi ahankali tace "Mummy na" waigawa tayi ta kalli kofar dakin ganin a kulle babu kowa yasa dasauri tasauka daga kan gadon, wayar tadauka tana kallon kofa saikuma tayi kofan data tabbatar cewa na bayi ne ta shiga, maida kofar tayi tarufe tasa sakata sanan tabude wayan tana addu'a Allah yasa ba password aiko taga babu, number Mummy ta shiga sakawa hannunta har rawa yake tai dialing number saidai harya gama ringing ba'a dagaba, sake dailing tayi akaro na biyu wayan na gabda tsinkewa aka daga kafin Mummy tai magana tace "Mummy nine Auta, call me please kar agane nakiraki in kudin wayan yakare" jin muryan Rahima yasa da sauri Mummy tace "to to" katse wayan tayi takirata back da sauri Rahima ta dauka muryanta narawa sosai tace "Mummy na ya jikin ki kinji sauki?" murmushi Mummy tayi tana shiga daki ta maida kofar ta tarufe harda saka key gudun karajita ta shiga bayi tace "awwwn don't worry about me naji sauki, I have to be strong 4 u Rahima na, ni kadai ce on your side in this whole planet I need to help you, ya kike" kasa amsawa Rahima tayi tafashe da kuka sosai tana tuna yanda jikin Mummy yayrudu rudu tace "Mummy na are you sure kinji sauki? Narasa yanda zanyi nakiraki banda waya I've been so worried bama na iya bacci da kyau, Mummy nagaji da komi ke kawai nakeso nagani, Mummy please help me wajenki nakeso nadawo am not happy at all Mummy, kaman ina cikin keji tareda aljani nakeji am so scared of him sabida karya zaneni, Mummy nima ranan saida yazaneni sosai sai jiya jikina yadena ciwo" tafashe da sabon kuka, cikeda damuwa Mummy tace "Rahima Rahima, Autana" ahankali Rahima tace "uhm" cikin kuka, cikin makirin voice dake kara dulmiyar da Rahima tace "listen to me Autana inhar ina rate aduniyar nan wlh babu wanda ya isa ya wahalar min dake, ba dukana ba ko kasheni Sameer zaiyi I must come and get you kuma gobe da shirina zanzo kema ki shirya kinji" da sauri Rahima tace "to Mummy" ahankali Mummy tace "anya kinsha abubuwan nan kuwa dan inda kinsha daban jiki da mugun sanyi hakaba, Auta na danasani dakeda tsiwa bata tsoron akwana balle tai yami, bakida energy, babu inspiration bakida vibe u sounds so dull, anya kinsha kuwa?" girgixa mata kai Rahima tayi tasa hannu ta goge hawayen daya zubomata ahankali tace "nakasa sha Mummy, inya kamani nasha zai iya kasheni wlh, Mummy mugune shi sosai gashi katoto, ko karkashin gadon banma kara lekawa ba tundaga ranan" sosai Mummy taji badadi ko kadan bataji dadin rashin shanta ba dan wanan mix din ko kaffara bazatayi ba in Rahima tasha sai kwakwalwanta yajuya irin mix dinan ne da yan shaye shaye nasha shikenan kuma saiya taba brain dinsu su haukace combination of crack ne da indian herm saikuma wasu kwayoyi da ake kira _Tsigai tayi yami amma sai bala'i aiki_ tun ranan data kawo take kasa kunne taji an kwantar da Rahima a hospital amma taji shiru rasa yanda zatai tai magana da itane yasa kawai tai shiru ta zubama sarautan Allah ido, danne zuciyarta tayi tace "yamiki wani abune ya sadu dake?" ahankali tace "a'a ni am on my period ma" wani irin murmushi Mummy tayi tace "to yaushe zaki gama?" cikin yar muryanta tace "gobe is the last day, the fourth day, jibi zanyi wanka" gyadamata kai Mummy tayi tace "shikenan dudda gobe zanzo dole nafada miki wanan maganan for security purpose, Rahima in mutumin nan yazo zai sadu dake ke sai inda karfinki ya kare, dambe zakiyi dashi kome kika samu ki buga mai, keko zai kasheki da kuka gwara ya kasheki din amma karki yarda ki yardan mishi yay amfani dake dan yanayi ya zubamiki kanjamau kenan S, HIV, HIV baida cure yana zuba miki mutuwarki yazo kenan gashi ke bakison mutuwa, koba wanan ba dama nariga na tsine miki albarka inhar kika yarda ya sadu dake, Rahima inhar zaki iya budema wanda yama mahaifiyar ki lilis gaba yaciki ai keba yar halas bane, sanan baki kishin mahaifiyar ki, Sameer makiyin kine, makiyanki nahar abada, ko hannun ki bai kamata kibari yarike ba Rahima, Rahima banson nafadi miki ne, kuma baniso nafadi ma Abban ki dan nasan nagayamai Sameer yamin dukan fitan hankali saiya kusa kasheshi zai iya samun heart attack Abban ku ya tsufa but Rahima naji jiki sosai a hannun Sameer....." tafashe da kuka sosai daya wani irin mugun taba zuciyan Rahima event din ranan yadawo mata sabo fil arai, hawaye ta share tace "kiyakuri Mummy kinji, wlh sainasan yanda nayi na ramamiki, mugu kawai azzalumi, Mummy kiyi shiru in kina kuka jinake kaman zan mutu kaman in kashe kaina, Mummy banso ana batamiki rai am sorry Mummy....n.....a" tai maganan muryanta na rawa zata sake fashewa da kuka, murmushi Mummy tayi ganin ta dana tarkon da kyau tana kara yabama kanta wato tagama da zuciyan Rahima ne tatas da babu wani matsiyaci aduniyan nan daya isa yace zai shigo yafadi nashi Rahima taji, ahankali Mummy tai magana cikin muryan ban tausayi ta yanda Rahima zata kara dilmiyawa tace "is okay, am fine, zanzo na daukeki gobe garinma zamu bari gabaki daya, nakaiki wani gari daban da babu wanda ya isa ya ganki, gobe kawai ki zauna da shiri sanan ki ijiye kunnenki akasa, take good care of yourself kinji, I love you so much Autana, kin tuna wakan danake miki?" gyadama Mummy kai tayi cikin wani irin kuka mara sauti gwanin ban tausayi tana mugun kewan Mummy tace "uh.....mm" jin muryanta yasa Mummy cikeda so tace "I said is okay kinji, don't cry your Mummy is coming tommorow, and trust me I am coming da shiri na babu abinda ya isa yamin so karkiji tsoron komi, stop crying wipe your precious tears, dakiyi kuka gwara kowa na duniyan nan yayi da Autana tayi, oya oya goge fuskar nan tass Mumy's heartbeat" da sauri Rahima ta goge hawayen tanajin kaman duk duniya batada kaman Mummy, Mummy tace "yauwaaa Auta na, My little little Rahima, my ballarina girl, bari namiki wakan kiji" _"Rahima Rahimomi, ta burka uban tumbudi, tadinga uban karni, yan-yan-yaaaaaaa"_ kyalkyacewa da dariya sosai Rahima tayi harta manta tana ma cikin bayine cikeda shagwaba ta turo baki tace "Mummy nifa bana tumbudi" da sauri Mummy tace "wai wai wai ai kece tumbudi factory Auta, kinsan nono baya kosanki anhada miki da madara aiko dan jijjiga kadan burrrrr kin burko tumvudi" dariya Rahima tadinga yi kaman ba itaba aranta tana cewa uwa dabance yaushe rabon datai dariya haka niko nace Rahima bakisan dawa kike tareba, Mummy ne ta dakatar da ita tahanyar cewa "okay okay dariyan ya isa haka, jeki ijiyema masu waya waya, wait, a inama kika sami waya dan wanan ba number Sameer bane" cikeda dariya kan fuskanta tace "gidansu mukazo, wayar matar kanin shi ne, Mummy kinga tsoho ne duk kannenshi sunyi aure" da sauri Mummy tace "bashine nake fadamiki ba, yaki auruwa ne, wace jakace zata yarda ta auri mai kanjamau shima babanki baya bincike ne saisa nakeso nazo na daukeki mu gudu na kaiki chan wani gari" aranta tace "straight to gidan karuwanci" sanan tace "just stay put koki ganni da wuri ko akasin hakan, karki fadama kowa da zuwana, oya bye" murmushi tayi